Showing 27001 words to 30000 words out of 117786 words

Chapter 10 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

454

har da masu birgima a ‘kasa. Ammar ne yace “Dahda anya ba aljannnun gidan nan bane suma suka shafesu kmar yarda suka yiwa hajja” dahda ya girgiza kai ba mamaki ammar yanzu dai kira doctornmu ya dubasu” shi dai Imran yana daga gefe sai murmushi yake yana hango kuma shatu data la’be bayan ‘kofa tana zabga dariya kamar yace ga babbar aljannahr can sai dai yaja bakinsa yayi shiru kada ya jawowa kansa daga ruwan hammata ta bashi ruwan tsarki.

Kafin doctor yazo haukane kawai ba suyi ba sai da Ammar ya shigo ya sanar dasu shigowar doctor sannan Imran ya kalli shaheeda ransa a ‘bace yace “Go and cover your body ko kunya baki ji” wani kallo ta watsa masa kafin tayi magana doctor ya shigo da sauri Imran ya dafa kansa ya jata ya turata d’aki yana tsaki. Ko da ta shiga d’aki hijab kawai ta zira ta sake fitowa a guje. Doctor ya gama dubasu sannan ya fito da allura ya fara yi musu don dama dahda yayi masa bayanin ciwon. Sai kusan ‘karfe 4:00 na dare sannan abin ya lafa musu amma fa sunji jiki duk jiknnan yayi luhu-luhu balle idonsu.basu koma d’akunansu ba don suna tunanin tabbas aljannun ne tun da a d’akin da hajja take sauka suka sauka yau kam sun gasgata zancen hajja. Jin shigowar su mommah yasa shatu shiga d’aki da sauri tana tuntsira dariya. Amma mamakinta d’aya me yasa Imran bai tona mata asiri ba karo na biyu kenan yana kamata da irin wannan.shi kansa Imran tunda ya shiga d’aki yake smilling shi kad’ai ya lura yarinyar nan comedian ce ta bugawa a news.

Da safe ma basu koma d’akin ba a sashen amarya suka koma zama suna sake la’antar mommah don a cewarsu aljannu take turo musu ai kuwa indai sune su zuba su da ita gida dai baza su barshi ba sai sun kai kwanakin da suka ‘kayyadewa kansu tunda a goben zasu tafi abuja kai lefe. Hameedah tana sake girgiza ‘kafa ranta a matu’kar ‘bace tace “wallahi wannan matar muka ‘kyaleta nan gaba raba mu za tayi da yaya manga gaba d’aya dole mu tashi tsaye a kanta mu har a gaya mana malamai mu da
Muku jinin barebari.” Falmata ma cewa tayi”wallahi kuwa naga alama kuma lefe tayiwa kanta tunda hajja tace mu kai kada ma mu nemi danginta wallahi kaiwa zamuyi ke kuma shaheedah sai kin dage sosai duk abinda muka kawo miki kada kiyi wasa dashi munyi al’kawarin sai mun dasa mata ninkin ‘bacin ran da ta sakawa manga sai mu zuba mu gani tana ji tana gani Imran sai dai ta hange shi daga ness” gaba d’aya suka saka shewa har da amarya zainab. Fanna na gyara zama tace mai yafi wannan takaici ace d’anka yana auren ‘yar kishiyarka kuma zainab ke kin samu d’a daga sama kamar yarda uwarta ta samu manga daga sama suke juya mana shi son ransu.” Dariya suka ‘kara yi.


Ko da ta gama shirin school tana fitowa general parlour ta gansu murmushi ta saki ta fara wa’kar ado gwanja ta casss. A harzu’ke suke kallonta,Hameedah ta mi’ke da sauri tana jifanta da wani irin kallo “ke don uwraki da wa kike?” Shatu rausayar da kai tayi gefe kafin tace “kawai don ina wa’kata sai ki zageni” fitowar Imran da Ammar kenan sunyi shirin fita su ka ji hameedah tana wallahi sai na sake jibgarki kamar yarda nayi miki jiya shegiya mai idon aljannu.” Imran waro ido yayi yana kallon hameedah mamaki fal ransa lalle bata san sharrin yarinyar nan ba bata san itace gayyar aljannun da suke wajigasu ba, har shatu ta karkace zata yi rashin kunya Ammar ransa a ‘bace ya jata “wuce ki tafi school tun d’azu driver na jiranki kin tsaya jan magana.” Baki ta zun’buro irin na shagwa’ba “Yaya Ammar uwata fa ta zaga.” Harara ya zuba mata “kin wuce ko sai na mangareki tayi ta zaginki ma yana tsiro ne? Oya maza-maza wuce school kafin na sameki a wajen” sum sum ta wuce har taje ‘kofa ta juyo da ‘karfi tace “an fad’a d’in a sosa cass a sosa iya da razor.” Imran bai san sanda murmushi ya ku’buce masa Ammar kuwa darawa yayi sosai yace “kai shatu danger” hameedah kuwa ‘kwafa tayi tana zabgawa Ammar harara.


Kashegari kuwa suka isa abuja dangin baban shaheeda suka kai lefe ba tare da dangin mommah ko d’aya ba duk da kuwa suna cikin abujar. Haka suka dawo da sha tara ta arziki duk da suma ba lefen wasa suka kai ba lefene na gaske na gani a fad’a na kuma d’orawa a instagram,a yayata a duniya. Biki kuwa aka saka shi sati uku cif don suma dangin uban shaheedahn a shirye suke tsaf kuma masu farcen susa ne tabbas kuwa za’ayi biki na kece raini. Bayan sun dawo kano da kwana d’aya suka wuce maiduguri hannayensa dam’ke da sha tara ta arziki. Mommah ba tace musu Komai ba duk da ta tambayi Hajiya mama kuma ta tabbatar mata ba a gaya musu kai lefen ta basu ha’kuri. Hajiya mama ta girgiza kai a cikin wayar tace”Lala lala dijah ke zan bawa ha’kuri kiyi ha’kuri da jarrabawar da Allah yayi miki ta fitinannun dangi miji kina zaune ubangiji zaiyi miki sakayya suma fa mata ne kuma sun haifi mata ki zuba musu ido yanzu ubangiji ai tun a duniya yake sakayya ba kayi ba ma anyi maka ina ga kayi kiyi ha’kuri kullum shine abinda zan iya ce miki.” Hawaye ya zubowa mommah sai dai ba ta nunawa hajiya mama kuka take ba tayi godiya ta kashe wayar a zuciyarta tace “akwai ranar ‘kin dillaci ranar da zata cusa musu nasu ‘bacin ran dole ne su girbi abinda suka shuka d’a dai nata ne kuma ba zata bari su juya shi kamar yarda suke muradi ba.



*****************
A hankali awanni suka yi ta shigewa suna zama kwanaki daga kwanaki kuwa,har satittikan biki suka zo gidan a hargitse yake kowa sai shiri yake ana ji da lamarin bikin to ba dole ba ta kowane side jikan farko kuma d’an gaban goshi ake yiwa Aure,tun ana saura sati biki dahda yasa shaheedah dole ta koma gidan babanta duk da ba haka suka so ba uwarta taso ta tsaya ta cigaba da banka mata mallakin mallaka sai dai dole ta tafi. Hajja ma ana saura satin tazo ta tare a part d’in dahda daga gefe a babban parlournsa akwai wani bedroom and toilet anan ta baje danginta kuma suna d’aki mai Aljannu.

Mutanen katagum ma sun hallara ciki kuwa har da Dada tsohuwa mai ran ‘karfe. Tuni mommah ta fara gyara d’iyarta tsaf fatarta ta goge a spa haka nan an yi mata saloon gashin nnan an jawo shi tsahonsa har da na Mamaki.

Suna dawowa daga spa a gajiye suka tarar Hajiya mama tazo ita ma da ‘yan uwanta na yola ga Hafsa da Nahna da sauri shatu ta rungume uncle Hisham shi kuwa duk da nauyin da tayi masa haka ya shiga wulwulata yana fad’in a cafe a cafe ‘yar gidan mommah mai mommah ke baki ne kika yi wani fresh har glowing kike?” Kayan dad’i” ta furta tana murmushi har hushiryarta ta fito. Still Ammar yayi yana kallonta har bakinsa ya gaza shiru yace “mommah ‘karin gashi kika kaita aka yi mata da wankin fata?” Gaba d’aya gurin ba wanda baiyi dariya ba Hafsa tace “Ammar ko dai kana ciki ne a d’aura gobe da kai kawai.” Girgiza kai yayi “Ina ni ina rigimar shatu ni ‘kabilar ibira ma zan aura sun fi iya kula da miji” shatu ma harara ta zabga masa Allah ya kiyaye ma in aureka kayi fari da yawa ni nafi son irin Yaya Imran wanda baya magana sosai kai kuwa surutu kamar parrot.” Dariya sosai parlorn duka suka ganin Imran yana tahowa yana ware ido alamar yaji zancenta sarai. Tamke fuskarsa yayi ya zuba kallonsa akan shatu da tayi saurin jan gyale ta rufe fuskarta alamar kunya tsaki “kada ma ki saka rai da samun irina ke ai irinki Ammar d’in ne ya dace dake sai kuje ku haifi parrots d’in”Dada tsohuwa ta ta’be baki “Yo Allah na tuba kada dai inga mutum yazo yana ‘yar murya kana ganin yarinya zankad’aziyya wanke hannu ka ta’ba da mai matarka ta ka tafi ta to ku ku zama shaida ko nan gaba kada Imran yazo yace a bashi balarabiyar nan.” Tsaki yaja yana mi’kewa “MAI ZAN YI DA ITA? Ni kuwa God forbid gayyar ‘kazanta da surutun tsiya Ina da mata ta ‘yar gayu ta bugawa a jarida.” Ran shatu ne ya ‘baci tun da take bata ta’ba jin haushin kalamansa ba sai yau hawaye ya fara bin fuskarta.

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-18


ELEGANT ONLINE WRITERS


Sosai take hawayen saboda kalaman Imran sun ‘bata mata rai. Momma ta jata jikinta da sauri tana jifan Imran d’in da harara “fice min daga nan tunda burinka ya cika ka saka shatu kuka yo itama su’butar baki Tayi idan banda haka mai za tayi da kai a haife ka haifeta tunda ka ninka shekarunta.” Ficewa yayi ba tare da yace komai ba Allah ya tsari gatari da saran shuka” ya raya a zuciyarsa.

Ana gobe kamu masu tafiya abuja suka dinga dandazon tafiya dangin mommah dai ba suje ba a cewarsu bikin namiji suke zo ba ruwansu da dangin mace sun san ma kun sunje wula’kanci zasu sha,gida ya d’ad’e ba kowa daga mommah sai danginta suke Ta tsara yarda bikinsu zai kasance.Juma’a ne d’aurin aure don haka ranar asabar za suyi dinner lahadi suyi bud’ar kai ango ma alhamis d’in zasu wuce da abokansa da suka zo daga wurare da dama wasu ma ba ‘yan ‘kasar nan bane.


Don haka yau part d’insu na samarin gidan a cike yake sosai don ma babban parlour ne sai bedrooms guda hud’u a ciki don gidan dahda ba dai girma ba gari guda ne. Tana zaune a gefen dada tsohuwa tana shan dariyar labarin da dadan take bata na Imran da yake yaro yana tsoron saniya ita kuwa sai dariya take su antynta nahna suna zaune suna cire mata jan lallen da akayi mata na salatip ba ‘karamin kyau yayi ba ya haskaka kyakykyawar ‘kafarta ta.tana mi’kewa mommah Ta shigo parlourn tana dubanta daga ita sai wata riga da tsayinta yaje mata gwiwa sai skinny black pant ajikinta gashinta kuwa an tufke mata shi guda biyu ya sauka har fin gefen Kafad’unta duk da ba kwalliya tayi ba tayi kyau sosai kamar ka saceta ka gudu”maza jeki ki kira wo min yayanku Imran” mommah tace tana zama a kujera had’e da ri’ke kai alamar a gajiye take sosai. Ba tare da jin komai ba shatu ta fice tana jin dada na ‘kwala mata kira amma tayi shiru dada tayi tsaki “kaji y’ar banzan yarinya a haka zata fita kai ba kallabi ke kuma dijah kina kallonta ta fara fa ‘kirgar dangi ita ko ta ido bata dashi ne? ‘yar nan” mommah murmushi kawai tayi “To dada nawa shatun take?” Dada ta girgiza kai “nawa take? Wannan d’irkekiyar budurwar ake kira nawa take yarinya ta fara ‘kirgamu yanzu haka ma ta fara al’ada” mommah ta girgiza kai “Bata fara ba wallahi dada ai da ta fara nima ba zan bari ta dinga zama haka ba na san shari’a ta hau kanta” “zancen banza shari’a kuma ta yaushe tunda ga abubuwa nan sun fara bayyana” ita dai mommah shiru tayi tana jin dada na ta masifa.

Ta dad’e tsaye tana knocking a ‘kofar ba a bud’e ba
ga hayaniya ta cika gurin,ba tare da tunanin komai ba ta tura ‘kofar ta shiga. Sai kuma sannan tayi turus ganin maza duk kunya ta lullu’beta gashi duk sun zuba mata ido gaba d’aya ta diririce,idonta akan Imran da yake zabga mata harara cikin ‘bacin rai yace “fice daga nan kafin inzo nan shashasha kawai ko kunya ba kya ji wai ma mai kika zo yi?” Idonta ya kawo raurau za tayi kuka haka kawai taji tana son yin kuka ganin kallon da suke binta dashi tana ji masu fad’ar masha Allah na fad’a masu cewa wow na fad’a. Da sauri ta fara wasa da hannunta kafin tace”mommah ce ke kiranka” tana fad’a ta fita a guje ashe shatu an fara girma ana tsoron maza tana ji suka tuntsire da dariya d’aya daga abokansa yace “Imran manga wannan wacece?” Kallo d’aya yayi masa yace “Sister”duk ido suka zuba masa abdul yace “Na zata baku da sister mace koma dai menene gaskiya babyn ta had’u ina ciki.” Sai aka d’au hayaniya guri kowa yana fadin bai isaba suma suna so Aliyu da yafi kowa serious ya dafa shi “Don Allah Imran ya kuke da yarinyar nan ni dai na san ku biyu ne kacal a gidannan” mi’kewa yayi yana gyara wristwatch d’insa fuska a d’aure yace”cousin” daga haka ya fice amsa kiran mommah a zuciyarsa ya furta “mayun mata abin nasu kuma har da ‘kwailaye”yana jin su suna sake yaba surarta Ali yana cewa yarinyarnan idan ta girma wallahi za’a ja kaya musamman idan ta samu kula ni wallahi ya dawo ko yanzu ya raka ni wajen mommah na nemi aurenta. Imran murmushi kawai yake yana tafiya don ya san basu san wacece shatu ba.
Tana jikin mommah a kanainaye kamar ta shige ciki ya lura tana da son jiki kamr mage.mommah na ganinsa tace “Yauwa Imran abincinku nace ya za’a yi dashi?” “Momma wannan yarinyar me yasa take fita haka kai ba tie” mommah harara ta watsa masa “Ga maganar da nake maka kana min wata banzar magana” dada Ta gyara zama “a to kai ma dai ka fad’a kai da yake kafi uwar taka hankali nayi magana ance yarinya ce wai wannan baligar ce yarinya?shiga sai kace a garin ‘kedarai to ni da ban isa ba ance yarinyace ai ‘kafata ‘kafar yarinyar nan don na lura uwarka lalata ta za tayi ta sangarta ‘ya kullum tana cinya kamar mai shan mama to ba dani ba.” Hajiya mama dai sai murmushi take.Imran ya shige kitchen yana cewa “ki rabu dasu dada gashi nan ai samari sun fara kawo mata farmaki ba sun ganta da shigar banza ba.”Dada ta zabga salati “kai Imrana ka rantse da Allah mhmnn to dai wallahi Allah ya kyauta lamarin uwarka ni kuwa ‘kafata ‘kafar bararo wallahi”dariya yayi yana shigewa kitchen a zuciyarsa yace Ai gwara ki d’auketa wallahi dada.


Ko da ya koma zancen dai Ali ya ya tayar masa tsaki yayi “ku dai Allah ya shiryeku duk ‘yan matan garinnan ku rasa ta kulawa sai wannan ‘kwailar” Abdul tsaki yayi “Ai wallahi Imran kayi ba’kar dabara ya za’a yi da wannan a gidanmu inje neman auran wata ba zaka zauna ka jira wannan d’in ka kiwatata kaje kana auren wata ‘kemasashshiya zubin turawa ga zubin larabawa haba Alhaji wallahi ka cuci kanka.” Imran ya masa wani duban banza”God forbid Allah ya kiyaye kai ka sanni ka san waye ni kuma ka san burina na auren matured wacce ta san ciwon kanta kuma mace mai tsafta ba kuma na san mace mai tsananin kyau saboda bana son ko wani rubbish ya dinga kai idonsa kan matata so wannan bata cikin layin matan da nake so mace mai kyau ai hatsarice.” Gaba d’aya ta’be baki suka yi suna kallonsa su basu ta’ba jin mutum ma mai irin ra’ayinsa ba.Ali yace “Allah ya raba mu da auren mummuna mun fi son kyakykyawa ta shiga taro.”Imran tsaki yayi “Allah ya kyauta sai ku shirya kar’bar ciwon hawan jini don ba abinda ‘kananan yara zasu saka muku idan ba su saka muku hawan jini ba.”




Ranar Alhamis da daddare su hajja suka dawo saboda ranar juma’a ne d’aurin aure kuma sun fi son su kar’bi amarya da kansu. Ko kallon arziki ba wanda yayiwa su mommah da suke zaune a general parlour suna tayi musu sannu da zuwa, a ciki suke amsawa Hajja zube a parlour ana Ta d’aga kai ‘kafa d’aya kan d’aya tana ‘karewa Hajiya mama kallon banza ita dole sai dai Ta nuna gidan d’anta ne. Hajiya mama da yake bata iya fad’a ba ta mi’ke tana kallon mommah da dada tace “Dada muje daga ciki ku barsu su huta.”Dada ta girgiza kai “oh oh babu inda zani anan zan zauna ina kallon mai shige da fice to ina dalili zaki turani can ciki ban san mai duniya take ciki ba wanda yaga ba zai iya zama ba shi dai ya tafi amma dada kam zama daram”Hajiya mama ba tayi magana ba tayi shigewarta d’aki.dama su nahna basa nan sun tafi kar’bar d’inki tana ji hameedah na shewa tana cewa “Oh Hajja aure dai ya d’auru Allah yaso ba’a ruguza shi da surkullen fulani ba” Hajja ta masa “Da wallahi kuwa” Mommah tana jinsu ta shige kitchen ranta a ‘bace tasa masu aiki suka kai musu abinci daga haka Ta shige part d’inta wajen Hajiya mama tana dialling call d’in dahda.


Da daddare kuwa ta sake jaddadawa dahda burinta Na son d’aura auren gaba d’aya a gobe “ka d’aura a can abujan kawai dangin Ubanta ba matsala bane daga baya ta kaini har garin nayi musu bayani duk da dai basu damu da ita ba da sun damu da ita ai da sun biyo sahu.”Dahda yayi murmushi yana jan hannunta “Your wish is my command Dija na I do as you said.” Murmushi tayi tana had’a goshinsu waje d’aya.



********RANA BATA ‘KARYA******


Dandazon mutanene suka halarci d’aurin auren a babban masallacin Na garin Abuja, duk inda ka juya jama’a ce Imran fuskarsa d’auke da fara’a at last dai zai mallaki burin ransa shaheedah da ya dad’e yana mafarki a matsayin matarsa matured mai tsafta kuma ‘yar gayu kuma ‘yar ‘kwalisa kamar yarda yake son matarsa ta kasance. Suna zaune shida abokansa suka ji an fara shelar za’a d’aura auren ayi shiri jama’a. Ai kuwa cikin yardar Allah aka samu ba’kuncin shiru mai shela bayan mintuna kad’an ya shela cewar an d’aura auren Imran da Haleemah shaheeda akan kud’in miliyan d’aya lakadan ba ajalan ba Alhamdulillah Imran ya fad’a a zuciyarsa Finally angon shaheedah inji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login