Showing 1 words to 3000 words out of 91651 words

Chapter 1 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

604


*AZAAD JUNAID*

The young Billionaire
Na
Jeeddah Aliyu

*Haske Writers Association*

*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare duk wnd yy using set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali😘just start placing ur orders dearies DNT be left behind
Available product👇
Herbal whitening black soap:3k
Beauty kit:11k
Blacksoap/molato whitening soap: 3500
Bridal kit:20k
Muna maraba da masu siyan daya ko sari
Chat
08062991549
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀�?

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee

Sannan munada frames masu kyau shima siyan daya ko sari 07046881166
08062991549

Sannan gamai bukatan abinci, cakes,meatpie,samosa nd spring rolls, traditional juices nabiki shima yy hanzari yy mgn 08062991549
Mungode🤝



Free Page
1....

"Wai ke Salima wacce irin mace ce sau nawa zan faɗa miki ban amince da wannan tafiyar taki ba?"

Ta cikin mirror da take zaune a gabanshi tana gyara daurin d'an kwalin dank'areren lace da ke jikinta ta aika mishi Kallon uku saura kwa6o tare da ta6e bakinta. Kana ta mik'e ta nufi wata k'atuwar show glass mai d'auke da tarin designers shoes & handbags tsaye tai ta k'urawa show glass ɗin idanu tana nazari wanda ya dace tasa
Ta d'auki half cover golden in colour na company lamis elwan tare da handbag ɗinsu. Ta ra6a gefenshi ta wuce abinta sosai hakan ya k'ara linka masa 6acin rai da yake ciki, ya dunkule hannunshi na dama ya nushi bango d'akin ba tun yau ba yake nukurkusa bakin cikin matarshi Salima wacce shi kanshi a yanzu ya fara yarda da tafi k'arfin shi. Bai isa ya faɗa ta ji ba tabbas a wannan karon zai tabbatar mata da shi ke iko da ita ba ita ke iko dashi ba.
Cikin zafin nama ya bi bayanta da k'arfi yake taka steps hakan ne yasa yai nasarar cin mata a downstairs parlor.

"Salima!

Yadda ya kira sunanta da k'arfi yasa housemaid ɗin da ke cikin parlor suka fice da sauri ba tare da sun bari ya had'a idanu dasu ba. Nanny Lacey da ke zaune a dinning room tana ba wa k'aramar 'yar su Ahlam abinci tai sauri daukarta ta nufi d'akin yara da ita.

"Wannan wane irin wulak'anci ne ina magana za ki fita ki bar ni wato ga mahaukaci ko?"

Ya k'arasa magana yana huci.

"Look Azaad Kar ka nemi tashin hankali dani domin karshenta za ka dawo kana regretting.

Ta faɗa ba tare da ta juyo ta dube shi ba ta ci gaba da tafiya.

"Da gaske nake yi ban amince ba asalima inaso ki rubuta resigning letter, lokaci ya yi da za ki zama full housewife ki kula da tarbiyyar 'ya'yanki domin gaba d'aya tarbiyyar su a gur6ace take. Kina kallon abin da ya faru yau a school ɗinsu yaushe aka haifi Anisa da har za tai dambe da schoolteacher ɗinsu.....

"Enough is enough Azaad!

Ta katse shi cikin tsawa da tada murya tuni sautin muryar ta ya kere nashi kana ta ci gaba da faɗin

"Na fahimce dukan da aka yiwa Anisa kai ko a jikinka asalima so kake yi ka d'auki laifi kachokan! Ka dora min. Idan har kana jin ba za ka iya sauya mata school ba, to ni zan iya domin sani kanka ne ban dogara da abin hannunka ba....

"Ya ishe ki Salima! Nace ya isa! Har sau nawa kike so a sauyawa Anisa makaranta sa'o'inta suna aji huɗu a secondary amma ita tana jss three shin hakan Kaɗai bai isa ya haska miki lalaci 'yar ki ya yi yawa ba?"

"Yar ta Azaad kace 'yar ta wato ni Kaɗai Allah ya ɗorawa tarbiyya yara kai ubansu ba da kai ba ko?"

"Kwarai kuwa domin kece uwa ke ya dace ki zauna gida cikin 'ya'yanki ki kula dasu ba ni ba. Abin da ya rataya akaina shine hakkin ci da sha kuma dai-dai gwargwado na tsare muku su. sannan ki tuna ina da hakki akanki sai mu share watani uku Salima ban had'a shinfid'a dake ba. Angaya miki ni dutse ne ko waliyi da bana buk'atar mace?"

"Yanzu kan na fahimce inda ka dosa Azaad kawai ka fito fili ka faɗa min ba ka so ci gabana. Allah ya rufa min asiri na dogara da kaina bana tsayawa jiran sai kayi min, shine kake so ka tauye ni to bari ka ji inaso aikina domin bana ko tantama da banida kud'i ko na fito gidan babu da ba yadda za a yi kai ɗin ka aure ni.

Cike da takaici yake K'are mata kallo ko wane furunci dake fitowa daga bakinta k'ara mishi 6acin rai yake yi, shi mutum ne da bayaso hayaniya yana da matuk'ar sanyi hali shiyasa a koda yaushe Salima take zantar da hukunci kuma dole ya bi koda hakan bai masa dad'i ba. Amma tsabar sanyi halinsa ba zai ta6a bari ta fahimci hakan ba, ita kuma anata 6acewar basira take gani kamar tsoronta yake yi.

"Ki sani Salima furuncin nan kin sha faɗa min shi ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Kin faɗa min shi bila'adadin, kuma yana cikin kalamin ki da ke matuk'ar sosan rai

"ka ga Azaad ka bar ni haka nagaji da saurare tsofaffin maganganun ka, domin duk ciki abin da ka faɗa babu sabon abu a wurina kana bata lokaci ne kawai.

Ta gyara mayafin jikinta wanda shi babu duk d'aya ta buɗe k'ofa ta fice abinta, ya bi k'ofar da ta fita da kallo zuciyarsa tamkar za ta fasa k'irjinshi ta fito ya d'auki dogon lokaci tsaya a falon kafin sake haura upstairs saidai a wannan karo tangamemen bangare shi ya nufa katon parlor na farko ya fara wucewa kafin ya iso na biyu wanda yafi na farko tsaruwa saidai na farkon yafi girma, ya buɗe k'ofar gilashi wacce za ta sada shi da Master bedroom ɗinshi, kaitsaye resting chair ya nufa ya zauna, ya shiga shafar kwantattace saje shi da hannunshi na dama. Ya rasa a duniya me Salima take nema ne duk wani jin dad'i duniya Allah ya bashi ya tara dukiyar da har jikokin 'ya'yanta za su mora to me ya rage da za ta nema face lahirarta. Kuma gaba d'aya a tsarinta babu lahira a ciki a shekaru 16 da aure har kawo yau ɗinan ba wani abu da zai bugi k'irji yace ya samu na farin ciki, kullum rayuwarshi a k'unci take gashi Allah ya bashi duniya amma ya ga-gara samun farin ciki ya tashi maraya ba uwa ba uba a wurin haihuwar shi mahaifiyarshi Hindu ta rasu, a hannun kakar shi Jadda ya taso wacce ta haifi mahaifiyarshi yana degree shi na farko ya rasa mahaifin shi wanda ya rasu yabar tarin dukiya ta fitar hankali, da kuma tarin 'ya'ya domin yabar matan aure uku mahaifiyar Azaad ce ta uku bayan rasuwar ta ne ya sake wani aure, Kuma duk a cikinsu ita ce mai d'a d'aya Azaad.
Azaad Junaid matashi ne ne d'an shekara 47 cikakke business tycoon ne wanda tauraronsa ke haskawa a faɗin duniya.
Ya mallaki dukiya wacce shi kanshi a yanzu bai san adadinta ba. Azaad Junaid mutum ne mai matuk'ar sauk'in kai ba za ka fahimci hakan ba har sai ka zauna dashi. Azaad yana da matuk'ar kyauta da alkhairi ga tallakawa yana kyautatawa na k'asa dashi yana da gaskiya da rik'on amana, mutum ne mai rik'o da addini sai dai san baya daukar reni yana son a girmama shi matuk'a.
Babbar matsala shi a duniya ita ce matarshi Salima sun yi aure a bisa so da k'auna, Salima mace mai zurfin ilmin boko na addini ne ya yi k'aranci a gareta, ba yadda ban yi ba akan ta zurfafa ilmin nata na addini amma abin yaci turo dole yana ji yana gani ya zuba mata idanu. Ga wasu Dabi'u da halayenta da take dasu, sun sha ban-ban da na matan hausa/fulani mace ce mai bala'in girman kai da dogon buri babban burinta sunanta ya zagaya duniya, tayi fice fiyye da mijinta. Mahaifinta mai kud'in gaske ne kuma ita ce babban 'yar shi sai k'anneta maza uku sai Wanda suke 'yan uba su biyar maza biyu mata uku.
Salima tayi karatu mai zurfi akan kasuwanci saboda kwarewar da iya kasuwanci yasa mahaifinta Alhaji Kabir Dala tun kafin ya rasu ya mik'a mata ragamar kula da babban kamfaninsa na building and contracting company wanda a halin yanzu ita ce mafi rinjayi hannu jari a company.
Burinta ta mallake company ita Kaɗai, sai da 'yan uwanta sun amincewa su sayar mata da hannun jarinsu tasha alwashi sai ta mallaki company kamar yadda ta mallaki wasu k'anana companies ɗin nasu.
Azaad Junaid ya haɗu da Salima ne a wani meeting a birnin tarayya Abuja, dukansu su na neman contract d'aya na gina wasu gidaje a nan birnin tarayya Abuja tun kafin su fara gabatar da meeting ɗin ya ji firar da Salima take yi da wata colleague ɗinta yadda samun contract ɗin yake da matuk'ar muhimmanci a gareta da irin hasara da za ta tanka idan ta rasa shi, saboda har makudan kud'ad'e ta yi bribery ɗin wasu daga mukarabai gwanati. Duk abin da take faɗa batasan cewa akan kunne Azaad Junaid sai kawai ya yi sanyyaye murmushi domin yasan muddin ya ri gata gabatar da presentation shine zai sami contract ɗin, tausayi ta bashi matuk'a ba tare da sanin ta ba yasa aka bata contract ɗin duk da akwai 'yan kwangila da suka fi ta amma kasancewar the young Billionaire ne ya yi magana sai aka bata, a lokaci ba k'aramin dad'i da farin ciki ta ji ba. Suna fitowa daga conference room ta mik'a mishi tattasan hannunta da nufi su yi shaking hands sai ya ɗaga mata yatsun shi biyu, ya wuce wurin motar shi tun daga lokaci ta dinga bibbiyar shi har ta sami nasarar suka k'ula alak'a ta friendship daga bisani abuta ta rikide ta koma soyayya. Azaad Junaid yana matuk'ar son Salima ita ma haka abin yake a wurinta, ko wane su commitment ya yi mishi yawa kullum cikin neman duniya suke. Sai su share dogon lokaci ba su haɗu ko a waya su na d'ibar kwanaki ba su yi waya wa junan su ba. Suna kawai sun yi aure a haka ta haifi Anisa tun tana jinjira ta mik'a ragamar kula da ita a hannu Nanny Lacey Anisa tana da shakaru 6 ta sake haifar Airah wacce ita ma ta bi ayarin tawali'u hannun Nanny Lacey, tun daga haifar Airah tace ta gama haihuwa Allah da ikonsa babu zato ba tsanmani sai ga ciki Ahlam ba yadda bataso tayi abortion amma ciki yak'i ya fita, a lokaci ba k'aramin tashin hankali suka yi ita da Azaad ba sai da ya kai fagge furta mata muddin ta zubar mishi da ciki a bakin aure ta shine dole ta hak'ura. Duk a cikin yaranta Ahlam ta fiso rashin samun kulawarta duk watani tara ne da ita amma duka bai fi sau biyu ko uku da tasha nono Salima ba. Shiyasa babu wata shakuwa a tsakanin su daga Nanny Lacey sai siblings ɗinta sai Kuma Daddynta Kaɗai tasani. Saboda duk yawan commitment ɗinshi ya kan ware lokaci na musanmman ya zauna tare da yaranshi wani lokaci har daukar su yake yi tare da Nanny Lacey wacece ta maye musu gurbin uwa su fita kasashe waje yawon buɗa ido.
Anisa ta taso da masiffafen girman kai da faɗin rai ga d'an banza rashin kunya da fitsara, kowa kallon bai isa ba take mishi kullum Madam Salima cikin sauya mata school take ko Kaɗan bataso a faɗi laifin yaranta, dama bahaushe yace inda saniyar gaba tasha ruwa anan ta baya za ta sha, duk wani iskanci na Anisa K'anwar ta Airah ta kwashe tass duk da haka Airah tafi ta dama domin ita idan Nanny Lacey ta tsawa ta mata tana ji.
Ba yadda Jadda ba tayi da Azaad ya k'ara aure amma yak'i saboda duk duniya ba abin da Madam Salima ta tsana irin kishiya, sai kuma ta taki sa'a da Azaad Junaid ba shi da ra'ayi mace fiyye da d'aya. Shiyasa take tsula tsiyarta iya son ranta yanzu haka Jadda bata da daraja da za ta shiga bangare ta alhali su na rayuwa a gida d'aya asalima ba wacce ta tsana irinta saboda kawai tana faɗa mata gaskiya sai ta d'auki k'iyayyar duniya ta ɗorawa mata.

K'arfaffiyar ajiyar zuciya Azaad Junaid ya sauke kafin ya mik'e ya sauya kaya jikinsa zuwa tsadaddiyar shadda getzner ash colour, ya ɗora hula zanna bukar wanda ta dace da kayan jikinsa. Ya saka penny loafers a k'afarshi yayin da yake fitar da sihirtattace k'amshi designer perfume na poundland black dust, ya tattara wasu documents da ke kan center table tare da wayoyin shi har guda uku. A hankali yake taka steps duk da ranshi babu dad'i ba kowa bane zai fahimci hakan ba, saboda koda yaushe fuskarshi a murtuk'e take bashida yawan fara'a ko abu ya yi mishi dad'i sai dai kawai ya yi murmushi, ba kowa a downstairs parlor muddin yana gida housemaids ba su kai da kawo ko wane su zai ya kame kanshi, musanmman yau da gida yake a hartsune dole su yi taka-tsan-tsan.
Tun daga main gate direbanshi mr Richard ya hango shi da ya tashi ya jawo mota ya iso daff dashi kafin mr Richard ya fito ya buɗe mishi k'ofa ya budewa kanshi.
*******************
Kuka take yi sosai tana d'auke da marar lafiyar K'anwata Amal wacce bata motsi, wuyanta ya langwa6e ya yi baya bata da ban-banci da matatciya tunaninta ma ta mutu ne. Cikin hak'i ta shiga d'akin kakarsu wacce ta haifi mahaifinta tsabar tashin hankali da take ciki yasa ta manta da dokar da Dadda ta shinfid'a musu na hanasu shiga mata d'aki daga ita har k'anneta guda biyu twins Amal da Amrah. Ta ban kad'a curtain da k'ani mahaifinta ta fara yada ganinta akan shi, da sauri ta nufe wurinshi cikin muryar kuka take magana.

"Baffa Don Allah ka taimaka ka duba min Amal bata numfashi na shiga uku Baffa ba dai Amal ta mutu ba?"

"Ke!

Ya daka mata tsawa yana muzurai kamar zai kife ta da mari, cikin hargowa ya ci gaba da faɗin.

"Kar ki sake ki kawo ta kusa dani. Na duba ta ni likita ne ko ke ba ki san hanyar asibiti bane?" saboda tsabar iskaci da rashin mutunci za ki kawo min ita"

"Allah yasa ta mutu mu rage mugun iri jinin arna"

Hajja Dadda ce ta faɗa tana baro wajen zamanta sai lokaci Aslamiyya tasan da zamanta a falo, a fusace cikin rashin tausayi ta dank'e dantse hannun Aslamiyya ta hankad'a ta waje da k'arfi daga ita har Amal ɗin take d'auke da ita suka faɗi yayin da Aslamiyya ta faɗa kan hannunta na hagu, ta kwalla k'ara Amal kuma kanta ya buge sumunti hakan ne ya haddasa mata jan dogon numfashi ta farfado daga suman da tayi, duk da tsananin zogi da hannun Aslamiyya ke mata hakan bai hana mata rerafawa akan gwiwoyinta biyu ta jawo Amal cikin jikinta a matuk'ar tsorace ta ɗago ta tace.

"Amal! Amal! Kina ji na kuwa?" Don Allah idan kina ji na ki buɗe idanuwanki nagani, Amal karki mutu ki bar mu. Muna matuk'ar buk'atarki ni da Amrah ki tuna ba mu da kowa sai junan mu. Don girman Allah ki tashi kin ji K'anwata?"

Cikin tsananin zafin ciwo Amal ta shiga k'ok'arin buɗe idanuwan nata dake rufe ruff! Da kyar da sudin goshi tai nasarar buɗe su sai dai dishi-dishi take gani Aslamiyya.


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login