Showing 24001 words to 27000 words out of 91651 words

Chapter 9 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

611

nayi magana da Hakeem ya ce cikin sati nan za ta tare amma za ki iya bincikarshi da kanki.

"Shikenan tashi ka tafi Allah ya tsare yasa ayi kyakkyawar tafiya"

"Amin thumma amin!

Ya faɗa tare da sa kai ya fita bakinshi d'auke da addu'ar fita daga gida.
***************

Tun daga ranar da Miyya ta ji zance aurenta ta tashi hankalinta, yayin da Aunty Zaliha take bin ta da rarrashi haɗi da nasiha sannu a hankali nasiharta tafara tasiri akanta. Hakan yasaka Aunty Zaliha ta dukufa wajen gyarata idan ka ga yanda Miyya ta dawo da matuk'ar wahala ka iya gane nan take.
Tayi bul-bul k'irjinta ya k'ara cika, fatar jikinta tayi smooth gwanin sha'awa ita kanta sau dama idan ta shiga wanka sai ta 6ata dogon lokaci gaban mirror tana kallon yadda jikinta ya dawo ita kanta tana jin sha'awar kanta balle ga lafiyayye namiji ya yi arba da ita..
Zaune take gaban dressing mirror fitowarta daga wanka kenan, jikinta na fitarda sihirtattace k'amshi saboda ko wanka za tayi sai Aunty Zaliha ta zuba mata kalolin turaruka wanka daban-dabam shiyasa duk idan ta zauna sai tabar k'amshinta. Aunty Zaliha ta shigo rik'e da ma-dai-daci cup tana shigowa Miyya ta 6ata fuska saboda ta riga da tasan kwanan zance.

"Kar6i ki shanye ki bani cup"

Bata yi gardama ba ta amsa ta shanye tass ta mik'a mata cup, aunty Zaliha tana murmushi ta juya ta fita. Miyya ta bi ta da kallo har yau ta kasa daina mamakinta.
*****************

"Hasheem Kaɗai bi lamari nan a natse cikin hikima da dabara, wallahi-tallahi Azaad ya fi ka shu'umanci. Kana dai kallon irin mutuwar k'as-k'anci da Babban Yaya da Alhaji Buba suka yi ko kare gidana bana fatar ya yi irinta.

Ahmadu ya faɗa yana share d'an uban gumin da ya tsatsafo mishi a goshi, ya rasa dalili ko sunan Azaad ya anbata sai ya tsinci kanshi cikin mugun yanayi.

"Mtsss.... Kaɗai Yaya Ahmadu an yi matsoraci ni nan da ka ganni ba Azaad ba ko uwarshi dake lahira da za ta dawo duniya sai na wulak'anta rayuwarta, balle wani k'aramin gwaro irinsa.

Jin furuncinshi yasa Alhaji Abdallah ya girgiza kai sai da ya k'are mishi kallo kafin ya ce.

"Kaɗai bi a hankali kamar yadda Ahmadu ya faɗa Hasheem. Gudun kada allura ta tono galma, da za ku d'auki shawarata da nace mu hak'ura da son ganin baya Azaad, saboda ba tun yau ake ruwa k'asa tana shanyewa ba. Ku duba tsawon lokaci da muka d'auka muna binsa da bi ta da k'uli sai asarar dukiyoyinmu muke yi wurin malaman tsinbo da bokaye a banza. Har ta kai da mun fara rasa rayukanmu, tsakani da Allah banaso nayi mutuwa irinta su Babban Yaya mu je gidan shahararru bokaye har ma da matsafa ko yau ɗinan mu je wurin wani matsafi, da idanuwanku kun ga abin da ya faru ya kira sunan Azaad a madubin tsafinsa a maimakon ya fito shi Kaɗai sai ya fito tare da aljanarsa dake bashi kariya. Dakyar mu kasha saboda haka magani bari kar a fara ni mu dai ri ga da mun fara amma Kuma lokaci bai k'ure mana ba mu rufawa kanmu asiri mu watsar da makaman yak'inmu, ko don gudun mutuwar wulak'anci..

"Dakata Alhaji Abdallah!

Hasheem ya faɗa cikin tsawa tamkar yana yi da sa'anshi.

"Tun farko ba kidahumancin ku ne ya jawo ba. Na sha faɗa muku bokayenku duk makaryata ne, basu iya komai ba sai gilla k'arya. Ku bani dama za ku ga aiki da cikawa zan nemo professional killers su cika masa aiki kyaftawa gira su turo shi garin da ba a dawowa.

"Shikenan ku je Allah ya bada sa'a saidai inason ku sani a wannan karo kuma a wannan tafiya ba dani ba, saboda gani ga wane ya isa wane tsoron Allah.

Cewar Alhaji Abdallah yana k'arashe magana ya Kade babbar rigarshi ya k'ara gaba, gaba ɗayansu suka bi shi da kallo kafin su sake dawowa da natsuwarsu kan Hasheem, wanda ya fito da karan sigari ya jefa baki yana shirin cinna mata wuta Hajiya Kubra ta dakatar dashi.

"Kar ka sake ka kuna mana sigari anan domin ba so warinta nake yi ba yanzu nan sai ta ɗaga min hankali, ka bari sai ka fita can waje ka kunna abarka.

Ya galla mata harara kana ya yi kwafa tare da cizo la66anshi na k'asa, yana jinjina ranarda duk tashigo hannunshi irin wulak'anci da zai shuka mata dole ya cire sigarin ba don ranshi naso ba.
Ahmadu kan ya kasa yak'i da zuciyarsa sai ya ji kamar ya bi bayan Alhaji Abdallah sai kuma wata zuciya ta kwa6e shi gara ya zauna ayi dashi gudun kada giwa ta faɗi aci nama ba dashi ba. Kuma ai ba wurin boka za a je ba balle Aljanar Azaad ta kashe su.

***************

A yau Hakeem ya yanke shawarar ya faɗawa Miyya gaskiyar al'amarin, saboda yana so ta tare kafin Azaad ya dawo daga business trip ɗin da ya tafi. Shiyasa ya aika kiranta lokaci da sak'on ya risketa sai da taji matsananci faɗuwar gaba.
Tsawon lokaci da ya aika kiranta ta kasa tashi ta je sai tufka da warwara take yi saboda tun daga ranar da taji zancen aurenta dashi take wasan 6oya koda kuskure bata bari suka haɗu ba. Shi kanshi Hakeem yana shakkar yadda zai faɗa mata wannan bak'on al'amarin saboda sun yi wasa da hankalinta ba Kaɗan ba. Amma dole ce tasa su yin hakan.

"Wai Miyya ba za ki fito daga d'akin bane ko sai Abban Rayhan ya zo da kanshi?"

Muryar Aunty Zaliha ce ta dawo da ita daga duniyar tunani da ta lula, cikin sanyi jiki ta fito sanye da dogon hijab har k'asa tana shigowa falon ta sadda kanta k'asa can nesa dasu ta nema ta zauna, ta shiga wasa da babban yatsar k'afarta ta dama. Hakeem ya rasa ta inda zai fara kama bakin zare sai musu- musu yake da baki kamar mai jan casbi, can dai ya yi ta ɗiya maza ya yi gyaran murya kana ya ce.

"Da farkon dai zan fara cewa dake Aslamiyya ki yi hak'uri domin akwai abubuwa da yawa da ya kamata ki sani kafin yau sai dai na 6oye miki ne na bi ki da yadda kika fahimci al'amari ba don komai ba sai don ki sami natsuwa da kwanciyar hankali to Al-hamdu-lillah burina ya cika. Miyya dangane da zancen aurenmu dake ba gaskiya bane amma zancen an d'aura miki aure gaskiya ne. A zahirin gaskiya ba dani aka d'aura miki aure ba da aminina ne kuma d'an uwana Azaad Junaid.

A firgice Miyya ta ciro kanta daga k'asa ta jefawa Hakeem wani irin rikittace kallo mai cike da tarin tambayoyi hakan yasa ya gintse bakinshi ya kasa ci gaba da magana...
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004

13...

Kallo d'aya za ka yiwa Miyya ka gano ba k'aramin firgici da tashi hankali take ciki ba.
Ta kasa gasgata abin da kunneta ya ji daga bakin Hakeem gani take yi kamar wasa ne yake yi, kawai so yake ya gwadata shiyasa ya bijiro mata da wannan zance mai kama da almara.
Gani ta kasa furta kalma ko d'aya daga bakinta yasa Hakeem ya ci gaba da faɗar

"Azaad mutumin kirki ne abokina ne tun na yarinta nasan shi ciki da waje da yana da wata matsala ko gacci da ba zan nema mishi aurenki ba.

"Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Hasbunallahu wal'imal wakil.....Ni kan na shiga uku ni Miyya wai meke shirin faruwa da rayuwata ne?"

"Alkhairi Miyya Alkhairi ne yake bibbiyarki, wallahi-tallahi da Azaad yana da wata matsala ina da tabbacin Abban Rayhan ba zai shige mishi gaba wajen naman aurenki ba...

"Ya isa nace ya isheku haka! an gayamuku rayuwata kwallo ce da za ku dinga jefata raga a duk lokaci da ku kaso?" Ko an gayamuku don banida gata yana nufi ku yi wasa da zuciyata yadda ku ga dama?"

Kasa ci gaba da magana tayi sakamakon wani irin nauyi da k'irjinta ya yi kamar an ɗora mata dutsi, tasa hannu ta dafe saitin zuciyarta da ke bugawa da k'arfin gaske. Aunty Zaliha ta taso da sauri ta ɗagota kana ta mik'ar da ita tsaye. Miyya ta kalli Aunty Zaliha da idanuwanta suka fara komawa jajjaye muryarta na rawa ta ce.

"Sake ni Aunty Zaliha duk abin da ku ka yi min ba zan ga laifinku ba. Domin da Baffana da kakata ba su ba ku k'ofa ba da ba za ku yi wasa da hankalina har haka ba. Ban ta6a jin haushi kasancewata marar gata ba sai yau. Da ina da gata ko Kaɗan ba za ku kwatata rikita min hankali da tunani ba.

"Miyya please Kar ki yi mana mummuna fahimta da fari ki natsu na fahimtar da ke ta yadda za ki fahimci lamarin cikin sauk'i.

"Haba uncle Hakeem ya ka ke magana tamkar kana nufi babu zuciya a k'irjina. Miyasa tun farko ba ka fito min a mutum ba. Sai ka yi amfani da rud'add'iyar hanya ka rud'a zuciya da tunanina?"

"Nasani Miyya ta yanda mu ka fito miki ba mu kyauta ba. Amma inaso ki sani mu yi hakan ne a dalili ta yanda ki ka fahimci al'amari, mun za6i mu 6oye miki ne saboda ki sami natsuwa da kwanciyar hankali. Ba mu yi haka don cutarwa a gareki ba mu yi ne domin samuwar farin cikinki. Miyya Ina da yak'ini akan Azaad Junaid zai inganta rayuwarki, zai ba ki duk wani farin ciki da kika rasa haɗi da gatan da kike kirara kin rasa. Allah shine shedata na d'auki ke da 'yan uwanki tamkar 'ya'ya da na haifa idan har zan iya cutar dasu to tabbas zan cutar daku.

"Na ji uncle Hakeem ba za ka iya cutar dani a zahiri ba amma kasani ka cutar dani a badili, da tun farko ka umarce ni da na aure abokinka nan take zan amince ba tare da dogon tunani ba. Domin hallaci da ka yi min ni da 'yan uwana ka can-canci ka bani umarni na bi. Ka tuna Uncle kaine ka ceto rayuwar 'yar uwanta Amal a lokaci dangin mahaifinmu suke so labarin mutuwarta ya riske su. Ka sanya su makarantar islamiyya da boko ka yi musu gatan da Baffa da Dadda suka kasa yi mana shin wannan Kaɗai bai isa ya haska maka girman da k'ima da kake dashi a idanuwana ba. Fargaba ta d'aya uncle shima Azaad ɗin da saninshi ka auro masa ni ko shima wasa da hankali ka yi mishi kamar dai yanda ka yi min?"

Wani irin faɗuwar gaba Hakeem ya ji ya kasa koda kwakkwaran motsi sai kawai ya tsare Miyya da idanuwanshi ya rasa abin faɗa gani haka yasa Miyya ta ce.

"Kar ka damu uncle Hakeem tawa k'addara ce ta zo da haka.

Kafin ya lalla6o abin faɗa ta cire hannun Aunty Zaliha daga rik'e ta da tayi, ta nufi d'akinsu. Hakeem ya kalli Aunty Zaliha yai mata nuni da ta bi ta har ta buɗe baki za tayi magana ya tari numfashinta.

"Je ki kawai Zaliha ki k'arasa faɗa mata anjima za mu rakata gidan mijinta.

"Amma Kuma Abban Rayhan.....

"Kar ki ce komai Zaliha kawai ki yi abin da nace.

"Shikenan.

Ta faɗa ba don ranta yaso ba.
***********
LOS ANGELES.

Su Madam Salima an kammala taro successfully, burinta ya cika ta haɗu da manya-manya jiga-jigai 'yan kasuwa na duniya babu wani kwakkwaran bincike ta dinga zuba hannu jari a duk wani company da ya yi mata. Anan ta haɗu da wata fitattaciyar 'yar kasuwa mai suna Roseline Yaqub Gambella 'yar asalin kasar ethiopian. kasancewar Miss Gambella ta yi suna sosai a duniya kusan ita ce ita the most popular business woman ta biyu a duniya ta shahara a kasuwanci ba Kaɗan ba. Ita ce special guest a taro tun daga lokaci da madam Salima ta kyala ido ta ganta taji tanaso kula alak'ar kasuwanci da ita. Saboda haka ta shiga bibbiyar ta sai a rana ta k'arshe da za a kammala taron ta sami damar haɗuwa da ita, cikin kwantar da kai madam Salima ta nemi da su k'ula k'awance har ta nemi miss Gambella da tasaka hannun jari a company ta da farko miss Gambella bata so ba, saboda ko sunan k'asar Nigeria bata so ta ji an anbata mata, sakamakon wani babban al'amari da ya faru da rayuwarta a can.
Wanda har yau ta kasa mantawa balle ta goge shi daga zuciyarta. Yanda madam Salima dinga rarrashinta yasa ta amince, ba don ranta yana so ba sai don wani tunani da ya faɗo mata,ta ware manyan kud'ad'e tai investing hakan a wurin madam Salima ba k'aramar nasara bace domin da yawa su na so tai investing a kamfanoninsu amma basu sami wannan damar ba.
Shiyasa alfarinta da izzarta suka k'ara linkawa, tana gani wani tudu ne ta fara takawa na nassarar cika burinta. Washe gari da suka kammala taro ta sake lulawa kasar Turkey, ko tunani yaranta da ta baro bata yi tun lokaci da ta baro gida Nigeria kusan three weeks kenan bata kira waya ta ji lafiyar su ba. Ko Kaɗan yara basu dameta ba ko tana gida ba wani kulawa suke samu daga gareta ba. Sai ta share kwanaki bata saka su a ido ba alhali suna gida d'aya, babu abinda ya dameta tana d'akinta suna nasu kuma bata basu damar zuwa mata bedroom ba.
ko shekara d'ari za su yi basu gannta ba, ba su isa su je nemanta a bedroom ɗinta ba. Shiyasa babu shakuwa irin ta uwa da 'ya'yanta a tsakaninsu. A takaice ma mugun tsoronta suke yi.
*****************
Misali k'arfe biyar da rabi na yamma aunty Zaliha ta shiga d'akin da Miyya, ta tararda ita ta zabga tagumi ta dukufa tunani makomarta a gidan mutumin da ta ji an kiranshi da suna Azaad. Tashin hankalinta bai wuce Uncle Hakeem ya ce a wurinshi za ta bar Amrah da Amal a cewer shi sai ya ga ta kwantar da hankalinta a gidan mijinta, sannan zai dawo dasu hannunta. Taso tai mishi turjiya saidai kwarjinishi ya hanata.
Dafa kafad'arta da Aunty Zaliha ta yi yasa natsuwarta ta dawo jikinta.

"Tashi mu tafi Abban Rayhan yana jiran mu a parking lot"

Miyya ta 6ata fuska tamkar za tasa kuka, sai kawai tayi k'ok'arin danne hawayenta bata so ta yi kuka gudun jefa k'annaita a damuwa. Batare da ta ce komai ta mik'e already ta shirya cikin Abaya maroon colour, tayi rolling da veil ɗin rigar.
Aunty Zaliha ta rik'o hannunta a falo suka iske su Amrah su na jiran fitowarsu.
kaitsaye parking lot suka nufa inda Hakeem ke zaman jiran fitowarsu, Amal ta buɗe k'ofar mota aunty Zaliha ta zaunar da ita sai lokaci tai k'arfin hali ɗago idanuwanta ta dubi 'yan uwanta wanda ko Kaɗan bata ga damuwa rabuwarsu da ita akan fuskokinsu ba. Sai ma farin ciki da ta ga su na yi ta girgiza kanta tana mamakin kurciyarsu.
Su har sun ga abin farin ciki anan gudun kada ta rusa musu farin cikin nasu yasa ta dangana ta mik'awa ubangiji al'amuranta, abu d'aya tasa aranta muddin 'yan uwanta za suyi farin ciki to kuwa za ta sadaukar da nata. Har Hakeem ya ja mota suna ɗaga mata hannu. Bata mayar musu ba domin gani take da ta mayar musu sun rabu kenan har abada.
Suna tafiya Hakeem da Zaliha na mata nasiha da haka suka iso katafare tangamemen Azaad Junaid mansion, tun daga bakin gate ɗin gidan ta gano wata daula duniya ce ta shigo wacce ko a mafalkinta bata zaci za ta tsinci kanta a ciki ba.
Kasancewar securities ɗin gidan su san Hakeem da kuma matsayinsa a wurin Azaad Junaid yasa nan take suka buɗe masa gate ya wuce gate na d'aya kana ya zarce na biyu anan ma buɗe masa aka yi sai daff da shiga k'ofar main falo ya yi parking Aunty Zaliha ce ta fara fitowa kana ta buɗewa Miyya k'ofa wacce ta dawo tamkar jini baya gudana a sassa jikinta, idanuwa da gangar jikinta kawai ke aiki yayin da tunani da natsuwarta suka kaura a gareta.
Hakeem ya wuce gaba suka mara mishi baya door bell ya danna cikin abin da bai fi 60 seconds ba Nanny Lacey ta buɗe k'ofa......
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004

14...

A babban falon gidan suka zauna. Nanny Lacey ta kawo musu ruwan sha da juice. Murya can k'asa Hakeem ya gabatar mata da Miyya. Ya kuma k'ara gargadinta kada ta faɗawa kowa matsayinta a gidan duk da k'asa-kasa ya yi magana kuma cikin harshen turanci ba wani turanci kirki take ji ba amma ta fahimci abin da yake faɗi.
Sosai ta k'ara shiga damuwa har ta fara zanci zuci "oh! Ni Miyya naga takaina wannan wane irin aure ne ya Rabbi ka taimake ni ka bani ikon cinye wannan jarabawa"

"Miyya wannan ita ce Nanny Lacey ita ke kula da cikin gidanan tasan komai akanki, sannu a hankali za ta sanarda ke abin da Azaad yake so da wanda baya so za ta kuma warware miki duk wani abu da ya shige miki duhu.

Miyya ta ɗago da idanuwanta ta kalli Hakeem kana tasake sadda kanta k'asa, batare da tace komai ba. Hakeem ya umarci Nanny Lacey da ta kira mishi Aneesah da Airah. Ko wace tana d'akinta a k'unshe sun ri ga da sun saba da zaman d'aki idan basu d'aki suna study room. In ko ka ga sun fito downstairs parlor abinci za su ci ko kuma malami da ke faɗa musu karatu al'qur'ani ne ya zo. Rayuwarsu a tak'ure take basu san komai ba sai karatu gara Princess Aneesah tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login