Showing 6001 words to 9000 words out of 91651 words
cire hular kanshi ya yi, ya aje akan desk ɗin ya shiga shafar suma kanshi. Damuwa tana neman tai mishi yawa tsoronshi daya kada ciwon hawan jini ko ciwon zuciya, ya kama shi. Ga dukiya mai tarin yawa Allah ya albarkace shi da ita amma ya ga-gara samun farin ciki da natsuwar zuciya kullum cikin k'unci da 6acin rai yake.
K'arar k'ararawa da ya karad'e office ɗin nashi ya dawo dashi daga duniyar tunani da ya nutse, ya kai duban shi akan allon cctv da ya ke iya gani wanda keso shigowar office ɗin, amininsa kuma MD na company sa Abdul-hakeem Daura ya gani tsaye yana jira ya buɗe masa k'ofa ya shigo, kasancewar k'ofar tana using da code dole sai in shi ya buɗewa mutum zai iya shigowa da remote control ya yi amfani k'ofar ta zuge kanta Abdul-hakeem ya baiyana. Duk faɗin duniya ba shi da wani amini d'an uwa sai Abdul-hakeem saboda 'yan uwanshi da suka had'a uba ba k'aunarshi suke yi ba. Su na bak'in ciki da hasada da daukakkar da Allah ya yi mishi. Burinsu a kullum bai wuce su sami hanyar da za su kawo k'arshen sa.
Da shigowar Abdul-hakeem ya yi tsaye ya saka Azaad gaba yana kallo, nan take ya fahimci halin damuwa da yake ciki. ko bai tambaye shi ba yana da tabbaci Madam Salima ce damuwar shi, saboda duk faɗin duniya ita ce matsalarshi ita ce mai jefa shi halin damuwa.
Ya girgiza kai haɗi da jan kujera dake kallon Azaad ya zauna.
"Aj ya kamata ka dinga sassautawa kanka yawan tunani kada ya zo ya shafi lafiyarka. Tunani ba shi bane solution ɗin matsalolin ka ba.
Azaad ya ja gwaron numfashi kana ya lashe lips ɗinsa, cikin zazzak'ar muryarsa mai dad'i da tafiyar da ruhin mai sauraren shi yace.
"Ni kaina ba so tunani nake yi ba Abdul zuwa min kawai yake yi. matsaloli su min yawa ga na 'yan uwana ga na iyalina da wane zan ji?" Yanzu duk wanda ya gani zai dauki cewa na fi kowa farin ciki a duniya saboda ina da tarin dukiya ba asan cewa wani tallaka wanda bai da ci yau balle na gobe ya fi ni domin shi, yana samun natsuwar da kwanciyar hankali daga iyalinsa.
"Zance na gaskiya Aj kaine ka za6awa kanka wannan matsala, Salima ba za ta ta6a sauyawa ba. To saboda me kai ba za ka nemowa kanka mafita ba?" Tun yaushe ni da Jadda muke ba ka shawara ka k'ara aure amma ka k'i sai ka zauna bak'in ciki mace d'aya ya kashe ka.
"Please Abdul-hakeem ka fahimce matsalata ba ta k'arin aure bace. sai fa ka ji dad'i abu kake neman k'arinsa.
"Matsalarka kenan Aj idan aka yi gabas sai kayi yamma, dole fa sai ka cire tsoron Salima ko don farfado da tarbiyyar 'ya'yanka ka tuna yaranka mata ne dole su na buk'ata ingantattaciyar tarbiyya. Idan mahaifiyarsu ta kasa sai ka nemo wacce za ta maye gurbinta mana.
Mik'ewa Azaad Junaid ya yi hannayenshi zube cikin aljihun wandonshi, ya taka a natse zuwa gaban widow da ke kallon titi. Yaye labule idanuwanshi suka sauka akan motoci da ke kai da komuwa. Shima Abdul-hakeem mik'ewa ya yi ya isa daff dashi kana ya dafa kafad'arsa.
"Ka yarda dani Aj aure shine yafi dacewa da kai ka tuna kullum shekarunmu k'ara tafiya suke yi dole sai muna samun natsuwar da kwanciyar hankali, so ka ga kenan don ka k'aro aure ba wani abu bane. Allah yasani kayi hak'uri iya hak'uri da Salima lokaci ya yi da za ka d'and'ani zak'i da gard'i dake cikin aure"
D'an gajere murmushi Azaad Junaid ya yi wanda ya tsaya iya fatar bakinshi, kana ya juya yana facing Abdul-hakeem.
"To naji idan ma na amince zan k'aro aure wa zan aura?" Sani kanka ne Abdul tun daga lokaci da na auri Salima ko mafalki ban ta6a kallo wata 'ya mace naji ina sonta ba. Ta ya ya ka ke tunani zan yi aure?"
"Mtsss...!
Abdul-hakeem ya ja siririn tsaki da ke baiyanar da takaicinsa a fili.
"Ba dole bane sai ka ji son mace za ka aure ta ba, kai da za ka yi auren huci haushi ina ruwanka da soyayya. Alhaji ka amince kawai ka ga aiki da cikawa ni da kaina zan nemo ma matashiyar budurwa wacce Nonuwanta suke tsaye cakk! Ka sha shagali abinka.
Zaro idanuwa Azaad Junaid ya yi tamkar ya ga abin tsoro kana yasa dariya wanda rabon da ya yi irinta har ya manta.
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪
*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*
*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*
*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*
*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*
*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*
*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*
*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*
*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*
*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*
*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*
KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*
SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*
SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*
*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Wattpad:-jeedddahaliyu
Haske writers Association.
Top Ten Takun Haske Batch:A
Free press
3....
Amrah na fita bata zarce a ko ina ba sai wani k'aramin super market, kamar za tayi siyaya sai da taga hankali mutane baya kanta. Ta dinga tsintar biscuits da Madara na sachet tana cusawa cikin zaninta batare da ta bari an ganta ba ta fice da mugun sauri.
Gudun kada a ganota da fitarta ta kwasa da gudun bala'in ta nufi gida, cikin sa'a babu kowa a tsakar gida tai wuff! Ta shige d'akinsu kamar wacce aka jefo. Daga Aslamiyya har Amal sai da suka firgita domin a zatonsu ko Dadda ce.
Kallo daya za ka yi wa Amrah ka gano bata da gaskiya sai wuk'i-wuk'i take da idanu kanta a k'asa ta k'araso cikin d'akin. Ta cire hijab tare da kayan da ta sato ta ajiye ta d'auki wani tsohon kofi wanda tun na aure mahaifiyarsu ne bata ce dasu k'ala ba ta fita gindin famfo ta nufa ta taro ruwa rabin kofi.
Koda ta dawo d'akin Aslamiyya tana jujjuya biscuits da madara ɗin.
"Ga ruwa ki k'adawa Amal madara ta haɗa da biscuit ko da na koma wajen mai koko ya k'are shine na siyo mana madara da biscuits sai dai na manta ban siyo sugar ba. Sai da na iso k'ofar gida na tuna.
Tana magana Aslamiyya ta k'ure ta da manyan idanuwanta, sai da ta saki 6oyayyen numfashi kafin tace.
"Ina kika sami kud'i Amrah?" Iya sanina naira hamsi muke dashi kin Kuma ri ga da kin siyo koko ya zube"
"Keɗai miyya kin cika bincike wallahi"
"Bincike dole ne Amrah banaso wani mugun abu ya faru daku saboda 6ata gari sun yi yawa mutane basu da imani.
"Uhm...miyya ki dinga kyautata zato Abba Saleem ne ya bani kud'in wankau da nayi mu su na kwanaki, da basu biya ni ba. To shine Ina dawowa daga siye koko na haɗu shi a k'ofar gidanshi ya bani"
"Amrah!"
"Miyya!"
Amrah ta kira sunanta kaman yadda Aslamiyya ta kira ta, har tana had'awa da turo baki.
"Amrah idanuwanki sun nuna min akawai rashin gaskiya da kika yi faɗa min me kika aikata?"
"Da zan shigo na haɗu da Baffa Sani a k'ofar gida nai kaman ban ganshi ba shine yaso ya dake ni dalili da yasa na shigo da gudu kenan baya ga wannan ban yi komi ba.
"Ya yi miki kyau Amrah duk abun da na hane ki ba za ki hanu ba ko?".
"I'm sorry mommana!
Cewar Amrah tana rik'e k'unneta da hannunta daya yayin da ɗayan ke rik'e da cup. Miyya ta yarda da k'arya da Amrah ta shara mata dalili kuwa tasan tana bin bashin kud'in wankau gidan Maman Saleem. Sai kawai ta mik'a hannunta ta kar6i cup ɗin ta haɗa mu su madara, Amal ta fara ba wa tasha ta k'oshi saboda iya ruwan madara take iya sha.
**********************
Sosai Azaad Junaid yake kyakyata dariya Abdul-hakeem ya rik'e baki yana kallonshi. Saboda shi bai ga abin dariya ba, da kyar ya yi controlled dariyar tashi, kana ya nufi water dispenser ya tsiyaya a handle cup ya sha fiyye da rabin ruwan.
"You're insane Abdul in ban da kana mahaukaci ko zan yi aure sai na rasa wacce zan aura sai k'aramar yarinya?"
Murmushi Abdul-hakeem ya yi kafin ya nufi kujera da ya tashi akai ya sake zama, ya dubi Azaad da girar ido a ɗage...
"Gata nake so nai ma Aj ka samu ka more garar da muka dad'e muna kwasa"
"Na yafe idan kana so mai nonuwan a tsaye ka nemi abarka, ni kuma nai maka alk'awari ni ne zan biya kud'in sadaki"
"Wai gatse kake min?"
"Miye abin gatse anan Abdul naga kaman ka fi ni buk'ata"
Ya k'arasa magana yana gintse baki.
"Shikenan Aj tun da ba ka so a yanzu amma nasan komai dare dadewa sai ka nemi hakan.
"Allah ya tsare ni da abin kunya"
"K'ara sunnah shine abin kunya?"
"Ba haka nake nufi ba auren k'aramar yarinya ne ba zan iya ba.
"Are you sure?"
Abdul-hakeem ya faɗa yana murmushi.
Sai da Azaad ya nemi daya daga cikin cushion ɗin da ke cikin office ɗin ya zauna, kafin ya furta.
"Hundred percent sure!
Har Abdul-hakeem ya yi yunk'uri sake furta wata magana ya katse shi ta hanyar faɗin
"Please Abdul mu ajiye zance mai nonuwa a tsaye mu yi aiki da ke gabanmu"
Daga haka suka shiga tattaunawa aKan contract ɗin da suke, aiki akai. Sai yamma lis suka rabu Azaad ya nufo gidanshi a downstairs parlor ya tarar da Nanny Lacey tare da Ahlam ke wasa da toys ɗinta. Airah tana Assignment princess Aneesa kuma tana d'akinta, tana chat da friends ɗinta.
Nanny Lacey ta gaida shi ya amsa ta hanya ɗaga mata hannu, Airah ta ɗago tare da furta.
"Welcome Daddy!
Ita ma hannu ya ɗaga mata kamar yadda ya yi wa Nanny Lacey, kaitsaye ya wuce bedroom ɗinshi dake upstairs. Wanka ya yi ya shirya cikin dark blue ɗin jallabiya ya wuce masallaci sai da ya sallaci sallar isha sannan ya dawo gida ya shiga 6angaren Jadda koda ya mai aikinta Mero ya tarar a falo, Jadda tana bedroom ɗinta. Direct d'akin ya nufa tana zaune akan sallaya da casbi a hannunta, ya nemi gefen gadonta ya zauna. Cikin natsatsiyar muryarshi ya gaidata ta amsa mishi cikin kulawa.
Kana suka zarce da fira sai ga Mero ta shigo da k'aton tray mai d'auke da tsadaddin warmers ta sauke a gabanshi, tasake fita ta dauko mishi lemo da ruwa. Jadda da kanta tai mishi serving tuwon semovita da miyar agusi taji tantakwashi da tsokar busasshe kifi. Sosai ya ci tuwon saboda shi mutum ne mai matuk'ar son abincin mu na gargajiya sai dai kashh! Allah bai had'a shi da wacce ta iya ba. Madam Salima ko ruwan zafi na shan tea bata da lokaci dafawa. Duk wata kulawa da ya dace ta ba wa mijinta housemaids ke yi mishi ga Azaad da shegen kyamkyami. Kuma gaba d'aya 'yan aikinta Christan ne ba Musulma ko d'aya, shiyasa Azaad ya k'auracewa abincin 6angarenshi sai dai ya zo na Jadda ya cika cikinshi.
Bayan ya kammala cin tuwonshi hadda su taune k'ashi Jadda ta tsare shi da kallon tausayi, har sai yaushe Azaad zai zama cikakken mutum?"
Domin a ganinta bai cika mutum ba rabin mutum ne, tayi iya k'ok'arinta akan ya k'ara aure abin yaci turo dole tana ji tana gani ta zuba mishi ido, duk da al'amarin iyalinsa yana ci mata tuwo a kwarya kullum cikin masa addu'a take Allah ya kawo mishi sauya.
"Anya kuwa Datti wannan rayuwa da ka za6awa kanka za ta fishe ka kuwa?"
"Jadda in-sha-Allah nesa ta zo kusa domin na sanar da Salima ta ajiye aikinta....
"Dallah..! Rufe min baki sakaran banza nusari kullum cikin faɗar haka kake yi har yau ka sa aiwatar da komi. Saboda haka na ba ka nan da wata uku ko ta ajiye aikinta ta cikakkiyar matar aure ta amshi ragamar kula da gidanta hannun arna. Ko kuma ni na nemo maka wacce za ta kula min kai da yaranka"
"Ki yi hak'uri Jadda in-sha-Allahu ba ma zai kai mu da haka ba .
"Sai ta Kai mu domin ba ajiye aikinta za ta yi ba ni kuma idan har ba mutuwa tai min sauri ba sai na auro ma 'yar mutunci mai nagartattaciya tarbiyya.
"Ni dai ina k'ara ba ki hak'uri Jadda"
"Hak'urin ka na banza da wofi, ka dai ji na faɗa ma wata uku na ba ka, idan ba haka ba k'arin aure ya zame maka dole. Ba kuma shawartarka nake ba ko jin ra'ayinka.
"Jadda rigima Keɗai sam bakyaso a zauna lafiya mu ajiye wannan zance ki sha maganinki"
Ya k'arasa magana tare da dauko mata ledar maganinta da ke aje akan bedside drawer, bayan tasha magani ya shafa mata na ciwon k'afa sannan ya koma 6angareshi. Har zuwa lokaci madam Salima bata dawo gida ba, Kuma tun fitar ta da safe.
Dama haka take yi in tafita sai baba ta gani take dawowa dabi'unta sam ba su yi kama dana musu aure ba, tafi Kama da masu zaman kansu.
D'akin yara ya wuce ya tarar da Airah tana game a laptop princess Aneesa, tana aikin nata na chat ganinshi yasa ko wace ta dakatar da abin da take yi.
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪
*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*
*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*
*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*
*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*
*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*
*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*
*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*
*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*
*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*
*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*
KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*
SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*
SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*
*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Wattpad:-jeedddahaliyu
Haske writers Association.
Top Ten Takun Haske Batch:A
Free page
4....
Zaune suke a katafare falon farmhouse da ya kasance mallakin Alhaji Yusuf Junaid su taru ne kamar yadda suka saba taruwa a can baya. Domin gudanar da secret meeting ɗinsu. su 8 ne maza 6 mata biyu kowa ne fuskarshi a turbune da ka dube su za ka hango tsananin 6aci rai da suke ciki. Hakan ya samo asali ne da har yanzu sun kasa cimma dad'en burinsu akan d'an uwansu Azaad Junaid.
D'aya daga cikinsu ne ya fara magana wanda da ganinshi yafi sauran mugunta da zafin rai, zuciyarsa na tafarfasa yace.
"Tsakani da Allah nagaji da jiran gawon shanu, zuwa yanzu yaci ace mun shafe babin Azaad a ɗora k'asa kuna kallo dai yadda kullum k'ara daukaka yake yi dukiyarshi sai habbaka take yi kamar shuka ana zuba mata fertilizer mun kasa yi komai. Idan har dukanku kwakwalenku sun daina aiki ni zan sa ayi masa mai gaba d'aya haihuwa da hanji...
"Dakata Ahmadu!
Hajiya kubra ta katse shi a tsawace dama can kawarsu bata gamo ba, duk lokaci da suka haɗu sai sun yi uwar watsi. Ta ci gaba da faɗin
"Kai miyasa ka cika fushi da daukar zafi?" Garin bak'ar zuciyar taka za ka iya kai mu ka baro kai mana shiru mu ji dalilin kiran gaggawa da muka samu daga babban yaya.
"Ke Kubra ki shiga taitayinki dani nafi ki rashin mutunci wallahi...
"Dallah ya isa haka ku kenan da zarar kun haɗu ba za ku ta6a rabuwa lafiya ba. Sai kun sai da hali.
Alhaji Yusuf Junaid ne ya kawo k'arshen musayar yawun nasu. Ya ci gaba da faɗin.
"Dalilin da yasa na me ganinku da gaggawa jiya ne Alhaji Buba ya zo min da labari wani shararren boka sha yanzu magani take. Aikinsa yana ci domin ya yi masa aiki cikin kwana uku