Showing 36001 words to 39000 words out of 91651 words
ke wanke plates ɗin da su Aneesah suka yi amfani dasu.
zaunar da Ahlam tayi akan kitchen cabinets saboda tasan halinta ba yarda za ta yi wani ya d'auke ta ba. Ta kammala had'a madara a fida sake daukarta tayi suka fito zuwa parlor tana cikin bata ta shak'i k'amshinsa take ta ji faɗuwar gaba haɗi da tsoro ya ratsata, batasan lokaci da tayi wata 'yar shassheka kamar mai jin sanyi. Ta ɗago idanuwanta a hankali kamar wacce aka yi wa dole karaff... idanuwanta suka sark'e da nashi yana sanye da ash colour suit ya ɗora green colour necktie ya yi mishi balthus Knott style sosai kayan suka k'ara fitowa da shahararren kyawonshi. Da sauri ta janye idanuwanta daga gareshi, saboda Sam bata iya jure kallon cikin fitinannu idanuwanshi sosai suke rud'ata tare da cika mata nata idanuwa. Ya yi kamar bai gannta ba ya nufi dining room, da sauri Nanny Lacey ta fito daga kitchen ta kalli Miyya tai k'asa da murya kamar mai rada ta ce.
"Pretty tashi ki je ki yi wa Yalla6ai Azaad serving tun da kina nan babu amfani na ci gaba da yi mishi.
Wani iri kallo Miyya take mata baki buɗe kafin ita ma cikin rad'a ta ce.
"Ni kuma Nanny haba Dan Allah miyasa kike so ki dinga jefani hurumin da ba nawa ba?"
"Saboda ke matarsa ce pretty saboda irin wannan sakaci ya jawo wa Madam Salima zuwanki gidanan, har kika kafa fada mai girma ban kuma san me zai faru anan gaba ba.
Miyya tai shiru tana wasa da fida da ke rik'e a hannunta, yayin da gabanta ke ci gaba da dukan tara-tara.
"Tashi mana kada ki 6ata masa lokaci yana da kyau ki kiyaye wannan Yalla6ai bayaso wasa da lokaci.
Batare da ta ce uffan ba ta tashi d'auke da Ahlam Nanny Lacey bata yi yunk'uri kar6a Ahlam ba, saboda tasan yana da buk'atar ganinta. Ta bi bayan Miyya da kallo tana tuna girman wannan aikin da Hakeem ya sakata tun tafiya ta yi nisa ta fara gani haske.
Cikin tafiyarta ta natsuwa mai kama da yanga ta ratso cikin dining room ɗin, hankalinshi yana kan wayarshi yana duba sak'oni{messages} sallama ta fara yi cikin sanyi murya, kafin ta gaida shi.
Can k'asan mak'oshi ya amsa mata lips ɗinshi haɗi da adams apples ɗinshi taga sun motsa ya shine ya bata tabbaci ya amsa mata.
Ya ajiye wayarshi akan dining table ya mik'o mata santala-santala hannuwanshi tuni ta gano abin da yake nufi ta matsa kusa dashi tare da mik'a masa Ahlam, wacce taso tak'i zuwa ya fizgota da k'arfi ya shiga yi mata wasa.
A fakace Miyya ta galla masa harara saboda ya bata haushi ta yadda ya fizge Ahlam ɗin. Batasan cewa duk abin da take yana ganinta ba. Haka zalika duk abin da ya faru tsakaninta da Nanny Lacey ya ji su sarai.
Ta zari plate ta zuba masa soyayar doya da haɗin source na kidney & liver ta zuba masa kunu gyada a mug. Sannan ta kar6i Ahlam har ta juya kamar daga sama taji sautin muryarshi.
"Nagode Sosai da irin kulawar da kike bai wa Ahlam idan buk'atar wani abu ta taso ki zo kaitsaye ki faɗa min.
Miyya ta ja dogon numfashi tare da saukewa abin ya zo mata wani iri tarasa amsar da za ta bashi sai kawai tayi murmushi tare da juyawa ta fice daga dining room ɗin. Cike da natsuwa ya shiga cin abincinsa har ya kammala yana jin kansa kamar ba shi ba. Ya bi ta flat ɗin Jadda ya duba lafiyarta kana ya wuce office, yana shiga office ɗinshi Hakeem na danno kai dama tun d'azu yake dakon zuwanshi, shaking hands suka yi kafin ko wane su ya nemi matsugunni.
"Ya ake ciki Aj mijin kwaila ya ka baro kwailar taka?"
Hakeem ya faɗa yana k'unshe dariyar shek'inyaci. Azaad ya bata rai cike da miskilancinsa ya ce
"Ban kira ka office ɗinan ba don ka karanta min iskaci ba. Na kira ne domin nasan menene matakin karatunta tana da buk'atar komawa makaranta, kasancewarta mai karancin shekaru bai kamata a tauye mata wannan damar ba.
Hakeem ya saki murmushi yana kallon Azaad Junaid da girar ido a ɗage, shi Kaɗai yasan abin da yake karanta akan fuskarshi kafin ya ce.
"Karatunta ya tsaya ne a matakin k'aramar sakandire {junior secondary School}
Azaad ya ta6e baki cikin izza ya ce. "Sai abu na gaba gargadi ne ina fatar za ka natsu ka bani aron hankalinka saboda banaso ace sai na sake mai-maita gargadin nawa.......
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Top Ten Takun Haske Batch:A
*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004
19.....
Hakeem ya k'ure shi da kallon mamaki kafin ya ta6e baki ya ce.
"Karata gargadin naka kunne ke ji saboda haka ina saurarenka.
Saida Azaad ya share 60 seconds kafin ya ce.
"Sabon suna da naji ka kirani dashi Ida ka sake kirana dashi za mu kwashe za mu hau sama mu faɗo saboda haka ka kiyaye....
Kafin ya k'arasa magana Hakeem ya kwashe da dariyar mugunta har da su dafe ciki, Azaad ya tsare shi da idanuwa yana mamaki abin da yakewa dariya. Sai da Hakeem yaci dariya iya son ranshi sannan ya kalli Azaad da raguwar murmushi akan fuskarshi ya ce.
"Ai yanzu Aj bakada suna da wuce mijin kwaila ko mijin mai nonuwa tsaye Kaɗai ka yi k'ok'ari ka kafa ka tsare ka bada himma nan da wata tara mu sami second Aj...
Yadda Azaad ya zazzare idanuwa za ka yi tsanmani wani mugun abu Hakeem ya faɗa, gaba daya ya kasa koda kwakkwaran motsi wani irin tsoron Allah ya lullu6eshi.
"Kai miye haka ka wani tsareni da jarababbun idanuwanka Miyya ce ba ta isa daukar ciki ba ko kaine kwanka ya daina fidda tsiro?"
"Mtsss.....!!
Azaad ya ja dogon tsaki kana ya ɗage girar ido yana yiwa Hakeem kallon kama rena ni.
"Gaskiya Hakeem bata ta6a sani da k'asurgumin mahaukaci nake zaune ba sai yau. Har ni Azaad Junaid kake kwatatawa da haɗa shinfid'a da yarinya k'arama sa'ar 'yar cikina? Tsakani da Allah Hakeem ka cuceni and I'll never forgive you....
"D'an dakata mana abokina haramun ne don ka kwanta da sa'ar 'yar cikinka naga dai matarka ce ta sunnah mun shaida ka biya sadakinta, wallahi tun wuri kada ka sa girman kai ka cuce kanka ka ba kasan cewa masu k'anana shekaru nan sun fi juriya da jajircewa ba.
D'aure fuska Azaad ya yi saboda ya fahimci damarshi da Hakeem yake gani ne yasa yake kawo mishi wannan zance banzan.
"Hakeem please mu rufe wannan zance mu yi abin da yake gabanmu domin kana daff da k'ure min maleji"
"To shikenan amma ina tabbatar maka muna nan dakai wata rana za ka canza shek'a ka yi wadak'arka ba tare da ka tuna da k'aranci shekarunta ba.
"Aikin banza da wofi an gayamaka ni tsuntsu ne da zan canza shek'a dallah malam ka bani files ɗin na duba ko na bar ka da kayanka.
Da sauri Hakeem ya mik'a masa documents ɗin hannunshi ya fizge da kar6i yana dubawa yana zabga tsaki, saboda ba k'aramin haushi Hakeem ya bashi ba.
Yayin da Hakeem sai dariya yake yi k'asa-kasa.
***** **** ****
A cikin kwanaki biyu Azaad ya nemawa Miyya gur6i karatu a school ɗin su Aneesah, saboda tsabar murna da Aneesah da Airah saida suka haɗa kwarya-kwayan party a d'akin Aneesah har da su saka music suka sha rawa abin da ba su ta6a yi ba tsawon rayuwarsu.
Ranar da Miyya ta za ta fara zuwa school tsabar zumudi tun kiran asuba na farko ta falka duk da zumudi da take yi sai da ta shiga kitchen taya Nanny Lacey suka haɗa breakfast.
Karfe 7:20am direba ya ajiye su lokaci da Miyya ta shiga aji ta kasa sakin jikinta irin dai bakunta nan da new students ke yi.
Sai misali karfe uku suka dawo gida a gajiye ko wane su ya wuce d'akinshi, kawai Miyya tayi ta fito neman Ahlam wacce taci kukan nemanta tana ganinta tafara zillo hannuwanta da sauri Miyya ta sunkuceta ta ɗagata sama tana mata Wasa ita kuma sai wangale baki take yi.
Da dare da Azaad ya fito ya yi dinner Nanny Lacey ta shiga har d'akin Miyya ta taso ta ta zo tai mishi serving wanda zuwa yanzu har ya bi jikin Miyya a natse za ta zuba mishi abinci tai tafiyarta abinta sau dama Nanny Lacey tana mata faɗa akan tafiyar da take yi ta barshi, ta kasa sabawar kanta da zaunawa idan yana ci abinci gani take yi kamar zai iya embarrassed ɗinta.
Lokaci da Nanny Lacey ta faɗa mata tana kwance sanye da silky material gown mai armless, tasaki gashin kanta ita kanta Nanny da ta kalleta sai da taji ta burgeta matuk'a balle ga d'an namiji mai cikakkiyar lafiya.
Turo baki tayi saboda sam bataso abin da zai kusanta ta dashi, ita Kaɗai tasan yanayi da take tsintar kanta a duk lokaci da ta ke6e daga ita sai shi. Mita tashi ga yi wa Nanny.
"Nanny please ki barni na huta mana yau fa ne first day ɗina a school dole akwai gajiya a jikina, ga kuma assignment ɗin da aka bani yanzu nakeso nayi kika shigo.
"Pretty yaushe kika zama stubborn girl huh?"
"Ba haka bane Nanny naga da can kafin zuwana ke ce mai kula da abincinshi, yanzu ma tun da ina da uziri ba sai ki fanshe ni ba?"
"Ba zan fashe ki ba kuma dole ki tashi ki ba mijinki abinci wannan ai sakarci ne da rashin sani ciwon kai tashi mana ina magana ki na zaune.
Nanny ta k'arashe magana cikin tsawa babu shiri Miyya ta mik'e tsaye tare da daukar k'aramin mayafinta da ke aje a gefen gado{Lol..dama kusan mutuniyar taku da d'an banza tsoro kamar farar kura} jikinta har rawa yake yi saboda ta zaci bayan tsawa za ta ji saukar yatsun Nanny Lacey akan kumatunta.
Cikin rashin kuzari ta isa dining room gaba ɗaya k'amshinsa ya cika dining ɗin, tayi sallama cikin siririyar murya kana ta d'an runsuna ta gaida shi ya amsa mata kamar yadda ya saba amsawa, ta zuba abinci a plate ta kai gabanshi, duk abin da take yi yana satar kallonta yayin da har yanzu jikinta bai daina rawa ba ta nufi fridge ta dauko ruwa da drinks, ta je ajiyewa ta take masa k'afa batare da ta lura da k'afar tashi ba. Sosai ta firgita cikin tsananin tsoro ta zabura, sai kawai k'afarta ta bugi kujerar da ke kusa da ita, tayi baya za ta faɗi cikin zafin nama ya rik'o hannunta.
Daga zaune da yake bai tashi ba gashi yanayi da ya cafko hannunta taji zafi, ta runtse idanuwanta ga jikinta sai rawa yake yi kamar mai jin sanyi.
"Ki dinga duba idan kike tafiya garin wannan rawar kan naki za ki illata kanki a wofi.
Cike da k'asaita ya yi magana bai kuma kalleta ba. Miyya ta buɗe tsoratattacin idanuwanta ta sauke su akanshi mamaki ne ya kamata haɗi da kwankwato anyya kuwa shine ya yi magana?" Shine mana Miyya ba gashi nan rik'e da hannunki ba Kuma ai kin waye muryarshi ko a cikin magagin barci za ki iya sheidata. Ta ja gwaron numfashi tare da saukewa a sanyayye ta ja hannunta dake cikin nashi gani haka yasa ya sake ta. Sai lokaci ya ɗago mayatattun idanuwanshi ya kalleta dasu....
_Not Edited!!!_
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Top Ten Takun Haske Batch:A
*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004
20...
Dukkan jikin Miyya ya d'auki rawa komai yana neman kwance mata, ta rasa wane irin sirri ne a cikin idanuwanshi da duk lokaci da ta kalleshi noti kanta ke kwancewa.
A hankali ta juya cikin sanyi jiki bata wuce tako biyu zuwa uku ba ta ji sautin muryarshi.
"Ki faɗawa Nanny ta kai min hot coffee falona.
Da k'arfi ta waiga ta kalleshi yana ci abincinshi hankali kwance, tasaki ajiyar zuciya kana ta k'arasa ficewa kaitsaye d'akin Nanny Lacey ta shiga ta sanarda ita sak'onshi.
Har ta juya Nanny ta tsayar da ita.
"Ai kin iya haɗa coffee ki je ki haɗa ki kai mishi a falonshi dake sama"
"Ni Kuma Nanny ke fa yace ki kai mishi ba ni ba?"
Murmushi Nanny Lacey tayi ta mik'e tsaye ta dafa kafad'ar Miyya, ta ce.
"Daga yau ke ce za ki dinga kai mishi kuma banaso gardama ki je kawai ki yi abin da nasaki.
"Nanny please ki daina sakani hurumin da ba nawa ba kina gani ko yanzu sai da ya yi min gori ya kirani da mai rawar kai"
Ta k'arashe magana kamar za ta fashe da kuka. Nanny ta d'aure fuska tamau alamar babu wasa a tare da ita.
"Pretty wai miyasa kike da taurin kai ne?"
"Ba haka bane Nanny wallahi mutumin nan ko gaida shi nayi da kyar yake amsawa"
"Koma menene wannan ba zai zama hujjar da za ki dogara da ita ki kasa kyautata mishi, a matsayinsa na mijinki. Pretty na fi ki shekaru dole na fi ki sani abin da ya dace da wanda bai dace ba dan haka ki shafawa kanki lafiya ki bi umarni da na ba ki.
Kasa furtawa Nanny uffan tayi cikin yana yi na takaici ta juya ta buɗe k'ofa ta fita, zuciyarta tana wani iri tuk'uk'i duk k'ok'arinta na ta hanawa kanta zubda hawaye hakan bai samu ba sai da zafafan hawaye suka wanke kuncinta. Kitchen ta wuce tana haɗa mishi coffee tana shar6a hawaye ko Kaɗan bata k'aunar abin da zai haɗata da Azaad domin ita Kaɗai tasan hali da take shiga a duk lokaci tayi arba dashi. Ta kammala haɗa coffee ta daura mug ɗin aKan k'aramin tray, cikin tsoro take taka matattak'alar benen da zai sada ta da 6angarenshi da ta iso k'ofar falonshi na farko zuciya ta k'ara sautin bugawa fiyye da farko tahowarta, sai ta kai hannunta za ta turo k'ofa sai ta janye, da kyar ta rinjaye zuciyarta ta turo k'ofar ta wangale bugun zuciyarta ya k'ara tsananta cikin tako d'addaya ta fara takawa zuwa cikin ainihin falon. Bata tararda shi cikin falon ba hakan yasa ta sauke k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta dire tray ɗin kan center table ɗin da tagani a tsikyar falon. Ta juya abinta har ta rik'e handle ta tuna da Nanny ta ce da ita ba a falon farko za ta kai ba a falonshi na biyu ji tayi kamar ta ɗora hannu akai ta kurma ihu. Dawowa tayi dole ta sunkuce tray, ta nufi k'ofar glass ta tura batare da ta tsaya shawara ba kamar yadda tayi a farkon shigowarta, Yadda ya ɗago da sauri kalleta yasa ta daskare a tsaye ita bata k'arasa ba bata kuma koma inda tafito ba.
Mamaki ganinta yake a dai-dai wannan lokaci a kuma falonshi da ko yaranshi basu ta6a shigar shi ba. Iyakacinsu su tsaya a falonshi na farko.
Siririyar sallamarta ce ta katse mishi mamakin da yake.
Ya amsa mata cikin taushin murya, sadda kai k'asa tayi ta kasa k'arasawa duk da ya amsa mata sallama.
Ya maida ganinshi akan screen ɗin laptop da ke gabanshi, shiru-shiru bai ji ta k'araso ba ya ɗago kanshi ya ganta tsaye kamar an dasa ta ya kira ta ta hanyar ɗaga mata yatsanshi.
Tafiya take ta doshi wajenshi yayin da kafafuwanta ke neman hard'ewa waje guda. Da taimakon Allah ta iso gabanshi.
k'aramin center table ɗin da ke girke a gabanshi, ta ture tulin files ɗin da ta gani a gefe kana ta aje tray ɗin. Cikin sanyi murya ta ce.
"Barka da hutawa Daddy"
A natse ya ɗago idanuwanshi ya sauke su akan kyakkyawar fuskarta, sunan da ta kira shi dashi ne ya ji shi wani iri duk da ba yau ne karo na farko da aka kira shi sunan ba. Ya d'an waro idanu waje tare da shafo sajenshi.
"Yauwa Sannu"
Ya faɗa cikin izza da k'asaita.
"Nanny ce ta ce na kawo maka coffee"
"Uhmm... thanks!
Ya faɗa a takaice yadda yake furta magana cikin izza da k'asaita yai masifar burgeta, har batasan lokaci da murmushi ya subuce mata ba.
Har ta kai k'ofar fita ta waiwaya ta kalleshi sai kawai ta tsinci kanta da faɗar.
"Daddy iya coffee kake buk'ata Koda akwai wani abu da za ai maka?"
Jin muryarta ya sanya shi sake ɗagowa ya cire medical eyes glass, dake lullu6e da kwayar idanunshi hakan ya bashi damar k'are mata kallo from head to toe, ya lefe jikin resting chair da yake zaune tare da lumsashe idanuwanshi. Sai kawai Miyya ta harde hannuwanta a k'irjinta itama ta shiga kare mishi kallo, tana yaba kyawon halittarshi ganinshi take tamkar saurayi d'an shekara 25 idan ba farin sani kai mishi ba. Ba za ka ce shine ya haifi su Aneesah ba. Duk yadda taso ta dauke idanuwanta daga kanshi kafin ya buɗe nashi idanu hakan ya ga-gareta yana ɗago idanuwanshi shima samun kanshi ya yi da kallon cikin idanuwanta, take wani maganadisu ya tsarga musu a jiki tamkar an jona musu wutar lantarki, da sauri ta runtse idanuwanta da baya-baya ta isa ga bango falon ta jinginar da bayanta gudu kada ta faɗi. Wannan shine karo na farko da ta ta6a samun kanta cikin yanayi irin wannan.
"Daddy in tafi?"
Ta tambaye shi cikin lafazinta mai kama da na mai koyon magana.
Samun kanshi ya yi da girgiza mata kai, a hankali ta baro jikin bango ta tunk'aro shi duk takonta d'aya sai ya ji faɗuwar gaba wanda ya rasa na menene.
Ta kalleshi tana murmushi wanda ya k'ara jefashi cikin rud'ani.
"Daddy me kake so ai maka ne?"
Shiru kawai ya yi yana aikin kallonta turo d'an k'aramin bakinta, tayi wanda bata masan tayi ba muryarta cike da shagwa6a ta ce.
"Daddy kayi magana mana"
Sauri Kiriss numfashi Azaad ya fita daga gangar jikinsa da kyar ya iya dai-daita natsuwarsa, ya zuba mata idanuwanshi wanda suka soma sauya launi.
"Za ki iya