Showing 60001 words to 63000 words out of 91651 words

Chapter 21 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

619

yake mishi bai sake tankawa ba. Kafin su isa gida ya umarci Mr Richard ya tsaya a wani tsadadden restaurant ya yi musu takeaway ɗin abinci ya kuma siyo musu lafiyayyun gasassun kaji.
Koda suka iso gida goma da rabi ta gotta, dai-dai k'ofar main parlor ya kar6i kayan dake hannun Mr Richard. Kafin ya Isa d'akinta sai da ya wuce kitchen ya d'auko plate haɗi da drinks masu sanyi, a kwana nan ya k'ara gyara gidan hatta da foodstuffs akwai, a hankali ya buɗe k'ofa ya tsaya cakk dalili hango ta da ya yi ta jingina bayanta ga bangon d'akin tana sharar barcin abita. K'ayatatcen murmushi ya saki ya ajiye kayan hannunshi akan mirror kana nufi wajenta ya tsuguna yana kallon innocent face ɗinta yayin da zazzafar soyayyarta ke k'ara huda sassan jikinshi, ko zai kwana anan yana kallonta ba zai gaji ba. Yatsanshi yasa yana zagaye tattausan lips ɗinta suna d'aya daga cikin halittar jikinta da yake masifar so. Can cikin barcinta mai dad'i ta ji ana mata tafiyar tsutsa a le66e tai sauri buɗe idanuwanta tass...akan kyakkyawar fuskarshi, tasake lumshe idanunta masu cike da barci k'ok'arin rabata da hijabin jikinta da yake yi yasa ta sake buɗe idanuwanta. Cikin mayen barci ta ce.

"Daddy ka dawo?"

"Eh....my pretty ki yi hak'uri na bar ki da yunwa tashi ki ci abinci.

"Daddy barci nake ji ka ajiye abinci nan da safe zan ci.

"Haba.... Prettyn Daddy kina so yi min sakaci da lafiyarki ki d'aure ko d'an kaɗan ne ki ci.

Ya k'arasa magana dai-dai ya cire mata hijab, ya ajiye shi a gefe ya kamata ta mik'e tsaye sai lokaci ya lura da rigar jikinta saura Kiriss numfashinsa ya fita daga gangar jikinsa, ba k'aramin namijin k'ok'ari ya yi ba da ya samu ya dai-daita shi. Akan resting chair ya zaunar da ita ya d'auko abinci ya juye a plate, yatsine fuska tayi kafin ta ce.

"Banaso ci abinci Daddy ka bani tea ya isa ko fresh milk"

Fresh milk ɗin ya d'auko ya zuba mata a cup ya dinga bata a baki yana haɗa mata da kazar amaryaci sosai taci har dasu gyatsa, ya kalleta ya yi gyaran murya ya ce.

"Tashi ki je ki yi brush da alwala ki zo ki kwata.

"Haba Daddy wane irin brush da dare nan?"

Ta tambaye shi tana tura baki.

"In ba za ki iya zuwa bathroom ɗin ba, bari na zo na kai da kaina"

Yana dasa aya ta zabura da sauri ta tashi, koda ta fito ba shi cikin d'akin ya fita cikin sauri ta haye gado, ta lullu6e jikinta da duvet fuskarta kawai ta bari a buɗe ta lumshe idanuwanta, k'amshin turarenshi da ta shak'a ya ba tabbaci dawowar shi ta ware idanunta tana kallonshi, ya sauya kayan jikinsa zuwa royal blue pyjamas yana zuwa ya ye duvet ɗin da ta rufawa jikinta ya rik'o kafand'unta dole ta tashi zaune.

"Tashi mu yi sallah"

Ya faɗa cikin dakakkiyar murya gudun kada ta kawo mishi wargi ta 6ata mishi dare, gani yadda ya haɗe fuska yasa ta kasa yi mishi gardama bayan su kammala nafila raka'a biyu ya shiga yi mata tambayoyi game da addini cikin natsatsiyar muryarta take bashi amsa.

"Ma-sha-Allah ashe Prettyn Daddy hafiza ce qur'ani ce?"

Ya faɗa yana murmushi wani irin farin ciki yake ji musanmman da tace dashi ta haddace al'qur'ani mai girma.

"Ban zaci kina da ilmin addini mai tarin yawa ba pretty musanmman, idan aka yi duba da yadda ku ka taso a hannu Dadda?"

Murmushi tayi tare da sadda kanta k'asa ta ce.

"Uhm.....shima Dadda tayi ne dalilin kada mu yi sha'awar addini mahaifyarmu, ta datse mana karatun boko a cewar ta garin bokon ne Abbanmu ya auro umminmu sam ba za ta bari tarihi ya sake mai-maita kanshi ba a ganinta idan ta wadata mu da ilimin addini musulunci ba za mu ta6a sha'awa kasancewar tare da mahaifyarmu ba.


Murmushi ya yi tare da danke hannunta cikin nashi a hankali ya shiga massaging tafin hannun nata.

"Allah ya sakawa Dadda da gidan ajanna bisa ga jajircewa da tayi kika sami dinbin ilmin irin wannan.

Turo baki tayi tana gun-guni k'asa-kasa don ita kan bata ga dalilin wannan addu'a da ya yi wa Dadda ba. Matar kullum burinta su mutu.
Mik'ar da ita tsaye ya yi ya cire mata hijab, ya matso ta cikin jikinshi ta yadda babu rata a tsakaninsu ya zagaye waist ɗinta da hannuwanshi wani irin abu yake ji yana ratsa jinin jikinshi yana so ya hak'ura da kusantarta saboda tayi k'ank'anta da yawa ba za ta iya dashi ba a wani 6angare na zuciyarsa yana k'ara azalzalar shi, ya kasa kama makama guda daya kwakwara ya yi ko ya hak'ura ya danne masiffafiyar sha'awarta da ke barazana raba shi da numfashinsa....
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004


31...


Da taimakon Hafsat shinkafi Salima ta iya kawo kanta flat ɗinta. Nanny Lacey kawai suka tararda a main parlor inda Allah ya taimake ta su Aneesah suna rooms ɗinsu. Koda ta shiga bedroom ji take yi kamar numfashinta zai fita ne daga gangar jikinta. Hafsat ta d'auko rubar ruwa faro mai sanyi ta 6alle murfi ta kafa mata a bakin cikin fitar hayyaci ta dinga tsuk'a sai da tasha fiye da rabi kafin Hafsat ta ciro rubar daga bakinta ta maida murfi ta rufe. Tayi ajiyar zuciya kafin ta ce.

"Salima idan kina so aurenki dole ki bi duk wata doka da order da Azaad ya kafa miki, ni dai ina k'ara shawarta ki da d'aura ki nemi sani akan addini kin ga ko sallarki ba za a rasa kurakurai ba a cikinta, ki sani ba wayewa bace zama cikin duhun jahilci, ki godewa Allah yana sonki da rahama shiyasa ya kawo sabanin saki tsakaninki da Azaad domin ki yi amfani da wannan damar ki gyara gobenki da kin mutu a wannan hali da kin shiga uku.

Ajiyar zuciya Salima tayi kafin ta ciro kanta ta kalli Hafsat cikin muryarta wacce daga ji ta kasan taci kuka har na fitar hankali ta ce.

"Banida bakin gode miki Hafsat ke k'awa ce tagari wacce za a sha matuk'ar wahala kafin a sami ta biyunki. Da ace tun farkon Ina d'aukar shawara da nasiharki da ban tsinci kaina a wannan yana yi ba.

"Ba komai Salima aminci da ke tsakaninmu ya zarce yadda kike tunani, inaso ki sa aranki no matter how ina tare da ke.
*** **** *****
A kowace dak'ik'a k'ara rura mishi wutar sha'awarta ake yi, kyakkyawar runguma yai mata cikin jikinshi yayin da bugun zuciyarsu ya tsananta sai faman sauke numfashi suke yi, cikin fitar hayyaci ya lalla6o zip ɗin rigarta ya yi zipping ɗinta ta faɗi k'asa. Hannuwanshi suka dinga kai, da komo a sassan jikinta musanmman k'irjinta da suka fi zauta shi sosai tsoro ya lullu6e ta 'yar k'aramar kwakwalwarta ta kasa dauka sabon darasi da Daddynta yake koya mata. Yadda jikinta ke rawa yasa ya ɗagata cakk ya shinfid'eta akan gado ya yi mata rumfa da faɗaɗɗen k'irjinshi ya haɗe bakinsu wurin d'aya, sosai ya yi romancing ɗinta kafin da kyar da sudin goshi ya samu ya dan kutsa ta kasancewar k'ofar k'arama ce sai dai sannun a hankali yake bi da ita saboda shi kanshi yana tausayawa k'ananu shekarunta, a hankali kake ji fitar sautin kukanta, Azaad bai barta ba saida ya kauda matsalarshi ta wata da watani. Wata irin natsuwa yake ji tana shigarshi rungumeta yai cikin jikinshi sai sauke numfashi yake akai-akai Miyya kuma sai rera kuka take, a hankali yake shafar gadon bayanta yana hura mata iskar bakinshi cikin kunneta na dama tayi lamo tana sauke ajiyar zuciya alamar taci kuka.
Bayan Hafsat shinkafi ta wuce Salima ta lalla6a ta shiga bathroom tayi wanka, simple makeup tayi tasaka sleeping gown mai jan hankali ta nufi part ɗin Azaad a tunaninta yana bathroom, kasancewar bata ganshi a parlor ba kuma baya cikin bedroom sai tai zaton ya shiga bathroom ta nemi gefen gado ta zauna. Wasa-wasa ba Azaad babu labarinsa har ta fara gyagyadi, jikinta a sanyayye ta tashi ta nufi k'ofar bathroom ta buɗe nan take taji mashahurin faɗuwar gaba kafafuwanta suka k'asa daukarta, jiri ya kwasheta tai sauri dafa bango wani irin abu take ji mai nauyi ya tokare mata zuciya, kasa maida kanta d'akinta tayi a wahale ta hau gadonshi ta kwanta ta lumshe idanuwanta tare da dafe k'irjinta. Bata k'ara shiga tashin hankali ba saida taga karfe uku dare ta buga Azaad bai dawo ba. Wasa-wasa har asuba Salima bata ga Azaad ya dawo ba. Hankalinta ya k'ara tashi fiye da farko. Saboda tasan ba halinsa bane kwana waje muddin yana gari.
Barci sosai suka yi Azaad na farin ciki Miyya Kuma na wahala da rashin sabo koda Azaad ya falka har karfe bakwai ta gota, ya manta rabon da ya yi missing sallar asuba. Idanuwanshi ya sauke akan kyakkyawar fuskarta tausayi da sabuwar k'aunarta suka dinga huda sassan jikinshi, a hankali ya sauke kanta bisa pillow da sauri ya shiga wanka ya fito d'aure da towel ya buɗe k'ofa ya nufi d'akinshi yasa white jallabiya ya yi sallah. Duk abin da yake akan idon Miyya basan cewa tun lokaci da ya janye jikinshi daga nata ba ta falka, tsananin kunyar da take ji ne ya hanata nunawa. Tana gani ya fice ta tattaro bedsheet ta suturta jikinta dashi ta shiga k'ok'arin saukowa daga gado, jin tayi tamkar an d'aure mata kugunta da kafafuwanta da igiya, duk lokaci da tai yunk'uri tashi ta ji ta kasa, kuma ko kaɗan bata so ya dawo ya tararda ita a haka ta dafa bango cikin tsananin azaba ta tashi tana bin bango saura kaɗan ta isa ga k'ofar bathroom, taga an turo k'ofa cikin sauri ta waiga bayanta ta haɗa idanu dashi.

"Subhanalillah......!

Ya faɗa cikin sarkewar harshe cikin sauri ya iso wurinta kafin ya k'araso ta sulele k'asa ta sunne kanta cikin bedsheet ɗin jikinta. Yana zuwa d'auketa yasa k'afarshi ya tura k'ofar bathroom.

"Dan Allah Daddy ka sauke ni zan iya tafiya da kafafuwana"

Murmushi kawai ya yi, ya zaunar da ita akan toilet seat ya haɗa ruwa masu zafi cikin bathtub, sai magiya take mishi ya fita za ta iya da kanta banza ya yi mata sosai ya gaggasa mata jikinta, ita kanta ta ji dad'in hakan ya fita ya barta ta tsalkakke jikinta, kanta a k'asa ta fito Azaad ya ɗago daga dambe da yake da bedsheet, da sauri ya aje pillowcase ya nufo ta, ya kamata gefen gado ya zaunar da ita ya mik'a mata ash colour abaya cike da kunya ta kar6a daga zaune da take ta zura rigar tasa hijab ya shinfid'a mata praymat, tana sujadda ya fita.
Koda ya dawo dauke da mug ɗin tea ta gama sallah har ta koma bisa gado ta kunduddune kanta, kunyarshi take ji matuk'a shi kuma yak'i ya fahimta. Bata ta6a tsanmani irin wannan abun zai shiga tsakaninsu ba. Kusa da kanta ya zauna cikin taushin murya ya ce.

"Prettyn Daddy tashi kisha tea yanzu nan zan kira doctor ta duba min ke Allah yasa ban ji miki ciwo ba?"

Sunan doctor da ya anbata yasa tai sauri janye hijabin da ta rufe fuskarta dashi, cikin kad'uwa take kallonshi, kafin ta fara hawaye cikin k'aramin sauti ta ce.

"Daddy please karka kira doctor za ka tona mana asiri ne.

Murmushi mai sauti ya yi ya matso ta jikinshi kana ya ɗago ha6arta, tai sauri runtse idanuwanta ya sumbace cheeks ɗinta.

"Lallai Prettyn Daddy kurciya ta miki yawa in bada haka miye abin tono asiri sai kace wanda suka aikata zina, ko kin manta ke ɗin mallakina ce halak-malak sai da na biya sadaki kafin Baffanki ya daura mana aure.

"Duk da haka Daddy banaso ka kira doctor in-sha-Allah zan warke in ka kafe lallai sai ka kirata wallahi zan yi ta yi maka kuka"

Ta k'arasa magana cikin shagwa6a6iyar murya, dariya ya yi tare da jan karan hancinta.

"To shikenan ba zan kiranta ɗin ba amma tashi ki sha tea, na ba ki pain killer ki sha sai ki yi barcinki kin ji my pretty?"

Kar6a mug ɗin tayi daga hannunshi ta shanye tass dama yunwa take ji kamar an yashe mata hanjin cikinta, pain killer ya bata tasha kana ya kwanta tare da ɗora ta a k'irjinshi ya rungumeta tamkar zai mayarda ita ciki a haka barci mai dad'in gaske ya d'auke su.
Har gari waye Salima ba ta ga Azaad ya dawo ba ta kira wayoyinshi duka a rufe nan take hankalinta ya k'ara tashi, ba dai saboda ita Azaad ya bar gida ba. Hankalinta ya kasa kwaciya ta kira direbanta ya bata number direbanshi Mr Richard ta kira shi da ya d'auka ya sharara mata k'arya da cewa Azaad yana meeting jiya kuma a gida ya kwana saidai ya kai dare sosai kafin dawo da zarar ya fito daga meeting zai faɗa mishi ta kira.
Tun jiya da Ahmadu ya ga Miyya a hospital ya kasa samun natsuwa da kwaciyar hankali da ya rufe idanuwanshi ita yake gani tsaye sanye da dogon hijabi tana kallonshi da idanuwanta masu kama dana magge, yau kuma mafalkin ya yi ta rutsa shi da shar6e6iyar wuk'a da tana zuwa ta yanke shi a datse hannunshi na dama, ta kuma kashe mishi gargadi da muryarta mai matuk'ar ban tsoro muddin bai daina bin Azaad ɗinta da sharri ba sai ta kashe shi. Cikin ihu da kururuwa ya falka daga mugun mafalki da yake yi abin mamaki sai ya ga jini yana zuba daga hannunshi shatata...kamar an buɗe famfo, da gudu ya banke k'ofar d'akinshi ya fito yana ta kurma ihu matanshi da yaranshi suka yi dafifi su na kallon ikon sai ya kai harabar gida ya sake dawowa cikin gida da gudu, haka ya dinga yi kamar zautatce da taimakon maigadi da makwacinsa suka kama shi a ka saka shi mota zuwa asibiti.
Azaad da Miyya barcinsu suka sha sosai sai misali sha biyu da rabi Miyya ce ta fara falkawa saida ta k'arewa kamilalliyar fuskarshi kallo, sannu hankali ta cire jikinta daga nashi, sannan ta sauko daga gado tayi mik'a tare da salati cikin zuciyarta.
Cikin dingishi ta shiga bathroom, ta haɗa ruwan zafi kamar yadda ta ga Daddy d'azu da safe ya haɗa mata saida ta gaggasa jikinta sosai kafin tayi wanka da liquid soap mai k'amshin strawberry. Koda ta fito bata ga Azaad ba dama akan idonshi ta falka.
A natse ta shirya kanta cikin d'aya daga cikin gowns ɗin jiya ta sauka mata iya cinyoyi. Ta tattare gashinta da ke da sauran dashin ruwa ta d'aure da hairband. Tana fesa turare ya shigo d'akin da sallamarshi, ta juyo cike da kunya ta zuba masa idanu a ranta take raya yanzu shikenan ita dashi sun zama abu d'aya?" Tai saurin kawar da tunaninta ta hanyar cewa.

"Ina kwana Daddy?"

Ta faɗa tare da d'an runsuna, ya matsa jikinta ya rungumeta ya ɗora kanshi a kafad'arta, fuskarshi cike da annuri ya ce.

"Lafiya qalau my pretty ya jikinki hope babu inda yake miki ciwo?"

Cikin sanyi murya ta bashi amsa ta hanyar faɗin.

"Al-hamdu-lillah! Akwai zafi saidai ba kamar d'azu da safe ba. Shima zuwa anjima in nasake shiga ruwan zafi zai daina gaba ɗaya.

Murmushi ya yi yana shafar kumatunta ya yabawa jarumtar ta matuk'a, bai ta6a tsanmani za ta iya d'auke shi ba, ya zaci duk ranar da ya kusanceta sai ya danganta ta da asibiti sai gashi ta tashi garau, har tana tafiya da kafafuwanta. Sai yanzu ya fahimci abin ba daga shekaru bane.

"Daddynki bai kyauta ba my pretty duk ya bi ya wahalar min da ke, yanzu faɗa min me kike so ki ci na kira waya akawo miki?"

"Duk abin da Daddyna yake so"

Tayi magana tana sanda kanta k'asa d'an siriri hannun rigarta ya ja yana murmushi jin kanshi yake tamkar bashi bane kamar an sauya shi daga Azaad Junaid ɗin da yasani a baya. Yana rungumeta da ita suka fito zuwa parlornshi, ya zauna tare da zaunar da ita a gefenshi hannuwanta ya dank'e cikin nashi with serious face ya ce.

"Ba zan 6oye miki ba Aslamiyya ina jin soyayyarki wata kyauta ce ta musanmman agareni, da ban ta6a samun kwata-kwacin ta ba a rayuwarta. Da farko na zaci aurena da ke ba mai ɗorewa bane, bansan ya aka yi ba na waye gari dumu-dumu a soyayyarki, har ji nake tamkar akanki na fara sani kalmar so. Farin ciki baya ɗorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, saboda haka ki sa aranki a kowane hali na tsincin kaina ba zan ta6a mantawa dake ba. Aslamiyya kin zama jini jikina, bugun zuciyata na kan raba dare ina rok'on Allah ya haɗa ni da mace tagari wacce za ta goge min bakin ciki da na share shekaru a ciki sai gashi Allah ya kar6i addu'ata ya bani ke. A yanzu babban burina a duniya shine kasancewa tare da ke har abada wannan kaɗai ya isheni rayuwa.

Har ya dasa aya a zancesa bata d'auke idanuwanta daga kanshi ba, maganganunshi sun ratsa jinin jikinta su bi bargo da jijiyoyin magudanar jininta, ta kuma yi musu muhalli na musanmman ta adana su cikin zuciyarta. Bata ta6a tsanmani za ta sami dadd'ad'an kalaman soyayya irin wannan daga bakinsa ba. Musanmman da tayi duba da yana yin shekarunsa a tunaninta ya riga da ya gama mallakawa Madam Salima su ashe da akwai raguwar su ba duka ya bata ba ya rage mata saura.
Kunyarshi take ji sosai ba za ta iya mayar mishi da martani kalamanshi ba amma tayi alk'awali duk lokaci da kunyar ta rage za ta bashi mamaki, sai kawai ta matsa tasake haɗe tazarar dake tsakaninsu ta ɗora kanta a kafad'arshi ta lumshe idanuwanta, hannu yasa dinga shafa sumar kanta, yana da tabbaci kunyarshi da take ji ne ya hanata magana shiyasa ko kaɗan shirunta bai dame shi ba. Throughout bai fita ko nan da k'ofar gida ba yana manne da ita wayoyinshi duka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login