Showing 90001 words to 91651 words out of 91651 words
zai fitarda ni a cikinsa sai mutuwa.
Farin cikin sosai kalamanta suka haifar masa baisan sanda yasa hannunwanshi duka biyu ya zagaye waist d'inta ba. Suka sa dariya.
Farin ciki suke ji sosai kamar ba su ta6a shiga 6acin rai da bak'in ciki ba.
Mr Michael yana baro asibiti ya nemi wani hotel nesa da gari ya kama d'aki, saida dare ya raba tsaka irin around 3 o'clock ya fice daga hotel d'in kaitaye babban kamfanin Madam Salima ya yi wa tsinke, ya koma can bayan company ta yadda masu gadi ba za su ganshi ba. Ya zagaye lungu da sak'o na wuri da fetur ya cilla lighter akan idanunshi company ya kama da wuta, ya dinga cilla gallon d'in fetur a ciki yadda wutar za ta k'azanta. Ai kuwa ta k'azanta fire alarm sai kararawa yake yi kafin fire service su zo company ya k'one kurmus! Toka kawai yai saura.
A takaice saida Mr Michael ya bi duk wani kamfaninta da manya-manya malls ya k'ona ya kuma tsire abinsa.
Lokaci da labari ya riske madam Salima take furucin Mr Michael ya dawo mata, shi kenan duk dukiyar da take tink'aho da ita wacce tai shekaru tana fafutukar nema, tana tarawa ta kuna wofitar da igiyoyin aurenta da yaranta akanta cikin rana d'aya ta rasa ta. Nan take ta yanke jiki ta fad'i inda Allah ya taimake ta tana cikin asibiti da sai abin yafi muni rabin jikinta ya daina aiki kuma a tsagin da hannunta ya karye. Madam Salima ta dawo abin tausayi ita da matatciya basu da ban-banci suna tana raye ne kawai sai lokaci mahaifiyyarta da 'yan uwanta suka gano aurenta ya mutu har Azaad Junaid ya yi aure, ba k'aramin bakin ciki haka suka yi mata ba domin sun sa shi kenan ta rasa komai nata.
Watani biyu Miss Gambella tayi a Nigeria kafin ta koma Australia da ta tashi tafiya da twins da Dadda ta taho da su anan twins za su ci gaba da karatunsu yara sun dawo 'yan gata gaba da baya.
Azaad da Miyya rayuwa ta masu dad'i basu da sauran wata damuwa, ko a gaban waye bata jin kunya nuna mishi kulawarta da soyayyarta.
Cikin hukunci ubangiji suna kammala final exams ta fara laulayin ciki.
Azaad ya yi musu visa daga ita har yaranshi da Kakarshi Jadda suka nufi k'asar Australian kafin su wuce sai da suka biya ta gidan iyayyen Madam Salima inda take jinya har yau ba wani sauki saboda bata magana bata kuma gane kowa. Aneesah tasa kuka a duk lokaci da ta kawowa Madam ziyara da kuka take komawa gida, ita kanta Miyya bata zaci jikin nata ya yi tsananin har haka ba tun daga lokaci da kwanta jinya bata ganta ba sai yau daga Miyya har Jadda tsohuwar mai ran karfe kuka suke taya Aneesah gani sun taro suna kuka yasa Airah ta shiga tayasu baby Ahlam kan batasan wainar da ake toyawa ba.
Gani haka yasa Azaad ya umarce su da su tashi su tafi kada su yi missing flight.
A cikin dare jirginsu ya yi landing Miss Gambella ta tura tsadaddun motoci na alfama aka dauko su daga airport, tarba ta musanmman aka yi musu a gidanta lokaci da Miyya ta ga Dadda zaro idanuwa tayi cikin kad'uwa ta ce.
"Dadda ina tsufanki gaba d'aya naga kin canza min kin dawo yarinya d'ayya sharaf!
Gaba d'aya aka sa dariya Dadda ta shiga matsar hawaye tare da fad'in.
"Bari kawai Aslamiyya ni kadai nasan irin kulawar da nake samu daga wurin Roseline, koda Usman yana duniya iya abin da zai yi min kenan.
Da sauri Miyya ta rungume Dadda tana dariya.
Wata irin rayuwa mai cike da zallar farin ciki suke gudanarwa a Australian kasancewar Azaad Junaid yana da gida anan shiyasa suka saki jiki gani yadda suke jin dad'in garin yasa Azaad ya yanke shawarar su zauna, zama na din-din. Hakan ba k'aramin farin ciki Miyya da su Aneesah suka yi ba. Rayuwa ta dawo musu sabuwa duk wani bak'in ciki da kunci da Azaad Junaid yake ciki a yanzu ya kau, a Koda yaushe ka ganshi yana ciki walwala da farin ciki.
Cikin Miyya na da wata uku aka yi mata scanning likitoci suka tabbatar mata da 'yan uku ne{triplets} ita kan abin tsoro ya bata yayin da family d'inta ke murna da farin ciki musanmman uban gayya tun a asibiti ya kira Hakeem ya sanar mishi tun daga lokaci kulawar da yake bata ta linka ta baya linki-ba-linki. Hakan yasa ya dauko Nanny Lacey ita ma ta dawo Australia da zama.
Idan ka ga yadda ciki Miyya ya yi girma ya rinjaye ta ga ta dama tana da manya nonuwa sai abin ya k'ara armashi {lol} cikinta yana da wata bakwai a duniya cikin dare nakuda ta taso mata suna zuwa asibiti nan take aka yi mata cs aka ciro Babys dukkansu maza, ranar kamar Azaad zai zare saboda murna da farin ciki a ranar ya yi wa Hakeem kyauta ta musanmman wacce tai matuk'ar girgiza kwakwalwar da tunaninsa ya mallaka mishi kamfanoninsa har guda biyu d'aya a China do d'aya kuma a gida Nigeria sai tangamemen gida aljannar duniya a babban birnin tarayya Abuja Hakeem har da kuka sai da ya yi.
Baffa Sani ma ba a barshi a baya ba shima Azaad yasa an rusa gidanshi a sake gina mishi na zamani ya bashi mota ya kuma ba yaranshi biyu maza aiki a d'aya daga cikin manyan companies d'inshi.
Ranar suna yara suka ci sunan Junaid shine babba suna kira shi da Ansar sai Usman me sunan mahaifin Miyya shi Kuma suna kira shi da Affan sai Abdul-Hakeem suna kira shi da Abdul.
Yaran sun tashi cikin gata da kulawa ta kowa ne 6angare washe gari sunansu ne miss Gambella ta kar6i musulunci karki so kike ga farin ciki wurin wad'annan iyalin, Dadda ta fi kowa murna don har da kukanta musanmman da tuna da furucin da mahaifin Miyya yake mata a koda yaushe.
"Ki yi hak'uri Dadda ki kar6i Roseline a haka ba Wanda ya isa ya shiryarda wanda Allah bai shiryarsuwa ba, idan Allah yaso ta da shiriya wata rana za ki ga ta kar6i musulunci.
Sai gashi Usman baya duniya amma furuncinsa ya zama gaske. Inda Roseline ta tashi daga sunanta ta koma Aminatu.
A gida Kuma Nigeria madam Salima ba abin da ya sauya kullum ciwonta gaba-gaba yake yi lamarin nata har ya shafi kwakwalwar ta. Duk d'an abin da ya rage na daga cikin dukiyarta ya k'ari wajen nema mata magani.
Triplets na da shekaru hudu yayin da Miyya tana shekarar k'arshe a karatunta.
Ta sake haihuwar d'a namiji yaci sunan Muhammad Azaad suka yi masa laqabi da little Daddy.
Dama burin Azaad Junaid kenan ya tara iyali masu yawa sakamakon shi kadai mahaifiyarshi ta haifa, yayin da ita ma ita kadai Jadda ta haifa shiyasa bashida buri da ya wuce a haifa masa 'ya'ya, duk wani abu da Azaad Junaid ya rasa Saida ubangiji ya dawo masa da madadinsa. Shiyasa a koda yaushe cikin godiyar ubangiji yake.
Aneesah ta kammala karatunta ta zama cikakkiyar likitan yara, Airah Kuma tana shekarar k'arshe a secondary school.
Lokaci da Aneesah tayi graduation ta nemi alfarma a wuri Daddy za ta je Nigeria ta duba mommy bai hanata ba, washe gari ta d'aga sai Nigeria a cikin kwanaki da tayi a Nigeria cikin hukunci ubangiji Madam Salima tafara samun sauki tafara gane, mutane musanmman Aneesah don har tambayar ta Airah da Ahlam tayi.
Hakan ba k'aramin haifar masu da farin ciki ya yi ba ashe saukin tafiya ne a cikin dare ciwonta ya tashi tun kafin su isa asibiti Madam Salima ta kar6i kiran mahalincinta.
Aneesah ta sha kuka kamar za ta yi hauka sai aka rasa tsakaninta da Hafsat Shinkafi wacce tafi shiga tashin hankali, saboda tun lokaci da madam Salima ta kwanta jinya Hafsat Shinkafi take tare da ita har izuwa yau da ALLAH ya kar6i ranta.
Sai a ranar sadakar uku Azaad Junaid ya iso Nigeria tare da iyalinsa.
Saida aka yi sadakar bakwai sannan suka koma Australia.
Haka suka ci gaba da gudanar rayuwarsu cikin tattalin juna had'i da zallar farin ciki, little Daddy yana da shekara biyar a duniya sannan Miyya ta sake haifar d'iya mace koda ta haihu Azaad bayanan ya tafi wani business trip a Ukraine.
Koda ya dawo har Miyya da Aneesah sun rad'awa yarinya suna Salima little mommy, bai yi mamaki ba don Miyya ta yi wa Madam Salima takwara saboda yasan tsananin kirkinta da kawaicinta za ta aikata fiyye da hakan.
A lokaci Miyya da Aneesah suka kirkikkira kungiya ta tallafawa marayu da gajiyyayu mai sunan Madam Salima foundation, sosai kungiyar tasu ke ba da tallafi ga mabuk'ata su yi hakan ne da nufi Allah ya kai haske kabarin Madam Salima.
Miyya sanye cikin had'add'u riga da wando na barci masu masifar jan hankali tasha kwalliya ta ban mamaki kamar ba mai jego ba, sai uban k'amshin take zubawa. Kaitaye d'akin Azaad ta nufa tana tura k'ofa ta hango shi kwance akan gado yana ganinta ya mik'e zaune ya mik'a mata hannunshi ta kama, ya fizgota ta fad'a jikinshi yai mata kyakkyawar runguma, kana ya d'ago fuskarta ma'a6ociya kyau ya had'e bakinshi da nata yayin da ita ma cikin kwarewa ta shiga taya shi, gani yana k'ok'arin tsallaka border yasa ta shiga yi masa ihu.
"Wayyo Allah na shiga uku please Daddy ka daina jego nake yi, banaso Dan Allah ka bari har nayi arba'in.
"Ba arba'in ba sittuna za ki yi ni fa yau sabon ango ne ki yi ihu iya k'arfinki ba Wanda ya isa ya canza hakan...
Kafin ta an kara har ya yi nasarar rabata da kayan jikinta duka ta dawo naked ya kashe bulb nan take d'akin ya guraye da duhu daga nan nace......
*TAMMAT BI-HAMDILLAH*
MA-SHA-ALLAH DAMA DUK ABIN DA YA YI FARKO CIKIN HUKUNCI UBANGIJI YANA DA K'ARSHE NI MA ANAN NA KAWO K'ARSHEN WANNAN LABARI MAI TAKEN AZAAD JUNAID the young Billionaire KURAKURAI DA KE CIKINSA INA ROK'ON ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA YA YAFE MIN ABIN DA NA FAD'A DAI-DAI ALLAH YASA YA AMFANE NI DA MUSULMI BAKI D'AYA.