Showing 9001 words to 12000 words out of 91651 words

Chapter 4 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

609

buk'atarsa ta biya. Shine naga dacewar mu kai masa ziyara watakil adace ya kawar mana da Azaad.

"Haba Yaya har yaushe za ku gano aikin bokaye nan duk k'arya da yaudara ne?" Kawai ku bar min wuka da nama ku ka aiki da cikawa 'yan ta'adda za nemo su yi mishi yanka rago.

Hasheem ne ya yi magana yana hura hanci duk cikinsu shine mai k'anana shekaru.

Alhaji Abdallah ne ya kar6e zance ta hanyar faɗin.

"Kai dallah rufe mana baki idan har kai ba ka da hankali mu ba sakakkaru bane irinka, muddin muka sa aka kashe Azaad ta wannan hanya jami'an tsaro ba za su yi shiru ba, za su tsananta bincike kasancewar Azaad babban mai kud'i. Nan take za a gano mu. Saboda haka mu gwada zuwa wajen bokan ya kashe mana shi."

"Shikenan Babban Yaya gaba ɗayan mu, mun amince gobe da sassafe sai mu shirya mu tafe k'auye da boka yake.

Da wannan shawara suka kawo k'arshen secret meeting ɗin nasu.
**********************
"Aneesa ina so ki bani aron kunnenki, ki saurare abin da zan faɗa.

Azaad ya yi magana fuskarshi a daure tamau..

"Tam Daddy!

Aneesa ta faɗa tare sadda kai k'asa tana wasa da wayar hannunta.

"Daga yau mai kama da rana ta yau Kar ki sake bari na kama ki da laifi rashin ɗa'a a school ke ba iya school ba ko a gidanan naji labari kin ma wani daga cikin housemaids rashin kunya, za ki sha mamaki irin hukunci da zan zantar akanki. A dalili abin da kike yi aikatawa ga Airah nan ta fara koyi da halinki. Haka ku ke so rayuwarku ta dinga tafiya a baud'e?" Idan har ita mahaifiyarku bata damu tarbiyyarku ba, ni hakke ne da ya rayata a wuyana, da izzini ubangiji sai inda k'arfina ya k'are."

Tun daga lokaci da ya fara magana har ya dasa aya bata ɗago ba jikinta sai rawa yake yi, saboda duk iya shegenta tana bala'in tsoran mahaifinta. Ta ɗago kanta da kyar bakinta na rawa tace.

"Kayi hak'uri Dadda in-sha-Allahu na daina ba zan k'ara ba.

"Da yafi miki.

Ya faɗa a takaice kana ya juyo kan Airah wacce tuni tsoro ya gama bai-bayeta, dama tasan za a yi haka daga zarar ya gama da Aneesa kanta zai dawo.

"Ke kuma da kike koyi da Aneesa miye abin burgewa a cikin halayenta da har za ki koya?" To bari ki ji duk irin hukunci da zan zantarwa da Aneesa kema irinshi zan maki.

A matuk'ar tsorace Airah take kallon shi, har idanuwanta sun fara kawo ruwan hawaye.

"Daddy Don Allah ka yi hak'uri ka yafe min sharrin shaidan ne.

Ta k'arasa magana kamar za ta fashe da kuka, ya nemi kusa da ita ya zauna, a natse ya shiga yi musu nasiha ya kuma saka Aneesa ta rubuta apologies letter gobe ta kai school ɗinsu, sai around 9:40pm ya fito daga d'akinsu.
Ya sauya kayan jikinsa zuwa na barci, ya dauko laptop ɗinshi ya yi switch on yana da online meeting sai misali k'arfe 11:30pm ya kammala yana cikin rufe laptop ɗin ya ji horn tara da k'arar buɗe gate, da sauri ya baro daga wajen zaman shi ya ye labulle widow ya lek'a ya hango madam Salima ta nufo cikin gida tana tafiya kamar bata kashi. Sosai ran Azaad ya 6aci yanzu fissibillahi matar arziki ce za ta fita tun safe sai dare za ta dawo. Zance na gaskiya ya kamata ya yi wa kanshi karatu ta natsu, idan har Salima ta kafe ba za ta bar aikinta ba. To tabbas kuwa zai bi shawarar Abdul-Hakeem da Jadda ko don saboda rayuwar 'ya'yanshi. Ya murzawa k'ofar d'akinshi key ya kwanta yasan ba nemanshi za ta yi ba. Da safe ma ta ri ga shi fita sosai hakan ya k'ara harzuk'a shi duk da hakan ba bakon abu bane a wurinshi. Cike da haushinta ya isa company.
*****************
Koda safiya ta waye hannun Aslamiyya ya kumbura sumtum sai azabar ciwo yake mata, daren jiya ko runtsawa bata yi ba. A haka Dadda ta saka ta aikin gida Amrah kuma tai sammako bari gida ta tafi nemo musu abin karin kumallo. Koda Aslamiyya ta fito daga band'aki ta sace jiki ta fita. Tsintsiya ta dauko da ɗayan hannunta mai lafiya ta shiga sharar tsakar gida Dadda kuma ta kasa ta tsare sai antaya mata zagi take.

"Yi maza ki kammala shara ki zo don uwarki arniya ki min wanke-wanke don ni babu ruwana da ciwon hannunki shegiya yarinya tsatso kafurai.

Sosai zagi ya k'ona mata rai duk ta saba jin iri-irinsa daga bakin Dadda amma zuciyarta ta kasa sabawa, duk lokaci da tai musu irin zagin sai zuciyarta ta buga. Kuka take yi har hawayenta su na diga a floor.
Da Amrah ta fito daga gida yau bata je super market ɗin jiya ba, sai ta nufi wani provision store kasancewar safiya ce babu mutane sosai a shagon sai kawai ta nemi gefe ta tsaya, kamar tana jiran wani sai kawai taga mai shagon ya fito da sauri da waya a kunnenshi tana gani ya fita ta afka shago ta dauko k'aton bread ta cusa cikin hijabinta, dai-dai mai shagon ya shigo ashe lokaci da ta shi ga shagonshi ya ganta shiyasa ya dawo.


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_


Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske writers Association.

Top Ten Takun Haske Batch:A

Free Page

5....


Koda Aslamiyya ta kammala shara zuwa lokaci ta jigata matuk'a, ga yunwa ga azabar zogi da hannunta ke yi kamar zai tsinke. Duk da halin da take ciki bata fasa tattaro tulin wanke-wanke wanda ba na Dadda Kaɗai bane hadda na surukanta. Tun daga lokaci da ta fara wanke kwanuka har ta kammala kuka take yi idanuwanta sun yi luhu-luhu.
Amrah tai ido biyu da mai shago da ya tare k'ofar fita, gabanta yai mummuna faɗuwa gani yadda mutume ya murtuk'e fuska ya haddasawa cikinta murd'awa.

"Ke! uban me ya shigo dake shagona?"

Yadda ya daka mata tsawa yana zare ido ta daburce ta rasa abin faɗa jikinta ya fara mahaukacin rawa. Gani haka ya fahimtar dashi bata da gaskiya musanmman da ya shiga K'are mata kallo ya ga hannuwanta cikin hijabinta tana kiciniya 6oye wani abu.

"Menene a cikin hijabinki me kika sata fito dashi don ubanki?"

Kusan tare ya watsa mata wad'annan jarin tambayoyi, tsora ne ya k'ara lullu6eta,ta tabbata yau dubunta ya cika, mai kwatar ta hannun wannan mutume mai zubin samudawa sai Allah. Ta shiga yawo da idanuwanta lugu da sako na shagon ko Allah zai sa taga hanyar fita kafin ta gama dube-dubenta ta ji an finko ta da k'arfi bai tsaya wata-wata ba ya cire mata hijab sai ga bread sakade a hamanta ta. Ta saki bread ɗin ya fado k'asa.

"Don Allah malam kayi hak'uri wallahi ba halina bane yunwa da rashin gata yasa ni na sata maka bread...

Tun kafin ta k'arasa magana ya kifa mata mari, wasu jajayyen taurari suka ma-maye ganinta cike da rashin imani ya shiga jibgarta kamar ya sami sa'anshi. Ya sukunce ta ya fito da ita waje yana mata ihun 6arauniya kafin kace kwa6o wurin ya cika da mutane yara 'yan makaranta sa'o'inta sai kallonta suke yi. Baki da hancinta na zubda jini Amrah bata k'ara shiga tashin hankali ba sai da taga mutume yana faɗawa mutane wai ko jiya ya gannta ta shigo mishi shago tana fita, ya nemi kud'insa dubu d'ari ya rasa saboda haka ta fito mishi da kud'insa ko ya mik'a ta hannun 'yan sanda. Sosai take kuka tana mishi magiya mutane da ke kallo abin da ke faruwa sai la'anta ta suke yi, gata k'aramar yarinya ace tana sata. Tana ji tana gani ya kwashe ta zuwa police station, tana kallonshi ya ba wa 'yan sanda statement ɗin k'arya wai ta sace mishi dubu d'ari.
Ba tare da duba da k'aranci shekarunta ba suka jefa ta bayan kanta, cikin muryarta da ta disasshe saboda kuka tace.

"Ku dubi girman Allah ku yi min rai wallahi azim ban d'auki kud'insa ba. Biredi na sata kuma tun a shago na ajiye mishi abinsa...

"Ke! Rufe mana baki 6arauniyar banza da wofi daga ni idanuwanki za ki aikata, iri-irinku ne idan kun girma ku ke zama shararrun 'yan ta'adda.

Wani dogon d'an sanda ne ya ke magana har yana nuna ta da kulkin hannunshi. Tun Amrah tana kuka da hawaye har ta dawo kukan zuci ga yunwa na nukurkusar hanjinta ga d'an banza duka da tasha hannun mutumen. Ga kuma tsoro shigowar ta hannun police domin abu ne da bai ta6a faruwa da ita ba. Duk k'anana sace-sace da take yi cikin gidaje da shaguna ba a ta6a kamata ba.
********************
Madam Salima tare da k'awarta Hafsat Shinkafi a office ɗinta dake cikin kamfaninta, asalin Hafsat 'yar jahar zamfara ce aure ne ya kawo ta Kano mijinta ya rasu ya barta da yara 4 bata sake yi aure ba, a ganinta aure zai ta kura ta ya hanata neman kud'i, duk wani gantali neman duniya tare suke yi abinsu. Dabi'unta da na Madam Salima sak iri daya babu ban-banci shiyasa k'awance su ya yi armashi.

"Salima duk laifinki ne sau nawa ina faɗa miki ki fitar da yaranki k'asar waje su yi karatu za su fi samun cikakken kulawa, dukiyar nan Allah ya ba ki ita kullum cikin nema kike kina tarawa, to miye amfaninta idan 'ya'yanki ba su sakata sun wala ba?"

Sai da Madam Salima ta shak'i iska kana ta fesar ta k'ofufin hancinta kafin tace.

"Ba wai nak'i shawara ki bane Hafsat kema kinsan kafiya da taurin kai irin na Azaad, ba zai ta6a bari yaranshi su yi nesa da gida ba. Yanzu ɗin ma kullum a cikin tuhumata yake akan tarbiyyarsu. Ina gaya miki jiya da haukar shi ya motsa cewa ya yi sai na ajiye aikina ko uban me zan sama idan na zauna gida?"

"Whats! Ki ajiye aikinki?"

"Wallahi kuwa haka ya faɗa. Sai dai ko kusa bushak'insa bai yi tasiri akaina ba.

"Zance na gaskiya Salima ki tashi tsaye domin sare-sarin hauka zubda miyau. Na fahimci manufar Azaad guda biyu ne dole ɗaya daga ciki ya kasance gaskiya na d'aya kodai so yake ya rusa ki yana bak'in ciki da yadda duniya ta fara haska tauraronki. Saboda ya ga kin fara kamo k'afarshi a arziki shine yake so yai miki k'afar ungulu. Na biyu Ko so yake ya k'aro aure....

"Dallah ya isa Hafsat haka! hasashen ki ne ya ba ki hakan. Azaad ba haka yake ba, kawai dai yana so na kar6i ragamar kula da gidana saboda yaranmu sun fara girma....

"Matsalarki kenan Salima har yau kin kasa buɗe idanuwanki ki fahimci gaskiya, kin yarda da Azaad ɗinan shi kuma Sam bai yarda dake ba, kin d'auki soyayyar duniya kin ɗora mishi shi Kuma ya gaji da zama dake duk wannan salo ya fito miki da shi ne saboda kin kasa haifa mishi d'a namiji wanda zai gaje shi, shiyasa ya fito miki ta wannan sigar

"No....no... please Hafsat don't say that me ya kawo zance haifar namiji da rashin haihuwarshi?" Kar ki saka min shakku akan mijina mana. Ina miki korafi ne akan rashin jituwa da muke fuskanta a koda yaushe ke kuma kina neman shigowa da wani sabon al'amari.

"Ba sabon al'amari bane Salima kece kika kasa gano hakan da kanki, ki yarda dani Salima akwai k'amshin gaskiya a cikin abubuwan da na lissafa miki. Shi zama yake yi ne gida naga kullum yana yawo a sama kamar tsuntsu yau yana wannan k'asar gobe yana waccan. Ko kuma ke Kaɗai Allah ya dorawa nauyin tarbiyyar yara?" Ki yi amfani da kwa-kwalwarki mana.

Har Hafsat ta dasa aya a zance ta idanuwan Madam Salima na lumshe tana girgiza kanta, ta d'auki lokaci a haka kafin da sauri ta buɗe idanuwanta gabanta na mugun faɗuwa mik'ewa tayi da sauri tare da harde hannuwanta a k'irji sai ta kai bangon farko na office ɗinta ta dawo na k'arshe. Hafsat sai bin ta da kallo take gani safa da marwanta ba mai k'arewa bane yasa ta mik'e ta kamo hannunta

"calm down k'awata....

Ta fincike hannun nata da k'arfi ta ja da baya tana wani girgiza kai, cikin kaushin murya tace.

"Kina faɗar min mijina zai k'ara aure kuma kina gaya min I should calm down as how Hafsat tell me as how??"

"Ni ban ce dake zai k'ara aure ba kawai I'm trying to get your brain clean up"

Ajiyar zuciya tayi ta dako cike da izzarta da tak'ama ta iso gaban Hafsat ta dafa kafad'arta, tace.

"Hafsat a rayuwata abu biyu nakeso neman kud'i da Azaad. Haka zalika abu biyu na tsana talauci da kishiya. Ki sani Azaad ba shida ra'ayi mace fiyye da d'aya haka zalika yana matuk'ar so 'ya'yanshi fiyye da son da ni nake musu, bai ta6a nuna min yana son haifar ɗa namiji ba. Da mace da namiji there are all equal to him ko yanzu ya bijiro da zance ajiye aikina a dalilin dambe da Aneesa tai da schoolteacher ɗinsu. Saboda haka tun wuri mu ajiye wannan zance, kafin maganganunki su yi tasiri a zuciyata"

"Kenan kin amince za ki bi abin da yake so za ki mika ragamar kamfaninku ga 'yan uwanki, burinki na mallakar kamfanin ke Kaɗai ya bi iska?"

Yatsine fuska tayi kana cikin zallan izgilanci tace.

"Bari ki ji Hafsat ko ubana Kabir Dala da shine silar arziki na ace zai baro lahira ya zo duniya ya nemi na ajiye aikina billahil-azim ba zan masa biyayya ba, balle wani Azaad Junaid da yake tamkar steering mota sai yadda na juya shi.

Lokaci ɗaya suka kwashe da dariyar shek'inyaci tare da tafawa, Hafsat ta shiga kod'ata tana zuba mata kirari.
******************
Fitowar Azaad Junaid da Abdul-hakeem Daura daga meeting wayar Abdul-hakeem tai ringing, ya ɗaga tare da k'arawa a kunnenshi. Muryar k'anwarshi Zainab ya ji tana rera kuka.

"Will you shut up and tell me what exactly happened?"

Shiru ya yi yana sauraren bayani da zainab take mishi, ya shiga furta

"Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Zainab sau nawa zan faɗa miki ki daina tafiya mai nisa ba tare direba har sai kin kwarewa da driving, da yake kunnen k'ashi ne dake ki ka k'i ji. Shi Kenan ganina zuwa"

Ya kashe waya ya mayar da dubanshi kan Azaad wanda ya tsare shi da idanuwa.

"Zainab ce ta kirani wai ta buge wani d'an acha6a tana police station.

"Subhanalillah....Allah yasa da sauk'i ka je kawai za mu yi waya"

Cikin sauri Abdul-hakeem ya fice kaitsaye police station ɗin ya nufa, cikin yarda Allah d'an acha6a bai ji ciwo sosai ba machine ɗinsa ne ya yi damage cikin k'ank'ani lokaci Abdul-hakeem ya biya kud'in machine ɗin ya kuma yi bail ɗin K'anwar sa. Tun yana cikin office ɗin inspector ya ke ji kukan Amrah da magiyar da take wa 'yan sanda....



*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login