Showing 78001 words to 81000 words out of 91651 words

Chapter 27 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

627

faman yawo yake yi da idanuwanshi daga hoton jikin magazine zuwa da wanda Hakeem ya bashi ba ko tan-tama wannan matar ta jikin magazine da hoton da ke hannunshi na mahaifiyar Miyya ya yi kama sak da na jikin magazine miss Roseline Yaqub Gambella ce fitattaciyar 'yar kasuwa wacce tayi fice a duniya. Ba sai ya tsaya wahalarda kwakwalwarshi ba wurin tanttace kamanunta da Miyya ba saboda kamar tasu har ta 6ace da ka kalleta kasan ita ce mahaifiyarta saidai ita ta d'an tsofa sa6ani Miyya da ke da zallar kurciya amma duk da haka kamarsu d'aya sak.

"Alhamdullilah.....Allah abin godiya ba ko shakka miss Gambella ce mahaifiyar prettyn Daddy na rasa ina zan jefa kaina saboda farin ciki Hakeem.

"Lamarin ubangiji kenan Aj kawai mu ci gaba da godewa Allah da sannu al-amurranka za su dai-daita, yanzu ka bar komai a hannuna zan shirya mana tafiya zuwa Australian, saboda a bincike da nayi na gano tana zaune ne a Australian ba k'asarta, ta haihuwa ba Ethiopia. Gara mu je mu zo da ita a Nigeria aganina hakan zai fi saurin walwale mana matsalolinmu.

"Shikenan Hakeem duk yadda ka tsara dai-dai ne zuciyata cike take da tsintsa farin ciki prettyna za ta had'u da mahaifiyarta, watakila a dalilin hakan za ta yafemin kashe mata mahaifi da nayi.

"Koda ba ka had'ata da mahaifiyarta ba Aj in-sh-allah Aslamiyya ba za ta kulace ka ba, domin tasan k'addara yanzu ka tashi ka je ka ji neman da Alhaji Abbas yake maka Allah yasa alkhairi ne sa6ani abin da muke tunani.

"Amin Hakeem amma tare za mu je saboda mr Richard yana wurin gyaran mota.

"Okay ba damuwa tashi mu tafi.

Shi kanshi direban yara ya shiga tashin hankali ba kad'an ba, lokaci da madam Salima ta sanarda shi buk'atarta na zuwa gidan da Azaad ya kai Miyya. Saidai bai isa ya bijirewa umarninta ba domin bijire mata yana nufi rasa aikinshi gaba d'aya.
Da suka iso gate din gidan hannunshi har makyarkyata yake yi, da ya je danna horn security ya bud'e musu gate ya danno hancin motar a farfajiyar gidan da parking d'inshi da fitar Madam Salima duk lokaci d'aya tun da ya dauko ta yasan ba alkhairi bane ya kawo ta yanzu kuma da ta fice daga mota cikin sauri ya k'ara tabbatar da zarginshi.
A tsorace ya fito daga cikin mota ya jingina jikinshi da motar ya bita da kallo ji yake kamar ya kira Azaad ya fad'a mishi zuwanta gidan amma tsoron hukunci da zai biyo ta kanshi ya hana shi.
Ma'aikatan gidan sai faman gaidata suke yi kasantuwa sunsan matsayinta ga maigidan. Tana zuwa ta turo k'ofar shiga main parlour da karfin gaske cikin sa'a k'ofar ta bud'e yadda ta bude k'ofar ya janyo hankalin Nanny Lacey dake kitchen tana wanke-wanke da sauri ta fito tana goge hannunta da d'an k'aramin towel da kuzarinta ta fito amma tana arba da madam Salima ta kasa k'arasawa cikin parlour tai tsaye turusss tana mata kallon tsoro.

"Zo nan munafukar banza har ni za ki ciwa amana Nanny Lacey na yarda dake amma kika munafuce ni.

Kasa bin umarninta Nanny Lacey tayi sai ma tayi k'ok'arin komawa kitchen, a nufinta ta shiga kitchen ta kargame k'ofa kafin ta cimma manufarta madam Salima ta nufo wajenta da sauri ta cafko dantse hannunta tare da fizgota da mugun k'arfi kamar za ta raba hannunta da gangar jikinta ba k'aramin zafi Nanny Lacey ta ji ba.
Har sai da ta rintse idanuwanta, sosai madam Salima ta zageta tasss ko kad'an bata raga mata ba hakan ba k'aramin konawa Nanny Lacey rai ya yi ba, abinka da zuciya batada k'ashi sai tai k'ok'arin maida mata martani ta hanyar fad'ar.

"Madam ki daina gani laifi idan ma akwai mai laifi ce to ke ce, ni fa 'yar aikinku ce kawai.
Daga ke har yalla6ai Azaad ina bin umarni duk abin da ku ka umarce ni saboda haka ki tuhume mijinki da laifi cin amanarki amma ba ni ba.

Baki bud'e madam Salima ke kallon Nanny Lacey tana mamaki ina ta samu wannan kwarin gwiwar mayar mata da magana, duk tsawon shekaru da suka dauka tana aiki a gidanta bata ta6a musanya yawu da ita ba sai yau lallai idan bata yi da gaske ba hatta da 'yan aikinta za su rena ta saboda haka cikin tafarfasar zuciya ta wankewa Nanny fuska da tagwaye maruka a kuncinta na hagu da dama kana ta nunata da yatsa tana huci.

"How dare you Lacey! Har ni za ki kalla ki fad'awa magana lallai kuwa k'arshen zamanki ya zo a gidanan, ai ba Azaad ya dauke aiki ba ni ce sanadin zuwanki kano saboda haka a yau d'inan za ki tattara komatsa ki, ki koma Jos.

"Ban yi mamaki ba madam don kin mare fuskata, ban kuma yi mamaki jin irin wad'annan maganganu sun fito daga bakinki ba. Saboda nasan a irin halin da kika tsinci kanki fiyye da hakan ma za ki aikata saidai ina miki albishir da cewa idan kika ga na bar garin Kano yalla6ai Azaad ne ya sallame ni ba wai ke korarriyar gida ba.

Daga haka Nanny Lacey ta juya dafe da kunceta, ta nufi kitchen yayin da Madam ta bita da ashariya.

"To shikenan Nanny zan nuna miki ni nake da iko da gidanan da zaran na gama da tsinaniya yarinya nan akanki zan dawo sai nasa kin kwashe kashinki a hannu banza butulu.

D'akunan da ke downstairs ta fara bi tana bubbudawa ko za ta ga Miyya, ta dai ci karo da Ahlam tana sharar barci abinta ko ta kanta bata bi ba. Ta haura upstairs tana bud'e d'aki na biyu wanda ya kasance na Azaad ta hango Miyya a kwance akan katafare gadon barcinsa, wani irin duhu ya mayewa ganinta jin k'arar bud'e k'ofa yasa ta kalli k'ofar shigowa tai tozali da wacce ko a mafalki bata ta6a zaton ganinta ba. Kafin tai wani yunk'uri Madam ta iso gunta daga kwance da ke ta saka hannuwanta biyu ta shak'e mata wuya saida taji tana kakarin mutuwa sannan ta saki mata wuya ta shiga zuba mata maruka a kumatunta tuni baki da hanci Miyya suka fashe jini sai zuba yake akan pillow da kanta yake kai. Da k'arfi madam Salima ta finciko ta ta yar6e ta akan tiles tasa k'afarta ta dinga ball da ita ihu da Miyya take yi ya isa kunne Nanny Lacey, da gudu ta shigo d'akin duk k'ok'arinta na gani ta kwaci Miyya abin yaci turu kasancewar Madam Salima tafi ta k'arfi nesa ba kusa ba. Daga k'arshe ma sai had'e su tai su biyu tana bugu kamar wata sabon kamun hauka.
Gani haka ya sanya Nanny Lacey ta kwaci kanta tasake kwasa da gudu ta sauko k'asa, ta fita compound ta nemo agaji securities. Da madam Salima ta gaji da jingar Miyya ta cukume wuyan rigarta ta jawo ta a k'asa kamar dai kana jan dabba ba mutum d'an adam ba. A haka ta tattaka matattakala bene da ita a garin jan da take mata hannunta ya buge k'arfen da ke jikin bene ta kwalla k'ara mai tsananin gaske kana ta suma. Daga lokaci bata sake sani me ke faruwa ba.
Koda Azaad ya iso family house babban falo ya cika taff da 'yan uwanshi, da shigowarshi ya bisu d'aya bayan d'aya yana basu hannu sun yi musabaha kafin ya nemi kujera ya zauna sai lokaci idanuwanshi suka yi mishi tozali da Ahmadu dake kwance a k'asa yana sauke numfashi d'addaya, sai kuma Hasheem da ke zaune a keken kuragu idanuwanshi sun yi jajir ga wani irin miyau mai yauk'i yana fita daga bakinshi.

"Subhanalillah.....me yafaru da Hasheem shi da yake asibiti me ya kawo shi nan?"
Shi kuma Ya Ahmadu me ya same shi ne, ko shima bashida lafiya ne?"

Azaad ya fad'a fuskarshi dauke da tsagoron mamaki, yana kallon fuskar Alhaji Abdallah wanda shi yake facing da sauri Alhaji Abdallah ya kauda fuskarshi yayin da wasu hawaye bazata suka biyo kuncinsa.

"Shine babban mak'asudin taruwar mu anan Azaad, daga Ahmadu har Hasheem sun tsinci kansu a wannan halin ta dalilinka. Ba wai iya su biyu kadai ba hatta da mutuwar babban yaya Alhaji Yusuf da amininsa Alhaji Babu...

"Ni kuma Yaya?

Azaad ya katse shi a razane har yana nuna k'irjinshi da yatsa, cikin matuk'ar mamaki ya sake fad'in.

"Me ya alak'anta ni da mutuwar babban yaya da amininsa, balle halin da su Ya Ahmadu suke ciki?" Yaya Abbas kowa anan wurin yasan cewa babban yaya da Alhaji Buba accident suka yi Hasheem kuma wasu 'yan ta'adda da ba a san ko su waye ba suka har6eshi shi kanshi yace baisan su ba.
Ya Ahmadu kuma bansan me ya faru dashi ba sai yanzu nan da na shigo na ganshi kwace a cikin wannan hali.

"Kwantar da hankalinka Azaad duk Wanda ke cikin falonan yasan kai mutume kirki ne mai tsalkakkiyar zuciya, shiyasa ubangiji ya kare ka a duk lokaci da 'yan uwanka suka yi yunk'uri cutarda kai daga k'arshe ma sai kaik'ayi ne ya koma kan mashek'iya ga dai su nan a zaune su ba ka labarin abin da suka aikata da bakinsu waka a bakin mai ita yafi dad'in sauraro, ni kan ba zan arin bakinsu naci musu albasa ba gara ka ji daga bakinsu.

Tirya-tirya Ahmadu ya shiga bankad'o sirrikansu daga nan kwance da yake wanda ba dasu cikin tafiyar ba suka dinga tafa hannuwa suna salati da sallalame tare da yi musu tofin Allah tsine, gaba d'aya falon ya kaure da hayaniyarsu.

"Ya isa haka!

Alhaji Abbas ya daka musu tsawa dole suka yi shiru ba don ransu yaso ba, yayin da Azaad Junaid ya sadda kanshi k'asa hawaye na bin kumatunshi biyu, yasan cewa 'yan uwanshi ba su k'aunarshi amma bai ta6a tsanmani kiyayyar tayi kamari har haka ba. Wani irin zafi yake ji can cikin k'asan zuciyarshi.

"Azaad ka ji abin da 'yan uwanka na jini suka aikata maka domin babu bare a cikinsu, da Allah ya tashi tona asirnsu aljana ce ta shiga jikin Ahmadu tun jiya take bashi wahala ita ce ta tilassa shi fad'ar gaskiya, ga malam Abubakar nan zaune shine yai magana da ita ta fad'a mana tun kana yaro take ba ka kariya duk wanda ya yi k'ok'arin cutarda kai sai ta kawarda shi a dalilin kakarka Jadda ta ta6a taimakonta a tunaninta mutum ce tun daga lokaci take bibbiyar al'amurranka.
Da sauri Azaad Junaid ya d'ago kanshi ya kalli Ya Abubakar wanda duk cikin 'yan uwanshi tasu tafi zuwa d'aya.

"Kwarai kuwa Azaad aljana ce ta kuma tabbatar mana da zarar ka zo sun fad'in gaskiya za ta bar jikin Ahmadu.

Malam Abubakar ya fad'a fuskarshi shinfid'e da tausayin Azaad. Tsawon lokaci Azaad ya dauka shiru yana dafe da bakinshi ya rasa wacce kalma zai furta gaba d'aya al'amari ya zo mishi wani iri gani yake kamar al'mara da kyar ya rinjaye raunaniyar zuciyarshi ya ce.

"Me nai muku da ku ka tsaneni har haka shin a cikinku akwai wanda nai wa wani laifi ne da na cancanci irin wannan hukunci daga gare ku?"

Shiru suka yi ba wanda yake da kwarin gwiwar amsa mishi sai malam Abubakar ne ya amsa da cewa.

"Ba abin da kayi musu Azaad tsabar hasada ce kawai da son zuciya, kuma gashinan inda son zuciyar tasu ya kai su sai ka k'ara godewa Allah da ya kare ka daga kaidinsu, ko a haka Allah yabarsu sun ga aya ya kuma zama izzina da masu irin hali nasu.

Sosai furuncin malam Abubakar ya k'ara karyawa Azaad zuciya hawaye suka ci gaba da silalowa akan tattausan kumatunshi, ya kalle su d'aya baya d'aya kana cikin rauni murya ya ce.

"Nagode wa Allah da ya kare ni daga sharrinku, kamar yadda ya Abubakar ya fad'a ko a haka kun ga aya 'yan uwana ne ku banida tamkar ku duk da kun kasance ba ku k'aunata ni ina sonku har abada ba zan ta6a sauya k'aunar da nake muku ba, saboda haka ku je na yafe muku.

Gaba d'aya falon dauki amon sautin muryoyi daban-dabam saboda basu zaci zai yafe ciki sauki ba, saida Alhaji Abbas ya tsawata masu kana suka yi shiru malam Abubakar ya kai duba gun da Ahmadu yake kwance yana nishi d'addaya ya ce.

"Ya ke wannan baiwar Allah ki yi hak'uri ki fita daga jikinshi domin wanda aka cutar ya furta da bakinshi ya yafe kamar yadda kika buk'ata.

Azaad ya kar6e zance ta hanyar fad'ar.

"Dan Allah ki fita daga jikinshi kuma na rok'e ki daga yau kada ki sake cutarda wani akaina.

"Tabbas Azaad ka banbanta da sauran bil'adama kana da kyakkyawar zuciya in-sh-allah za ka yi farin ciki rayuwarka za ta cika da haske kadai k'ara jurewa ka kuma ci gaba da addu'a.

Aljana Bahijja da ke jikin Ahmadu ta fad'a ta hanyar sautin muryasa daga haka tai musu sallama ta fita daga jikin Ahmadu yayin da jama'ar dake falon suka shiga ba Azaad hak'uri musanmman Ahmadu da Hasheem kuka suke yi kamar ransu ya fita.

"Ku daina bani hak'uri ya isa haka gaba d'ayanku na yafe muku suma su Babban yaya ina musu fatan rahama ubangiji.

Azaad ya fad'a yana d'an murmushi da bai wuce iya fatar bakinshi ba, ya mik'e yana cewa.

"Ni zan tafi na bar Hakeem a k'ofar gida yana jirana na barku lafiya.

Ya k'arashe magana tare da ficewa gaba d'ayansu suka bishi da kallo, tun kafin ya k'arasa wajen da suka yi parking mota ya hango Hakeem yana safa da marwa Hakeem yana hangonshi ya rugu da azama muryarshi tana rawa ya ce.

"Aj ya aka yi ka jima a ciki?

"Abubuwan ne suka yi kamari Hakeem bansan ta ina zan fara ba ka labari ba.

"Aj ka jinginar da labarinan har mu sami natsuwa bayan shigar ka ciki aka kira d'aya daga cikin wayoyinka, da na duba mai kira sai naga Nanny Lacey ce sai kawai nai receiving hankalinta a tashe take fad'amin Salima ta je can gidan ta yi wa Miyya d'an banza duka har ta suma yanzu haka sun dauki Miyya zuwa asibiti......
5/14/22, 09:49 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004



39...



Lokaci da Salima ta zo k'arshen stairs bai wuce tako uku zuwa hudu sai kawai ta wulgo Miyya, ta dinga mulmula yayin da kanta ya buge last stairs jini ya yi tsirtuwa ya wanke gaba d'aya fuskarta. Koda securities d'in da Nanny Lacey ta je neman taimakonsu suka shigo madam Salima na ci gaba da ball da ita, da gudunsu suka yo kanta biyu daga cikinsu suka rirrik'e ta yayin da guda d'ayan ya tsuguna gaban Miyya ya kai hannunshi a hancita ya ji tana numfashi saboda a zatonshi ta mutu cikin sa'a ya ji da raguwar numfashi a jikinta. A rikice ya kinkimeta da gudu ya nufi k'ofar fita Nanny Lacey ta bishi a baya a gafe d'aya Madam Salima sai zabure-zabure take yi su saketa, ta k'arasa kashe Miyya had'i antaya masu zagi tare da alk'awali sai ta kore su aiki saida da suka ga an fita da Miyya sai kawai suka sake ta, da sauri direban yara ya jawo mota suka saka Miyya wacce bata da maraba da matattaciya koda madam Salima ta fito har motar ta fice gateman yana rufe gate ko kad'an ba haka taso ba.
Cikin tsananin tashin hankali Azaad Junaid yake yawo da idanuwanshi da ke cike da zallar tsoro yana kallon Hakeem kamar bai fahimci abin da yake fad'a ba.
Fizgo hannunshi Hakeem ya yi yasa shi a mota ya rufe k'ofa kana ya zagaya ya shiga ya tashi motar da k'arfi, koda suka iso hospital din zuciyar Azaad kamar za ta yaga k'irjinshi ta fito da Nanny Lacey ya fara ci karo gaba d'aya White long sleeve shirt da ke jikinta ta rine da jini sai zarya take yi daga bango gabans zuwa na yamma, tana gani Azaad ta fashe da kuka tare da durk'ushewa k'asa da hanzari Azaad ya kana kafand'uta biyu ya tashe ta tsaye cikin rikitatciyar murya ya ce.

"Nanny Lacey wane hali pretty take ciki tana raye ko ta mutu ne Dan Allah ki fad'a min halin da take ciki?"

"Bansani ba yalla6ai Azaad tun zuwanmu aka shiga da ita wannan d'akin sun tabbatar mana ba za su ta6a ta ba har sai mun zo da police saboda murder Case ne direban yara ya je ya zo da police din...

Kafin ta rufe baki Azaad ya yi wuff ya fad'a d'akin da ta nuna mishi likitoci biyu had'i da nurses uku ya gani tsaye akan Aslamiyya sun dukufa akanta, ya tsaya cakkk tare da long breath ya sauke gaba d'aya hankalin likitoci da nurses din ya dawo kanshi, basu sha wahala gane shi kasancewar fitatce kuma sananne, tun kawota da su Nanny Lacey suka yi suka fad'in cewa matarshi ce shiyasa ma suka fara duba ta kafin zuwan Police din.

"Yalla6ai dan Allah ka fita waje mu k'arasa aikinmu.

D'aya daga cikin doctors din ya fad'a cikin low voice. Jiki a sanyaye Azaad ya juya ya fito dai-dai direban yara na isowa da zuga police domin su na ji Case d'in daga gidan young billionaire Azaad Junaid ne jikinsu na rawa suka ciko mota guda, cike da girmamawa suka gaida Azaad tare da tambayar shi suna so su dauki statement, k'ala Azaad bai ce dasu ba sai Nanny Lacey ce ta fad'a masu yadda abin ya faru da suka ji cewa uwargidan Azaad ce tai wannan aika-aika sai kawai suka dinga kallon Azaad su na jiran su ji ta bakinshi, Hakeem ne ya matso kusa da su ya umarce su da su tafi kawai tun da sun dauki statement d'in.
Kana ya kama hannu Azaad suka koma gafe.

"Aj please ka kwatar da hankali in-sh-allah ba abin da zai sami Aslamiyya...

"Innalillahi wa'inna illaihim raji'um.....

Azaad Junaid ya fad'a tare da dafe kokon kanshi, da yake jinsa tamkar ba a jikinshi yake ba. Kana cikin rauni murya ya ci gaba da fad'in.

"Hakeem na ga jarabawa a rayuwata daga wannan sai wannan, miyasa Salima za ta nemi salwantarda rayuwar innocent

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login