Showing 12001 words to 15000 words out of 91651 words

Chapter 5 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

606

Niamey.
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_


Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske writers Association.

Top Ten Takun Haske Batch:A


6....


Aslamiyya ta mik'e zubur ta nufi k'ofar gida, wannan fitar da tayi shine karo na shidda. Da taje k'ofar gida tayi tsaye tana kallon hanya ta ina Amrah za ta 6illo. Tun fitarta take jin matsananci tsoro haɗi da faɗuwar gaba.
Ta je makota inda take sa ran gani Amrah yafi a kirga gashi Kuma tana tsoro ta fita daga unguwa zuwa nemanta, ta bar Amal ita Kaɗai saboda yanayi jikinta. Abin ka da ruwa-ruwa babu juriya sai afki kuka, lokaci zuwa lokaci take sharar hawaye gashi tun safe babu abinda suka ci, inda Allah ya taimake ta akwai raguwar sachet daya na madarar da jiya Amrah ta sato, ta k'adawa Amal. Da batasan inda za ta nemowa Amal abinda za ta ci ba.
Sake komawa tai cikin gida tana shiga d'aki ta tarar da Amal zaune, da alama yau jikin nata da sauk'i jiki a sanyyaye ta zauna kusa da Amal k'ok'ari take ta 6oye mata hali da ake ciki. Saidai kashh! Tuni Amal ta gano damuwar da take ciki ga kuma idanuwanta da suka nuna tayi kuka.

"Meke faruwa Miyya naga kamar kina cikin damuwa?"

"Ba komai.

Ta faɗa a takaice tare da kauda kanta tana kallon bangon d'aki.

Amal ta matsa daff da ita ta kwantar da kanta aKan kafad'arta cikin sanyi muryarta mai kama da Aslamiyya sak tace.

"Miyasa za ki 6oye min Miyya bayan ga idanuwanki nan sun nuna kin yi kuka?"

"Amal tun safe da Amrah ta fita bata dawo ba. Wani irin fargaba haɗi da tsoro ke damuna. Ina tsoro kada wani mummuna abu ya sameta.

Ta k'arashe magana tana hawaye. A hankali Amal ta sauke ajiyar zuciya kana tace.

"Ki kwantar da hankalinki da yarda ubangiji ba abin da zai same ta. in-sha-Allah za ta dawo cikin k'oshin lafiya.

"Allah yasa!

Aslamiyya ta faɗa tana goge hawayen fuskarta.

***************

Cakk.... Abdul-hakeem ya tsaya Yana kallon Amrah wacce ke ta faman rusa kuka, duk da yadda wani tsamurarre constable ke mata tsawa da hargagin ta rufe mu su baki ko ya maketa da kulkin hannunshi. Bata fasa kuka da magiya ba.

Ya dawo da ganinshi akan inspector Sa'eed wanda rashin gaskiya ya baiyana 6aro-6aro akan fuskarshi. Gaba d'aya ya rud'e sai wani kame-kame yake yi.

"Ranka ya dad'e sata tayi shine aka kawo ta nan.

"Waye ya kawo ta, me kuma ta sata?"

"Wani mutum ne yace kud'insa ta sace har kimani naira dubu d'ari, yarinyar tana da kafiya da taurin kai, tak'i ta faɗi inda ta 6oye kud'in"

D'an murmushi gefen baki Abdul-hakeem ya yi.

"Gaskiya inspector ba kasan aikinka ba wannan k'aramar yarinya ce za ta iya satar dubu d'ari?"

"Ranka ya dad'e haka mai shago ya faɗa.

"Kai kuma da yake kidahumi ne sai ka yarda.

Kafin inspector Sa'eed yai magana Amrah ta riga shi ta hanyar cewa.

"Wallahi-tallahi Abba ban d'auki kud'insa ba. Biredi na dauka kuma ya kar6e abinsa, Don Allah Abba ka taimake ni yadda Allah ya taimake ka, fitarda ni wurinan.

Sosai Abdul-hakeem ya k'ure mata idanuwanshi babu ko kyaftawa, kyakkyawar yarinya fara tass...a shekrunta na haihuwa ba za ta zarce goma sha biyu zuwa sha uku sa'ar Sadiq ce second born ɗinsa. Tausayin ta ya yi mishi dirar mikiya, sai kawai ya rufe police ɗin da faɗa kaman zai dake su musanmman inspector Sa'eed, kasancewar D.P.O baya nan shine babba a wurin. Kamata ya yi ya tsananta bincike haka kawai daga kawo mishi 'yar mutane ya k'argame ta. Sai Kiran mai shago aka yi da ya zo shima ya rudewa ya yi gani attajirin mai kud'in da ya tsawa Amrah, daga k'arshe sai faɗan gaskiyar al'amarin ya yi. Ya dawo yana ba wa Amrah hak'uri.

"Ka ga irinta ko inspector yanzu ina za ku da hakki yarinya nan kun zalince ta ba Kaɗan ba?"

"A yi hak'uri Ranka ya dad'e sharrin shaidan ne.

"Rufemin baki ba wani sharrin shaidan so zuciya ne da kar6a cin hanci da har abada ba za ku bar shi ba. Ke zo mu tafi Allah ya saka miki, yadda suka yi miki Allah yai musu haka nan.

Jikin Amrah yana rawa ta fito daya daga cikin constable ya mik'a mata hijabinta da slippers, ta saka da sauri Abdul-hakeem ya rik'o hannunta har sun kai bak'in k'ofar fita, ya juyo ya dube su yana faɗin.

"Maganar nan ba wai ta k'are iya nan ba, ku jira abin da zai biyo daga baya.

Daga mai shago har inspector cikinsu ya hau k'ugi da mugun sauri suka bi bayan Abdul-hakeem, wanda ya har ya kai wajen da ya yi parking motarsa.

"Ranka ya dad'e Don girman Allah kayi hak'uri ka rufa mana asiri"

Cewar inspector har yana durkusawa k'asa. Amrah ta dubi Abdul-hakeem da kumburarrin idanuwanta tace.

"Abba ka yafe musu dukkansu na fiso laifi domin da na bi nasihar da Miyya take min a kullum da hakan bata faru dani ba.

Ta k'arashe magana wasu zafafan hawaye masu zafin gaske, suka gangaro saman kuncinta. Jikin Abdul-hakeem yai sanyi ya kalle inspector da har lokaci ya ke a durkushe.

"Shikenan ku tashi ku tafi Allah ya so ku tana da kyakkyawar zuciya ta yafe muku da sai na koya maku hankali.

Godiya suka shiga yi masa bai bi ta kansu ba ya buɗewa Amrah backseat ta shiga, saboda har lokaci takaicinsu bai k'arashe sakinsa ba. Zainab dake front seat wacce tun a police station bata furta uffan ba sai lokaci ta Sami damar waigawa gefen da Amrah take tace.

"Ya sunanki wacce unguwa kike?"

"Sunana Amrah a kawo nake.

"Ke kuwa me ya kai ki satar biredi?"

Shiru Amrah tai ta rasa amsar bata sai kawai ta shiga wasa da yatsu hannunta.

"Amrah ki yi magana mana?

A wannan karon Abdul-hakeem ne ya yi magana.

Cikin zazzak'ar muryarta tace.

"Saboda ba mu da abin da za mu ci nida 'yan uwana.

"Ina iyayyenki?"

"Abbana ya rasu tun Ina da 2yrs mamanmu kuma naji Dadda tace bayan mutuwar Abbanmu ta gudu tabar mu nida twins sisterna da Yayata Miyya, wacce ita ce take kula damu tun baya da muka rasa iyayyen mu.

K'arfaffiyar ajiyar zuciya Hakeem ya yi sosai tausayinta ya k'ara lullu6e shi. Cikin sanyi murya yace.

"Ina dangin mahaifinku dana mahaifiyarku da za su bar ku da yunwa Amrah za su iya kula da ci da shan ku, ba sai kin yi sata ba?"

""Hannun kakarmu wacce ta haifi Abbanmu muke ita kuma bata sonmu. Kullum cikin gana mana azaba take, dangin mahaifyarmu kuma ba musan su ba. Asalima ba musan gari da suke ba.

Tsabar rud'ani da Hakeem ya shiga yasa ya kasa magana Zainab ce tai k'arfin halin cewa.

"Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Ki ka ce mahaifiyar Abbanku, ke kuwa Amrah me ku ka aikata mata har haka da ta tsane ku.

"Saboda Abbanmu ya aure mahaifiyar mu ba da saninta ba sannan kuma mahaifiyarmu ba Musulma bace.

"Amrah wannan ba hujja bace da za ta dogaro da ita har ta tsane ku, ai ba laifinku bane na mahaifinku ne saboda shine ya yi mata ba dai-dai ba. Kuma babu inda addinin musulunci ya yi hani da aure wacce ba Musulma ba. Kawai dai kakarku muguwa ce azzaluma sai Allah ya yi muku sakay....

"Ya isa haka Zainab!

Hakeem ya katse mata numfashi daga haka ba wanda ya sake magana a cikinsu, wani super market ya tsaya ya yi wa Amrah shopping na kayan tea da bread haɗi da indomie har dasu chocolate cake da biscuits. Tun a farkon layin unguwarsu tace ya sauke ta bai ce komai ba, ya yi parking ta fito shima fitowa Amrah tai mishi godiya har ta juya ya kira sunanta ya fito da shopping bags da kwalin indomie ya ajiye a gabanta bai ce komai ba ya shiga mota har ya yi reverse sai kuma ya tsaya ya kira ta, da ta zo ya mik'a mata card mai d'auke da phone numbers tare da company address ɗinsa. Ta koma wajen tulin kayan da ya ajiye mata ta ɗora kwalin indomie aka ta d'auki shopping bags, ta nufi gida sai da ta fara lekawa tsakar gida kamar yadda ta saba ta ga babu kowa tai wuff ta shige d'akinsu kasancewar su ne a farkon shigowa...

*****************

Yau ma da wuri Azaad Junaid ya shigo gida, sai da ya lek'a 6angare Jadda saboda ya zame mishi al'ada duk dare sai ya je yaci abinci a wajenta sannan yake dawowa apartment ɗinsa.
Sai da ya duba lafiyar yaranshi kafin ya nufi nashi d'aki, yana cikin online meeting ya ji an turo k'ofar d'akinsa. Ko bai ɗago ba yasan ko wacece ke da zarar shigo mishi d'aki a dai-dai wannan lokaci, shiyasa bai damu da sai ya kalli wanda ke shigowa ba.
Cikin dakon k'assaita da nuna ita ɗin wata ce ta shigo ba ko sallama sai wani yatsina da take yi, sai uban k'amshi na fitar hankali dake fita daga jikinta sanye take da sleeping gown wacce ta sauka izuwa gwiwarta, cike da izza haɗi da tak'ama ta nemi gefen gado ta zauna. Ta ɗora k'afa daya kan daya, har ta zauna bai da niyar ɗagowa ya kalle ta balle tasa ran za tanka mata.

Ta aika mishi da malalacin kallo, mai nuni da batasan darajarsa ko Kaɗan ba. Wani sai kad'awa k'afafuwanta take yi. Cikin gadara tace.

"Azaad inaso nai magana da kai please can I have your attention?"

Ya ci gaba da magana da yake da colleague ɗinsa da suke online meeting yai banza da ita, hakan ba k'aramin sosa mata rai ya yi ba. Abin ka da mai hurt temper har ta harzuk'e.

"Da kai nake magana Azaad ka yi wani kunnen uwar shagu dani. kuma san na tsani ina magana ayi banza dani, kai kuma abin da ka fi kwarewa dashi kenan.

Ta k'arashe magana cikin ɗaga murya, da sauri ya yi disconnected video call ɗin tare da rufe laptop ɗin. Gudun kada hankali colleague ɗinsa ya dawo kanshi har su fahimci abun da ke faruwa, A tsanake ya ɗora manyan idanuwanshi masu masifar daukar hankali akan kyakkyawar fuskarta da batada make up amma sai glowing take abinta. Yayin da hasken blue colour bulbs dake d'akin yana k'ara haskaka fuskarta ta, ya jefa mata kallon nan nashi mai sanyi da kashe jiki tare da faɗin.

"Me kike nema a bedroom ɗina a dai-dai wannan lokaci?"

"Na zo ne muyi magana akan sauyawa Aneesa school d'azu na aika P.A ɗina ya je school ɗinsu su ya kar6o min transferring letter ɗinta, sai ya dawo min da zance wai kayi magana da principal Aneesa za ta ci gaba da karatu a school ɗinta har da saka Aneesa ta rubuta apologies letter for what reason za ta ba da hak'uri?"

"Tunda ta fara magana idanuwanshi ke kafe akanta babu ko kyaftawa yayin da wani tuk'uk'in bak'in ciki haɗi da takaicinta suka mishi dirar mikiya a karo na ba adadi, saboda ba yau ne ranar farko da ya fara jin hakan akanta ba...


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_


Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske writers Association.

Top Ten Takun Haske Batch:A

Free page

7....

Ido biyu Amrah tai da Aslamiyya kallon tuhuma ta bin ta dashi har tasauke kwalin indomie da ke kanta, bata dauke idanuwanta daga kanta ba.
Tana jin lokaci da Miyya ta sauke k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta buɗe baki a rud'e ta ce.

"Subhanalillah....Amrah me same ki ne naga fuskarki da idanuwanki a kumbure?"

Amrah ta sadda kai k'asa idanuwanta suka ci-ciko da hawaye tasan asirinta ya ri ga da tonu babu saura 6oye-6oye, cikin muryar kuka ta zube gaban Aslamiyya.

"Don Allah kiyi hak'uri ki yafemin miyya nasan abin da na aikata ban kyauta miki ba, wallahi na tuba ba zan k'ara satar kayan kowa ba....

A matuk'ar tsorace Aslamiyya ta finciko kafand'unta ta mik'ar da ita tsaye.

"Na shiga uku Amrah sata fa kika ce?"

Amrah ta gyada kanta saboda kukan da yaci k'arfinta ba zai bata damar buɗe bakinta ba.

"Kin cuceni Amrah kin yaudare ni wato ba gidan Maman Saleem kike zuwa tayata aiki ba, sata kike fita wayyo ni Miyya wacce irin rayuwa Amrah ta jefa kanta?"

"Ban cuce ki ba Miyya asalima ina yi sata ne domin kare mutuncina sau uku Baban Saleem, yana yunk'uri lalata min rayuwa da taimakon ubangiji nake samun na kwace kaina. Haka ma gidan Maman Bobo sau babu adadi Bobo yana ta6a min k'irji. Na 6oye ban faɗa miki ba gudun kada ki shiga tashin hankali. Tun daga lokaci na daina shiga gidajen jama'a sai dai na bi shaguna na sato mana abin da za mu ci"

Da sauri Aslamiyya ta rungume Amrah tana wani irin gunji kuka, kamar ranta zai fita. Amal da ke kwance sai kallonsu take tana shar6a hawaye. Bayan Amrah ta tsagaita da kukanta, ta shiga ba Miyya labarin taimakon da Abdul-hakeem ya yi mata.

"Allah yasaka mishi da masauki a gidan aljanna firdausu! Ina gargadinki Amrah daga yau kar ki sake ta6a kayan kowa ba tare da sanin mai abu ba. Sata babban kask'anci ce tana zubar da mutunci da k'ima tana rusa darajar mutum a idanu jama'ar duniya, duk hali da muke ciki mu dogara da Allah sai ki ga ya kawo mana mafita ba tare da dabarar mu ba.

"Na daina wallahi ba zan sake ba. Ai naga aya in-sha-Allah babu ni ba sata har abada"

Aslamiyya ta sauke ajiyar zuciya tare da zaunawa kusa da Amal.

****************

"Azaad da kai nake magana fa"

Sai da ya sauke zazzafan numfashi kafin ya ce.

"Saboda ni ne mahaifin Aneesa ni ke da cikakken iko akanta ba ke ba.

"Wow! Thats good to hear that from you Azaad ashe kasan da haka ka keso rusa min career, ka ke so ka hana min business ɗina, Wato abin naka mugunta ne ko?"

Ta k'arashe magana tana ɗage girar idanuwanta, da ka kalle shi za kasan cewa he's deeply in hurt babu komai a cikin zuciyarshi sai takaici da bak'in ciki how long zai ta kasancewar cikin wannan takaici da 6acin rai?"

"Salima!

Ya kira sunanta cikin zazzak'ar muryarshi ma'abociya sanyi, duk yadda ranshi ya kai da 6acin ba kasafai yake nunawa ba. Sai dai ya 6oye shiyasa duk ranar da aka kaishi mak'ura hukunci da zai dauka sai ya girgiza mutum, shiyasa bai cika yanke hukunci nan take ba saboda kaifi d'aya ne.

"Ina da hak'uri Salima kema kinsan da wannan, kada ki yi amfani da hak'uri na ki yi min yadda kike so hakan ba dai-dai bane Salima ki tuna ni fa mijinki ne uban 'ya'yanki.....

"Dallah ya isa! Ni ba wannan ne ya kawo ni dakinka ba, ka nace aKan lallai sai Aneesa ta yi karatu a school ɗin da banaso okay fine naji amma inaso kasani idan har zan zantarwa da hukunci akan yara ka nuna min ban isa ba, har kana faɗin kafini k'arfin iko akansu to hakan na nuni da babu amfani ka cilastani mik'a ragamar dukiya ta a hunnun wani. Don haka na faɗa da babbar murya ba zan ajiye aikina ba.

"Shikenan naji abin da kika faɗa amma inaso ki sani ba cilasta ki nake ba umarni ne a matsayina na mijinki, idan har ke ba ki min biyayya ba. Nima babu amfani na bi son ranki. Saboda haka ki bi yanda ranki yake so nima na bi nawa anan za a tantatace waye gaba tsani ni da ke.

Cikin izgilanci ta kece da dariyar reni, kana ta mik'e tsaye tana tafa hannuwanta, ta dube shi a wulak'anci ta ce.

"Babu abin da za ka iya Azaad tun yaushe kake wannan 6a-6atun da cika baki, sai fa ka gama wannan cika bakin naka ka dawo kana rarrashi da bani hak'uri.

"Shikenan naji Salima duk abin da za ki faɗa go ahead ba zan hanaki ba. Domin ban isa ba amma inaso ki rubuta ki ajiye ni Azaad Junaid sai na shayar dake zallan ruwan mamaki.....oya fita min daga d'aki I don't want any arguing with you just go and do what you want.

"Zan fita dama ban shigo ba don in zauna d'akinka amma kafin in fita inaso ka dawo min da passport ɗina da ka d'auke na nema kaura wambai ban ganshi ba. Na kuma tabbatar kaine ka d'auka ka dawo min da kayana domin tafiyata babu fashi.

"I say get out of my room before I loose my control....

"I'm not going anywhere until you return my passport.

A fusace ya mik'e ya buɗe closet ɗinshi ya zura hannun cikin aljihun coat ɗinshi, ya ciro passport ɗinta ya jefa mata.

"Ga tsiyar ki nan dauka ki fita min daga d'aki"

"Hakan ya fi ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login