Showing 39001 words to 42000 words out of 91651 words

Chapter 14 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

614

gyara min gado?"

Ya faɗa cikin taushin murya.

"Zan iya mana"

Tayi magana tana k'ara k'awata fuskarta da yalwatatce murmushi, da hannunshi ya nuna mata Master bedroom ɗinshi wanda tsawon rayuwarshi madam Salima ce Kaɗai ke shigarshi sai kuma yau da shi da kanshi ya lamuncewa yarinyar da ya yi kirari da ba abin da zai yi da ita.
D'akin ta nufa tana wani iri cat walks wanda za ka zaci da gangan take yi shi, alhali kuwa halitta ta ce a haka. Bai d'auke idanuwanshi daga kanta ba har saida ta shige d'akin ya daina ganinta kana ya yi ajiyar zuciya.
Tana shigar bedroom ɗin ta ja tayi tsaye tana kallon haɗuwa da tsarin d'akin nashi ba k'aramin burgeta d'akin ya yi ba.
Komai na d'akin very neat gado ba wani ya lalacewa da ya yi, sai kawai ta canza mishi bedsheet ta wanke bathroom.
Koda ta dawo falo ya mik'ar da bayanshi ga jikin resting chair, ya ɗora kafafuwanshi akan center table idanuwanshi suna rufe, saida ta kalle mishi fuska iya son ranta kafin ta dai-daita muryarta ta furta.

"Daddy na gama har bathroom na wanke maka"

"Thank you!

Ya faɗa cikin muryarshi da bata fita sosai saboda k'arfin izza da k'asaita, da kuma bakon al'amari dake yawo cikin jini da bargonsa.

"Goodnight Daddy"

"Goodnight!

Ya furta can k'asan mak'oshi still idanuwanshi a rufe, ta taka a hankali ta nufi k'ofar fita tana daff da ficewa ta waiwaya ta kalleshi idanuwanshi fess...akanta tasaki mishi murmushi mai tsayawa a rai tare da rufu k'ofar. Tana ya fita ya ja k'arfaffiyar ajiyar zuciya gaba ɗaya jikinshi ya saki kasala ta lullu6eshi. Ya kasa ci gaba da aiki da yake yi sai tsallake tulin files ya yi ko ta kanta coffee da ta kawo mishi bai bi ba, ya shige bedroom, ya tsaya tsakk.....yana kallon yadda ta gyara mishi gado karo na farko a tsawon rayuwarshi da mace ta gyara mishi gado kasancewar bai yarda housemaids su shiga mishi d'akin kwana ba.
Madam Salima kuma ko lokaci kanta bata da balle na gyara wani abu wai shi gado. Numfashi ya sake saukewa kana ya bi lafiyar gado.
Da fitar Miyya ta zarce kitchen ta dauko rubar ruwa a dalili wani irin bushewa da mak'oshinta ya yi d'akin Ahlam da yanzu ya kasance nata ta nufa gefen gado ta zauna ta sha fiyye da rabin ruwan, ta ajiye raguwar bisa bedside kana ta nemi kusa da Ahlam ta kwanta tana runtse idanuwanta kyakkyawar fuskarshi ma'abociya kyau da kwarjini ta bayyana gareta da sauri ta buɗe idanun nata duk yadda taso barci ya d'auke ta hakan ya kasa samuwa.
Ta 6angare Azaad shima hakan ce ta faru dashi sai misali karfe uku na dare barci ya d'auke shi, saidai wani abin mamaki gaba ɗaya barcin nashi ya raya shi ne cike da mafalkan Miyya, cikin tsananin firgita ya falka ya tashi zaune kana jinginar da jikinsa ga kan gado, yasa hannunshi yana shafar kwatattce sajenshi cikin yanayi na mamaki da Kuma al'ajabi yake backwards ɗin mafalkin nashi a hankali yabi jikin wando pajamas ɗin jikinsa da kallo, ba ko shakka wanka janabba ya Kama shi. Tun a farkon balagarshi rabon shi da ya yi mafalkin yana saduwa da mace sai yau ko yau ɗin da Miyya da yake yi wa kallon 'yar cikinsa. A gareshi wannan babban abin kunya ne wannan wacce irin masifa ce takeso kunnuwa rayuwarsa?"
Ya sauk'o daga gado ya shiga bathroom zuciyarsa fal.....damuwa a haka ya tsaftace jikinsa wani abin mamaki wata irin natsuwa da gansuwa yake ji tamkar a fili ne ya rage mararshi ba a mafalki ba. Yadda ya sami wannan gansuwar a mafalki a wurinta, ya tabbata a bayyane zai sami fiyye da yadda ya samu a mafalki.
Praymat ya shinfid'a ya shiga zuba nafilfili yana kai wa ubangiji mai kowa mai komai buk'atunsa.
Misali karfe 7:15am Miyya ta fito downstairs parlor sanye da school uniform, tea kawai tasha saboda daren jiya bata samu wadatatce barci ba. A dalili tunanin Azaad Junaid da ya hanata sakatt.....
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004



21.....



Sai kai da komo Hasheem ya ke yi ya kasa zaune ya kasa tsaye, idanuwanshi sun kad'a sun yi jajir lokaci zuwa lokaci yake fesar da zazzafar iska daga bakinsa. Can kuma ya dunk'ule hannunshi na dama ya nushi tafin hannunshi na hagu ya yi hakan yafi a kirga. Tajo ya buɗe k'ofa saida KK ya fara wucewa sannan shi kuma ya biyo shi a baya, tun kafin su k'araso tsakiyar falon Hasheem ya nufe su da gaggawa 6acin ranshi ya kai koluluwa shiyasa yana zuwa ya chafko wuyan Tajo.

"Ni za ku yaudara ni za ku cinyewa kud'i batare da kun min aiki da nasaku ba sannan har kai Tajo kake min barazana a waya?"

Kafin Tajo ya yi yunk'uri kwatar kanshi Kk ya fito da pistol daga aljihun black leather jacket ɗin jikinsa, ya nuna Hasheem da ita cikin kakkausar muryar ya ce.

"Sake shi ko na tashi kokon kanka da wannan.

Da mugun sauri Hasheem ya saki Tajo jikinsa ya shiga kakkarwa.

"Karka yi haka kk ka dawo min da kudina tun da kun kasa aiwatar da contract ɗin, na k'ara muku two days nan ma kun kasa komai kuma a gabanku Azaad Junaid zai wuce ba ku yi masa komai ba. Ko jiya ina la6e ina kallonku naga lokaci da ya fito daga gidanshi ya wuce ku amma ba ku yi masa komai ba. Hakan ke nuni da cewa ba za ku iya ba.....

"Rufemin baki kafin na sauke dukkan fushina akanka Hasheem. Kana tsanmani kisan Azaad Junaid sauk'i ne dashi?" Kaine kake yi wa Azaad kallon sakarai amma shi yasan abin da ya taka. Shu'umancinsa ya zarce naka, zai fi maka alkhairi da ka hak'ura da son ganin bayansa. A cikin kwanaki biyu da ka k'ara mana kasan irin bala'o'in da muka dinga cin karo dasu a duk lokaci da muka yi yunk'uri sheke shi?" Jiya har dare muna la6e a jikin katangar kamfaninsa, a maimakon na kashe shi ni ne na kusa mutuwa saboda haka ka nemo wani yai maka wannan aiki, Amma inaso kasani
duk yadda kake tunani Azaad Junaid ya zarcewa tunaninka. Kud'inka kuma k'arfi yaci idan ka matsa sai na dawo dasu to kasani komai zai iya faruwa daga ciki har da rasa rayuwarka. Saboda haka ka za6a ranka ko kud'inka?"

"Ba zai yu ba kk kud'inan su na da yawa fa.....

Kafin ya k'arasa magana kk ya buge tsakiyar kanshi da bindigar hannunshi, zafi da radadin azaba suka ratsa kwakwalwar Hasheem ya kurma ihun neman taimako tare da sulelewa k'asa yana dafe da fasashe kanshi da ke zubda jini, duk da haka kk bai kyaleshi ba saida ya har6eshi a k'afarshi ta dama yana k'ok'ari sake saki mashi wani harsashe a k'irji Tajo ya dakatar dashi ta hanyar jan shi da k'arfi suka fice daga falon. Kasancewar a gidan gona suke, gate yana da nisa da inda suke shiyasa duk ihu da kururuwar da Hasheem ke yi maigadi bai ji ba.
Har jini ya buge shi ya some.
***** **** ******
A hankali take saukowa daga matattak'alar jirgi yayin da k'awarta Hafsat Shinkafi ke biye da ita kamar jela. Tun kafin su k'araso direbanta mr Michael ya buɗe musu k'ofufin mota duk lokaci da tai tafiya Mr Michael ne Kaɗai ke sani dawowarta.
Duk gaisuwa da yake mata ko kallo bai isheta ba, sai Hajiya Hafsat ce ta amsa mishi. Sai da suka fara sauke Hafsat Shinkafi gidanta koda ta iso gidanta ana kiran sallar magarib.

Cike da izza ta fito daga mota da azama mr Michael ya nufi k'ofar main parlor ya buɗe mata, jin k'arar takon takalminta ya sanya Nanny Lacey ɗagowa daga tattara toys ɗin da Ahlam da ta gama wasa dasu, gabanta ya yi mummunan faɗuwa sakamakon gani madam Salima. Jikinta na rawa ta gaidata tsabar girman kanta da izzarta basu bari ta amsa ba sai yatsunta guda biyu ta ɗagawa Nanny Lacey, ta haura staircase ta nufi 6angarenta.
Nanny ta bi ta da kallo inda sabo ta saba da ɗagawa da izzar madam Salima.

Yanzu duk tsawon shekaru da ta d'auka tana mata hidima da yaranta ace bata kallonta da gashin arziki, kusan watani biyu har da sati uku kenan da tayi tafiya ko a waya bata ta6a kiranta ta ji lafiyar yaranta ba.
Hakazalika ta dawo ko ba za ta tayi lafiyarta ai ta tambaye na yaranta.
Shigowar mr Michael janye da luggage ɗinta ya katsewa Nanny zance zuci da take. Ta kar6i trolley ɗin daga hannunshi ta kai mata d'akinta koda ta shigo tana cire kayan jikinta a hankali ta ajiye mata luggage ɗin har Nanny ta buɗe k'ofa za ta fita ta ji ta kira sunanta.

"Nanny!

"Yes madam!

"Ki sanarda Azaad na dawo amma karki faɗawa yara ki bari sai zuwa gobe, saboda ina da buk'atar cikakken hutu.

Tsabar takaicinta da ya lullu6e Nanny Lacey kasa magana tayi sai jinjina kanta tayi, har ta koma d'akinta tana yaba rashin k'awa zuci irin na madam Salima.
Miyya ta fito daga wanka a gaugauce ta tsane raguwar ruwan jikinta ta zura doguwar riga da hijab tayi sallar magarib bata tashi ba har saida tayi sallar isha.

Samun kanta tayi da yi simple makeup ta sanya wide legs trouser haɗi da pink bias top ta yane kanta da scarf jikinta na fitarda sanyayye kamshi.
D'akin Aneesah ta shiga domin ta k'ara mata haske akan assignment ɗin da aka basu bayan su kammala assignment ɗin.
Su kayi dinner sannan ta dawo d'akinta.

Nanny Lacey na cikin goge dining table Azaad ya shigo cikin girmamawa suka gaisa, kana ta sanarda shi madam ta dawo nan take annurin kan fuskarshi ya d'auke cakk... kamar an yi ruwan sama an dauke, ita kanta Nanny ta lura da sauyawa tashi faratt d'aya. Bai ce da ita uffan ba ya nufi 6angarenshi.

Har Miyya ta kwanta ta tuna da bata bai wa Daddy abinci ba ta tashi zubur, ta d'auki scarf ɗinta da ta cire ta fito downstairs parlor. Ta nemi cushion ta zauna tana jiran fitowarshi har 11:00pm ta buga bai fito ba. Batasan cewa yau a 6angaren Jadda ya yi dinner ba. Da taga ji da zama sai kawai ta yanke shawara ta kai mishi coffee.
Tana sanda kamar 6arauniya haka take tattaka matattak'alar bene da zai sadata da 6angarenshi, tana zuwa k'ofar falo bata tsaya neman izzini ba ta buɗe ta shiga kanta tsaye ta wuce falonshi na biyu.

Yana zaune da system a gabanshi yana gudanar da online meeting, sallamarta ce tasa shi ɗagowa, har ta k'araso inda yake zaune bai d'auke idanuwanshi daga kanta ba. A k'asan zuciyarshi yake yaba tsin-tsan kyau da tayi a cikin kwanaki nan completely ta sauya wa sanin da ya yi mata, gashi ta hanawa zuciya da gangar jikinsa natsuwa bashida aiki sai na tunaninta, idan har bai yi da gaske ba yarinya k'arama za ta zauta shi saboda haka zai taka mata birki, kada ta kai shi da aikata abin kunya.
Ta sauke tray hannunta akan center table cikin sanyayya murya ta ce.

"Daddy yau lafiya ba ka fito dinner ba?"

Ya kalleta cikin d'aure fuska gudun kada taga damarshi, ya ce.

"Naci a 6angaren Jadda.

"Iyeee....ashe yau Daddy dad'i kaci.

Ta faɗa tana dariya mai ban sha'awa......
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004



22....




Baisan lokaci ya da ya saki mata murmushi ba, a k'asan zuciyarshi so yake ya taka mata birki ta daina shigowa mishi part amma ya kasa furta mata sai kawai ya tsincin kanshi da faɗin.

"Kema za ki iya zuwa ki ci dad'in.

Ya k'arasa magana yana zuba mata idanuwanshi, masu rikita ta a duk lokaci da ya kalleta dasu.
Ta rausayar da kai tana ci gaba da murmusawa cikin sigar shagwa6ar da murya ta ce.

"Ba wani nan Daddy da kaso naci dad'in da ka zo min da nawa ko kuma lokaci da za ka je 6angarenta da ka aiko min da katin gayyata"

Yadda take magana tai masifar tafiya da ruhi da gangar jikinsa, ya gama fahimta muddin bai da gaske ba tsaf k'aramar yarinya nan za ta zuzuta shi a hankali ya ɗago idanuwashi ya sauke su akan fuskarta wacce ke ta glowing cikin haske bulb ya saki murmushi tare da furta.

"Wai ke bakya ji barci ne?"

"Uhm..bana ji"

Ta faɗa tana turo d'an k'aramin bakinta, hakan ya k'ara kunna wutar abin da yake ji akanta da sauri ya kauda fuskarshi yayin da gabanshi ke wani iri bugawa da k'arfi. Ya sauke numfashi kana ya nuna cushion ɗin da ke facing ɗinshi da hannunshi batare da ya yi magana ba. Da kanta ta fahimci abin da yake nufi cikin salon tafiyarta mai jan hankali ta nufi kujerar ta zauna, ta ɗago idanuwanta suka sark'e da nashi bugun zuciyarsu ya tsananta. Tai sauri runtse idanuwanta tana jan wahalallen numfashi.
Ta sadda kanta k'asa.
Shiru ya biyo baya shi bai tanka ta ita kuma bata sake yi magana ba ko wane su yana faman da bugun zuciya, Azaad ya kasa samun wadatatciyar natsuwa da zai ci gaba da gudanar da meeting ɗinshi lokaci zuwa lokaci take ɗagowa ta saci kallonshi kuma duk sanda ta ɗago idanuwashi na kafe akanta tamkar yana karanta wani abu, akanta ne.
Rashin natsuwa da yake ji yasa sai faman shafar sajenshi yake yi can kuma cikin rikitatciyar murya ya ce.

"Pretty ki je ki kwanta please kinsan gobe kina da school ko kinaso ki yi latti tashi ne?"


Kamar jira take yi ya bata umarnin tashi ta mik'e zubur ta nufi k'ofar fita saida ta rik'e handle ta juya tare da faɗin.

"Goodnight Daddy!

"Goodnight"

Ya faɗa kamar mai ciwo hak'ora. Ta k'arasa ficewa kamar yadda ta shiga part ɗin nashi cikin sand'a haka ta fito tana sand'a tana isa k'ofar d'akinta tai wuff....ta shige tare da rufu k'ofa. A tsorace take gudun kada tsautsayi ya gitta Aneesah ko Airah wani daga cikinsu ya gannta ta fito part ɗin Daddynsu, dole su tambaye me ta je yi a halin yanzu batasan amsar da za ta basu wacce za ta zama kariya agareta.
Da wuri Miyya ta tashi kamar yadda ta saba ta shirya cikin school uniform ɗinta sosai uniform ɗin suka k'ara fidda kyawonta.
Side by side suke tafiya ita da Aneesah zuwa parking lot kasancewar Airah tariga su fita tuni take zaune a mota tana zaman jiransu sai faman zabga tsaki da duba agogo take yi, saboda tana da presentation gashi suna so 6ata mata lokaci.

Azaad Junaid da ke tsaye a balcony da mug ɗin coffee a hannunshi lokaci zuwa lokaci yake sipping idanuwanshi suka sauka akan fuskar Miyya dai-dai tana kai ma Aneesah duka a kafad'a da alama Aneesah ɗin tana tsokanar ta ne. Har suka isa gun mota suna wasa a tsakaninsu.
Yayin da dai-dai da second d'aya bai d'auke idanuwanshi akanta ba. Gani yadda skirt ɗin uniform ɗinta ya tsaya iya gwiwoyinta, gashi d'an k'aramin hijabi half sunna suke sakawa ga hijabi yabi k'irjinta shiyasa ake iya gani satin cikakkun boobs ɗinta.
Take ji wani iri mashahurin kishi wanda tsawon zamanshi da Salima bai ta6a ji kwatan-kwacinsa ba.
Ga Salima ba iri banzar shigar da bata yi da sauri yasa ɗayan hannunshi ya dafe saitin zuciyarsa da ke mishi barazanar tsalle ta faɗo k'asa.

"Na shiga uku ni Azaad meke shiri faruwa dani?"

Ya faɗa a baiyane, yayin da fuskarshi ta bayyana tsoron da ke shigar shi ya sauke wata k'arfaffiyar ajiyar zuciya, jikinshi a mace ya nufi gym room{d'akin motsa jiki} gym mat machine ya fara hawa tsawon lokaci ya share akanshi kafin ya yi switch off ɗinsa.
Jikinshi ya jik'e sharkaf da gumi. Direct bathroom ya wuce ya yi wanka cikin minti goma ya shirya cikin black suit yana cikin ɗora wrist watch, ya ji an turo k'ofa ta jikin mirror da yake tsaye ya hango madam Salima tana sanye da bathrobe ta ɗora small white towel akanta da alama fitowarta daga wanka kenan ta shigo part ɗin nashi.
Yana arba da ita ya ji wani irin 6acin rai shiyasa yai sauri d'auke idanuwanshi akanta ya mayar bisa wrist watch ɗin.
Ta k'araso cikin izza da jiji da kai ta zauna gefen gadonshi tai crossing legs ɗinta babu sallama balle ya ci daraja gaisuwa ta kalleshi cikin izzarta da tafi komai bashi haushi a tattara da ita ta fara magana kamar wacce aka yi wa dole.

"Ina da tabbacin kana da masaniya da tun jiya na dawo, am very sure Nanny ta faɗa maka sak'on dawowata.

Ta d'an dakata da magana tana wani yatsine fuska tana jiran ta ji ya fara apologies ɗinta sai taga kawai yana k'ok'arin saka derbies black cover shoe ɗinsa Kuma ta lura da tun lokaci da ta shigo ko kallonta bai yi ba.
Hakan ba k'aramin sosa mata rai ya yi ba. Cikin fushi ta kira sunanshi.

"Azaad!

A hankali ya ɗago idanuwashi ya k'are mata kallo tass....kana ya cije lower lips ɗinshi tare da ɗage girar ido idan Azaad Junaid yana so yai mata mutum wulak'anci irin kallonan yake yi gani yake ba k'aramin koma baya bane a gareshi ya tsaya, musanya yawu da ita musanmman da yake da important meeting, saboda haka ya d'auki briefcase ɗinshi da ke aje akan bedside drawer ya nufi k'ofar fita cikin yanayi tafiyarshi ta k'asaita.

"What hell think you're Azaad ina magana da kai you're ignored me?" Lets me tell I can take this anymore.

Girgiza kanshi tare da buɗe k'ofa ya fice abinsa, ta taso cike da masifa ta biyo shi a baya tana ci gaba da zazzaga mishi masifa.

"Azaad come back here I want to talk to you karka fita ka tsaya nace zan yi magana da kai banso wulak'anci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login