Showing 30001 words to 33000 words out of 91651 words

Chapter 11 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

608

nace dake na tsaneta?"

"Ba sai kin faɗa min ba Aneey ga alamomi nan a bayane, ko magana tai miki a lalace kike amsawa Ina laifin wanda ya damu da kai.

"Wai ke Airah meke damunki ne huh?" zuwan wannan Miyya gaba daya kin canza, ba ki da zance sai nata wato ta zo ban bata fuska ba shine ta turo ki, da yake bakida kunya shine za ki zo ki cika min kunne Dan Allah tashi ki fita min daga d'aki banaso tak'ura.

Haushinta ne ya turnuk'e Airah ta juya a fusace ta buɗe k'ofa da k'arfi, ta fita. A falon k'asa ta tararda da Miyya tana zaune Ahlam tana kwance akan cinyoyinta taso tai mata korafi akan zuwanta d'akin Aneesah sai kuma ta fasa, ta kalleta a natse ta ce.

" Pretty ko za ki tashi mu tafi flat ɗin Jadda kwana biyu ba mu lek'a ta ba.?"

Da sauri ta tashi dama tana sanye da gown na atamfa ta yane kanta da k'aramin veil.
A falo suka iske Jadda tare da mai aikinta Mero, da yake wannan zuwan shine karo na uku da Miyya ta je 6angare Jadda.
Da yake Jadda tasan komai akan Miyya, ta yaba matuk'a da hankali da natsuwarta Sosai taji ta kwanta mata a rai. Saidai fargabarta d'aya idan uban gayya Azaad ya dawo zai kar6e ta kuwa ya kuma zamanta da Madam Salima zai kasance?" Da yake Azaad bai faɗa mata ya saki Madam Salima ba.
Shiyasa duk lokaci da suke je 6angarenta sai ta ke6e gefe d'aya da Miyya tayi mata nasiha.
Sosai Miyya ke jin k'aunar Jadda a zuciyarta.
**** ***** ******
Misali k'arfe biyu na dare ciwon mara mai tsanani ya tashi Aneesah, sai juyi take yi ita Kaɗai akan gado dama ga goganyar taku da raki tsiya ta 6are baki ta shiga rera kuka duk lokaci da za tayi menstruation sai tayi ta fama da ciwon mara.
Tun tana kuka da k'aramin sauti har ta dawo tana yi da k'arfi, gani kuka ba zai mata magani komai ba ta d'auki wayarta, ta kira Nanny Lacey.
Can cikin barci Miyya ta ji ringing ɗin wayar Nanny Lacey da Airah ta aro mata tayi waya da Amrah da Amal, ashe Airah ta manta bata mayar mata ba.
Cikin magagin barci ta mik'a hannu ta d'auki wayar da ke aje akan bedside, da nufi tai switch off ɗinta sai kawai taci karo da sunan Aneesah gabanta ne ya fara faɗuwa, saboda tasan da wuya in kira na lafiya ne kasancewar da ta dauko wayar sai da dubi lokaci.
Tai picking tare da karawa a kunneta cikin muryarta mai cike da barci ta ce.

"Hello.....Aneey Miyya ce wayar Nanny Lacey tana hannuna kina bukatar wani abu ne ko na Kai mata wayar ne?"

"Wayyo Allah pretty ki taimake ni zan mutu...

Muryar Aneesah tai mata dirar mikiya a dodon kunneta, babu shiri ta wartsake daga raguwar barci da bai k'arasa sakinta ba. Cikin azama ta mik'e zaune.

"Subhanalillah.....Aneey ba ki da lafiya ne?"

"Mara ta ke ciwo dan girman Allah ki taimaka min ki kira Nanny Lacey.

"Okay..gani nan zuwa.

Ta faɗa cikin rawar murya a rikice ta saka thongs slippers ta buɗe k'ofa, a rud'e take haura staircase tana murd'a handle ta ji k'ofa ta buɗe, ta kutsa kai ta hango Aneesah kwance sai mul-mula take yi in ta kai k'arshen gado ta dawo farko da gudu ta nufe ta gaba ɗaya ra rungumo ta zuwa jikinta.

"Sannu....sannu....Aneey kin sha magani kuwa?"

Cikin tsananin zafin ciwo Aneesah ta girgiza kanta.

"Akwai magani ne ko na tashi driver mu kai ki asibiti?"

"Ki duba cikin bedside drawer yana ciki.

Aiko kamar jira Miyya take yi ta ɗora kanta a pillow ta k'arasa da sauri ta binciko magani, ta buɗe fridge ta dauko water bottle hannunta na rawa ta 6alle murfi tare da 6allo magani ta ɗago Aneesah tasa mata a baki tasha.
Sai faman sannu take mata.
Aneesah sarkin raki ta bi ta k'am-k'ame Miyya, hakan da tayi sai ya k'arawa Miyya tausayinta, batasan lokaci da ta fara tayata kuka ba.
Sai daff da asuba barci ya d'auke ta, kanta na bisa cinyoyin Miyya ita kuma ta jinginar da bayanta ga gado a haka tayi barci k'arar alarm da ya karad'e d'akin ya falkar da Miyya ta dauke kan Aneesah a hankali daga cinyoyinta ta ɗora a pillow kana ta wuce bathroom tayi koda ta kammala sallah Aneesah ta buɗe idanuwanta a hankali ta bi d'akin nata da kallo karaf idanuwanta ya sauka akan Miyya.
Kwakwalwarta ta soma yi mata backwards ɗin abin da ya faru, da hanzari Miyya ta cire hijabi ta nufo wajenta.

"Sannu Aneey ya jikin naki?"

Da sauri ta rufe idanuwanta cike da tsan-tsan kunyar tunawa da irin wulak'anci da ta dinga yi wa Miyya, amma bata kunlace ta ba. Ta kuma taimake ta a lokaci da take tsananin buk'atar taimako. Kasa amsawa tayi sai kawai ta yunk'ura ta sauk'o daga gado batasan cewa lokaci da take barci period ɗinta ya zo gaba ɗaya sleeping dress ɗin jikinta da bedsheet ya lalace da jini.
Da sauri ta runtse idanuwanta Miyya ta dafa kafad'arta cikin sanyi murya ta ce.

"Sannu Aneey tun da ya zo ai lafiya ta samu bari na had'a miki ruwan wanka.

Bata jira jin ta bakinta ba ta shiga bathroom da saurinta ta had'a mata ruwa kana ta fito da towel t mik'a mata, jikin Aneesah ya yi sanyi lak'ass...ta kar6i towel ɗin cike da kunya ta cire kayan jikinta tana rik'e da kayan ta shiga bathroom Koda ta fito Miyya ta canza mata bedsheet.
Tana cikin saka kaya Miyya ta shiga bathroom babu kyama balle kyakyami ta wanke bedsheet da kayan da ta cire ta fito dasu cikin rubber bucket.
Sosai Aneesah ta girgiza da gani hakan nan take ta tuna da ranar da ta fara menstruation hakan ne ya faru da ita a lokaci, madam Salima tana gida bata yi duba da shine ranar ta na farko ba ta 6al-6aleta da masifa, wai bata so k'azanta da sakarci haka ta fita abinta tabar ta sai Nanny Lacey ce ta taimaka mata ta kuma nuna mata yadda ake yi. Tsabar haushi abin da mommynta tayi mata yini tai tana kuka a d'aki sai gashi yau, wacce ta rena ta kuma tsana tayi mata abin da uwar da ta haife ta ta kasa yi mata.
Har Miyya ta fita ta Sanya kayan a backyard ta dawo Aneesah tana tsaye gaban mirror tana zuba tunani.

"Aneey ki kwanta ki huta yau ba sai kin je school ba tun da ba ki da lafiya bara na haɗu miki breakfast"

Muryar Miyya ta dawo da ita natsuwarta, har Miyya ta juya ta ji Aneesah ta rungumeta ta baya tana shasshekar kuka cikin muryar kuka take faɗin.

"I'm very sorry pretty please forgive me I know I hurt you several times, Dan Allah ki ce kin yafewa marar kirki Aneey...

Da sauri Miyya ta juyo da ita ta rik'e hannayenta duka biyu ta kalli cikin idanuwanta tana murmushi, kana ta ce.

"Na yafe miki Aneey dama ban ta6a rik'e ki a zuciya ta ba. Kawai nasaka araina rashin fahimta ne a tsakaninmu, Kuma wata rana za ki fahimce ni.

"Thank you so much Pretty you're the simplest, sweetest and best person I ever come across in my entire thank you for having you in my life. Zuwanki alkhairi ne a gidanmu da ma rayuwarmu duka.

Ta k'arasa magana tare da sake hugging Miyya tightly, tuni tasa Miyya 'yan mata hawaye Aneesah ce ta fara janye jikinta, tasa hannu ta goge hawayen kumatunta tana jin wani irin farin ciki da annashuwa wanda ta dad'e rabon da ta ji kanta a ciki.
Miyya ta fice kaitsaye d'akinsu ta wuce koda ta shiga Airah ta fito daga wanka, a gurguje ta ba wa Airah labari abin da ya faru sosai Airah tai farin ciki jin Aneesah ta sauko har ta ba wa Miyya hak'uri.
Daga ranar Miyya da Aneesah shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakaninsu suka dawo k'awaye, dukansu sun matsu daddy ya dawo akai miyya school ɗinsu.
A cikin dare jirgin da Azaad Junaid ya shigo ya sauka a Malam Aminu Kano international airport.....


*Not Edited!!*
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004



17....


Yana yi yadda yake kallonta yasa ta k'ara rikicewa, yayin da Yana yinta ke sauyawa a hankali ta sauke idanuwanta k'asa, a dalili wani bak'on al'amari da take ji yana shigarta.
Ci gaba da k'ureta da kallon kurilla ya yi, babu ko alama dake nuna shi ɗin zai d'auke rikitattun idanuwanshi daga kanta.
Ya ja dogon numfashi kana ya sauke, a hankali ya girgiza kai so yake ya k'aryata zarginshi ko ta hali yaya, sai kawai ya ciro wayarshi, daga aljihu ya kira Dr Jannat ita ce likitar da ke kula da yaranshi.
Ya dubi Miyya da raguwar mamaki da har yanzu ya kasa sakinsa cikin dakakkiyar muryarshi mai cike da k'asaita ya ce.

"Je ki tsaftace mata jikinta kafin Doc ta k'araso.

Da sauri Miyya ta nufi d'akinta da ita cikin k'ank'ani lokaci ta gyarawa Ahlam jikinta ita ma ta sauya kayan jikinta, kasancewar Ahlam bata da Kaya a d'akinta yasa ta lullu6e ta cikin towel ta fito sa6e da ita a kafad'a.
Ta haura upstairs inda d'akin Ahlam yake babu ce kawai babu a d'akin. Duk wani abu na more rayuwa an zuba mata a ciki kama daga toys da teddy bear gasu nan birjik.
Duk lokaci da Miyya ta shigo d'akin nata sai ta tsaye ta k'arasa masa kallo kusurwa-kusurwa, tana mamaki yarinyar da bata ko cika shekara d'aya ba ke da wannan tangamemen d'aki.
Closet ɗinta ta buɗe mai d'auke da suturanta kala daban-dabam.
Ta ciro pink gown tana cikin saka mata ta sake shak'a wani amai, gaba ɗaya rigar tasake lalacewa.
Tsananin tausayinta ya sake kanainaye zuciyar Miyya, musanmman yadda take ta kakarin amai, dole ta sake komawa bathroom da ita ta wanke mata jikinta, ta kuma wanke gun da amai ya sami rigarta.
Tana fitowa sa6e da ita a kafad'a Azaad tare da Doc Jannat su na shigowa.
Miyya tai tsaye turuss...a bakin kofar bathroom ta kasa k'arasowa, suna had'a idanu ta ji wani iri yarrrr....tsigar jikinta ya tashi.

"K'awo ta mana na duba ta"

Sautin muryar Doc Jannat ya hankaltar da ita hali da take ciki. Ta tako a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ta mik'awa Doc Jannat ita da sauri Ahlam ta mak'alewa Miyya alamar bata zuwa, gani haka yasa Miyya ta dosana duwawunta a gefen gado yayin da Doc Jannat ta dukufa duba ta.
A hankali Miyya ta ɗago idanuwanta ta saci kallon Azaad Junaid da ke tsaye a dai-dai k'ofar shigowa ya tattara hankalinshi akan wayar hannunshi.
Jikinshi ya bashi cewa ana kallonshi yana ɗagowa Miyya na sauri sadda kanta k'asa, tuni ya gano ita ce mai kallon nashi.
Doc Jannat ta kammala duba Ahlam ta fiddo da drip ta saka mata ihunta yasa Miyya ta ɗago babu shiri, Doc Jannat ta gani rik'e da hannun Ahlam tana, neman jijjiya, duk inda ta soka allura sai ta cire saboda, bata do gun da jijjiyar take ba.
Ta saki ɗayan hannunta ta sake kama ɗayan. Duk lokaci da Doc ta soki hannun Ahlam sai Miyya ta runtse idanuwanta tamkar jikinta ne ake hudawa. Duk abin da ta ke yi Azaad yana kallonta ta gefen ido yadda take runtsar idanu yai masifar bashi dariya sai kawai ya yi murmushin gefen baki.
Sau biyu doc Jannat tana sukar hannun Ahlam bata Sami jijjiya ɗin ba.
Tana shirin yi na uku Miyya ta rik'e mata hannu tamkar za ta fashe da kuka ta ce.

"Please Doc ki kyaleta haka mana, kalli dukan hannuwanta duk ki bi ki huda su kamar kin sami kwarya"

Dakatawa Doc Jannat tayi ta ɗago da yawaltatce murmushi akan fuskarta ta ce.

"Nima ba a so raina nake huda ta ba, ki yi hak'uri na k'arasa aikina.

K'in sake ta tayi sai ma k'ara dank'e hannun nata tayi, yayin da idanuwanta suka ci-ciko da hawaye.

"Ki barta tayi aiki kada ki 6ata mata lokaci"

Muryar Azaad ta daki dodon kunneta, ta ɗago manyan idanuwanta ta galla mishi harara, don ba k'aramin haushinsa take ji ba.
Tun shigowarsa yake tsaye yana dannar waya, kamar bai damu da taratsi kukan Ahlam ba. Ba don ranta ya so ba ta saki hannun Doc Jannat, tare da kauda fuskarta sai da Doc ta kammala mata fixing drip ɗin sannan ta dawo da ganinta akan Ahlam wacce ta lumshe idanuwanta alamar tanaso tayi barci.
Gani haka yasa Azaad ya fita daga d'akin Doc Jannat tattara kayanta ta bi shi a baya.
A downstairs parlor ya tsaya still idanuwanshi na kan wayarshi ya shiga tambayar Doc Jannat ciwon da ke damun Ahlam.

"Zazza6in hak'ora ne ke damunta Yalla6ai zan dawo da yamma idan bata daina amai ba, gaskiya sai an sake k'ara mata wani drip"

Ya jinjina kanshi.
Doc Jannat ta mik'a mishi prescription ta tare da furta.

"Kafin na dawo ayi k'ok'ari a siyo wad'annan magunguna.

Nan ma sake jinjina kanshi ya yi bayan doc Jannat ta tafi, ya nufi 6angaren Jadda ya nufa zuciyarshi a cakude bayan ya gaisa da Jadda mero ta kawo mishi Karin kumallo ya d'an tsakura Kaɗan saboda damuwar da yake ciki, zance na gaskiya idan har hasashen shi ya hasaso masa gaskiya wannan tatsutsuwar yarinya da ya gani sa'ar Aneesah matashi to kuwa akwai matsala babba. Wannan ai abin kunya ne gotai-gotai dashi ya aure sa'ar 'yar cikinsa. Ai sai girma da k'imarshi su zube a idanu mutane duniya.
Wayarshi ya dauko ya kira Hakeem ya zo yana so ganinshi gara ya zo su yi ta manya-manya daga tushe, kafin Hakeem ya iso ya kalli Jadda da ke mishi zance Aslamiyya kamar tasan abin da ke nukurkusar zuciyarsa. Rai 6ace ya fara magana.

"Wai Jadda kina nufi wannan 'yar k'ank'anuwa yarinya da nagani ita ce matar tawa?"

"Kwarai kuwa ita ce ai nice nace da Hakeem ya 6oye kada ya yi saurin baiyana maka da ita gudun kada kace tayi maka k'ank'anta, ka fasa auren ni kuma a duniya nan ta maliki yaumidini bana da buri da ya wuce ka k'ara aure kai da yaranka za ku sami kyakkyawar kulawa da gantalalliyar matarka ta kasa ba ku.

Ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauke tare da shafa kwantattace sajenshi wanda hakan ya zame masa dabi'a. Kafin ya tattaro natsuwashi wuri guda ya ce.

"Jadda idan kina min hasashen kulawa to kin tafka kuskure domin wannan kwaila ba abinda za ta iya, azahirin gaskiya ni an cuceni tare da linkeni bai-bai saboda Hakeem ce min ya yi bazawara ce har da yara biyu. Ashe duk k'arya ce da yaudara saboda haka yadda yadda kawota haka zai dawo ya d'auki abarshi don ni ba mutumin banza bane balle araina min hankali"

Hakeem da ya turo k'ofa zai shigo karaf furuncin Azaad na k'arshe ya sauka a kunnenshi, cikin mutuwar jiki yai sallama Jadda ce Kaɗai ta amsa Azaad kuma ya amsa a cikin zuciyarsa. Muryar Hakeem Kaɗai da ya ji saida ya k'ara linka masa 6acin rai da takaicinsa.
Hakeem ya mik'a masa hannu da nufi su yi musabaha, ya kwada masa katuwar harara, ya kauda fuska.
Hakeem ya mak'e kafad'a tare ta6e baki ya nemi cushion dake facing ɗinshi ya zauna, ya gaida Jadda ta amsa kana ya zarce da faɗin.

"Jadda ki shiga cikin lamari nan saboda Aj ya dau zafi dani, ni kuma shawara da kika ɗorani akai na bi. Don haka kar ya sake ya ga laifina.

"Wannan haka yake Hakeem tun kafin ka zo na faɗa na Kuma k'ara jadaddawa Aslamiyya tayi min d'ari bisa d'ari....

"Haba Jadda ya za ki faɗi haka gaskiya ni dai ba ai min adalci ba?" Kuma inaso kasani Hakeem saboda yarda da nayi maka yasa na ba ka ragamar rayuwata da ta iyalina sai gashi ka rusa wannan yarda.

"Karka faɗi haka Aj domin wallahi-tallahi ban zantar da hukunci ba saida amincewar Jadda, aganina ko mayya Jadda ta nuna tanaso ka aura za ka amince da gaggawa ba tare da tambayar ba'asi ba. Balle yarinya mai cike da nagarta iri Aslamiyya wacce samun irinta a wannan zamani sai an sha matuk'ar wuya. Duk wani qualities da kakeso a jikin mace Aslamiyya tana dashi, ita ce mace da za ka faɗa ta ji, ka kafa doka ta bi ba tare da tayi fatali da ita ba. Ita ce za ta girmamaka ta mutunta igiyar aurenka ta kuma zame maka ma'adanar sirrinka, ta so ka ta k'aunace 'ya'yanka Aj kada ka bi rudin zuciya ka daure Dan Allah da manzonsa ka kar6i, Aslamiyya a matsayin matarka. Yarinya nan rayuwarta cike take da k'alubali a tunanina kaine za ka kawo mata sauyi a rayuwarta kamar yadda nake da yak'ini za ta kawo babban sauyi a rayuwar gidanka"

Azaad ya dafe kokon kanshi saboda Hakeem da Jadda sun ri ga da sun gama daure shi da kalamansu. Yana matuk'ar k'aunar Jadda domin ita Kaɗai ta rage mishi ita ce yake kallo a matsayin mahaifiyarshi yayin da Hakeem yake da babban matsayi agareshi, abokinshi ne tun na yarinta duk wata gwagwarmayar rayuwa a tare suka yi shima maraye ne kamar shi saidai Hakeem yana da K'anwa daya kachal Zainab sa6ani shi da Jadda ce Kaɗai yake da sai shirgin 'yan uba da kullum burinsu su ga bayanshi. Kasa magana ya yi hakan ya bai wa Hakeem damar zayyane masa tarihin Miyya bai 6oye masa komai ba. Sosai ya ji ya tausaya musu ya kuma kudurta aranshi zai kula da ita a matsayi 'ya ba mata ba, har sai zuwa lokaci da za ta mallaki hankalin kanta ta yadda za ta iya 6ance-6ance tsakani abin da takeso da wanda bataso.
Ya yi shiru bai sake magana ba sai ma jinginar da gadon bayanshi ya yi a jikinta ya lumshe idanuwanshi gani haka yasa Hakeem ya yi hamdallah domin shiru da ya yi shine amincewarsa da bai amince ba tashi kawai zai yi ya bar musu falon.
**** ****** *****
Miyya tana rik'e da hannu Ahlam ko nan da can bata gusa ba, yanzu haka fitsari take ji amma ba za ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login