Showing 33001 words to 36000 words out of 91651 words

Chapter 12 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

616

iya shiga bathroom ta barta Kaɗai ba.
Sai da drip ya k'ara ta fita kiran Nanny Lacey ta zo ta cire mata sai lokaci ta faɗa bathroom ta rage nauyi tare da d'aura alwala saboda lokaci sallar Azhar ya yi har kuma zuwa lokaci Ahlam tana sharar barci abinta.
Hatta da abinci Nanny Lacey ce ta kawowa Miyya a d'aki sai misali k'arfe uku Aneesah da Airah suka dawo daga school, sai lokaci su ka san Daddynsu ya dawo sosai suka shiga murna ganinshi.
Yini daya kacal har Ahlam tayi rama tun tana mamaki rashin dawowar Azaad ya duba Ahlam har ta dawo tana zance zuci.

"Wannan wane irin uba ne?" Fissibillahi 'yarka bata da lafiya ka kasa nuna kulawarka akai.

Wani 6angare na zuciyarta ya ce.

"Daina ganin laifinsa Miyya mahaifiyarta ta fi shi laifi kasancewar mace Kuma uwa amma ta iya tsallakewa uwar duniya ta bar 'yarta mai watani goma.

Abin da ke d'aure mata Kai ya Kuma k'ara dumulmula mata tunani tare da hargitsa mata kwakwalwa, bai wuce tun zuwanta gida dai-dai da rana d'aya bata ta6a gani Madam Salima ta kira waya domin ta ji lafiyar yaranta. Dama Azaad kafin ya dawo kusan kullum sai yai waya dasu which means Azaad ya fi damu dasu fiyye da Madam Salima. Idan kuwa hasashenta ya kasance gaskiya tabbas Madam Salima batasan ciwon kanta ba, ta kuma san darajar 'ya'ya ba.
Ta 6angaren Azaad Junaid yana damu sosai da son sani hali da Ahlam take ciki, ya tambayi Nanny Lacey ya kai sau uku ya jikinta sai ta ce dashi tana barci duk da haka hankalinshi bai kwanta ba, yana so ya je d'akinta ya gannta sai kuma ya tuna da Miyya tana d'akin baya so duk wani abu da zai danganta shi da ita. Gudun kada ta rena shi. misali k'arfe biyar na yamma ya Kira Doc Jannat ta zo ta k'ara duba Ahlam ta ji sauk'i sai da zafin jikinta da har yanzu bai rage ba. Amma ta daina amai duk da haka sai ta sake sa mata wani drip.
Gani yadda Ahlam ta jigata ya k'ara linka masa haushi da tsanar Madam Salima, ya kuma jefa shi cikin nadama haɗi da danasani aurenta.
Misali karfe 8:30pm ya 6aro flat ɗin Jadda ya kira Nanny Lacey ta kawo mishi Ahlam ya gannta yana part ɗinshi.
Koda Nanny Lacey ta shigo d'akin Miyya har tayi shirin kwanciya barci saboda throughout bata huta ba tana ta fama da Ahlam.

"Pretty har kin kwanta ne?"

Cewar Nanny Lacey lokaci da takai dubata wurin da Miyya take kwance sanye da sleeping gown yayin da Ahlam take kwance akan cikinta, sai da tayi k'ok'ari tashi zaune kana ta amsa da cewa.

"Eh! Nanny nagaji ne sosai ga Kuma barci da nake ji.

"Ayya sannu pretty ai kina k'ok'ari sosai ba Kaɗan ba, dama Yalla6ai ne ya ce akawo mishi Ahlam ya gannta"

Jin abin da ta faɗa yasa Miyya ta6e baki wato sai yanzu ya yi lokaci Ahlam ɗin, fuskarta babu wal-wala ta shiga k'ok'arin mik'awa Nanny Lacey Ahlam, yayin da Ahlam ta fasa ihu da sauri Miyya ta dawo da ita jikinta ta rungumeta tana shafar gadon bayanta.

"Nanny ki faɗa mishi wallahi yau gaba ɗaya yarinya nan k'iyya take ji bata yarda da kowa ai dai kin ga yadda nake fama da ita ko bathroom ban isa na shiga na barta ba.

"Nasani pretty daurewa za ki yi ki kai mishi ita tun da ni bata yarda dani.

Da sauri Miyya ta kalli Nanny Lacey fuskarta cike da zallan mamakin furuncinta.........



*Not Edited!!*
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004

16....


Azaad ya fito daga jirgi as usual fuskarshi a murtuk'e babu annuri ko Kaɗan. Ya shak'i sanyayye iskar mai dad'i gaske, kana ya saki ajiyar zuciya. Direbanshi mr Richard ya je daukarshi. Duk da yana cikin yana yi na rashin jin dad'i hakan, bai hanashi furta addu'ar neman tsari daga sharrin abin hawa ba.
"Bismillahi majraha wa mursaha Inna Rabbi laa ya gafurum Rahim"

Mr Richard ya buɗe mishi k'ofa ya kame a owners corner, tun shigar shi jirgi yake jin canji a jikinshi wanda ya rasa gane na menene.
Ta 6angaren Hasheem Kuma ya sami labarin dawowar Azaad.
Ya tura 'yan ta'adda da ya yo hiring su ka la6e a wajen Airport su na jiran fitowar Azaad. Akan idanuwansu Mr Richard ya fito daga cikin airport King Kevin ya duba agogon hannunshi k'arfe biyu da rabi yasaki kafirin murmushi, kana ya fito da silent pistol ya gyarata da kyau.
Kana abokin aikinshi Tajo ya kai hannunshi da suna ya tashe mota, ya ji babu key da sauri ya kunna haske dake cikin motar ya ga babu key cike da zallan mamaki ya ke duba k'asan kafafuwanshi Koda ya subuce ya faɗi.
Wasa-wasa key ɗin ya ci tudu ya ci rafi, da sauri dukan su suka fito daga mota Tajo sai faman lallu6e ajihunshi yake yi cike da takaici ya shure tayar mota tun su na iya hango hasken motar Azaad har ta 6ace musu fatt....su na ji su na gani mission ɗinsu ya yi failed. Babban abin da ya daure musu kai bai wuce lokaci da suka koma cikin mota ba sai ga key sakale a jikin mota, alamar yana nan a mazauninsa su ne Allah ya d'aukewa gani, shiyasa basu ganshi ba.
Cikin kariyar ubangiji da tsarewarshi Azaad Junaid ya iso gidanshi, cikin k'oshin lafiya.
Ya yi amfani da k'ofar baya ya shiga part ɗinshi dama haka yake yi duk lokaci da ya yi tafiya ya dawo cikin dare ta k'ofar yake bi.
**** ***** *****
*A WASHE GARI*

Tun Asuba da Miyya ta falka bata koma barci ba, ta zauna tana morning azkar, sai misali k'arfe 7:00am ta kammala.
Ta sauya kayan jikinta zuwa wata half gown wacce ta sauka iya gwiwoyinta, d'an zamanta da Aneesah ta koyi amfani da english dress.
Kitchen ta nufa ta tararda da Nanny Lacey tana fera Irish ta shiga taya ta cikin k'ank'ani lokaci suka kammala arranging table, kana ta wuce d'aki tayi wanka tana cikin sanya earrings. Aneesah ta shigo cikin school uniform, murmushi suka sakewa junansu.

"Ina Airah?"

Miyya ta faɗa tare da daukar perfume bottle tana fesawa jikin kayanta.

"Tana Dining room ke muke jira za mu wuce school kada mu yi latti.

"Okay mu tafi kawai dama na kammala shiryawa sai na tuna ban saka earrings ba shine na tsaya sakawa sai gashi kin shigo.

Ta k'arashe magana tare nufar k'ofar fita Aneesah tana biyo ta baya a haka suka isa dining room, agurguje Aneesah tasha ruwan tea, Miyya tai musu rakiya zuwa parking lot idan direbansu ke zaman jiransu. Har motarsu ta fice daga gate ɗin gidan tana tsaye rungume da hannayenta a k'irji, sosai take sha'awar karatun boko saidai a duk lokaci da tuna Amrah da Amal suna zuwa school, sai taji wani irin dad'i marar misaltuwa ya lullu6e ta. Ko bata samu damar ci gaba da karatu ba tun da siblings ɗinta sun samu shikenan burinta ya cika.
ta d'auki dogon lokaci a tsaye kafin ta dawo cikin gida.
Sai misali k'arfe 11:45am Azaad Junaid ya falka daga barcin gajiya ya yi wanka ya shirya cikin brown jallabiya, ya saka flip flops a k'afarshi jikinsa na fitarda sihirtattace k'amshin turaren casual oud gold edition. Cikin takonshi na k'asaita yake saukowa daga staircase. K'amshin turarenshi da Nanny Lacey ta shak'a daga kitchen ya isar mata da sak'on dawowarshi. Da sauri ta wanke hannuwanta ta fito, ta iske shi tsakiyar falo tsaye.

"Barka da dawowa Yalla6ai.

Ta faɗa cikin hausarta da ta zauna daram a halshenta. Ya amsa mata ba tare da ya kalle ta ba.

"Yalla6ai akwai abinci a dining room na zuba maka ne?"

Ta faɗa kanta yana kallon k'asa. Sai da ya d'auki lokaci kafin ya jinjina kanshi, da mugun sauri ta nufi dining room.
Miyya na zaune a d'aki rungume da Ahlam wacce ta lafe a jikinta tun jiya ta ji jikinta da zafi da safe da ta zo yi mata wanka ta ji jikin nata yafi jiya zafi a haka ta lalla6ata tai mata wanka ta shiryata cikin riga da wando ta ɗora mata cardigan akai.
Lokaci da ta je had'a mata madara a kitchen, ta sanarda Nanny Lacey ta bata maganin zazza6i madarar ma Kaɗan tasha ta kauda fuska, sai kawai Miyya ta bata magani shine fa ta sake yin barci a cikin barci ta zabura kamar wacce ta tsorata, ta fara tsala kuka a rikice Miyya ta fito daga bathroom. Ta d'auke ta taji jikinta ya yi wani irin mugun zafi, kafin tayi wani yunk'uri Ahlam ta fara kwara mata amai ta baki da hancinta duk idan hankali Miyya yake ya tashi, da gudu ta fito da dukan k'arfinta take kwallawa Nanny Lacey kira.

"Nanny Lacey! Nanny Lacey! zo ki gani jikin Ahlam ya yi tsanani sai amai ke fitowa ta baki da hancinta, na shiga uku Nanny Lacey kada wani abu ya sami ta...

Idanuwan Miyya sun rufe sam bata lura da Azaad Junaid dake tsaye nesa da ita Kaɗan yana waya da Hakeem, hatta da Hakeem sai da ya ji ihunta, ta cikin waya nan take ya ji matsanancin faɗuwar gaba a nufinshi yanzu da suke waya yana yunk'urin baiyanawa Azaad wacce ya auro mishi sai gashi Miyya ta rage mishi aiki ta baiyana kanta. Tun kafin shi ɗin ya baiyyanata.
A gigice Nanny Lacey ta fito daga dinning room hannunta rik'e da serving spoon tsabar rudewar da tayi manta da yana hannunta.
Azaad ya waiga a zafafe inda Miyya ke tsaye ya ga wacece ke mishi wannan ihun na fitar hankali, dai-dai lokaci da Ahlam ta sake kwara wani amai gaba ɗaya ya wankewa Miyya jiki.
Gudu-gudu ya iso wajen Nanny Lacey ta mik'a hannu za ta kar6e ta, sai kawai tsala ihu tare da k'am-k'ame Miyya.

"Kawo ta nan"

Cike da k'asaita ya yi magana tare da mik'a mata farare hannuwanshi tass.....da k'arfi Miyya ta kalle shi yadda take kallonshi ba ko kyaftawa zai tabbatar maka da ta tsorata matuk'a da ganinshi.
Tsananin rudewar da tayi yasa bata lura da lokaci da ya iso kusa dasu ba.
Yadda take kallonshi yai masifar bashi haushi.

"Ke nace ki mik'o min ita!

Ya faɗa cikin tsawa hakan ya tsorata Ahlam ta k'ara k'am-k'ameta, tana mai k'ara sautin kukanta. Jikin Miyya ya d'auki rawa ta shiga k'ok'ari ciro Ahlam daga jikinta yayin da ita kuma sai k'ara rirrik'eta take yi.
Gani ba za ta iya rabata da jikinta cikin sauk'i ba yasa Azaad ya zagaya bayan Miyya don Ahlam taga fuskarshi.

"Zo nan Ahlam zo wajen Daddy kinji?"

Ya yi magana tare da rik'o hannunta, ta ɗago idanuwanta ta kalle shi kamar tana so tunawa da fuskarshi, sai kuma ta sake fashewa da kuka ta fincike daga rik'e mata hannu da ya yi.
Wani irin mashahurin mamaki ya rufe shi saboda Ahlam bata ta6a mishi haka ba. Sosai shiga rud'ani wacece wannan yarinya menene alak'arta da gidanshi da har 'yarshi ta shak'u da ita har haka?"
Take furuncin Hakeem ya faɗo mishi lokaci da yake waya dashi, ya ji lokaci da ya ce dashi "Aj
Ina so mu yi magana ta fahimta akan amaryarka...
Sai kawai ji sautin ihun Miyya dole ya katse kiran.
Cikin tsananin tsoro mai cike da zallan tashin hankali Azaad Junaid ya dawo gaban Miyya ya ɗaga dara-dara manyan idanuwanshi, ya bi tun daga tsakiyar Kan Miyya har zuwa ga kafafuwanta da kallo.....

*Not Edited!!*
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004



18....

Cikin tsananin fusata Hasheem ya cakume collar rigar king Kevin yana k'ok'ari kai masa nushi gani haka yasa Tajo ya taso da sauri ya rik'e masa hannu domin ya tabbata idan har ya kuskura hannunshi ya sauka a jikin KK tabbas da wuya ya kai gobe.
Yayin da KK yake kallonshi hankali kwance jira yake yi ya aikata abin da yake nufin aikatawa ya tashi kokon kanshi da alburushi.
Tajo ya ja shi gefe yana bashi baki da kyar ya shawo kanshi ya k'ara musu two days idan har kwana biyu ya cika basu kashe masa Azaad Junaid ba, dole su dawo masa da kud'insa.
Wanda daga Tajo har KK suke gani ba abu mai yuwa bane dawo da kud'i koda kuwa ba su sami nasarar cimma manufarsu ba.
6ata musu lokaci da baro garinsu da suka yi ba za su yi shi a banza ba. Idan har Hasheem ya kafe lallai sai sun dawo mishi kud'insa to kuwa haka yana nufin numfashinsa za bar gangar jikinsa.
***** **** *****

"Ya naga kin 6ata rai?"

Nanny Lacey ta faɗa tana kallon Miyya wacce fuskarta ta baiyyanar da rashin walwalarta a fili ta ce.

"Ki yi hak'uri Nanny bai kamata na shiga flat ɗinshi ba, gara na tsaya matsayina na mai kula da yaranshi"

Cikin kwantar da murya Nanny Lacey haɗi da rarrashi ta ce.

"Haba pretty miyasa za ki faɗi haka ne? Shi fa mijinki ne mallakinki idan har kika ce za ki dinga nisanta kanki dashi babu amfani auren naku kenan.

"Ba laifina bane Nanny Lacey sai nake gani kamar shi ma ya fiso hakan"

"Ba haka bane Pretty yalla6ai yana da sauk'i kai ta wani 6angare zan iya cewa yana da wuyar sha'ani. Amma ba za ki fahimce hakan ba har kin bai wa aurenku muhimmanci.

"Nanny ba za ki gane bane shi ma fa yana da manufar da yasa ya aureni"

"Ke yarinya ce k'arama pretty ba za ki yi saurin fahimtar wasu abubuwa cikin sauk'i ba. Ki sani na dauke ki tamkar jikata shiyasa nakeso ki sami rayuwa mai inganci. Rayuwar Yalla6ai Azaad tana tsanani buk'atar mai tallafa mata, Kuma kece za ki kawo wannan tallafi ki d'aure ki yi min biyayya bisa ko wane umarni da zan dinga ba ki, wallahi ba zan ta6a yi abin da zai cutarda ke ba.

Shiru Miyya tayi tana nazari maganganu Nanny Lacey d'aya bayan d'aya hakan ne ya bai wa Nanny damar ci gaba da fayyace mata, yana yi rayuwar Azaad Junaid da ta iyalinsa. Kana ta zarce da rarrashinta da kalaman kwantarda hankali da haifar da natsuwa. Sosai jikin Miyya ya yi sanyi ta tsinci kanta da tausayawa su Amrah ko Kaɗan ba ta ji tausayi Azaad ba ganinta shi ya siyawa kanshi saboda shine miji madam Salima mata duk dokar da ya kafa mata dole ta bi koda ace ranta bayaso. Nanny Lacey ta d'an buge kafad'arta ta dawo natsuwarta ta sauke ajiyar zuciya.

"Naga Ahlam ta sami barci ki kwanta kawai zan faɗa mishi kun yi barci amma dan Allah pretty da safe ki yi k'ok'ari ki kai mishi ita kinga shi ba girmanshi bane ya dinga zuwa d'aki nan ba kinji yarinyar kirki?"

Miyya ta jinjina kanta amma a k'asan zuciyarta tana ji kamar ba za ta iya ba ta amsawa Nanny Lacey ne kawai don ta shafa mata lafiya. Nanny tai mata sai da safe ta fice kana Miyya ta maida kanta bisa pillow tare da rungume Ahlam cikin jikinta daga haka barci mai dad'i ya yi awon gaba da ita. Da fitar Nanny Lacey ta kira Azaad a waya ta faɗa mishi Ahlam tayi barci, duk sai ya ji ba dad'i saboda yana so yaga yanayi jikinta tun safe rabonshi da ita ya fi tsawon minti goma yana safa da marwa daga wannan kusrwa zuwa wannan, daga k'arshe yasaka flip flops a k'afarshi ya fito cikin takonshi na k'asaita d'akin Ahlam ya nufa duk da ba shi da tabbacin ko zai tararda ita, ko Kuma k'ofar d'akin tana a buɗe. A natse ya turo k'ofar luckily ta buɗe ya yi amfani da wayarshi ya haska d'akin idanuwanshi suka hasko masa kan gado Miyya rungume tsam....da Ahlam tamkar ita ce ta haifeta bai san adadin mintocin da ya d'auka yana kallonsu cike da sha'awa wani irin girma da matsayi ya ji zuciyarshi ta bai wa Miyya ya k'arasa daff dasu ya harde hannuwanshi yana mai ci gaba da kallonsu ji yake ko zai shekara a tsaye ba zai gaji da kallonsu ba. Irin kulawar da yake so ya ga Madam Salima tana bai wa yaranshi kenan saidai kashh...Salima bata da lokacinsu business ɗinta yafi mata muhimmanci fiyye da kula da yaranta sai gashi Allah ya kawo k'aramar yarinya mai k'anana shekaru ta magance masa wannan matsalar wacce bai ta6a tsanmani magance ta cikin sauk'i ba.
Ya girgiza kanshi tare da hamdallah, kana ya fice daga d'akin yana shiga d'akinshi ya zarce bathroom ya yi alwala ya shiga zuba nafilfili tare da rokon ubangiji ya k'ara wanzar da farin ciki a rayuwarshi da ta iyalinsa.
**** ****** ******
Washe gari da wuri Miyya ta tashi kamar yadda ta sabawa kanta, ta taimakawa Nanny Lacey suka had'a breakfast bayan Aneesah da Airah sun wuce school ta dawo d'aki tayi wanka ta shirya cikin tsadaddiyar material gown irin dinki ready made wanda ake zuwa dashi daga Dubai. Yana d'aya daga cikin kayan da Hakeem ya siya mata a yanzu kan hutu ya zauna a jikinta fatar jikinta ta k'ara haske sai shek'i take.
Miyya 'yar duma-duma ce bata da tsayi sosai za a iya sakata a jerin gajeru, tana da doguwar fuska tana da hanci dai-dai gwargwado tana da yalwatatce gashin kai da na gira k'irjinta cike yake fam...ga Kuma manyan hips tubarakallah Ma-sha-Allah!
Bata cika so d'an kwali ba shiyasa ta yane kanta da k'aramin veil da ya dace da kayan jikinta tana cikin fesa turare, Ahlam ta falka daga barci ta d'auke ta nufi bathroom da ita tai mata wanka, ta shiryata cikin red gown ta d'aure mata gashinta da red band, tayi matuk'ar kyau duk da ta d'an yi rama cikin hukunci na ubangiji yau da tashi babu zazza6i a jikinta.
Ta d'auke ta suka fito downstairs parlor kaitsaye kitchen ta nufa ta tararda Nanny Lacey tana goge gas cooker yayin da Linda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login