Showing 81001 words to 84000 words out of 91651 words

Chapter 28 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

630

girl ni ya dace ta kashe domin ni nayi mata laifi ba pretty ba.

"Ana ta hauka ba za ta fahimci haka ba Aj, ni wallahi narasa jinsi da zan jefa Salima ciki, ga dak'ik'anci ga zallar dabbanci da zubda k'ima banta6a sani mahaukaciyar ka auro ba Aj sai yau, to da ta kashe 'yar mutane tana gani za ta sha ne?"

"Ko yanzu Hakeem ba za ta sha ba jini prettyn Daddy ba zai zuba a banza ba, na rantse da Allah a wannan karo sai na nunawa Salima nima tantiri ne na k'arshen littafi, sai na wulak'antata wulakanci da ko sunana ta ji sai zuciyarta ta buga"

"Gaskiya this time ina bayanka abokina gara ka nuna mata kuskureta na dakar maka mata.

Azaad ya yi kwafa tare da cizo lower lips d'inshi, kusan one hour likitoci suka dauka akan Miyya, an mata dinki a gefen goshinta ga gocewa a hannunta na dama sai small injuries da ke sassan jikinta, bayan su kammala treatment d'inta aka kaita special room Azaad ya yi tsaye akanta yana kallon yadda fuskarta ta kumbure suntum gwanin ban tausayi, hawaye ya ji sun zo masa da sauri ya goge su bai barsu suka sauko ba. Ya kalli Nanny Lacey ya ce.

"Nanny Lacey ki zauna tare da ita zan fita amma ba zan dad'e ba zan dawo

"Okay Yalla6ai!

Nanny Lacey ta fad'a jiki a mace ta nemi d'aya d'aga cikin kujeru d'akin ta zauna, Azaad ya kalli Hakeem ya ce.

"Zo mu tafi Hakeem.

Cikin sauri Hakeem ya bishi a baya. Lokaci da Salima ta fito compound ta kira direbanta mr michael ya zo ya dauke ta, kaitsaye babban masana'antarta ya kai ta hankalinta kwace ta gudanar da meeting da employees kamfaninta, tana fittowa direbanta ya sake daukarta suka fice daga company.

Duk inda Azaad yake sa ran gani Salima ya je bai ganta ba lokaci da ya zo company aka ce dashi bata dad'e da fita ba, dole ya hak'ura ya umarce Hakeem su koma hospital har zuwa lokaci Miyya tana sharar barci.
Hakeem ya umarce Nanny Lacey ta tashi ya maidata gida, saboda yara ranta baiso ba so tayi sai taga Miyya ta farfado suna ficewa Azaad ya nufi gadon da take kwace ya kura mata idanuwa kafin ya zauna ya riko hannunta cikin nashi sallah ce ke fidda shi daga d'akin bata falka ba sai around 4:40pm, lokaci Azaad ya shiga bathroom koda ya fito tana rarraba idanuwanta kusurwa-kusrwa d'akin cikin sanyi jiki Azaad ya iso wurinta.

"Sannu pretty ashe kin falka na shiga bathroom ne?"

Ajiyar zuciya tayi batare da ta ce uffan ba ta shiga k'ok'arin tashi zaune, ya taimaka mata tare da saka mata pillow a bayanta ta jingina kana ya had'a mata ruwan Lipton mai zafi da tea spoon ya dinga diba yana bata a baki, saida tasha sosai kana ya zuba mata abinci da Hakeem ya kawo masu.

"Daddy kayi hak'uri Allah bai nufi zan girka maka abinci bud'a baki ba kamar yadda ka buk'ata amma idan naji sauki zan maka ka ji?"

Kamar daga sama ya ji zazzakar muryarta a dodon kunnenshi, da sauri ya d'ago daga rufe warmer d'in da yake yi yaga gaba d'aya idanuwanta na kanshi, wani irin tsananin tausayinta da zazzafar soyayyarta suka lullu6enshi baisan lokaci da ya jawota jikinshi ya rungumeta gam.

"Allah sarki prettyn Daddy kina cikin wannan hali amma kina tunanina, karki damu farin cikina fatana Allah ya ba ki lafiya kuma in-sh-allah sai na bi miki hakkinki sai na nunawa Salima kuskureta na ta6a min ke da tayi...

Da sauri ta d'ago daga jikinshi ta rufe mishi baki da tafin hannunta.

"Daddy Dan Allah ka yafe mata kada kayi mata komai, ko ba komai taci darajar 'ya'ya da ke tsakaninku..

"Ya isa pretty na fahimci ke bakisan ciwon kanki ba idan ba ki son kanki ni ina sonki fiyye da so da nake yi wa kaina, ba zan lamunci wata banza wacce ta gama wulak"antani ta nuna min ban isa ba ta ta6a min ke wallahi-azim a wannan karo sai naci zarafin Salima, koda kuwa mutane duniya ga baki d'aya za su taro akaina"

Yadda taga yana fad'a ya bata tsoro ta shige jikinshi ta zagaye cikinshi da hannuwanta, ya k'ara shigarda ita k'irjinshi yana shafar gadon bayanta wata irin natsuwa suka ji tana saukar masu a cikin sassan jikinsu.
Anan asibiti Azaad ya yi bud'a baki daga fitarshi masallaci kaitsaye gidanshi ya wuce a masallaci k'ofar gidanshi ya yi sallah magarib da isha'i, koda ya shiga gida 8:30pm tayi saboda ya tsaya waya da Hakeem direct d'akin Salima ya wuce yana tura k'ofa tana fitowa daga bathroom sanye da bathrope
5/16/22, 17:44 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004



40...

Duk da ganinshi da tai a dai-dai wannan lokacin. Ya haifar mata da matsananci fad'uwar gaba. Hakan baisa ta nuna a fuskarta ba, sai ma kallon uku saura kwabo da tai mishi kana ta nufi dressing mirror cikin tafiyarta mai cike da izza da zallar k'asaita tana mai ci gaba da goge sumar kanta da k'aramin towel d'in dake rik'e a hannunta.
Ganinta da Azaad yai da kuma halin ko in kula da ta nuna masa ga wata izza da tak'ama da take yi, ya k'ara harzuk'a shi, a fusace ya maida k'ofa ya rufe tare da murza mata key ya kuma cire key d'in ya saka a aljihun rigarshi.
Cikin kidima da tashin hankali Salima ta kalle shi da idanuwanta da a yanzu suka baiyanar da tsananin tsoratatta a fili, musanmman da taga yana tunk'arota fuskarshi a murtuk'e babu fara'a ko kad'an, duk tsawon shekaru da ta share tare dashi bata ta6a ganinshi a cikin irin yanayi nan ba. Shiyasa cikinta ya murd'a ya bada sauti mai k'arar gaske take taji gudanawa ya zo mata da son samu ne da ta ruga bathroom ta rage cikinta. Saidai tazarar dake tsakaninta da bathroom idan ta ce za ta ruga kafin ta kai k'ofar bathroom d'in yai mata kamun kazar kuku, ta tabbata wannan zuwan nashi bana alkhairi bane domin bahaushe ya ce labarin zuciya a tambaye fuska, yanayi fuskarshi kadai ya isa ya gamsar da ita manufarshi akanta ba mai kyau bace.
Duk ta bi ta rud'e ta rasa abin yi can kuma ta shiga ja da baya tare da furta.

"Me ya shigo da kai d'akina a dai-dai irin wannan lokaci ko ka manta ne da ka sake ni, a yanzu babu saura komai a tsaka....

Kafin ta k'arasa magana yai kukan kura ya dank'o wuyanta ya kaita jikin bango ya manna ta shiga ihu da neman dauki, saida ya tabbatar da ta jigata, sannan ya saki mata wuya kana ya had'e hannuwanta duka biyu da hannunshi guda, yasa d'ayan hannu ya shiga wanke mata fuska da maruka babu kakkautawa hanci da bakinta ya fashe sai zubda jini take, shi kuwa ko a jikinshi saida ya gaji da marinta kana ya saki hannunta ya bi ta da duka ta ko ina jingarta yake yi, ya murde mata hannu da dukkan karfinsa shi da kanshi ya ji lokaci da hannun nata ya ce kattt! Alamar da ke nuna ya goce ko ya karye tsananin ihu da kururuwar da take yi ya janyo hankali 'yan aiki da securities d'in gidan. Aneesah dake d'akinta a kwance damuwa ta fara yi mata yawa, kamar daga sama ta ji ihu mommy kamar da wasa ta ji ihu sai k'ara k'aruwa yake, babu shiri ta diro daga gado ta bud'e k'ofa da gudu ta fito koda ta iso main parlor ta tararda masu aiki da securities tsaye cirko-cirko kowane su yana tsoro ya shiga apartment din madam ya kira wa kansa ruwa. Da kallo Aneesah ta bisu dashi kafin ta sake kwasawa da gudun fanfalak'i ta haura matattakalar bene da zai sada da ta da apartment d'in mommy, da k'arfi ta tura k'ofar bedroom d'inta sai ta ji k'ofar a rufe ruff da dukkan k'arfinta ta shiga bugun k'ofar had'i da kiran sunanta.

"Mommy... mommy meke faruwa me kike yi wa ihu ke da waye a d'akin Dan Allah mommy ki zo ki bud'e k'ofar nan?"

Tun Aneesah tana magiya har ta dawo kuka da sauti mai k'arfi saboda sai k'ara jin ihu mommynta take yi, da alama tana cikin matuk'ar wahala.

"Na shiga uku mommy idan ba ki bud'e k'ofar nan ba wallahi zuciyata za ta iya bugawa.

Aneesah tai magana tare da gunji kuka, ta sulele k'asa dafe da kai, tun zuwanta Azaad ya ji muryarta 6acin ran da yake ciki ne ya hanashi daina dukan Salima yanzu kuma da ya ji sautin kukan Aneesah da farucin da tayi sai jikinshi yai sanyi ya saki Salima ta zube k'asa numfashinta yana fita guda-guda. Yasa k'afarshi yai mata mugun shuri a ciki sannan ya nufi k'ofar ya bud'e ido biyu yai da Aneesah wacce tana jin k'arar bud'ar k'ofa ta mik'e zubur, wani irin kallo take yi wa Daddy nata mai cike da tarin manufofi, batare da Azaad yai mata magana ba ya bi ta gefenta ya wuce cikin sauri.
Cikin zallar tashin hankali ta bishi da kallo domin ko kusa ba ta kawo aranta shine a d'aki ba ta dawo da ganinta akan k'ofar d'aki da ya barta a bud'e, ta k'arasa shiga ta tararda da Mommy kwace magashiyan, tana fidda numfashi da kyar a rikice ta durk'usa tana girgiza ta tana kuka.

"Mommy Dan Allah ki tashi mommy ki tashi mana Dan Allah karki mutu ki bar mu...

Da ta fahimce hakan ba zai fishe ta ba sai kawai ta mik'e da gudu ta sauko downstairs parlour ta nemi taimakon housemaid da har yanzu suna nan tsaye duk da akan idanuwansu Yalla6ai Azaad ya sauko ya wuce su ko gaisuwa da suke masa bai amsa ba. Balle su tambaye shi dalilin ihun Madam Salima.
Mr Michael da d'aya daga cikin securities d'in gidan ne suka taitayo Madam Salima wacce bata da ban-banci da gawa yadda take sanye da bathrope haka suka nufi asibiti da ita.

Azaad yana fitowa direbanshi mr Richard ya bud'e mishi mota ya shiga, kaitsaye asibiti ya koma. Koda ya shiga d'akin da Miyya take tana zaune Nanny Lacey ta dora mata bowl din fruits salad akan pillow tana sha da d'ayan hannuta mai lafiya, ta d'ago idanuwanta a hankali ta sauke su akan fuskarshi batasan lokaci da tasaki masa tattausan murmushi ba. Ya mayar mata da martani amma fa shi nashi bai wuce iya fatar bakinshi ba. Nanny Lacey ta gaida shi ya amsa can k'asan mak'oshi kana ya zarce da fad'in.

"Nanny ki je mr Richard yana waje ya maida ki gida, ki Kula da yara please"

"Okay sir!

Ta fad'a tare da tattara warmers d'in d'azu Hakeem ya kawo abinci ta tafi dasu. Kusa da ita ya zauna ya lek'a bowl d'in gabanta kafin ya kalle ta cike da kulawa ya ce.

"Ya jikin naki prettyna?"

"Na ji sauki Daddy saidai hannun ne kawai yake min ciwo sosai.

Ya kai dubanshi ga hannun nata cikin sigar tausayawa ya ce.

"In-sha-Allah shi ma very soon zai daina amma fa sai kinsa dauriya I know you my pretty you're very strong girl thats why I love you so much.

Ya k'arashe magana tare da jan karan hancinta, murmushi tai mai sauti ta je sauke bowl d'in da sauri ya kar6a tare da tambayarta.

"Kin k'oshi ne?

Ta gyad'a kai still da murmushi akan fuskarta, ta matso a hankali ta kwantarda kanta a kafad'arshi, ya ajiye bowl d'in ya k'ara shigar da ita k'irjinshi lokaci zuwa lokaci suke ta6a fira.
Likitoci suka dukafa akan madam Salima ba su sha wuya ba wajen farfado da ita, a bincike da suka yi sun gano ta karye a hannu.
Kuma likitan k'ashi baya nan dole sai zuwa safe za su nemo shi haka aka turata a gadon marasa lafiya zuwa ke6attace d'aki, daga Aneesa sai Kuma mr Michael ne tare da ita anan suka kwana mr Michael yana waje a cikin mota Aneesah Kuma ta kwana akan cushion d'in da ke girke a d'akin sai a washe gari madam Salima ta dawo hayyacinta yayin da Aneesah ta tsare ta da tarin tambayoyi.

"Mommy me ke faruwa ne tsakaninki da Daddy?"

"Me kika yi wa Daddy da har ya harzuk'a shi ya lakkad'a miki irin wannan duka kamar bai san inda kika fito ba?"

Madam Salima ta d'ago kumburarriyar fuskarta da ta dawo kamar ta doddaniya ta kalli Aneesah da idanuwanta da jini ya gama kwantawa a cikinsu ga Kuma bakinta da ya kumbura sutumm dama la66anta suna da d'an tudu yanzu kuma da suka sha masga sai abin ya k'ara armashi, cikin tsananin azaba da radadin da hannunta ke mata ta ce.

"Banaso iskaci Princess ni sa'arki ce da za ki tsare ni da wasu stupid questions naki, nan da nace ki had'a kayanki ki koma gidan tsinane Daddy naki ai k'in bi umarni na kika yi to gashinan abin da nake gudu ne ya faru, shegiyar matarshi ta zugu shi ya zo har cikin d'akin barcina ya ci zarafina wallahi ba zan kyale shi ba sai na kai shi kotu ta bi min hakkina."

Har ta dasa aya a zancenta Aneesah tana kallonta da baki bud'e, kafin ta rausayarda kanta gefe tana wasa da igiyoyin da ke gaban rigar barci da ke jikinta.

"Anya kuwa mommy wannan labari naki akwai k'amshin gaskiya a cikinsa, shi fa Daddy ba mahaukaciya bane balle a zugu shi ya zo ya rufe ki da duka akwai dai mummuna abu da kika aikata masa mommy haka kawai Daddy ba zai zo ya dake ki ba.

Aneesah tana rufe bakinta mommy na ridar pillow da hannunta mai lafiya ta jefa mata cikin tsananin fusata ta ce.

"Banta6a sani Princess bakya k'aunata ba sai yau yanzu duk cin zarafina da Azaad ya yi akan idanuwanki amma Kuma shi kike supporting maza ki 6ace min da gani tun kafin na tattaro fushina na sauke shi akanki banza heartless wacce batasan zafin mahaifiyyarta ba.

"Allah ya ba ki hak'uri mommy wallahi ban fad'in wannan maganar ba don na 6ata miki rai, kawai dai nasan dukan mace ba hali Daddy bane ko mu da ya haifa bai ta6a dukanmu ba, balle ke da kike tsohuwar matarshi, adai tsananta bincike akwai babban laifi da kika yi masa kowa ya kalli yadda ya sauya miki kamanu yasan ba k'aramin laifi kika masa ba.

"Princess ni kike fad'awa wannan maganar?"


"Mommy I'm sorry inasonki ne shiyasa nakeso ki gyara halinki ki dawo good mother to us wallahi mommy na fi ki jin zafi dukanki da Daddy yai amma hakan ba zai sa na dake gaskiya na goyi bayan k'arya�?.


"Fita ki bani wuri Aneesah kafin na ci uban naki da kike goyo bayansa, fita nace karki sake zuwa kusa dani gaba d'ayanku na yafe ku, kema ki bi sahun 'yan uwanki.

"Mommy please stop saying that....

"Aneesah ki fita na daina ganinki before I loose my control nai miki abin da ubanki yai min, ki fita nace!

Ta k'arashe magana cikin shouting da gudu Aneesah ta ridi takalmin ta a hannu ta bud'e k'ofa ta fita saboda ta tsoro da yadda mommy ta, haiyak'o mata kamar za ta cinye ta.
Saida ta fita sannan tasa takalminta tare da gyara hular kanta cike da jin kunya ta ratso reception sai faman kallonta ake yi, duk wanda ya ganta da sleeping dress ai dole ya kalleta tana zuwa parking lot ta hango mr Michael zaune cikin mota da saurinta ta bud'e mota ta shiga.

"Mr Michael mai dani gida"

"Okay!

Ya amsa tare da yi wa motar key baya ya sauke Aneesah ya dawo hospital d'in...
5/20/22, 08:35 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004


41....

*BAYAN KWANA BIYAR*

A cikin kwanaki biyar kacal Miyya ta fara samun sauki kasancewar tana sumun kyakkyawar kulawa daga 6angarori biyu doctors da Daddynta. Wanda tsabar kulawar da yake bata ko nan da can bayaso ya kusa kullum yana manne da ita. Hakan ba k'aramin k'ara ma su kusanci da shak'uwa ya yi ba.
Azaad tare da Hakeem na hango a Aminu Kano international airport yayi da Azaad yake rik'e da hannun Hakeem cikin sanyi murya yake magana.

"Nagode sosai Hakeem bakina ya kasa bari gode maka Kai amini ne nagari Wanda samun irinsa a wannan zamanin da yarda da aminci suka yi karanci yake da matukar wahala, Ina maka fatar alkhairi Allah ya tsare ka ya kai ka lafiya ya dawo mana da kai cikin k'oshin lafiya.

Murmushi Hakeem ya yi kana ya fizgo hannu Azaad ya rungume shi tare da d'an bubbuga bayanshi.

"Amin thumma Amin abokina! Nima Ina maka fatar wanzuwar farin ciki mai dorewa sai na dawo ka ci gaba da kulawa da Aslamiyya Kuma karka manta da maganar da muka yi d'azu Dan Allah da zarar ka koma asibiti ka fad'a mata sirri da muke, 6oye mata domin banga amfani ci gaba da 6oye mata ba na fiso kafin na zo da miss Gambella ka sanarda ita kome.

"Shi kenan abokina yanda kace haka za a yi.

Daga haka suka yi Sallama a maimakon Azaad ya nufi hospital sai kawai ya wuce gida da nufi ya sake wanka sannan ya kar6i abincin Miyya.
Mr Michael ya tura k'ofar d'akin da Madam Salima take kwance, hannunshi dauke da basket d'in abinci duk lokaci da Aneesah ta biyo Mr Michael sai Madam tai mata kashedi kada ta sake ganinta, jiya saura kiriss ta mareta shiyasa yau tak'i zuwa ta ba Mr Michael abincinta ya kawo mata, tsakani da Allah ta gaji da ji zagin da take yi ma Daddynta.
Gaidata Mr Michael ya fara yi kafin ya ajiye basket d'in, ta amsa mishi as usual a wulak'ance har yanzu fuskarta tana nan a kumbure bakinta ne ya d'an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login