Showing 84001 words to 87000 words out of 91651 words
rage shi ma ba sosai ba.
"Mr Michael Ina ka baro Princess?"
"Tana gida Madam.
Shiru madam Salima tai tana nazari kafin tai kwafa. Mr Michael ya nemi wuri ya zauna yana wani musu-musu da baki had'i da sosa k'eya alamar akwai magana a bakinshi saidai baisan daga inda zai fara ba. Saida madam ta wulga masa harara saboda haushin kowa take ji, hatta da k'awarta Hafsat Shinkafi sun 6ata tun a washe gari da aka kawota hospital dalili kawai ta nuna Azaad ya fita gaskiya, kuma duka da yai mata bata ga laifinshi ba. Shi kenan ta rufe idanuwanta taci wa Hafsat mutunci had'i da yi mata k'orar kare tun daga ranar Hafsat Shinkafi bata sake dawowa dubata ba.
"Ya aka yi ne Mr Michael akwai magana ne?"
Da sauri ya gyad'a kanshi yai zubur ya mik'e tsaye kamar dama jira yake yi tai mishi magana, ya isa kusa da ita.
"Madam ki yi hak'uri da abin da Yalla6ai Azaad yai miki, shiyasa na yanke shawarar zan ba ki wata dauka da nayi{video} zai miki matuk'ar amfani.
Ya k'arashe magana tare da ciro wayarshi a gaban aljihun White shirt d'in jikinshi, ya kamo ya ui scrolling video da yake so nuna mata yasaka play ya mik'a mata. A yatsine ta kar6i wayar daga hannunshi tun kafin video ya zo k'arshe ta mik'e daga kwance da take, ta ma manta da ciwo da ke hannunta jikinta har wani rawa yake yi, yayin da ta firfitowa da idanuwanta cikin kad'uwa ta ce.
"Tun tsawon wane lokaci Mr Michael kake dauke da wannan video?"
"At last four to five days madam da farko naso nai blackmail d'in Yalla6ai Azaad dashi sai kuma ga wannan dukan da yai miki saboda haka inaso mu had'a hannu ki dauki fansarki cikin sauki. Kuma wannan video zai raba tsakani Yalla6ai da waccan yarinya.
Murmushi Madam Salima tai sai taji gaba d'aya ciwo da take ji ya ragu wani irin k'arfi ta ji a jikinta, cike da izza ta shiga tsarawa Mr Michael yadda take so sabon plans d'inta ya tafi.
Mr Michael yai murmushi mugunta ya kalleta da idanuwanshi masu cike da zallar mugunta ya ce.
"Don't worry madam your work is done.
"Thats what I like to hear from you make sure ba a sami matsala ba.
Murmushi kawai yai ya fice daga d'aki.
Azaad na shiga d'akinshi ya d'an kishigid'e akan resting chair tun waye war gari yake ji kasala da ciwon kai na damunshi nan take barci yai awon gaba dashi.
Miyya tana zaune ita kadai akan gado a d'akin da aka yi admitted d'inta, duk ta bi ta damu da rashi gani Daddynta ko me ya hana shi dawowa wurinta tun asuba da ya fita ya ce da ita zai raka Hakeem Airport zai wakilce shi wani business trip a Australia gashi har Ten of o'clock ta buga bai dawo ba. Bai Kuma ta6a yi mata haka ba matsalar abin bata da waya balle ta kira shi ta ji ko lafiya.
Tana cikin wannan tunani ta ji an bud'e k'ofa da sauri ta waiga tana murmushi azatota ko shine sai kawai tai tozali da Mr Michael.
Sai ta ji duk ba dad'i har fuskarta ta sauya ga kuma gabanta da ta ji ya fad'i, ya k'araso tare da gaidata da jiki ta amsa mishi ya nemi kujera ya zauna yana wani rausayarda kai kamar kadangare tare da yi k'asa-k'asa murya ya ce.
"Kina da labarin Madam Salima ita ma bata da lafiya?"
"Subhanalillah! Ai kuwa Daddy ya manta bai gayamin ba meke damu ta ne?"
Murmushi yai kafin ya kalli k'ofar shigowa saboda yana jin tsoro kada tsautsayi ya gitta Azaad ya shigo ya ji abin da yake shirin fad'a.
"Ai Yalla6ai ba zai fad'a miki ba saboda dukanki da tayi ne ya janyo mata ya je har can gida ya yi mata mugun duka, sai ma kin ganta za ki zaci had'arin mota ne tayi gaba d'aya fuskarta tai damage abin ba ko kyau gani in takaice miki labari har da karya mata hannu ya yi.
Cikin kad'uwa Miyya ta zaro idanuwa, bakinta har rawa yake yi wajen furta.
"Ban fahimce ka ba Mr Michael Dan Allah ka yi min bayani ta yadda zan gane inda labarin naka ya dosa.
"Ai ba za ki fahimta ba cikin sauki saboda ke Yalla6ai Azaad yana tsananin sonki, akanki zai iya aikata kissan kai domin saura kiriss ya kai madam lahira. Duk da nima ban ga laifin shi ba duk Madam ce ta jayowa kanta.
Ya yi shiru tare da tsare Miyya da idanuwanshi yana karantar reaction d'inta, ya ga gaba d'aya fuskarta ta nuna alamar razana dama haka yake so tun farko yana da yak'ini ba zai sha wahala wurin dumilmiyar da tunaninta ba, musanmman da yai duba da k'anana shekarunta. Da ya fahimci ta fara afkawa tarkonshi sai kawai ya zage dantse ta hanyar ci gaba da fad'ar.
"Ba ma wannan ba pretty azahirin gaskiya Ina tausaya miki domin akwai wani 6oyayye sirri da Yalla6ai Azaad ya 6oye miki Wanda ni aganina bai dace ya 6oye miki shi ba. Idan kuma aka yi duba a wani 6angare dole ne ya 6oye miki watakila bai shiryawa tunka'arar guguwar da ke shirin tunk'aroshi ba.
Cikin mutuwar jiki had'i da fad'uwar gaba Miyya take kallon fuskar Mr Michael saboda ya fara tsorata ta, kafin tai k'arfi hali furta.
"Watakila 6oyayye sirri bai shafe ni bane Shiyasa ya 6oye min.
"Ba ko d'aya kawai dak yana 6oye miki ne.
"To wai wannan wane irin sirri ne Mr Michael ni fa banaso katsalandan akan abin da bai shafe ni ba?"
"Pretty ni fa ina magana ne akan kashe miki mahaifi da Yalla6ai Azaad ya yi, zan kuma tabbatar miki da zancena babu karya a cikinsa. Saidai ina rok'o ki da wannan ya zama sirri a tsakaninmu idan har maganar nan ta fita kashina ya bushe domin nima Yalla6ai Azaad zai iya kashe ni kamar yadda ya kashe mahaifinki.
Tsananin tashin hankali yasa Miyya ta diro daga kan gado.
Batasan lokaci da ta isa gaban Mr Michael ba. Zuciyata na wani irin bugawa, cikin sark'ewar lafazi ta shiga magana.
"K'arya kake yi Mr Michael Daddy ba mugu bane kyakkyawan halinsa ba zai bar shi ya kashe koda kiyashi balle d'an adam ba.
"Ni kaina pretty da farko kallon hakan nake masa amma tun daga ranar da naji yana fad'awa abokinsa Hakeem a waya shi ya kashe miki mahaifi nayi matukar girgiza, amma bari na tabbatar miki da zancena babu k'arya a ciki.
Ya k'arashe magana tare da nuna mata video da ya dauka a lokaci da motar Azaad ta lalace ya dauko shi zuwa company akan hanyarsu yake waya da Hakeem anan yai nasarar d'aukar video da nufi yai blackmail d'in Azaad sai Kuma yanzu ya canza shawara saboda yana hange samu mak'udan k'udi daga hannun madam Salima fiyye da in ya yi blackmailing d'in Azaad.
Wani irin wahalallen numfashi Miyya ta sauke, a lokaci d'aya hankali da tunaninta suka goshe. Jiri ya d'ibe ta tai baya kamar zai ta fad'i da sauri Mr Michael ya rik'o kafand'unta ya nufi gado ya zaunar da ita, hawaye masu matuk'ar zafi suka wanke mata kumatu yayin da wani irin kululun bakin ciki ya tokare mata mak'oshi.
Mr Michael ya durkusa da guiwowinshi biyu a k'asa ya hade hannuwanshi waje d'aya ya k'ask'antar da murya ya shiga rok'onta.
"Na rok'e ki pretty ki rufa min asiri kada ki fad'awa Yalla6ai Azaad ni ne na fad'a miki wannan magana. Domin sanarda shi zai iya kawo k'arshen rayuwata.
"Kada ka damu Mr Michael no matter how ba zan anbace sunanka ba, amma wallahi tallahi k'arshen zama na da Daddy ya zo. Wai me Abbana yai mishi ne da zai kashe shi?"
"Pretty amsar wannan tambayar tana bakinshi idan ya zo ki tutse shi ya fad'a miki laifin da yai mishi, saboda ni dai bani da wannan amsar. Zan tafi amma ina k'ara rok'onki kada sunana ya fito a wannan zance.
Kukan da ya zo mata ne ya hanata amsa mishi sai gyad'a kanta tayi, Mr Michael ya bud'e k'ofa ya fita yana murmushi duk da ya yi nasara amma a k'asan zuciyarshi tsoro ne fal domin ba k'aramin risky ne ya jefa kanshi ba. Saidai akan k'udi ba irin hatsari da ba zai iya tunk'ara ba.
Koda Azaad Junaid ya farka daga naunauye barci da ya dauke shi 11:47am shi kanshi ya yi mamaki irin barci da ya nad'a shiyasa a gurguje ya yi wanka ya shirya cikin blue sky men material ya fesa favorite perfumes d'inshi yasa takalmin sannan ya bud'e k'ofa ya fito dai-dai yana saukowa daga matattakalar bene Aneesah na turo k'ofar main parlour janye da k'aramin trolley a bayanta kuma direban yara ne janye da manya-manya trolley d'inta har guda biyu bai mamakin ganinta ko kadan ba domin yasan hakan ce za ta faru, ba yanda za a yi zamanta da madam Salima ya dore.
Yana k'arasa saukowa ta rugu da gudu ta rungume shi tana dariya, murmushi kawai ya yi ya ciro ta daga jikinshi kasancewar yana sauri yasa kira Nanny Lacey ta miko mishi basket d'in abincin Miyya, ya umarce Aneesah ta biyo shi saboda san akwai magana a bakinta. Akan hanya take bashi lafiya yanda ta wakana a tsakaninta da Mommy kana ta zarce da fad'in.
"Daddy wai laifi me mommy tai maka ne ka daketa har da k'arya mata hannu?"
Shiru ya yi ya kasa magana saboda ko yaya aka tuna mishi da Salima sai ya ji sabuwar tsanarta da 6acin rai sun lullu6e shi. Saida ya ji 6acin ran nashi ya lafa kana ya ba Aneesah labari abin da ya faru. Bata yi mamaki ba domin tasan hali mommynta za ta aikata fiyye da hakan, a 6angare d'aya ta tausayawa Pretty.
Koda suka iso hospital 12:21pm Azaad yana gaba Aneesah da Mr Richard na binsa a baya yana tura k'ofa......
*Dan girman Allah ku k'ara hak'uri saura kiriss mu zo k'arshen labarin*
6/2/22, 20:27 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Top Ten Takun Haske Batch:A
*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004
42....
Ba k'aramin farin ciki madam Salima ta yi ba lokaci da Mr Michael ya je mata da labari ya cika aikinta saura kawai su jira sakamako.
Azaad yana tura k'ofa da sautin kukan Miyya ya fara cin karo a kid'ime ya isa wajenta ya juyo da ita sakamakon ta basu baya, gaba d'aya idanuwanta da fuskarta sun kumbura a dalili kukan da ta ci.
"Subhanalillah....kuka me kike yi pretty kodai hannu ne ya mutsa?"
Ya fad'a a rud'e tana juyowa ta buge mishi hannu da k'arfi, cikin muryar kuka take fad'ar.
"Karka kuskura ka sake zuwa inda nake ko kayi yunkuri ta6ani, saboda na tsaneka banaso ganinka mugu mai kashe mutane.
Rass...rass.....fass..fass!
Sauti da ya dinga fitowa daga k'irjin Azaad kenan, wani irin tashin hankali ya kawo masa ziyara, kafin yai magana Aneesah ta ri ga shi ta hanyar dallawa Miyya harara saboda har ta ji haushi yadda ta gayawa Daddynta magana.
"Ke pretty kin haukace ne da za ki dinga fad'awa Daddy irin wannan maganar sa'anki ne shi?"
"Ke ce mahaukaciya Aneey ni nan rass nake Kuma wallahi tallahi ba zan ta6a yafewa Daddynki ba tun da ya kashe min Abbana ya maida mu k'ask'antattun marayu sai Allah ya bi mana hakkinmu.
Azaad yai matuk'ar rud'ewa da jin kalaman da ke fita daga bakin Miyya mamaki yake yi ko waye ya fad'a mata wannan magana, domin daga shi sai ubangijinsa sai Kuma Hakeem ne suka san da wannan maganar. Hakeem Kuma bayanan balle yai tunani ko shine ya fad'a mata, ya kuma tabbata Hakeem ba zai furta wannan maganar ga kowa ba.
"Dan Allah pretty ki dawo natsuwarki, kidaina yi wa Daddyna k'azafi domin ina da cikakke yak'ini akanshi ba zai iya kashe kowa ba.
A fusace Miyya ta dawo gaban Azaad ta kalle shi da idanuwanta da ke tsiyaya hawaye ta ce.
"Idan har abin da na fad'a ba gaskiya bane Daddy ka kalli cikin idanuwana ka k'arya ta hakan.
Kasa had'a idanuwa da ita yai sai kawai ya kauda fuskarshi.
Cikin sauri Aneesah ta kar6e zance.
"Daddy ka kalleta mana ka fad'a mata ba kai bane tai gaggawa kawarda wannan mummuna k'azafi akanka ko wallahi tallahi na manta da cewa ita d'in matarka ce Kuma k'awa agare ni.
Cikin raunin murya Azaad ya kalli Aneesah domin ba zai iya kallon Miyya ba ya fad'i maganar da yake shirin furtawa.
"Ba k'azafi bane Princess ni na kashe mahaifinta amma walla....
"Ya isa Daddy dama abin da nake jira kenan ka amsa da bakinka tun da ka amsa shi kenan komai ya zo karshe a tsakaninmu.
Miyya ta k'arasa magana cikin muryar kuka har tana shed'ewa, Azaad ya juya ya kalli Mr Richard wanda tun lokaci yake tsaye a bakin k'ofa rike da basket d'in abinci.
"Mr Richard please ka maida Aneesah gida.
Har Aneesah ta bud'e baki za ta yi magana Azaad ya dakatar da ita.
"Princess ki tafi gida kawai kin ji?"
Ta gyad'a kai tare da toshe bakinta sakamakon kukan da ya zo mata, suna ficewa Azaad ya nufi Miyya yai k'ok'arin rik'ota tai sauri ja da baya da ya ci gaba a da bin ta yana rok'onta ta saurare shi kawai ta rugu bathroom tai locking up d'in k'ofa.
Cikin tsananin tashin hankali had'i da kid'imewa, yake dukan k'ofar yana fad'ar.
"Pretty please open the damm door we have to talk, ya kamata ki tsaya ki saurare abin da zan fad'a kafin ki yanke min hukunci.
"Ba abin da za ka fad'a min da zan sake yarda da kai Daddy ka tafi kawai banaso ganinka mugu kawai.
Miyya ta mayar mishi da amsa ta cikin bathroom.
"Dan Allah pretty ki taimaka ki bani koda three minutes ne na fad'a miki yadda al'amarin ya faru wallahi-azim ba da gan-gan na kade shi ba tsautsayi ne.
"Dallah malam rufe min baki! Wannan kuma wata sabuwar k'arya ce za ka kirkikkira ni kuma bani da lokaci saurarenka gara tun wuri ka kama gabanka.
Yanda tai mishi magana cikin tsawa ya ji zafin hakan ba k'adan ba shiyasa ya rufawa kanshi asiri ya koma bisa cushion ya zauna dafe da kai tun yanzu ta fara daka mishi tsawa baisan zuwa gaba abin da zai biyo ba.
Miyya ta zauna dabass a k'asa tiles ta ci gaba da rare kukanta tanaso ta ji ta tsaneshi amma zuciya da gangar jikinta sun k'i amincewa da k'udurinta.
Kiran sallar azhar da aka fara yasa Azaad mik'ewa ya bud'e k'ofa ya fita duk halin da ya tsince kanshi sam baya wasa da lukuta sallah.
Miyya ta ji lokaci da ya bud'e k'ofa ya fita shiyasa tai zubur ta tashi cikin kuzarinta, ta bud'e k'ofa ta leko da kanta k'adan ta tabbatar da ya fita tai wufff ta fito, ta dauki hijabinta da take sallah tasaka ta bud'e k'ofar fita cikin sauri ta ratsa reception yanda ta fito cikin sauri kamar wata walkiya ta fice daga gate d'in asibiti. Tana shiga adaidaita Mr Richard ya hangota da sauri ya yi reverse ya bisu a baya. Duk fad'in garin kano bata da inda ya fi gidan Baffanta da Kakarta Dadda shiyasa kaitsaye can ta nufa koda za su kore ta ba inda za ta je gara ta zauna dasu da ta zauna da makashin Abbanta. Dai-dai k'ofar gida mai adaidaita yai parking ta ce ya jira ta ta kar6o mishi kud'insa, ta nufi cikin gidan tashin hankali da ta ciki ya dusashe wanda za ta, tarar a ciki tana shiga cikin gida, Mr Richard yana yin parking ya fito daga mota ya biya mai adaidaita, kana yai sauri komawa mota ya ja ya tafi. Tana shiga gida da Baffa Sani ta fara cin karo fuskarshi da dashin ruwa yana gyaran hannuwan rigar jikinshi da alamar arwala ya yi zai tafi masallaci tana ganinshi tun kafin yai mata magana ta durkusa tare da fashewa da wani irin kuka mai ta6a zuciya.
"Subhanalillah! Aslamiyya daga ina kike me ya same ki naga jikinki duk bandaging?"
"Baffa Dan Allah karka koreni ka rufa min asiri ka barni na zauna tare daku, bani da inda ya fi nan.
"Kwatar da hankalinki Aslamiyya ki shiga gida ki jirani in nadawo daga masallaci ki yi min bayani a natse.
"Tam! Baffa amma tare nake da mai adaidaita wallahi banida ko kwandala da zan biya shi yana nan k'ofar gida.
"Shi kenan tashi ki shiga ciki in na tafi zan bashi.
"Nagode! Baffa.
Ta fad'a a sanyaye tare da mik'ewa duk da tana cikin tashin hankali hakan bai hana mata mamakin sauyawa Baffa Sani ba. Kasa shiga d'akin Dadda tayi sai ta nemi jikin bango ta raku6e.
Baffa Sani yana fita bai ga d'an adaidaita ba ya duba kudu da arewa bai ganshi ba, gudun kada ya rasa jam6i sallah ya wuce abinsa masallaci.
Azaad yana gama sallah bai ko tsaya doguwar addu'a ba ya koma d'aki da Miyya take, yana tura k'ofa yai tozali da k'ofar bathroom a bud'e cikin kid'imewa ya k'arasa bathroom d'in yaga bata ciki da sauri ya fice daga d'akin cikin tafiyarshi ta k'asaita duk da yana cikin tsananin tashin hankali rashin ganinta a lokaci d'aya ba za ka iya fahimtar hakan ba. A natse ya tambaye nurses d'in da ke reception ko sun ga fitarta su ka ce ba su gani ba.
Yana fitowa harabar asibitin Mr Richard yana parking mota.
Baffa Sani yana shigowa gida ya hango Miyya raku6e a jikin bango d'akin Dadda, wani irin tausayinta had'i da nadamar abin da yai musu ita da 'yan uwanki uwanta ya lullu6e shi.
Har idanuwanshi suka kawo kwalla cikin mutuwar jiki ya k'araso kusa da ita da sauri ta ciro kanta, ta dube shi da idanuwanta masu cike da zallar tsoro kafin tai magana ya rigata ta hanyar cewa.
"Wuce mu shiga daga ciki.
Ya shige gaba ta bishi a baya, suna shigowa Dadda na shafa addu'a ta juyo da baki bud'e tana kallonsu.
"Sani ina ka fito da Aslamiyya hatsari tayi ko me naga jikinta duk ciwuka ne?"
"Zuwanta kenan Dadda nima tambayar da nai mata kenan amma bata bani amsa ba.
"Taho nan Aslamiyya bud'e baki ki fad'a mana meke faruwa da ke Ina kuma kika baro 'yan uwan