Showing 45001 words to 48000 words out of 91651 words
sallar magarib ne ya falkar da Miyya daga wahalallen barcin da ya kwashe ta. Jikinta gaba ɗaya ya mutu bata ji kuzari ko Kaɗan, ga wani irin masiffafen ciwon kai da ya sakota a gaba. Da kyar ta sauko daga kan gado tana dafe da for head ɗinta ta shiga bathroom ruwa ta watsawa jikinta koda jikin nata zai saki. Tana kammala sallah ta taso daga kan praymat ta nufi window da ke saiti da harabar gida ta buɗe shi sanyayyar iska mai dad'in gaske tana shigowa, ta rungume hannuwanta a k'irji.
Sai bayan sallar Isha Azaad ya shigo gidan Nanny Lacey Kaɗai ya tarar a falo tana ba Ahlam abincinta, ya faɗa mata ta gayawa yaranshi yau a tare za su yi dinner.
Lokaci da Azaad zai shigo gida Miyya tana tsaye tun daga fitowarshi mota bata d'auke idanuwanta daga kanshi ba, adadin kallon da take mishi adadin bugawar da zuciyarta ke yi. Lokaci da tai tozali dashi wani irin abu take ji mai kama da tafiyar tsutsa yana bi jini da 6argonta. Kamar ta ruga ta rungumeshi take ji aganinta hakan ne Kaɗai zai samar mata da natsuwa.
Yana 6acewa ganinta ta ja k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta baro jikin window ɗin. A sanyayye ta zauna a gefen gado bata jima da zama ba Airah ta shigo da sallama tana fara'a.
"Yadai pretty?"
Saida Miyya ta yatsine fuska kafin ta amsa da cewa.
"Headache ke damuna"
"Ayya sannu.
"Yauwa.
"Kin sha magani kuwa?"
Ta girgiza kanta mai ciwo.
"Ki tashi mu je mu yi dinner sai ki sha magani dinner yau special ne Daddy ya yi inviting ɗin mu, shine na shigo na faɗa miki.
Anbato sunanshi Kaɗai da Airah tayi saida bugun zuciyarta ya k'aru, ta lumshe idanuwanta.
"Ki je kawai Airah ba zan iya zuwa ba.
"Shikenan bari na kira Nanny ta kawo miki abinci da magani anan"
Jinjina kanta tayi saboda wani irin sarawa da ta ji kanta ya yi mata, Airah ta juya ta fita koda ta fito Daddy da Aneesah har sun hallara a dining room, yayin da Daddy ke yi wa Aneesah 'yan tambayoyi da suka shafi karatunta.
Bayan Airah ta gaidashi ta ja kujera ta zauna Nanny Lacey ta shiga zuba musu abinci.
"Nanny ki d'ibawa pretty abinci ki haɗa da Panadol extra ki kai mata d'akinta, headache ke damunta ba za ta iya fitowa ba.
Airah ta faɗa cikin k'aramin sauti, gaban Azaad yai mummunan faɗuwa gaba ɗaya ya ji hankalinshi ya tashi, duk da haka bai nuna wata alama da yaranshi za su gano sabon yanayi da shige shi.
Aneesah ta ɗago cike da damuwa ta ce.
"Gaske dai tun d'azu ban k'ara ganinta downstairs parlor ba. Nanny ki yi mata sannu kafin na shigo.
"Okay!
Ta faɗa a takaice kana ta d'auki plate ɗin da ta zubawa Miyya abinci, ta nufi d'akinta bayan fitar Airah ta kwanta tare da tattakewa cikin hijabinta tana tukure a gefen gado. Da sauri Nanny ta aje plate ɗin hannunta akan bedside drawer ta ɗago kanta tare da tatta6a goshinta.
"Sorry pretty jikinki ya yi zafi tashi ki ci abinci koda Kaɗan ne, sai ki sha magani.
Bata yi musu ba ta tashi zaune tana yatsine fuska iri na wanda ciwo ya matsawa, Nanny ta mik'a mata plate ta kar6a ba don tana ji so ci abinci ba asalima bata ji appetite a bakinta d'aci-d'aci take ji a bakin nata kamar wacce tai zazza6in malaria.
Nanny ta fita ta dauko mata ruwa da juice ta mik'a mata Panadol tare da yi mata fatan samun lafiya sannan ta fice.
Tana fita Miyya ta aje plate ɗin abinci ta sake komawa ta kwanta.
Madam Salima ta fito daga 6angarenta sanye da bubu na silky material kanta ba d'an kwali gashinta ya sha gyara na musanmman ta sake shi ya sauko zuwa gefe-gefen wuyanta.
Cikin takonta na k'asaita mai cike da k'arfin izzarta take tattaka staircase, tun kafin ta k'araso dining room k'amshinta ya isar da sak'on zuwanta. K'amshin turarenta Kaɗai da Azaad Junaid ya shak'a sai da ya ji tsanarta ta k'ara daduwa a zuciyarshi. Haushi da takaicinta suka lullu6e shi.
"Hey kids!
Ta faɗa sa'ilin da ta shigo dining ɗin.
"Hey.... Mom"
Suka faɗa a lokaci d'aya daga haka ba wacce ta dad'a ko ta k'ara sai ci abincinsu suke hankali kwance. Nanny Lacey ta shigo dining ɗin da sauri saboda taga shigowar Madam ta ja mata kujerar da ke kusa da Azaad saida ta kalli reaction ɗinshi kafin ta zauna a yangace.
Cikin girmamawa Nanny Lacey ta tambaye me za a zuba mata cikin kallon nan nata na izza ta furta.
"Anything yummy!
Nanny tai mata serving ta aje plate ɗin a gabanta hatta da ruwa sai da ta zuba mata kafin ta koma nesa Kaɗan dasu ta tsaya.
"Aj dinner ka shiryawa muku shine you're not invited me ko?"
Tayi magana k'asa-k'asa tana wani shegen blushing wanda ya k'arawa Azaad haushinta, ba don yana gudun yaranshi su gano rashin jituwarsu ba da ko kusa ba zai kulata ba balle har ya bata amsar maganarta. A wulak'ance ya ce.
"I think you're not interested shiyasa ban faɗa miki ba.
"Uhm!
Ta faɗa tare da ta6e baki ta maida ganinta akan Aneesah ta ce.
"Princess ya school hope ba wani matsala?"
"Babu mommy.
Aneesah ta bata amsa a gajarce.
"What about you my little princess?"
Ta faɗa tana kallon Airah. Ba tare da Airah ta kalleta ba ta furta.
"The same with her.
Tana cikin cin abinci ta sake watsa musu tambaya wacce duk cikin maganganunta tafi ba Azaad haushi.
"Where's my little girl Ahlam ko tayi barci ne tun da na dawo ban zauna ba balle na sami cikkaken lokaci da ita.
Airah ce tayi k'ok'arin bata amsa ta hanyar faɗin.
"Tana d'aki tare da pretty"
"Pretty...uhum.... pretty!
Ta faɗin sunan ta sake mai-maitawa yanayi yadda take furta sunan zai tabbatar maka da mamaki take yi, can kuma ta sake cewa.
"Ko ita ce d'azu na gani a downstairs parlor d'auke da Ahlam?"
"Yes mommy ita ce.
"Wa ya kawo ta gidanan?"
Airah ta kalli Aneesah ta sauke idanuwanta cikin plate ɗin abincinta, Aneesah ta ce.
"Uncle Hakeem ne!
"Uncle Hakeem!
Ta mai-maitawa sunanshi da Aneesah ta faɗa, sai kawai tayi kwafa ta kalli Azaad wanda tun lokaci da ta fara tambayoyinta ya ke ji tamkar ya shak'o wuyanta ya danna fuskarta cikin plate ɗin gabanta.
A lokaci d'aya Aneesah da Airah suka mik'e tsaye, tare da furta
"Goodnight Daddy, Goodnight mommy!
"Goodnight kids!
Azaad ya amsa musu yayin da Salima hankalinta ya bar jikinta ya lula da ita wata duniya ta daban.
Saida suka fara shiga d'akin Miyya su duba ta tana ji motsinsu tai sauri runtse idanuwanta, kamar tayi barci. Gani haka yasa suka fice kowace su d'akinta ta nufa.
Azaad yana Aneesah da Airah sun fita ya dire spoon ɗin hannunshi da k'arfi cikin plate, dama saboda su ne yake zaune, yanzu kuma da ba su nan bai ga amfani zamanshi ba. Ya mik'e da saurinshi ya fice daga dining room ɗin ya haura sama, Salima ta bishi da kallon mamaki kafin tayi kwafa tare da saki katuwar ajiyar zuciya ta tabbatar akwai jan aiki a gabanta, abinci ma sai ya fice mata arai ta ture plate tare da jifar da spoon ta tashi a fusace ta nufi d'akinshi.
Yana cikin saka rigar barci ta tura k'ofa ta shigo da sauri ya kauda fuskarshi, tayi tsaye tana kallonshi kamar yau ne ta fara ganinshi sosai kwarjinishi da kyakkyawar surar jikinsa suka k'ara linka mata sabuwar soyayyarshi tayi gyaran murya tare da faɗin.
"Da izzininka Hakeem ya kawo min bak'uwar fuska a gida?"
Ya juyo ya zuba mata fusatattun idanuwanshi, a ranshi yana raya ya wanke mata fuska da kyakkyawan mari ko za ta dawo hayyacinta.
"Point of correction Salima gidana ne asalima ba ki da wata danganta da gidanan, ko kin manta da na tsikar igiya biyu daga cikin igiyar aurenki uku da suke hannuna?"
"Azaad please ka daina zance saki nan ni fa gaskiya na faɗa maka ban yarda ba, kawai ka sauke duk wani zafin kanka ka dawo da aurenmu"
Cike da takaici yake kallonta up and down kafin ya ja dogon tsaki, idanuwanshi suka bayyanar da tsananin tsanarta k'arara.
"A tunanina a zaman da muka yi yaci ace kin san waye Azaad Junaid, ni fa kaifi d'aya ne idan nace a'a no matter how ba zan canza ba. Da kinsan yadda nake ji tsanarki da ba ki zo kusa dani ba. Karki ga na barki a gidana ki nemi wuce makadi da rawa nayi haka ne don na sauke hakkin musulunci da zarar kin gama iddarki ki tattara komatsanki ki barmin gidana.
Ya k'arasa magana cikin fushi da zallar 6acin rai.
Wani irin gumi ya tsa-tsafuwa Madam Salima karo na farko a rayuwarta da ta shiga yanayi irin wannan ta saki baki da hancinta tana kallonshi ta kasa koda kwakkwaran motsi.
Miyya ta tashi zaune tare da jingina bayanta ga pillow, zuciyarta sai azal-zalarta da so gani Azaad take yi yayin da a 6angaren d'aya take ji tsoro kada ta je ta haɗu da madam Salima, abin ka da mai raguwar zuciya sai ta fara zubda hawaye suna zuba a kumatunta ta gogewa da bayan hannunta cike da kwarin gwiwa ta diro kafafuwanta k'asa. Sannu a hankali ta buɗe k'ofar d'akinta sai da ta fara lek'awa lungu da sak'o na downstairs parlor bata ga kowa ba. Kafin ta fito kitchen ta shiga ta haɗa coffee, cikin sand'a tamkar tsohuwar 6arauniya ta dinga taka matattak'alar bene.....
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Top Ten Takun Haske Batch:A
*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004
25....
Madam Salima tayi k'ok'arin danne duk wani tashin hankalin da ta shiga, ta kalli Azaad da idanuwanta masu cike da zallar alhini ta kwantar da muryarta ta ce.
"Azaad...
Ko ɗagowa bai yi ba balle tasa ran zai amsa mata sai ma k'ok'arin bar mata d'akin da ya yi yana buɗe k'ofa, ta rik'o hannunshi na dama hakan yasa ya juyo a fusace.
A hankali Miyya ta buɗe k'ofar falonshi na farko dama tana da yak'ini ba za ta tararda shi a ciki ba. Sai kawai ta ci gaba da tafiya tana tunk'arar falo na biyu.
Cikin tsawa da ɗaga murya ya ce.
"Sake min hannu Salima tun kafin ki kaini bango nai miki abin da tsawon rayuwarki ba za ki ta6a iya mantawa dashi ba.
"Kayi hak'uri Azaad ka manta da abin da ya faru ka d'auke shi a matsayin kuskure, in-sha-Allah hakan ba za ta sake faruwa ba.
Ta faɗa tamkar wacce aka cillastawa, ta kuma kauda fuskarta ba tare da tasaki hannunshi ba, kamar yadda ya buk'ata.
Tun kafin Miyya ta k'araso ta hango su tsaye hannuwansu sark'e da juna kasancewar ya ri ga da ya buɗe k'ofar bai kai ga fita ba Salima ta rik'o shi. Wani mummunan faɗuwar gaba yai mata dirar mikiya hatta da kanta saida ya sara, da sauri ta juya yadda ta juya ya haddasawa tray ɗin hannunta subucewa ya faɗi mug ɗin coffee ya tararratse, gani haka yasa ta kwasa da gudun bala'i take tattaka staircase.
K'arar da suka ji yasa Salima ta sake shi babu shiri kusan a tare suka fito falon, dukkan su coffee da ke malale akan tiles tare da fasashe mug suka bi da kallo. Ya ja numfashi da k'arfi kana ya sauke tuni ya gano pretty ce ta shigo kawo mishi coffee kamar yadda ta saba, to amma bai san dalilinta na zubar dashi kuma ta gudu ba. Ya duk'a yana tattare fasashe mug ɗin yana zubawa cikin tray.
Miyya tana saukowa da gudu dai-dai Aneesah na fitowa daga d'akinta za ta kitchen ta d'auko ruwa saboda na cikin fridge ɗin d'akinta sun yi mata sanyi sosai. Cike da tsoro ta bi bayan Miyya da kallo wacce sam bata lura da ita ba. Ta shige d'akinta idan Aneesah ta dubi d'akin miyya ta dawo da idanuwanta akan 6angaren Daddy ta kasa fahimtar me Miyya ta je yi 6angaren Daddynsu.
Wanda ko su da suke 'ya'yanshi ba kasafai suke zuwa ba, gashi ta fito da gudu da alamar akwai abin da ya tsorata ta, ta sauke ajiyar zuciya ta nufi d'akin, so take ta ji abin da ya tsorata ta har haka. Har taka kama handle ɗin k'ofa sai kuma ta saki ta juya zuwa kitchen, zuciyarta cike da tarin tambayoyi.
Cikin masifa Salima ta ce.
"Wai waye ya yi wannan 6arnar kuma ya tafi ba tare da ya gyara ba?"
Uffan Azaad bai ce da ita ba sai aikin gabanshi yake yi, gani yadda bai kula ta ba yasa ta ci gaba da faɗar
"Ka barshi kawai na kira Nanny Lacey ta zo ta gyara waya sani ko ita ce ta zubda shi, nasanta da kaudin tsiya ko uban wa yace ta kawo maka coffee a cikin dare nan...
"Mtsss.....ya katse ta da tsaki kafin ya ɗago ya watsa mata mugun kallo duk lokaci da ta yi magana haushi da tsanarta k'ara hauhawa suke yi da shi mabugi mata ne da tuni ya ba je ta.
"Dalla.....malama fita ki bani waje surutunki ya isheni.
"Ba zan fita ba Azaad har sai ka hak'ura ka janye saki da ka yi min.
"Ashe kuwa za ki k'are rayuwarki kina jiran gawon shanu.
"Kana nufi ba za ka hak'ura ba kenan?"
"Zance na hak'ura ko ban hak'ura ba ya kau saboda ni taimakonki ne nayi na ba ki full freedom da za ki ci gaba da han6aka business career ɗinki. Ki shiga duk inda kike so ba wanda zai tak'ura ki.
"Azaad ban zo dakinka ba don ka dinga faɗa min duk maganar da ta fito daga bakinka ba. Na zo ne don neman sulhu wane hali kake so yaranmu su shiga idan suka sami labarin abin da ka aikata?"
Bai tanka mata ba sai da ya k'arasa tattare gurin ya mike a natse ya aje tray ɗin akan center table, kana ya dubeta a ɗage.
"Dad'ina da gobe saurin zuwa ashe akwai ranar da za ta zo da za ki tuna da kina da 'ya'ya. To albishirinki daga ni har yaran naki ba ma buk'atarki. Saboda haka ba sai kin yi amfani dasu ba cikin yaudararrun kalamanki ba.
Langwa6e kai tayi tana kallonshi tamkar ba Azaad ɗinta ba, mutumin da ada ko magana zai mata sai ya tausasa harshensa yau shine ke zaro mata maganganu masu zafi da d'aci. Tabbas tasan ba yin kansa bane.
Akwai manafukai da ke zuga shi ba kuma kowa bane sai Jadda da Hakeem, saboda haka gaba ɗayansu sai ta wanke musu allonsu tass...
Idan har ta ci gaba da bashi hak'uri zai ci gaba da gasa mata maganganu marasa dad'i. Ita kuma ba hak'uri za ta yi ba ta zuba ido ba. Saboda haka ta juya jiki a sanyayye ta fice.
Azaad ya bita da kallon tsana tare da faɗin
"Lallai Salima ke ɗin shahararriyar 'yar wasa ce na yaba miki tare da jinjina miki akan wannan fasahar taki. Da sannu za ki yi nadama a lokaci da ba ta da amfani.
Salima tana fitowa ta hango Aneesah ta fito daga kitchen, gabanta yai mummunan faɗuwa zuciyarta ta shiga kintsa mata Aneesah ce ta shiga kai ma Azaad coffee watakila ta ji faɗansu shine ta tsorata ta zubar da coffee ɗin.
Yadda Salima take mata kallon tuhuma ita ma hakan ne. Aneesah tana kallon mommy ne zatonta ita ce silar zuwan Miyya 6angare Daddy saboda tasan halin mommy bata so gani kowa ya ra6e su.
"Ke princess zo nan.
Madam faɗa tare da nufar d'akinta tana zama akan cushion ɗin da ke d'akin Aneesah na shigowa.
"Gani mommy!
"Dama tambayarki nakeso yi.
"Tam....mommy Allah yasa ina da amsar tambayar taki.
Saida Salima ta tsareta da idanuwa kafin ta ce.
"Miyasa da kika je kai ma Daddynku coffee kika zubar a maimakon ki tsaya ki gyara 6arnar da kika yi sai kika gudu?"
Gaban Aneesah ya faɗi rass....wato shine dalilin gudun Miyya, idan har ta faɗawa Mommy gaskiya Allah ne Kaɗai zai ceto Miyya daga wurinta saboda haka ta ce.
"Nima ba a son raina hakan ta faru ba amma ki yi hak'uri mommy in-sha-Allahu zan kiyaye gaba.
"Shikenan je ki kwanta.
Salima ta faɗa tare da shigewa bathroom Aneesah tai hamdallah. Ta fice.
Miyya tana shiga d'akinta ta faɗa kan gado, duk lokaci tai yunk'uri rufe idanuwanta hoton Azaad da Madam Salima take gani rik'e da hannuwan juna, duk yadda taso ta goge hoton abin a zuciyarta ya ga-gara gogewa. Ga zafin ciwon kai ga zafin gani Azaad da Salima wanda ta rasa dalilinta na jin zafin ganinsu tare. Tana so tai barci amma yak'i zuwa ya dauketa ga wani mugun zafi da take ji a k'irjinta da rasa yadda za tayi sai ta shiga rera kuka.
Bayan fitar Salima Azaad da kanshi ya goge coffee ɗin duk sai ya ji shi wani iri, kamar wanda bai da lakka a jikinshi akwai abin da zuciyarsa ke so gani amma ya rasa gane menene wannan abun.
Ya tusa tulin files a gabanshi ko d'aya ya kasa buɗewa, da ya ji motsi Kaɗan sai ya yi saurin kallon k'ofa yana zaton ko Miyya ce. Dare ranar dukkan su uku Azaad, Salima da Miyya ba wanda ya yi barcin kirki.
Misali karfe 7:00am Miyya ta fito cikin Shirin tafiya school, tsabar kukan da tasha idanuwanta sun yi luhu-luhu da ka kalleta ba sai ka tambaya ba, za ka fahimci kuka tayi ba Kaɗan ba.
Ta zauna a kujerar da ke kallon upstairs, addu'a take a k'asan zuciyarta Allah yasa Daddy ya fito kafin su wuce school. Airah ce ta fara fitowa tana arba da ita ta zaro ido.
"Subhanalillah.... pretty me ya sami idanuwanki ko har yanzu ciwon kai ne?"
Ta gyada mata kai saboda ko Kaɗan ba ta k'aunar tayi magana muddin tayi magana to kuka ne zai biyo baya.
"Sannu Allah ya ba ki lafiya amma kan da kin hak'ura da zuwa school ɗinan, kin ga yau Friday short time ne.
Kauda fuskarta tayi gudun kada Airah taga hawaye da suka silalo mata a kuncinta.
"Zan iya zuwa ba sosai Kan yake min ciwo ba, kuma kinsan yau muna da test ɗin chemistry banso nayi missing.
Tayi magana cikin dasasshiyar muryarta da bata fita sosai. Kafin Airah ta sake yi magana suka ji muryar Aneesah tana faɗin.
"Good morning girls!
I'm sorry yau na tashi a makare......
Ta kasa k'arasa magana sakamakon gani idanuwa Miyya wacce ta juyo lokaci da