Showing 63001 words to 66000 words out of 91651 words
rufe su ya yi sai in yana buk'atar wani abu ya buɗe ya kira Mr Richard.
Aneesah ta fito daga studies room, kallo d'aya za ka yi mata ka gano damuwar da take ciki. Kaitsaye kitchen ta wuce Nanny Lacey ta tarar tana zuzuba abincin dinner cikin warmers, wannan shine karo na uku kenan da ta tambaye ta Miyya.
"Sannu da aiki Nanny?"
Aneesah ta faɗa lokaci da ta shiga kitchen ɗin ta jingina bayanta a kitchen cabinet.
"Yauwa princess barka da fitowa.
"Nanny har yanzu babu wani labari akan Pretty wallahi hankalina yak'i kwanciya, ina fargaba idan ba rashin lafiyarta ne ya yi tsanani ba?" Gashi yau mommy tana gida bata fita ba balle na saci jiki direba ya kaini hospital na duba ta. Kuma duk lokaci da na kira wayar Daddy a kashe take balle naji ko yana da labarinta.
"Ki kwantar da hankalinki princess ki ci gaba da yi mata addu'a mu jira zuwa gobe idan muka ga bata dawo ba, nai miki alk'awali zan je da kaina na dubata.
"Tam.... shikenan Nanny bari naje nayi sallah.
Ta faɗa tare da ficewa daga kitchen ɗin. Nanny Lacey ta bi ta da kallon tausayi, tana fargaba zuwan ranar da Aneesah za ta san cewa Miyya matar Daddynta ce.
Cikin kwanaki biyu kacal Azaad da Miyya sun yi shak'uwa ta daban mamaki, tun tana d'ari-d'ari dashi har ta dawo ta saki jikinta kunyarshi ma da take ji yanzu ta ragu hatta da wanka tare suke yi Azaad ya yi mata sabo da abubuwa masu yawa a cikin sauk'i ba za ta iya rayuwa babu su ba.
Ta fito cikin shirin tafiya gida don tun safe take mishi magiyar ya maida ta gida, gashi gobe monday akwai school, ga Kuma Aneesah da Airah da ta ke da yak'ini suna cikin damuwar rashin ganinta. Daddy sai ja mata rai yake yi shiyasa yanzu ta fito cikin shirinta ko ya kaita ko ta kai kanta.....
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Top Ten Takun Haske Batch:A
*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004
32....
Kallo daya za ka yi ma madam Salima ka fahimci irin damuwar da take ciki ta zabge tayi muguwar rama, ko office ta daina zuwa kullum tana k'unshe a d'aki. kusan two days kenan rabon da tasa Azaad a idanuwanta in ta kira wayarshi a kashe ko kuma yak'i ɗaga kiranta. Ga baki ɗaya al'amuranta sai k'ara dagulewa suke yi, ta rasa tudun dafawa. Tana tsoro ta fita cikin mutane kada su fahimci tana cikin damuwa Bata Kuma tanadi irin amsar da za ta bayar ba idan aka tambaye dalilin ramarta shiyasa ko mahaifiyarta bata gayawa aurenta ya mutu ba. Duk duniya Hafsat shinkafi kaɗai ta faɗawa.
*** ***** *****
Karar buɗe k'ofa yasa Azaad ya ɗago ya ga Miyya ce ta shigo sanye da dogon hijabinta har yana ja a k'asa, yai sauri ciro wayar da ke manne da kunnenshi, ya saki mata k'ayatatcen murmushi irin mai shiga jiki ita ma ta mayar mishi da martani murmushin nashi hannunshi ya mik'a mata ta mak'e kafad'a alamar ba za ta zo ba. Ya nuna kanshi ta gyad'a kai ya waro idanuwanshi alamar mamaki.
"Wa ya ta6a min prettyna?
"Kaine!
Ta faɗa cikin shagwa6a6iyar murya tana cuno baki.
"Lallai Daddy bai kyau ta ba zo naji laifin da nayi"
Cikin shagwa6a6iyar murya tamkar za ta rushe da kuka take faɗin
"Daddy please ka tashi ka maida ni gida haka nan in Kuma ba ka gaji da zaman gidanan bane ka faɗawa Mr Richard ya maida ni.
Ajiyar zuciya ya sauke saboda yasan yana da aiki ba kaɗan ba. Ya sake mik'a mata hannunshi a karo na biyu bata yi gardama ba ta kama hannun nashi, fizgota da k'arfi ya yi ta faɗa jikinshi ya shiga k'ok'arin rabata da hijabin jikinta da sauri ta rik'e hijab ɗin.
"Please Daddy ka barmin hijabina mana.
Da sauri ya ɗago ha6arta yana kallon cikin idanuwanta yai wani had'e rai, ta kauda fuskarta tana gun-guni k'asa-kasa.
Yadda take magana sam ba ya ji abin da take faɗa bakinta kawai ke musu-musu, lips ɗinta ya kama da yatsunshi biyu.
"Ouchh....Daddy da zafi karka cire min le66e
mana.
Ta yi magana tana k'ok'arin ciro yatsunshi daga le66enta. Murmushi ya yi tare da fincike hijab ɗin ya jefar ya kwantarda kanshi a shoulder ɗinta, hancinshi ya tura ta gefen wuyanta yana shak'ar fitinanen k'amshinta sai faman tu-ture take yi tana kukan shagwa6a kuka da babu hawaye. Hak'oranshi yasa akan spaghetti hand ɗin gown jikinta ya saukar dashi zuwa hannunta, sai ruwan kisses yake mata a jiki. Da k'arfi ta fincike kanta ta mik'e tsaye jikinta sai rawa yake yi bata manta bak'ar azabar da tasha two days ago ba. Muryarta yana rawa ta ce.
"Ni fa Daddy nagaji da wannan masifar ka tashi ka maida ni gida.
Ya ɗago idanuwashi da suka fara canza launi ya tsare ta dasu gabanta yai mummunan faɗuwa, wani irin tsoronshi ta ji yana shigarta, kalamanta sun yi matuk'ar ta6a shi wato shine masifa shi za ta danganta da masifa kalmar tai mishi tsauri ta kuma 6ata mishi rai, sai kuma yai sauri danne zuciyarshi tunawa da yai da karancin shekarunta dole akwai wauta a tattare da ita watakila bata faɗa don ta 6ata mishi rai ba. Mik'a hannunshi ya yi cikin zafin nama ya jawota ta faɗa jikinshi yai mugun matseta, sai da tasa k'ara ya hade bakinshi da nata wani irin hot romance yake bata tamkar yau ne ranar farkonshi, Miyya ido ya rena fata sai migiya take mishi ya kyaleta, Azaad kan bidirinsa kawai yake yi bai masan tana yi ba, tana jin lokaci da kwatarda ita ya yi mata rumfa ta kasa daurewa sai ta fara kuka cikin sautin mai k'arfi bai saurara mata ko kaɗan ba sai da ya sami natsuwa, ya rungumeta a jikinshi sai faman sauke ajiyar zuciya take, a k'asan zuciyarta kuma sai Allah ya isa take mishi. Haka kawai zai dinga nanikarta ko gajiya ba ya yi ita kan ta gaji gara tun wuri tayi ta kanta kada ya k'arar mata da ruwan jiki.
Kamar yasan abin da take faɗa akanshi ya juyo da ita yana kallon fuskarta da idanuwanta da sun ka kumbura murmushi ya yi yana shafar lips ɗinta.
"Wa ya ta6a min prettyna naga idanuwanta da fuskarta sun kumbure?"
Buge mishi hannu tayi tasake fashewa da kuka, cikin muryar kuka take faɗin.
"Wallahi Daddy kai mugu ne daga yau ba zan k'ara kula ka ba.
"Haba prettyna yi hak'uri ba zan k'ara ba har sai kin nema da kanki"
Ture shi tai ta d'auki rigarta za ta saka ya fizge rigar ya yar ya jawota ya sake rungumeta, cikin kunneta ya rad'a mata I am terribly sorry for all the things I’ve done, please forgive me my pretty.
"Ko a wacan karo haka ka dinga faɗa ba za ka sake ba sai gashi ka sake yi, ba zan sake amincewa da kalaman bakinka ba.
Sosai furuncinta ya haifar mishi da nishadi, yasa dariya mai ban sha'awa ita kuma ta fashe da kuka ya cire ta daga jikinshi ya sauka daga gado yana k'ok'arin d'aukarta.
"Lemme take my pretty to the bathroom.
Ya faɗa yana dariya, buge mishi hannu tayi cikin kukanta mai cike da zallar sangarta ta ce.
"Leave me alone I don't want your help.
Ya sunkuceta ya nufi bathroom da ita sai faman wuntsila kafafuwa take yi, sai cikin bathtub ya sauke ta har ya gama wankanshi ya fita idanuwanta suna a rufe wai ita a dole kunyarshi take ji. A natse tayi wankanta muddin yana bathroom ɗin ba za barta tasami irin wannan natsuwar ba ya dinga jagwalgwalata kenan.
Ta fito d'aure da towel a k'irji hannunta rik'e da wani k'aramin towel tana goge jik'ak'k'iyar sumarta, ta bi ta gabanshi za ta wuce cikin sauri ya rik'o waist ɗinta ya dawo da ita gaban mirror da k'afarshi ya jawo stool ya zaunar da ita, ya kar6i towel ɗin hannunta ya shiga goge mata sumarta, sai faman kumbura fuska take yi tana turo baki gaba, shi Kuma sai zabga murmushi yake yi komai nata burgeshi yake, wannan tura baki da take yi ba k'aramin k'ara mishi kyau take yi ba. Ji yake kamar ya hadiye ta. Hannunshi ta rik'e cikin marairaice murya take magana.
"Daddy Dan Allah maida ni wurin su Aneesah ni dai wallahi na fi so can.
"Uhm... Pretty da ke mayya ce in kika dank'e kuruwar mutum da wuya ki saki, kin cika naci wallahi.
"Koma me za ka faɗa Daddy ba zai dameni ba idan har za ka barni na tafi ka kirani da abin da yafi mayya.
"Gara tun wuri ki soma shirya mana irin rayuwar da za mu yi anan gidan don kin zo kenan, ke da wancan gidan sai dai ziyara.
A mugun tsorace ta juyo ta kalleshi don gani take yi ta cikin mirror ba zai gansar da ita ba, ta zazaro idanuwanta cikin kad'uwa ta ce.
"Me kake nufi Daddy kayi min bayani gwari-gwari ta yadda zan fahimta?"
"Ina nufi nan shine gidan da na za6a mana da za mu yi rayuwa ni da ke a ciki, Ina da tarin gidaje da yawa a Nigeria har ma da wajenta idan wannan bai miki ba ki faɗa min na sauya miki wani. Saboda ba zan so wani abun cutarwa ya ra6e ki ba farin cikinki da kwanciyar hankalinki nakeso shiyasa na ware miki naki gida daban.
Ranta yai mugun 6aci har wani dishi-dishi take gani me Daddy yake nufi shikenan ya raba tsakaninta da yaranshi duk shak'uwar da suka yi ta tafi kenan ta ya za ta fara tunani rayuwa ita kaɗai a wannan k'aton gida?" Ba wani farin cikinta da yake so ya yi ne kawai don biyan buk'atar kanshi. A fusace ta ce
"Haba....Daddy....Haba...Dan Allah wannan ai son kai ne da tun farko nasan wannan ne kudurinka da ban amince na biyo ka ba. Tun farkon zuwana gidanka ya kamata ka gabatar da ni a matsayin matarka ba 'yar aiki ba sai yanzu da rana tsaka za ka bijiro da wannan zance da hankali ba zai dauka ba.
Tsananin mamakinta ya hanawa Azaad furta uffan sai kallonta yake, ba ko kiftawa gani ya yi shiru yana kallonta yasa ta bangaje shi ta wuce tana faɗin.
"Bani hanya na wuce yanzu-yanzu nan zan bar gidanan ba sai anjima ba, da tun farko ina da masaniya akan manufarka da ban tsaya 6atawa kaina lokaci ba da tuni ka nemi ni ka rasa ko an gayamaka bansan hanya bane. Bari ka ji Daddy dole tarayyarmu ta ci gaba da kasancewa a 6oye banaso yarda da aminci da ke tsakanina da Aneesah su sami rauni.
Da sauri ya rik'o hannunta ya jawota da k'arfi saura Kiriss towel ɗin jikinta ya cire tai sauri dafewa, kallon cikin idanuwanta yake yi so yake ya gasganta wai ita ɗin ce ko musanya aka yi mishi, gani yadda yake kallonta yasa ta sadda kanta k'asa, ya ɗago ha6arta tai saurin kauda fuska.
"Aslamiyya ni za ki nunawa 'yar da na haifa ta fini muhimmanci a wurinki, ashe kin fi k'aunar Aneesah akaina?"
Ya faɗa cikin taushin murya.
A razane ta dawo da ganinta akan fuskarshi ba komai bane yasata razana face sunanta da ya kira tsawon zamansu bai ta6a kiranta da sunanta ba, har ayyanawa take yi baisan sunanta na yanka ba.
"Kin kyauta Aslamiyya ba laifinki bane laifina ne da na nuna k'arara na mutu akanki, kuskuren nawa ne da na k'asa danne masiffafiyar soyayya da nake miki. je ki shirya Mr Richard zai kai ki duk inda kike so ba wurin Aneesah ba in kin iya ki tafi bango duniya da izzini ubangiji saboda da ke ba zan daina numfashi ba.
Yana k'arasa magana ya sake ta ya nufi dressing room, sosai maganganun shi suka ratsa ta ita fa ba nufinta Aneey ta fishi bane asalima k'aunar da take mishi ne ta shafi yaranshi, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi abin ka da mai raguwar zuciya sai kawai tasa kuka tana tsaye ya fito sanye da shadda blue colour kanshi sanye da hular tangaran, bi ta gefenta ya yi ya wuce saida ya buɗe k'ofa sannan ya tsaya ya ce.
"Lallai yarinyar nan dad'i yai miki yawa ni ne ya dace nai kuka ba ke ba. Amma bari na wakilce ki tun da kin fasa zuwa gun Aneesah ɗin ni bari naje na faɗa mata a yanzu matsayinki ya haura daga k'awarta kin koma second mom ɗinta.
Kafin tai magana ya maida k'ofa ya rufe, komawa tayi gefen gado ta zauna ta ci gaba da rera kukanta.
Azaad yana jin kukanta har cikin zuciyarshi ya yi mata haka ne, dalilin yadda ta nuna tafi gudun zuciya yaranshi akanshi, duk da yasan ta faɗi gaskiya maganarta dutse ce ba abar yarwa bace. Shi kanshi yana fargaba ta yadda zai gabatarwa da yaranshi ita. Da wannan tunani ya fito compound Mr Richard ya jawo mota ya buɗe mishi ya shiga, ɗayan gidanshi suka nufa gara ya je ayi ta ta k'are so yake ya zauna da yaranshi ya faɗa musu matsayin Aslamiyya, gara su ji a bakinshi da su ji a bakin wani. Ya fahimce Aslamiyya tana so ta haddasa mishi bugawar zuciya yadda yake ji soyayyarta ba zai iya 6oyeta ba a gaban ko ma waye, saboda haka gara a d'auko ta daga tushe
Har suka iso gidan bai sani ba saboda ya yi nisa a tunani k'arar buɗe mishi k'ofa da Mr Richard ya yi ne ya ankarar dashi. Cikin tafiyarshi ta k'asaita ya nufi cikin gida, ya murda handle ɗin k'ofar main parlor ya ji ta a rufe knocking ya shiga yi Nanny Lacey da ke kitchen ta amsa da
"Yes I'm coming"
Tana buɗe k'ofa tayi arba dashi ta runsuna tare da gaidashi ya amsa, cikin sanyi murya saida ya fara haura matattak'alar bene sannan ya juyo ya ce ta sanarda da Aneesah da Airah yana nemansu.
Akan idanuwa madam Salima Mr Richard ya shigo tana tsaye a balcony, har Azaad ya shigo main parlor tana kallonshi cikin sauri ta koma bedroom ɗinta ta sauya kayan jikinta, zuwa gown na atamfar super exclusive ta shafawa fuskarta powder ta zizirawa idanuwanta kwali bata shafa jan baki ba gudun wulak'anci Azaad sai kawai ta d'an shafawa lips ɗinta man le66e, turare kusan k'ala biyar ta fesa jikinta na fitar da mahaukaci k'amshi cikin takonta na tak'ama wanda ya zame mata jinin jiki ta tura k'ofar falonshi, idanuwanta suka sauka akan kyakkyawar fuskarshi yana zaune ya ɗora kafafuwanshi akan center table ya ture hular kanshi baya hannunshi rik'e da remote ɗin decoder yana canza channels cikin. Wani irin faruwar gaba taji ta rasa dalilin da yasa yanzu har tsoron haɗuwa da shi take yi ta kai morethan 3 minutes a tsaye ita bata shiga ba bata kuma koma inda ta fito ba. Dogon numfashi ta ja kafin tattaro dukkan courage ɗinta, ta soma tattaki izuwa cikin falon tun farko shigowarta ya ganta sai faman shak'ar k'amshinta yake sallama tayi cikin taushin murya ya amsa mata a dakile.
"Sannu da zuwa"
Ta faɗa tare da sadda kanta k'asa bai amsa ba sai ma k'ara d'aure fuska da ya yi, shiru ya biyo baya ita bata sake yi magana ba shi kuma sai faman canza channels yake yi, can ta danne tsoro da fargabarta ta ce.......
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Top Ten Takun Haske Batch:A
*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004
34...
*Assalamu Alaikum*
Sako na musanmman zuwa ga makaranta wannan littafi Ina mai ba ku hak'uri a dalilin yankewar labarin ya faru ne bisa ga dauke min waya da aka yi in-sh-allah za ku dinga gani update saidai ba kullum ba. A dalili har yanzu ban mallake waya tawa ta kaina ba. Ku k'ara hak'uri in-sh-allah saura kad'an na kammala, da fatan za ku kar6i uzirina da hannuwa bibbiyu.
Garin farfasa gilasai da madam Salima ke ta faman yi babu kakkautawa ya yanke ta a hannu jini ya soma zuba duk da ta ji zafin yankar hakan bai sa ta dakata da tu'anati da take yi ba. Sai ma k'ara mata kaimi da ya yi yanda Aneesah ta ga jininta yana zuba yasa ta tsorata da gudu ta iso wurinta ta rungumeta ta baya tasa kuka mai ta6a zuciya cikin muryar kuka take fad'in.
"Haba mommy miyasa kike so ki illata kanki akan abin da kika ri ga da kinsan kin rashi shi?"
Bata jira jin ta bakinta ba ta ci gaba da fad'ar.
"Wannan abin da kike aikatawa ba shi zai sa Daddy ya dawo gareki ba, ba kuma zai gyara abin da kika 6ata ba sai ma ya ta6a lafiyarki.
Da karfi Salima ta finciko Aneesah ta dawo da ita gabanta ta dire ta, tsabar masifar da ke cinta idanuwanta sun kad'a sun yi jajir, cikin hargowa ta ce.
"Princess idan har Daddynku ba zai dawo gareni ba, to kuwa ba zai ta6a zama mallaki ko wace 'ya mace ba a duniya. idan har hakan yana nufin na rasa shi kenan, nima ba zan barshi shi da wannan k'aramar yarinya sun yi numfashi mai dad'i ba.
"Mommy please ki dawo hayyacinki ki dai-daita harshenki, ba girmanki bane fad'ar iri-iri wad'annan maganganu ba.
Aneesah ta k'arasa magana tare da sake rushewa da kuka, don gani take yi tamkar mommy ta zare ne. Sakamakon yanda take ta fad'ar maganganu marasa dad'i da ma'ana, duk abin da ya zo bakinta fad'a take yi kamar dai wata zararriya.
Suna cikin wannan badak'ala sai ga Hafsat shinkafi ta shigo hankalinta a tashe direban madam Salima ne ya kira ta ya fesa mata wannan labari shine bata yi k'asa da gwiwa ba ta garzayo, da shigowarta idanuwanta suka sauka gane mata yadda Salima ta hargitsa falonta, ta fidda shi cikin hayyacinsa, ba k'aramar 6arna ta yi ba ta