Showing 15001 words to 18000 words out of 91651 words
alkhairi da kunnu wutar da ba ka da ruwan kasheta.
Ta faɗa tana wani shegen blushing na reni ta sunkuya ta d'auki passport ɗin, ta fice abinta cikin yanayi ko a jikina. Kasa ci gaba da meeting ɗin ya yi zuciyarsa sai tafarfasa take yi tabbas lokaci ya yi da zai nunawa Salima shi ba su-su bane kamar yadda ta dauka, sai yasaka ta nadama a bisa kowa ne furuncinta. Da wannan bak'in cikin nata ya kwanta.
****************
*AFTER TWO DAYS*{BAYAN KWANA BIYU}
Yau ne ya kasance ranar tafiyar Salima kasancewar morning flight za ta bi, batada niyar faɗawa Azaad tafiyarta saboda dama haka ta sabar mishi za ta bar k'asa batare da saninshi ba, sai ta isa k'asar da za ta sannan ta kira shi. Wani lokaci ma sai ta share wasu kwanaki kafin ta kira shi. Nanny Lacey janye da luggage ɗinta ita kuma tana biye da ita jikinta sanye da wide legs trouser tare belted top ta ɗora long black frock jacket ta yane kanta da multiple colour scarf, k'afarta sanye da kitten heel na company Hermes hannunta na dama rik'e da bolide handbag ita ma ta company hermes ɗin ne ga k'amshin designer perfumes dake fita daga jikinta.
Cikin tafiyarta ta izza da tak'ama take saukowa daga stairs, dai-dai lokaci da Azaad ya fito daga 6angare shi zai shiga gem room suka haɗu ta dauke kanta tana mai ci gaba da kashewa Nanny Lacey gargadin ta kula da gida.
Sosai jikinshi ya yi sanyi wato da gaske sai Salima tayi wannan tafiya da bayaso a natse ya kira sunanta gani batada niyar kula shi.
"Salima!
Kamar ba za ta tsaya ba sai kuma ta tsaya ta waigo fuskarta, a murtuk'e gudun kada yaga damarta ya kawo mata wargi.
"Ina za ki je da sanyi safiya?"
"Duk inda zan je is none your business please stop wasted my previous time to your silly questions.
Ta juya kawai ta ci gaba da tafiya, ajiyar zuciya ya yi tare da fesar da zazzafar iska daga bakinshi ya biyo ta a baya a parking lot ya tarar da ita har ta shiga mota ya dafa k'ofa, da sauri ta kalle shi saboda bata ta6a tunani zai biyo ta ba.
"Ina rok'onki a karo na ba adadi ki fasa wannan tafiya duk abin da kike so zan miki Salima. Ina da tarin dukiya mai yawan gaske miyasa za ki dinga wahalar da kanki?"
"Saboda inaso nai building ɗin nawa future ba na dogara da kai ba.
"Ke mace ce Salima wannan yawo bai Dace dake ba.
"Kaine kake gani rashin dacewar shi"
"Ina k'ara rok'onki da ki janye wannan tafiya"
"Ba zai yu ba saboda na jima ina neman wannan opportunity ba kuma Zan yi wasa dashi ba.
"Shin zan iya biyanki makudan kud'i domin ki yi handling business dinki ga siblings dinki, ki zauna gida ki kula min da kanki da yarana?"
"Ba kud'inka nakeso ba ko wata k'addara taka ba nawa nake nama gumin jikina nakeso Kai ma kasan da wannan Azaad?"
"Me kike nema Salima wallahi-azim zan miki, ni dai burina ki jinginar da wanna yawace-yawace da kike yi da sunan business ki zama full housewife"
"You're dreaming Azaad.
"I'm not Salima please accept my offer.
"Wallahi-tallahi ba zai yu ba Ina business ne ba don komai ba sai don na tara tawa dukiya, babban burina nayi suna a duniya inaso a lissafa sunana a cikin mata masu kud'in duniya, saboda haka kabarni na tafi kana 6ata min lokaci a banza.
"Shikenan Salima Allah ya tsare ya kai ki lafiya ya ba ki abin da kike je nema. Ni kuma Allah ya musanya min abin da na rasa Allah yasa wannan tafiyar taki ta zame mana buɗewar k'ofufin alkhairi ina miki fatan samun nasara a rayuwarki.
Daga haka ya juya yayin da yake ji kamar zai kife k'asa sakamakon wani duhu da ya lullu6e wa ganinsa, tafiya kawai yake batare da yasan inda yake jefa k'afarshi ba. Yana wucewa Salima ta ja tsaki.
"Mtsss.....aikin banza naga uban da ya isa ya hanani tafiya.
Adaddafe Azaad Junaid ya isa master bedroom ɗinshi, ya kwanta akan tangamemen gadonshi. Zuciyarsa na wani irin bugawa a duk lokaci da ya tuna da irin hukunci da ya tanadarwa Salima indan har tai wannan tafiya. Gaba d'aya yini ranar a d'aki ya yi shi zazza6i mai zafin gaske ya lullu6e shi, bayan ga coffee ba abin da yasawa cikinsa. Gashi yana da very importance meeting sai Hakeem ya kira ya wakilce shi.
Kusan kwana sa biyu a gida tare da yaranshi ko compound bai fita ba. Sai a kwana na uku ya fita office yana zaune a office ɗin nashi damuwa ta taro ta mishi yawa. Abdul-hakeem ya shigo d'auke da wasu files a hannunshi a natse ya shiga k'are mishi kallo ya rame sosai har ramar tashi ta baiyana k'arara akan kyakkyawar fuskarshi.
"Aj wai meke damunka ne, ni fa ban yarda da wannan rashin lafiyar nan taka ba gaba d'aya ka sauya bakada wal-wala da kuzari sai d'an banza tunani ka faɗa min menene ke haddasa maka shiga wannan hali?"
Sai da Azaad ya ja gwaron numfashi kana ya shafa kwantattace sajenshi, ya dauko d'aya daga cikin wayoyin shi ya danno wani ke66en folder batare da ya yi magana ba ya mikawa Hakeem. Jikinshi a sanyyaye ya kar6i wayan ya shiga karanta abin da ke rubuce, tun kafin ya k'arasa karatu ya ɗago a firgice yana kallon Azaad Wanda ya kauda kanshi yana kallon wani gun dabam.
"Innalillahi wa'aina illahim raji'un!
Cewar Hakeem yana faɗa yana k'ara nanatawa gaba d'aya ya dimauce ya gigice har yana k'ok'arin fita daga hayyacinsa......
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪
*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*
*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*
*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*
*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*
*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*
*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*
*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*
*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*
*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*
*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*
KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*
SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*
SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*
*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Wattpad:-jeedddahaliyu
Haske writers Association.
Top Ten Takun Haske Batch:A
Free page
8...
Tsabar d'imaucewa da Hakeem ya yi yasa kasa tsayuwa akan kafafuwanshi, da sauri ya ja kujera dake fuskantar Azaad ya zauna. Sai ya yi yunk'uri furta magana bakinshi ya dinga kakkarwa, da kyar ya yi control ɗin kanshi ya sami damar furta.
"Why Aj?"
Shiru Azaad ya yi har zuwa lokaci bai d'auke hannunshi daga kan sajenshi ba, sai faman sha-shafa shi yake yi tamkar shafar ce za ta rage mishi radadi da k'unci da yake ciki a karo na biyu Hakeem yasake watsa mishi tulin tambayoyi.
"Miyasa Aj, miyasa ka yanke irin wannan danye hukunci, miyasa ka bari shaitan ya rinjaye ka, ka yanke hukunci cikin fushi nasan Kuna matuk'ar son junanku Kai da Salima miyasa za ka sake ta alhali sakin zai iya cutar daku?"
"Ba a ciki fushi na yanke wannan hukunci rabuwa da Salima ba Hakeem. Nayi iya k'ok'arina nagani hakan bata faru a tsakaninmu ba, amma tak'i bani haɗin Kai.
"Amma sai nake gani kamar hakan bai dace ba Aj akwai hanyoyi da za a magance wannan matsala, ba wai sai lallai wannan da ka bi ba.
"Hakeem na bita na rarrashe ta duk da ni nake da cikakken iko akanta amma kamar k'ara ingizata ake yi. Idan har nace zan cigaba da hak'uri da Salima menene makoma ta da yarana?" Salima ta za6i neman duniya fiyye da igiyoyin aurena. Shin Salima ita Kaɗai ce mace da ba zan rayu ba sai da ita?"
"Ba Kaɗai bace Aj shiyasa tun farko na zo maka da shawarar Karin aure...
"Ya isa Hakeem aikin gama ya riga ya gama babu saura komai a tsakaninmu domin text ɗin ka karanta tun ranar da ta bar k'asar nan, na turo mata a hali yanzu inaso na nemowa kaina farin ciki da narasa tun ganiyar kurciyata. Nima inaso na zama sarki a cikin fadar gidana, idan nace ayi sai ayi idan nace abari abi umarnina ba wai ni na bi ba.
"Aj ni aganina ko don albarkaci yara bai kamata ka saketa ba.
"Me take tsinanawa yara dukansu babu Wanda yasan dad'inta ita da babu duk daya yake a wurinsu, rabuwarmu ba abin da zai shafe su dashi.
"Shikenan Allah yasa shi yafi zama alkhairi Allah ya musanya maka da wacce tafi ta wacce za ta kawo farin ciki a rayuwarka.
"Amin thumma amin! Nagode Sosai da wannan addu'a taka Hakeem. in-sha-Allah rabuwarmu za kawo wani haske a rayuwata Ina jin hakan a jikina. Shiyasa na yanke shawara zan yi aure kafin ta dawo kuma na mik'a maka ragamar nemo min mata wacce ta fito gidan tarbiyya 'yar mutunci wacce za ta mutunta ni da yarana.
Murmushi Abdul-hakeem ya yi farin cikinshi ya kasa 6oyuwa, ya taso da sauri ya rungume Azaad tare da furta.
"Al-hamdu-lillah! Al-hamdu-lillah! Allah kaine abin godiya.
Azaad ya janye shi daga jikinsa ya mik'e tsaye tara da saka hannuwanshi cikin aljihu, ya yi tattaki izuwa gaban fridge sai kuma ya tsaya tare da juyowa ya dube Hakeem kana ya ce.
"Banso budurwa bazawara za ka nemo saboda za ta fi kulawa da yarana"
Take annurin kan fuskar Hakeem ya gushe, ya dube shi da baki sake.
"Amma wallahi Aj kai wawa ne, banda wawanci uban me za ka tsinta a jikin bazawara sauran wani.
"Uban da ake tsinta a jikin kowa ce mace.
"Look abokina kar ka 6ata goma biyar bata gyaru ba, kabar komai a hannuna wallahi-tallahi zan nemo maka wacce tafi dacewa da kai, in ma bazawarar ce ko budurwa muradinka dai 'yar mutunci mai ingantattaciyar tarbiyya.
Azaad ya ja iska ya fesar daga bakinsa ba tare da yasake tankawa Hakeem ba, ya nufi k'ofar fita da sauri Hakeem ya bi bayansa.
******************
Zaune suke a gaban wani k'aton mushirinki boka wanda bashida kyau gani, ko Kaɗan. Wata katuwar kwarya a gabanshi mai d'auke da ruwa farare tass...sai tafarfasa suke alhali ba a kan wuta suke ba. Wani yare yake yi mai kama da buzanci can kuma ya tsaya da tsoki burutsunsa, kafin ya tattaro hankali da natsuwarsa akan Alhaji Yusuf Junaid tare da k'annesa uku da ya zo tare dasu don ayi komai akan idanuwansu. Sai kuma Alhaji Buba wanda shine ya yi musu jagoranci zuwa wajen bokan.
Cikin muryasa mai amon sauti ya fara magana.
"Tuni aka sanar dani zuwanku miyasa ku kayi gareje tun lokaci ba ku zo ba sai yau?"
Alhaji Yusuf Junaid ya gyara zaman babban rigar shi, ya ce.
"Tafiya ba zata ce ta zo min zuwa Abuja sai jiya na dawo.
Shiru boka ya yi yana ta bin su da jajayyen idanuwanshi, kafin ya ɗaga gefen buzun fatar daminsa da yake zaune akai, ya dauko wata katuwar layya, ya jefata cikin kwayar a hankali layya take nutsewa cikin ruwan har nutse duka kana ya dawo da ganinshi akansu ya ce.
"Kun zo nan ne domin kashe d'an uwanku Azaad Junaid, kun je wajen bokaye da malaman tsinbo bila'adadin amma ba ku yi nasara ba?"
"Haka ne....
Ahmadu ya faɗa a hanzar ce.
"A yau dad'add'e burinku zai cika ni nan zan cika muku shi amma a bisa sharadin, za ku biya naira miliyan uku za ku kawowa aljanu jini jariri sabuwar haihuwa, sai kuma shanu manya guda bakwai.
Kafin Alhaji Yusuf Junaid ya yi magana Ahmadu ya riga shi ta hanyar cewa
"Idan har za ka kawar mana dashi fiyye da abin da ka lissafa za mu yi maka mu dai burinmu, mutuwar Azaad Junaid domin ita Kaɗai ce hanyar da za ta sada mu da mafalkinmu.
Boka ya kece da dariya mai kama da kukan aurakin jaki, sai da ya yi mai isarshi kafin ya ce.
"Tabbas yau burinku zai cika ku zuba idanu ku sha kallo.
Jefa hannunshi cikin ruwan yana jujjaya shi tare da kiran sunan Azaad Junaid, ba a d'auki dogon lokaci ba hotonshi ya baiyana a cikin ruwan yana tsaye ya kare waya a kunnenshi yana magana, boka ya dauko wata karamar wuka da ganinta za tai mugun kaifi ya dubi saitin zuciyar Azaad ya caka sai kawai Aslamiyya ta baiyana a gabanshi kafin wuka ta ta6i jikinta wuta ta kama kwaryar hatta da wukar dake hannun boka ci take da wuta, duk iya k'ok'arinsa naso ya jefar da ita ya kasa hannunshi sai ci yake da wuta da ya ji uwar bari ya zabura da gudu bala'in ya fita daga bukkarshi. kamar jira ake bokan ya fita kwaryar tai wani irin tsalle ta dire kasa ta tarwatse, wuta ta kama bukkar, su Alhaji Yusuf Junaid suka kwasa da gudu suka nufi k'ofar fita gashi k'ofar karama ce, sai tu-ture juna suke, da kyar Ahmadu ya samu ya ture Alhaji Buba da ya yi ba-bakere a jikin k'ofar shi bai fita bai kuma janye ba. Ahmadu yana samu ya ture shi gefe ya fice Alhaji Abdallah ya biyo bayan Ahmadu, har Alhaji Yusuf Junaid ya yunk'ura ya tashi daga faɗuwar da ya yi saboda lokaci da Ahmadu ya ture Alhaji Buba shi kuma ya faɗa masa, suka faɗi kasa a tare sai dai wani abin mamaki ya kasa tashi kamar wanda aka danne, shi ma Alhaji Buba ya gwada tashi ya kasa, su Ahmadu dake wajen bukkar sai ihu da neman agaji suke abin ka da dokar daji babu wanda zai ji su balle ya kawo musu d'auki. Alhaji Yusuf da Alhaji Buba su na ji su na gani wuta ta fara cin jikinsu, sai ihu suke tun su na ihu har suka sulele k'asa, bukkar kuma ta Kama gaba d'aya......
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪
*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*
*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*
*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*
*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*
*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*
*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*
*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*
*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*
*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*
*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*
KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*
SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*
SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*
*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Wattpad:-jeedddahaliyu
Haske writers Association.
Top Ten Takun Haske Batch:A
Second to the last Free page
9...
Los Angeles international airport {LAX}
A tsakiyar dare jirgin da ya dauko su Salima ya yi landing a los Angeles international airport. Tsakiyar dare ne amma sai kamar lokaci safiya ta waye, Salima tana gaba Hafsat Shinkafi tana biye da ita a baya. Cab suka hau zuwa Roosevelt hotel wanda tun kafin zuwansu k'asar suka yi booking. Hotel ne mai mugun tsadar gaske Kuma a cikinsa ne za a gudanar da seminar da suka zo.
Seminar ce ta manyan mata 'yan kasuwa na duniya duk wata gwaska Wanda ta amsa sunanta international business women tana wajen hatta da ticket ɗin shiga wurin idan ka ji makudan kud'i da ake siye ta sai ka girgiza, tun saukar Salima k'asar wayarta ke rufe. Tana zaune a room ɗinta jikinta sanye da bathrobe towel fitowar ta daga wanka kenan. Ta d'auki system ɗinta, ta shiga duba sak'oni email, anan taci karo da sakon Azaad Junaid a maimakon ta girgiza ko ta rud'e sai ma wani shegen blushing take, wanda ke nuni da ko Kaɗan sakinta da Azaad ya yi bai dame ta kawai dai tayi mamaki inda ya sami kwarin gwiwar rubuta mata message na saki har biyu. Ta kudurta a ranta bata saku ba domin a ganinta Azaad bai isa ya yanke hukunci shi Kaɗai ba ita ma tana da ikon ya ji nata ra'ayinta idan