Showing 48001 words to 51000 words out of 91651 words

Chapter 17 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

622

ta ji muryarta.

"Na shiga uku pretty ba dai Apollo ne ya kama ki ba?"

"A'a!

Ta faɗa a gajarce.

"To me ya sami idanuwanki haka kin ga kuwa yadda suka kumbure?"

Kasa bata amsa Miyya tayi sai kawai ta ce.

"Aneey ki je kuyi breakfast ni na sha tea banso mu yi latti kinsan yau Ina da test, wannan kumburin da idanuwana suka yi na rashin wadatatce barci ne jiya na kwana ina karatu.

"Saidai Airah don nima nasha tea a d'akina.

Aneesah ta faɗa tana kallon Airah girgiza kai Airah tayi tare da faɗin.

"Nima am okay mu tafi kawai.

Tuni Miyya ta mik'e ta wuce gaba suka biyo ta a baya yayin da Aneesah ke tsokanarta.

"Pretty yau duk tunani test ne yasa ba za a goya school bag a baya ba aka rik'e ta a hannu?"

Wata harara ta yi wa Aneesah da kumburarrin idanuwanta, Aneesah ta fashe da dariya Airah tana taya ta. Tun kafin su k'arasa parking lot idanuwanta suka yi tozali da mutumin da daren jiya ta raya shi da tunaninshi.
Yana tsaye ya yi folding hannuwanshi a k'irji jikinshi sanye da dark blue ɗin jallabiya mai gajeren hannu yana magana da d'aya daga cikin securities ɗin gidan.
Gaban Miyya ya yi mummunan faɗuwa, ta sadda kanta k'asa tana kusantar parking lot gabanta yana k'ara bugawa. Hatta da yana yi tafiyarta saida ya sauya jikinta ya shiga kakkarwa kamar mai jin sanyi ko wacce zazza6i ya kama, hak'oranta har wani hard'ewa suke yi.
Azaad yana tozali da ita ya kasa d'auke idanuwanshi daga kanta, ya shiga yawo dasu bisa jikinta tana sanye ne da white sports wears dogon farin wando haɗe da farar t-shirt ta ɗora farar cardigan akai, k'afarta sanye da white sneakers kanta kuma dauke da p-cap ita ma white a sama p-cap ɗin an rubuta white house. Aneesah da Airah ma irin kayan ne a jikinsu saidai kowace da irin colour house ɗinta Aneesah pink house Airah kuma red house.
Shi kanshi security ɗin sai da ya fahimci hankali Azaad ya karkata wani gun dabam, sakamakon yana magana bai ji ya amsa mishi ba. Sai kawai ya bi da idanuwanshi gun da ya ga yana kallo.

"Good morning Daddy!

Aneesah da Airah suka faɗa lokaci da suka iso kusa dashi.

"Morning my beautiful babies!

Ya faɗa cikin sexy tone ɗinshi, saukar muryarshi a kunne Miyya yasa ta ɗago da sauri, idanuwanta suka sark'e da nashi bugun zuciyoyinsu ya karu aka rasa wanda zai janye ganinshi, tuni wani irin shauk'i ya d'ibe su ya lula dasu wata duniya mai wuyar fahimta. Aneesah da Airah har sun kai wajen mota kamar an ce Aneesah ta juya ta ga Miyya tsaye ta kafe Daddynta da maye kallo kamar tsohuwar mayya, yayin da shima Daddy ya tattaro dukkan natsuwarshi akanta tamkar ya ga wata sabuwar halitta da bai ta6a gani ba a tsawon shekaru da ya yi a cikin duniya, zaro idanu tayi cikin kidimewa ta dafe k'irjinta tare da furta "Na shiga uku ni Aneesah......
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004


26..�?


Daga ranar da Hasheem ya falka ya ga an cire masa k'afa, kullum sai ya yage baki yana kuka tamkar k'aramin yaro.
Yau ma hakan ce ta kasance, kuka yake yi har dasu shassheka matarsa Haneefa ta kalleshi taja dogon tsaki "mtsss... dallah malam ka rufewa mutane k'aton bakinka ka bi ka ishe mutane da kukanka na banza da wofi.

Hasheem ya ɗago jajjaye idanuwanshi da ke tsiyaya hawaye ya dubi Haneefa, cikin muryar kuka ya ce.

"Haneefa ba ki da imani ko Kaɗan wallahi Ina cikin wannan hali shine ba za ki tausaya min ba ni fa mijinki ne Haneefa?"

Wani k'ullutun bak'in ciki ya tokare ta, ta zabga mishi katuwa harara.

"Ba zan ta6a tausaya ma ba Hasheem domin mugun so zuciyarka na tsiya wanda ka tsotsa a nono shi ne ya janyo ma hali da kake ciki, wato kana zato bansan kaik'ayi ne ya komawa mashek'iya ba, jiya duk abin da kuke faɗa Kai dasu Ahmadu akan kunnena, jira nake da zarar an sallame ka daga asibiti ka bani takarda ta na k'ara gaba don ni ban iya zama da musaki, ka je can ka nemo musaka irinka ka aure. Da lafiyata ba zan lalace a wofi akan ba"

Sosai kalaman Haneefa suka 6atawa Hasheem rai, musanmman da ya tuna duk wani faɗi tashi da yake yana k'arewa ne akanta da 'ya'yanta shine yanzu don ya haɗu da tawaiya tun kafin tafiya tai nisa za ta guje shi.

"Karki yi min haka Haneefa kinsan inasonki ba zan iya rayuwa babu ke ba....

Jifa da tayi da gwangwani madarar peak yasa ya haɗiye raguwar kalamanshi, sauri Kiriss gwangwani ya kai gareshi gaba ɗaya madarar ta zube dama tana shirin haɗe mishi tea. Cikin masifa da ruwan bala'i ta rufe shi da faɗa kamar za ta cinye shi. Ahmadu ya buɗe k'ofa ya shigo duk da ta ganshi bata fasa faɗar duk abin da ya zo bakinta ba.
Tsoron Allah ne ya kama Ahmadu ya yi tsaye k'ik'an kamar bishiyar kwa-kwa yana kallonta inda take shiga ba nan take fita ba. Yayin da Hasheem ke ta babbaka kuka.

"Kai daina yi mata kuka!

Ahmadu ya daka masa tsawa.

"Amma Keɗai Haneefa an yi lalatatciya marar imani da tausayi kalli hali da bawan Allah nan yake ciki.....

"Dakata Ahmadu!"

Ta daka masa tsawa kamar ba yayan mijinta ba, cike da rashin kunya ta ce.

"Duk hali da yake ciki shi ya siya da kud'insa, Kuma muddin bai cire hassada da mummunan buri akan Azaad ba, ya dinga gani masifa da bala'i kenan. Wata rana sai an tsinto gawarsa tsakiyar bola karnuka na yaga.

"Innalillahi.....Haneefa anya kinaso ki ga manzo Allah mijinki ne fa uban 'ya'yanki shine kike masa bak'in k'azafi da mummunan fata, tsakani da Allah da matuk'ar wahala ki shiga aljanna.

"Mtsss.....ku ne dai ba za ku shiga ajanna ba masu zuciyar kafiran farko, wanda babu Allah a zuciyarsu Kaɗan ku ka fara gani. Wallahi Muddin ba ku tuba ba mutuwarku sai tafi ta su Babban Yaya da Alhaji Buba muni da k'azanta.

"Kai....Kai....Kai...

Ahmadu ya faɗa cikin kad'uwa yana k'ank'ance idanu, wannan shi ake kira kana barci wani yana maka minshari.

"Hasheem ashe kai sakarai ne ban sani ba shine don tsabar lalacewa ka yashe sirrinkan mu tass...ka faɗawa figaggiyar matarka mai kama da an tsoma tantabara cikin ruwan zafi?"

"Wallahi-tallahi Yaya Ahmadu ban faɗa mata komai ba jiya muna magana tai mana la6e.

Hasheem k'arasa magana yana goge hawaye, da gefen hospital gown dake sanye a jikinsa. Haneefa tai musu kallon sama da k'asa ta watsar ta buɗe k'ofa ta fice Ahmadu ya bi ta da zagi.

**** *** *******

A hankali idanuwa Miyya suka fara lumsashewa numfashinta ya fara yi sama, sannu-sannu hankalinta ya fara barin jikinta. Ta saki k'ara mai firgitarwa ta faɗi k'asa a some kamar gitawar walkiya Azaad ya iso wurinta.
Aneesah da Airah da gudunsu suka nufo wurin har security ya kai hannunshi ya ta6a ta da sauri Azaad ya rik'e hannu, tare da watsa mishi mugun kallo. Ya durkusa gefen fuskata ya rik'o hannunta ya ji wani irin mugun zafi.

"Subhanalillah......Daddy me ya sami pretty ne?

Airah ta faɗa muryarta tana rawa kamar za ta sa kuka, Aneesah ma duk ta bi ta rud'e. Ya ɗago ya kallesu ya ga kowace su hankalinta ya yi matuk'ar tashi ya ce.

"Ku kwantar da hankalinku zazza6i ne kawai ke damunta na ji jikinta da zafi, ku tafi direba yana jiranku kada ku yi latti"

Ba don ransu yaso ba suka tafi har motarsu ta fice su na waiwaye ta. Azaad ya sunkuce ta, ya nufi wurin mota da gudu direbanshi ya dauko key ya buɗe mishi backseat ya shiga tare da rungumeta jikinsa zafin jikinta yana sauka a nashi jiki, lokaci zuwa lokaci yake kiranta sunanta yana d'an bubbuga kumatunta. Duk bubbugata da yake yi ko ko d'an yatsanta ba ta motsa ba, sai can ya ji taja wani dogon snoring bai san sanda tayi barci barci, ba sai snoring ɗinta ya ji ga Kuma idanuwanta a birkice la66anta suka fara kakkarwa ta shiga wani irin yare wanda duk yawon duniyarsa bai ta6a ji irinsa ba. Nan take ya ji tsigar jikinsa ya tashi wani irin tsoro yana shigarsa tun tana magana a hankali Wanda shi Kaɗai ke ji har ta dawo yi da k'arfi hakan ya janyo hankali mr Richard har ya juyo yana tambayar Azaad wane irin yare ne take yi, Azaad ya daka mishi tsawa babu shiri ya maida ganinshi akan steering.
Addu'ar ya shiga karantawa yana tofa mata, kafin su iso asibiti ta daina surutun da take Azaad ya umarci Mr Richard da ya kai su prime hospital, saboda tafi kusa abinka da asibitin kud'i nan take aka shiga dubata musanmman ma da ya kasance the young billionaire ne ya kawo patient ɗin da kanshi, special room aka kaita tare da yi mata fixing ɗin drip. Duk wani abu da take yi ta daina kasancewar allurai da aka yi mata akwai na barci nan take tayi barci.
Sai lokaci hankali da natsuwar Azaad suka fara dawowa jikinsa, Saidai sam bai ji dad'i da doc Jamal ya faɗa mishi ciwonta har da damuwa a ciki kuma idan bata rage tunani ba za ta iya kamuwa da hawan jini. Ko nan da can bai ɗaga ba yana nan zaune har drip ya k'are aka cire mata, da zimmar anjima za a sake saka mata wani. Sai lokaci ya kira Hakeem ya faɗa mishi, Miyya bata da lafiya su na asibiti ya yi handled clients ɗinsu.
Duk tsawon zaman da Azaad ya yi dai-dai da second d'aya idanuwanshi ba su gushe daga kallonta ba. Tausayinta ya ke ji har can k'asan zuciyarshi gani yake yi aurenshi ne silar shigarta damuwa ya k'udurta aranshi zai sauk'ewa mata ba zai so ya ci gaba da ganinta cikin wannan hali ba. Balle har hawan jini ya kama ta.
Haka ya ci gaba da tunani iri-iri kala daban-dabam duk akan Miyya. Ya d'an jinginar da bayan shi akan kujerar da yake zaune akai, bai san lokaci da barci ya d'auke shi ba. Dama daren jiya bai yi barcin kirki ba.
Sha biyu da rabi Miyya ta falka ta buɗe idanuwanta ta shiga yawo dasu kafin ta sauke su akan fuskarshi, ta ja ajiyar zuciya kana ta shiga murmushi yadda yake barci hankali kwance ba k'aramin burgeta ya yi ba. Ta matsa jikinta Kaɗan ta ɗora hannunta a shoulder shi ta kira shi cikin siriyar muryarta.

"Daddy!

Ya buɗe idanuwanshi da suka yi ja Kaɗan. Ta langwa6e kanta tana kallonshi da idanuwanta masu rikirkita mishi lissafi, ya d'auke kanshi da sauri cikin faɗuwar gaba wacce ya rasa ta me ce ce ya ce.

"Sannu pretty ashe kin falka"

K'asa tayi da kanta tana murmushi ta ce.

"Daddy barci kayi a zaune ko na sauko na ba ka gado ka kwanta?"

Murmushi ya yi tare da girgiza kai, a tunaninshi bata gane inda take ba. Daga haka ba wanda ya sake tankawa sai satar kallon juna suke yi kowa ne da abin da yake ji Miyya tanaso ta tashi ta shiga bathroom fitsari take ji sosai, amma tana jin kunyarshi Allah ya taimake ta aka kira wayarshi tana gani ya yi pick up tare da mikewa tsaye, ya yi nesa da ita Kaɗan ta sauko a hankali, ba ta wuce yi tako biyu zuwa uku ba jiri ya d'ibe ta, tayi baya za ta faɗi kamar an ce ya juyo ya ga tayi baya bai san lokaci da ya jefar da waya ba, ya rugu da gudu kafin ta kai k'asa cikin zafin nama ya dank'o dantse hannunta. Ita kanta sai da ta ji zafin rik'on da ya yi mata kamar daga sama ta ji ta akan k'irjinshi, yasa hannunwanshi ya zagaye bayanta ya rungumeta irin runguma da ake yi wa laqabi da duk runtsi muna tare. Lumshe idanuwanshi ya yi yana ji bugawar zuciyarta yayin da numfashinta mai d'an zafi-zafi yake sauka a gefen kafad'arshi kasancewar akwai raguwar zazza6in da bai k'arasa sakinta ba. Wani shock mai k'arfin gaske ya ja shi gaba ɗaya magudanar jini jikinsa ta tsaya cakk...cikin wani bakon yanayi ya shiga shinshina gefe-gefen wuyanta yana had'awa da murza gadon bayanta da dukkan hannuwanshi, yana fitar da numfashi da sauri-sauri k'arar buɗe k'ofa yasa shi dawowa hayyacinsa idanuwanshi suka yi tozali da fuskar da ta rikita shi ta kuma firgita shi....
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004


27....



Hakeem ya yi tsaye ya saki bak'in da hanci tare da zaro idanuwanshi yana kallon ikon Allah. Sam ya kasa gasganta abin da idanunshi ya gane mishi arrogant Azaad Junaid ne rungume da yarinyar da ya yi kirari cewa ba abin da zai yi da ita tai mishi k'ank'anta. Wata irin mashahuriyar kunya ce ta lullu6e Azaad ya tabbata ganye shi ya Kad'e Hakeem ya ganshi yana romancing ɗin Miyya yau kam sai da ya toshe kunnuwanshi da auduga, don sai ya sha tsiya kala daban-dabam.
Azaad ya shiga yakice ta daga jikinshi ɗagowa da za tayi tai tozali da Hakeem da yai mutuwar tsaye, saurin sadda kanta k'asa tayi ta ra6a gefen Azaad ta shige bathroom da sauri ta maida k'ofa ta rufe.

"Sai ka rufe k'ofar ka k'araso wannan dai halin banza ne ka shigowa mutane d'akin bakatatan...ba knocking on.

Azaad ya faɗa a fusace yana wani muzurai shi a dole so yake ya fuske. Hakeem ya kwashe da mahaukaciyar dariya shak'inyaci har dasu dafe ciki ya maida k'ofar ya rufe yana ci gaba da ban-banka dariya. Dama Azaad yasan hakan zai faru yau kan ya shiga uku. Wai me ma ya kai shi romancing ɗinta miyasa ya kasa haɗiye kwadayinsa gashinan rashin hak'urinsa ya jawo masa shak'inyaci Hakeem.
K'arasowa Hakeem ya yi kusa da shi ya tsagaita da dariya amma still da murmushi akan fuskarshi.

"Kai mutumina tabarma kunya da hauka ake nade ta, to bari ka ji duk ta yanda ka nadeta ba zan fasa faɗar abin da idanuwana suka gane min ba. Yanzu fissibillahi....Aj nufinka a d'akin asibiti za ka haik'ewa 'yar mutane?"

Azaad ya yi shiru tare da lumshe idanuwanshi yana shafar sajenshi, hakan ne ya ba Hakeem damar ci gaba da yi masa tsiya.

"Ai wannan d'an gadon ba zai d'auke ku ba in fact bata da lafiya kodai har kayi abin ne shine silar rashin lafiyarta ta?"

"OMG.....!

Azaad ya faɗa sounding very angry ya buɗe jajjaye idanuwanshi ya kalle Hakeem dasu.

"Kai fa ba k'aramin tantiri bane Hakeem abin da ka gani ba wani abu bane jiri ne ya d'ibeta za ta faɗi na taro ta....

Kafin ya dasa aya Hakeem ya sake kwashewa da dariya har yana had'awa da bugun gado, Azaad ya kauda fuskarshi zafin dariya nan ta Hakeem yake ji ba Kaɗan ba. Sai da bashi da yadda zai yi illa ya zuba masa idanu.

"Gaskiya Aj mugun jarababbe ne kai bayan wanda kayi a gida a asibiti ma ba za ka bar 'yar mutane ta huta ba?"

"Banso iskaci Hakeem ka daina yi min wannan wasan banzan ka ji ko?"

Azaad ya faɗa cikin fushi. Hakeem ya sake tintsirewa da wata sabuwar dariya da ta fi ta farko da Azaad ya fahimce mahaukaci k'arfi da yaji Hakeem zai maida shi sai kawai ya kalle shi da girar ido ɗage ya ce.

"To wai kai miye naka a ciki don na raya sunnah a asibiti haramun ne?"

"Ba haramun bane saboda matarka ce halak-malak amma kuma ka tuna ana bari halak don kunya"

"Ashe dai kasan cewa matata ce saboda haka ka yi shiru da bakinka ka daina wannan dariyar iskancin naka, ko na kora ka waje.

Hakeem ya dafe bakinshi da hannunshi yana dariya mamaki yake yi yaushe Aj ya yi baki har haka, ba shakka Aslamiyya ta fara canza shi.
Da shigarta bathroom ta faɗi zaune dabasss....ta jingina bayanta ga bango tana sauke numfashi bi da bi, sosai take ji kunya haɗuwa da uncle Hakeem shikenan ya ganta ita da Daddynta su na rungume da juna yanzu Allah Kaɗai yasan irin fassara da zai musu.
Mararta ta murd'a a dalilin fitsari da ya cika ta taff...da rarafe ta isa wurin toilet seat tai fitsari tare da kama ruwa ta koma wajen da ta taso ta zauna.
Saida Hakeem ya gaji don kanshi, da yi wa Azaad tsiya kala daban-dabam wani ya mayar masa wani kuma sai ya yi shiru. Kafin suka d'auko wata fira can dabam har suka gangaro akan ciwon Miyya.

"Ikon Allah! Gaskiya Aj bana gani damuwarta ta ta'alak'a ne ga aurenka, kawai dai akwai abin da ke damunta da dabam amma ba wannan ba.

Hakeem ya faɗa yana kallon Azaad numfashi Azaad ya sauke tare da kallon k'ofar shiga bathroom kafin ya ce.

"Bana tunani a k'anana shekarunta ace akwai abin da zai jefa ta damuwa face wannan Kar ka manta Hakeem ba a son ranta aka yi mata aure ba. Kaga kuwa dole ta sa damuwa a ranta, ni gaskiya nayi decided na saukewa mata kuma in-sha-Allah zan ci gaba da kula da ita. Ba zan bari duk wani abun cutarwa ya ra6e ta ba. Zan yi gagarumin yak'i da duk wanda ya yi yunk'uri 6ata mata.

Tun tsawon lokaci da ya fara magana Hakeem ya tsare shi da idanu yana karanta reaction ɗinshi, ko wace kalma da take fitowa daga bakinshi yana fassarata da tashi fahimta.

"Aj are you in love with her?"

Hakeem ya watsa mishi tambayar ba zata damm..... gabanshi ya faɗi bai zaci wannan tambaya za ta fito daga bakin Hakeem ba. Shiru ya yi tare da haɗe tafin hannuwanshi wuri d'aya yana murzawa.
Murmushi Hakeem ya saki haɗi da yin hamdallah, ya karance halayar Azaad sosai duk lokaci da ka yi mishi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login