Showing 3001 words to 6000 words out of 91651 words

Chapter 2 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

605

na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske Writers Association.

Top Ten Takun Haske Batch: A

Free page

2....

Tafiya mai nisa gaske suka yi kamar za su bar gari, kafin suka nufe wani katafare kamfaninsa na sarafa danye gold mai suna AJ Gold Company ba wai iya sarafawa company ya tsaya ba. Yana siye tsofaffin gold ya mayar dashi new model, su na kuma siyarwa. Gate ɗin company Kaɗai abin kallo ne za ka yi zaton shima da gold ɗin aka k'era shi, sakamakon yadda yake shek'i da daukar ido.
Da sauri securities dake tsa-tsaye birjik su na ba wa company tsaro, biyu daga cikinsu suka wangale musu gate. Sai daff da k'ofar reception mr Richard ya yi parking d'aya daga cikin security dake tsaro k'ofar ya hanzarta buɗewa Azaad Junaid k'ofar mota ya fito cikin tsananin miskilancinsa da k'assaita ya ɗagawa ma'aikatan da ke mik'a masa gaisuwa hannu, k'ofar reception ɗin ta tsuge kanta kasancewar ta gilashi ce.
Kaitsaye ya nufi elevator ya hau wanda zai sada shi da office ɗinshi dake hawa na 6 mutane biyu ne suka take masa baya har izuwa cikin tangamemen office ɗin nasa.
*****************
Gani Amal ta buɗe idanuwanta yasa Aslamiyya ta sauke k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta shiga k'ok'arin ɗaga ta sai dai kashh! Ta kasa sakamakon yadda ta ji hannunta ya rik'e kamar an daure mata shi da igiya. Sai kawai ta fashe da kuka mai ta6a zuciya ta kifa kanta akan cikin Amal ta ci gaba da rera kukanta, Amrah ce ta shigo gidan bakinta d'auke da sallama hannunta rik'e da bak'ar leda mai d'auke da koko da ta siyo musu, su karya kumallo. Kafin ta k'arasa sallamar idanuwanta suka yi tozali da siblings ɗinta zube a tsakar gida ga Aslamiyya tana ta faman kuka batasan lokaci da ta jefar ledar koko ba, ya buge bango ledar ta fashe kokon ya malale akan sumunti, ta kwasa da gudu ta nufi wajensu. Aslamiyya na ganinta ta ɗago idanuwanta da suka fara renewa zuwa jajayye.

"Subhanalillah! Miyya me ya faru ne me kuke yi anan kuka me kike yi?"

Kusan a tare Amrah ta jero mata wad'annan tari tambayoyi ba ko shed'awa.

"Amal ce ta suma na zaci ko ta mutu ne na kawo ta wurin Dadda ta duba ta, shine ta hankad'o ni waje"

Ajiyar zuciya Amrah ta sauke cike da tausayi 'yan uwanta. Har sai yaushe Allah zai yanke musu wannan bak'ar wahala da suke ciki?" Kullum addu'ata da fatanta Allah ya kawo wanda zai za me musu bango majingina, ya yi musu gatan da suka rasa. wanda zai fitar dasu daga bala'in k'unci da tsangwama da suke ciki. Ranta a 6ace ta ɗago Aslamiyya ta mik'ar da ita tsaye

"Daina kuka Miyya in da sabo yaci ace kin saba da tozarci da ake mana, a gidanan. Da wahala tana kisa da tuni an shafe babin mu a doron duniya, sai Kuma gashi ubangiji ya yi mana tsawon rai duk da yadda akeso kawo k'arshen numfashin mu.

Ta k'arasa magana tare da sunkuyawa ta ci-ci6i Amal da ke kwance tana numfashi guda-guda, tsabar yadda ciwo ,ya cinyeta yasa ta dawo tamkar 'yar shekara huɗu ba 13 uku ba. Ta nufi d'akin da ya kasance mallakin su a gidan. Za ka sha matuk'ar mamaki ace d'akin da suke ciki mai rai ke kwana a cikinsa amma su ko a jikinsu saboda sun ri ga da sun saba da rayuwa a ciki. Akan wasu tulin tsomakarai wanda su ne suka kasance wurin kwanciyarsu Amrah ta shinfid'e Amal idanuwanta taff da hawaye sai k'ok'ari danne su take bataso Miyya ta gani, duk da kasancewar ita ce k'arama amma tafi Miyya k'arfin zuciya Aslamiyya irin jinsi mutane nan ne masu raguwar zuciya da rauni batada hayaniya ko Kaɗan ga sanyi hali kamar ruwan fridge, ga ta da matuk'ar hak'uri duk abin da za ai mata bata ta6a tankawa sai dai taci kukanta in tagaji tai shiru. Rayuwarta gaba d'aya ba abin da tasani ta kuma saba da shi irin kuka. Duk cikin su uku Amrah ce kawai halinsu ya ban-banta da nasu ita ma Amal halinta sak! Irin na Miyya ne.
Amrah ta dubi Aslamiyya da ke tsaye a jikin k'ofa tana ci gaba da aikin nata na kuka tace.

"Wai Miyya ba za ki hak'ura ki daina kuka nan haka ba?" Wallahi ki yiwa kanki k'iyamulaili ki adana raguwar hawayenki kada su k'are akan wad'anan mugaye mutane azzalumai da babu burbushin imani a zuk'atansu"

Sai da Miyya ta ja majina da ke k'ok'arin fito mata ta k'ofufin hanci ta maida ta inda ta fito, ta kuma ja dogon karan hancinta da yatsunta biyu kana ta k'arasa shiga d'akin ta zauna kusa da Amal, ta shiga shafa kanta a hankali Amal ta ɗago farare idanuwanta ta dubi yayar tasu wacce ta maye musu gurbin uwa da uba tasaki mata murmushin k'arfin hali ita ma Miyya murmushi tayi hawaye na zuba akan kumatunta.

"Sannu Amal Allah ya ba ki lafiya Allah ya kawo miki k'arshen wannan ciwo, Allah ya canza mana k'addarar mu ya kawo mana sauyi wata rana mu d'and'ani rayuwar farin ciki.

Da sauri Amrah ta durkusa ta rungume Miyya suka fashe da kuka, ba ka ji komai sai sautin kukansu gwanin ban tausayi, sai da suka ci kuka iya son ransu kafin su rarrashi kansu. Sai lokaci Amrah ta tuna da kokon su na naira hamsi da ta zubar zuciyarta tai mugun bugawa saboda tasan sanadin tashin ciwon Amal hadda yunwa a ciki, zubur ta tashi ta nufi k'ofar fita Miyya na kwalla mata kira ko juyowa ba tai yi ba ta fice daga gidan.
********************
Tun shigowar shi office ɗinsa ya kasa aiwatar da aikin komai ga tarin files zube akan desk da zai yi signing up. Amma ya ga-gara tabuk'a komai cire hular kanshi ya yi, ya aje akan desk ɗin ya shiga shafar suma kanshi. Damuwa tana neman tai mishi yawa tsoronshi daya kada ciwon hawan jini ko ciwon zuciya, ya kama shi. Ga dukiya mai tarin yawa Allah ya albarkace shi da ita amma ya ga-gara samun farin ciki da natsuwar zuciya kullum cikin k'unci da 6acin rai yake.

K'arar k'ararawa da ya karad'e office ɗin nashi ya dawo dashi daga duniyar tunani da ya nutse, ya kai duban shi akan allon cctv da ya ke iya gani wanda keso shigowar office ɗin, amininsa kuma MD na company sa Abdul-hakeem Daura ya gani tsaye yana jira ya buɗe masa k'ofa ya shigo, kasancewar k'ofar tana using da code dole sai in shi ya buɗewa mutum zai iya shigowa da remote control ya yi amfani k'ofar ta zuge kanta Abdul-hakeem ya baiyana. Duk faɗin duniya ba shi da wani amini d'an uwa sai Abdul-hakeem saboda 'yan uwanshi da suka had'a uba ba k'aunarshi suke yi ba. Su na bak'in ciki da hasada da daukakkar da Allah ya yi mishi. Burinsu a kullum bai wuce su sami hanyar da za su kawo k'arshen sa.

Da shigowar Abdul-hakeem ya yi tsaye ya saka Azaad gaba yana kallo, nan take ya fahimci halin damuwa da yake ciki. ko bai tambaye shi ba yana da tabbaci Madam Salima ce damuwar shi, saboda duk faɗin duniya ita ce matsalarshi ita ce mai jefa shi halin damuwa.
Ya girgiza kai haɗi da jan kujera dake kallon Azaad ya zauna.

"Aj ya kamata ka dinga sassautawa kanka yawan tunani kada ya zo ya shafi lafiyarka. Tunani ba shi bane solution ɗin matsalolin ka ba.

Azaad ya ja gwaron numfashi kana ya lashe lips ɗinsa, cikin zazzak'ar muryarsa mai dad'i da tafiyar da ruhin mai sauraren shi yace.

"Ni kaina ba so tunani nake yi ba Abdul zuwa min kawai yake yi. matsaloli su min yawa ga na 'yan uwana ga na iyalina da wane zan ji?" Yanzu duk wanda ya gani zai dauki cewa na fi kowa farin ciki a duniya saboda ina da tarin dukiya ba asan cewa wani tallaka wanda bai da ci yau balle na gobe ya fi ni domin shi, yana samun natsuwar da kwanciyar hankali daga iyalinsa.

"Zance na gaskiya Aj kaine ka za6awa kanka wannan matsala, Salima ba za ta ta6a sauyawa ba. To saboda me kai ba za ka nemowa kanka mafita ba?" Tun yaushe ni da Jadda muke ba ka shawara ka k'ara aure amma ka k'i sai ka zauna bak'in ciki mace d'aya ya kashe ka.

"Please Abdul-hakeem ka fahimce matsalata ba ta k'arin aure bace. sai fa ka ji dad'i abu kake neman k'arinsa.

"Matsalarka kenan Aj idan aka yi gabas sai kayi yamma, dole fa sai ka cire tsoron Salima ko don farfado da tarbiyyar 'ya'yanka ka tuna yaranka mata ne dole su na buk'ata ingantattaciyar tarbiyya. Idan mahaifiyarsu ta kasa sai ka nemo wacce za ta maye gurbinta mana.

Mik'ewa Azaad Junaid ya yi hannayenshi zube cikin aljihun wandonshi, ya taka a natse zuwa gaban widow da ke kallon titi. Yaye labule idanuwanshi suka sauka akan motoci da ke kai da komuwa. Shima Abdul-hakeem mik'ewa ya yi ya isa daff dashi kana ya dafa kafad'arsa.

"Ka yarda dani Aj aure shine yafi dacewa da kai ka tuna kullum shekarunmu k'ara tafiya suke yi dole sai muna samun natsuwar da kwanciyar hankali, so ka ga kenan don ka k'aro aure ba wani abu bane. Allah yasani kayi hak'uri iya hak'uri da Salima lokaci ya yi da za ka d'and'ani zak'i da gard'i dake cikin aure"

D'an gajere murmushi Azaad Junaid ya yi wanda ya tsaya iya fatar bakinshi, kana ya juya yana facing Abdul-hakeem.

"To naji idan ma na amince zan k'aro aure wa zan aura?" Sani kanka ne Abdul tun daga lokaci da na auri Salima ko mafalki ban ta6a kallo wata 'ya mace naji ina sonta ba. Ta ya ya ka ke tunani zan yi aure?"

"Mtsss...!

Abdul-hakeem ya ja siririn tsaki da ke baiyanar da takaicinsa a fili.

"Ba dole bane sai ka ji son mace za ka aure ta ba, kai da za ka yi auren huci haushi ina ruwanka da soyayya. Alhaji ka amince kawai ka ga aiki da cikawa ni da kaina zan nemo ma matashiyar budurwa wacce Nonuwanta suke tsaye cakk! Ka sha shagali abinka.

Zaro idanuwa Azaad Junaid ya yi tamkar ya ga abin tsoro kana yasa dariya wanda rabon da ya yi irinta har ya manta.

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske Writers Association.

Top Ten Takun Haske Batch: A

Free page

2....

Tafiya mai nisa gaske suka yi kamar za su bar gari, kafin suka nufe wani katafare kamfaninsa na sarafa danye gold mai suna AJ Gold Company ba wai iya sarafawa company ya tsaya ba. Yana siye tsofaffin gold ya mayar dashi new model, su na kuma siyarwa. Gate ɗin company Kaɗai abin kallo ne za ka yi zaton shima da gold ɗin aka k'era shi, sakamakon yadda yake shek'i da daukar ido.
Da sauri securities dake tsa-tsaye birjik su na ba wa company tsaro, biyu daga cikinsu suka wangale musu gate. Sai daff da k'ofar reception mr Richard ya yi parking d'aya daga cikin security dake tsaro k'ofar ya hanzarta buɗewa Azaad Junaid k'ofar mota ya fito cikin tsananin miskilancinsa da k'assaita ya ɗagawa ma'aikatan da ke mik'a masa gaisuwa hannu, k'ofar reception ɗin ta tsuge kanta kasancewar ta gilashi ce.
Kaitsaye ya nufi elevator ya hau wanda zai sada shi da office ɗinshi dake hawa na 6 mutane biyu ne suka take masa baya har izuwa cikin tangamemen office ɗin nasa.
*****************
Gani Amal ta buɗe idanuwanta yasa Aslamiyya ta sauke k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta shiga k'ok'arin ɗaga ta sai dai kashh! Ta kasa sakamakon yadda ta ji hannunta ya rik'e kamar an daure mata shi da igiya. Sai kawai ta fashe da kuka mai ta6a zuciya ta kifa kanta akan cikin Amal ta ci gaba da rera kukanta, Amrah ce ta shigo gidan bakinta d'auke da sallama hannunta rik'e da bak'ar leda mai d'auke da koko da ta siyo musu, su karya kumallo. Kafin ta k'arasa sallamar idanuwanta suka yi tozali da siblings ɗinta zube a tsakar gida ga Aslamiyya tana ta faman kuka batasan lokaci da ta jefar ledar koko ba, ya buge bango ledar ta fashe kokon ya malale akan sumunti, ta kwasa da gudu ta nufi wajensu. Aslamiyya na ganinta ta ɗago idanuwanta da suka fara renewa zuwa jajayye.

"Subhanalillah! Miyya me ya faru ne me kuke yi anan kuka me kike yi?"

Kusan a tare Amrah ta jero mata wad'annan tari tambayoyi ba ko shed'awa.

"Amal ce ta suma na zaci ko ta mutu ne na kawo ta wurin Dadda ta duba ta, shine ta hankad'o ni waje"

Ajiyar zuciya Amrah ta sauke cike da tausayi 'yan uwanta. Har sai yaushe Allah zai yanke musu wannan bak'ar wahala da suke ciki?" Kullum addu'ata da fatanta Allah ya kawo wanda zai za me musu bango majingina, ya yi musu gatan da suka rasa. wanda zai fitar dasu daga bala'in k'unci da tsangwama da suke ciki. Ranta a 6ace ta ɗago Aslamiyya ta mik'ar da ita tsaye

"Daina kuka Miyya in da sabo yaci ace kin saba da tozarci da ake mana, a gidanan. Da wahala tana kisa da tuni an shafe babin mu a doron duniya, sai Kuma gashi ubangiji ya yi mana tsawon rai duk da yadda akeso kawo k'arshen numfashin mu.

Ta k'arasa magana tare da sunkuyawa ta ci-ci6i Amal da ke kwance tana numfashi guda-guda, tsabar yadda ciwo ,ya cinyeta yasa ta dawo tamkar 'yar shekara huɗu ba 13 uku ba. Ta nufi d'akin da ya kasance mallakin su a gidan. Za ka sha matuk'ar mamaki ace d'akin da suke ciki mai rai ke kwana a cikinsa amma su ko a jikinsu saboda sun ri ga da sun saba da rayuwa a ciki. Akan wasu tulin tsomakarai wanda su ne suka kasance wurin kwanciyarsu Amrah ta shinfid'e Amal idanuwanta taff da hawaye sai k'ok'ari danne su take bataso Miyya ta gani, duk da kasancewar ita ce k'arama amma tafi Miyya k'arfin zuciya Aslamiyya irin jinsi mutane nan ne masu raguwar zuciya da rauni batada hayaniya ko Kaɗan ga sanyi hali kamar ruwan fridge, ga ta da matuk'ar hak'uri duk abin da za ai mata bata ta6a tankawa sai dai taci kukanta in tagaji tai shiru. Rayuwarta gaba d'aya ba abin da tasani ta kuma saba da shi irin kuka. Duk cikin su uku Amrah ce kawai halinsu ya ban-banta da nasu ita ma Amal halinta sak! Irin na Miyya ne.
Amrah ta dubi Aslamiyya da ke tsaye a jikin k'ofa tana ci gaba da aikin nata na kuka tace.

"Wai Miyya ba za ki hak'ura ki daina kuka nan haka ba?" Wallahi ki yiwa kanki k'iyamulaili ki adana raguwar hawayenki kada su k'are akan wad'anan mugaye mutane azzalumai da babu burbushin imani a zuk'atansu"

Sai da Miyya ta ja majina da ke k'ok'arin fito mata ta k'ofufin hanci ta maida ta inda ta fito, ta kuma ja dogon karan hancinta da yatsunta biyu kana ta k'arasa shiga d'akin ta zauna kusa da Amal, ta shiga shafa kanta a hankali Amal ta ɗago farare idanuwanta ta dubi yayar tasu wacce ta maye musu gurbin uwa da uba tasaki mata murmushin k'arfin hali ita ma Miyya murmushi tayi hawaye na zuba akan kumatunta.

"Sannu Amal Allah ya ba ki lafiya Allah ya kawo miki k'arshen wannan ciwo, Allah ya canza mana k'addarar mu ya kawo mana sauyi wata rana mu d'and'ani rayuwar farin ciki.

Da sauri Amrah ta durkusa ta rungume Miyya suka fashe da kuka, ba ka ji komai sai sautin kukansu gwanin ban tausayi, sai da suka ci kuka iya son ransu kafin su rarrashi kansu. Sai lokaci Amrah ta tuna da kokon su na naira hamsi da ta zubar zuciyarta tai mugun bugawa saboda tasan sanadin tashin ciwon Amal hadda yunwa a ciki, zubur ta tashi ta nufi k'ofar fita Miyya na kwalla mata kira ko juyowa ba tai yi ba ta fice daga gidan.
********************
Tun shigowar shi office ɗinsa ya kasa aiwatar da aikin komai ga tarin files zube akan desk da zai yi signing up. Amma ya ga-gara tabuk'a komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login