Showing 72001 words to 75000 words out of 91651 words

Chapter 25 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

615

tashi da sauri ya maidata jikinshi ji tayi yana sauke numfashi akai-akai tai sauri d'agowa ta kalli fuskarshi tasa hannunta akan kwatatcen sajenshi tana shafawa a hankali, cike da damuwa akan fuskarta ta ce.

"Daddy ya naji kana sauke numfashi ko ba ka da lafiya ne?"

"Lafiyana qalau na dai kwaso gajiya ne.

Ya fad'a cikin sauri tare da basarwa, gudun kada ta yi saurin gano yana cikin damuwa, domin shi mutum ne ba iya 6oye damuwa ba. Sai kawai yai saurin cireta daga jikinshi yana fad'in.

"Bari nai wanka ko jikina zai saki.

Ya yi magana tare da nufar bathroom, kafin ta sake yi magana har ya bud'e k'ofa ya shige bathroom din. Har ya fito daga wanka idanuwanta suna kafe a k'ofar bathroom, ya fito daure da white towel a k'ugunshi yayin da yake goge sumar kanshi da k'aramin towel tai sauri tasowa ta nufe shi.

"Daddy har ka fito?"

"Nayi sauri ne?"

"Ka dai dad'e saura kiriss na bi ka ciki Kawo towel din na taimaka maka.

Ta fad'a tana kallonshi tana dariya, mik'a mata towel din ya yi ya nufi gaban dressing mirror ya ja stool ya zauna yana cewa.

"Ai da kin bi ni da sai wanka yafi armashi.

Harararshi kawai tayi ta ci gaba da goge mishi jiki, komai ita tayi mishi hatta da kayan da zai saka ita ta za6a mishi. Sai lokaci ya mayarda hankalinshi akan gown d'inta take sanye da ita.

"Wow....gown d'inan tayi matuk'ar yi miki kyau, kamar na cinye ki prettyna.

Sosai furuncinshi na k'arshe ya bata dariya, ta dawo gabanshi tana ci gaba da dariya ta shiga jujjuyawa ta yadda zai k'ara gani rigar da kyau. Riko ta ya yi yana tayata dariya da take yi.

"Da gaske nake yi prettyna idan kina min irin wannan kwalliyar da wuya na iya fita.

"Rufa min asiri Daddy kada ace maka mijin tace ni dai mu je na ba ka abinci kada gari wannan zuzutawa da kake min kaina ya fashe.

Hannunshi ta riko suka nufi kofar fita, yana cewa.

"Karki damu prettyna wannan suna an jima da kirana dashi, ba a kanki za a fara ba, zan yi farin ciki idan aka kirana dashi ta dalilinki.

Wani irin farin ciki marar misaltuwa kalamansa suka haifar mata, sai murmushi take dokawa, da suka iso dining room tai sauri ja masa kujera ya zauna kafin ya kai zaune ya ce.

"Ban ji motsi Airah da Ahlam ba?"

"Ahlam tayi barci tana d'akin Nanny Lacey, Airah kuma tana d'akinta wayau nai mata nace zan je na gyara maka d'aki.

Ta k'arasa magana tana dariya tare da bud'e warmer mai dauke da tuwo ta ciro guda d'aya ta cire ledar da ke jikinshi ta saka a plate ta zuba mishi miya a k'aramin bowl ta sake bud'e warmer da farfesu yake ciki shima ta zuba mishi. Tun kafin ya ci tuwon yawunshi ya tsinke ya kalleta yana murmushi.

"Ashe my pretty tana da wayau har haka, ai ni na zaci yau ba zan ganki cikin sauki ba.

Saida ta tura mishi plate din gabanshi ta ja kujera ta zauna, kafin ta ce.

"Daddy kenan ai tuni ka gama awon gaba da zuciyata, shiyasa ba zan iya jure zama nesa da kai ba. Ko fitar nan da kayi Allah saida zazza6i ya kamani.

Zaro manyan idanuwanshi ya yi yana kallonta baki bud'e, tai sauri daukar murfin warmer ta kare fuskarta dashi, dariya ya yi tare da girgiza kai ko kad'an bai zaci Aslamiyya za ta iya maganganu masu tafiyar da ruhi har haka ba. Har ya bud'e baki zai yi magana tai sauri tarar numfashinsa. Batare da ta cire murfin da tasa ta kare fuskarta ba.

"Daddy please ka ci abincinka kada ya huce abinci yau special ne girki amarya ne fa in kaci sai ka bada tukuici na musanmman.

Ta k'arasa magana tana k'ara sunne fuska cikin murfin warmer din, dariya ya yi yana k'ara jin sonta yana k'ara link'aya a cikin zuciyarshi. Yana ci tuwo yana gyada kai alamar ya yi mishi dad'i kusan rabin ya cinye kafin ya dauki bowl din farfesu shima yaci sosai sannan ya sha ruwa da drinks d'inta ta zuba mishi a handle cup.

"Alhamdullilah....girkin amaryata ya yi dad'i ba kad'an ba saidai next time idan za tai min girki karta cika yaji sosai saboda angon nata bayaso yaji. Kuma in-sh-allah zan bada tukuici da abu mafi tsada da daraja.

Tun da ya fara magana take kallonshi tare da langwa6e kai, tayi rau-rau da idanuwanta ta ce.

"Afuwan rabin raina wallahi bansan na cikawa miyar yaji ba amma in-sh-allah a gaba zan kiyayye.

"Karki damu prettyna a hakan ma nagode miki sosai na kuma yi farin ciki marar misaltuwa, da zan iya tsaga zuciyata da na tsagata ki shiga ki ga yadda kika haifar min da farin ciki, domin yau shine ranar ta farko da ni Azaad Junaid naci abinci da matata ta aure ta girka min da hannuwanta, idan nace dake pretty ban ta6a cin abinci da Salima ta girka da hannuwanta ba. Watakila ba za ki yarda ba ko?"

"Zan yarda mana Daddy saboda na tabbata ba za ka fad'i abin da ba gaskiya ba.

Shiru ya yi zuciyarshi tana mishi wani iri anbatar suna Salima kadai da ya yi, hannunshi ya mik'a mata ta kama tare da tasowa yai mata masauki a cinyoyinshi.

"Bari nai feeding dinki prettyna saboda naji cikin nan naki ya k'are shafewa da yawa.

"Na goshi Daddy mun ci pancake ni da Airah.

Ta fad'a tana k'ara kwantar da kanta a k'irjinshi, a hankali ya sauke ajiyar zuciya sun jima a zaune suna ta6a fira yawanci firar ita ce ke yi iyakancinsa ya bata amsa a takaice ko kuma ya yi dariya mai k'aramin sauti, dogowur hamma tayi kafin tasa tafin hannunta ta rufe bakinta yai sauri kai nashi hannu ya rufe mata, da ta gama hammar ya cire hannunshi tare da sumbatar gefen wuyanta daga zaune da yake ya mik'e da ita ba tare da ya direta a k'asa ba. Ya nufi upstairs dauke da ita hannuwanta ta sakala a wuyanshi, har suka iso bedroom d'inshi tana aikin kallonshi, duk duniya idan da akwai abin da bata gajiya da kallonshi bai wuce fuskar Azaad ba.
Da kanshi ya sauya mata kayan jikinta zuwa sleeping dress, ya kwantar da ita kamar wata 'yar baby kana ya wuce bathroom ya yo brush, yana fitowa wayarshi tana fara ringing Miyya tai sauri mik'a hannunta akan bedside ta dauko mishi wayar, kamar an ce ta kalli sensor din wayar sai kawai ta ga suna Salima yana yawo gabanta yai mummunan fad'uwa....
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004



37...

Hannu Azaad ya mik'a mata da ta mik'o mishi wayarshi, kasa mik'a mishi tayi sai kawai ta tsare shi da idanuwanta masu cike da zallar tsoro da fargaba.

"Pretty bani wayar mana kada kiran ya tsinke"

Ya fad'a cikin taushin murya. Sai lokaci ta ankara da abin da tayi cikin sauri ta mik'a mishi dai-dai
kiran yana tsinkewa jikinta a sanyayye ta koma ta kwanta har da su jan duvet ta lullu6e rabin jikinta tare da lumsashe idanuwa.
Gani sunan Salima a matsayin wacce ta kira shi yasa ya ja siririn tsaki yana shirin rufe wayar ga baki d'aya kiranta na sake shigowa ranshi ya sake 6aci a fusace yai received cikin kakkausar murya ya ce.

"Ya aka yi ne Salima?"

"Ba irin wannan tambayar ya kamata kai min ba Azaad.

"Look Salima banaso shashanci ki fad'i maganarki kawai idan kuma ba ki da abin fad'a Kira kawai kika yi domin ki katse min jin dad'i da iyalina, ki sani ba za ki sake kira ba balle har na d'aga.

Sosai furuncinshi ya daketa tamkar an da6a mata wuka a kahon zuciya, batasan lokaci da ta fashe da kuka ba. Cikin muryar kuka take magana

"Ban ta6a tsanmani ni Salima zan zama abin wulak'antawarka ba, duk 6acin rai da ka shiga bai dace ka dinga fad'awa uwar 'ya'yanka uku bak'ak'en maganganu ba. Amma ba komai Azaad nan da d'an wani lokaci za ka fara nadama za ka dawo kana denied duk wasu munana kalamai da ka dinga furta min da bakinka.

Wani mugun tsaki Azaad ya yi yana huci domin ba k'aramin bak'anta mishi rai kalamanta suka yi ba, in banda wawanci da dabbanci har shine zai yi nadama ba ita ba. Tsabar takaici kashe wayarshi kawai ya yi ya nemi kusa da k'afafuwan Miyya ya zauna ya dafe kokon kanshi yana fitar da iska me zafin gaske daga bakinshi, tun daga lokaci da ya fara magana da Salima Miyya take aikin rarraba idanuwanta akanshi duk da ba wata maganar arziki yake yi da ita ba amma wani irin zafin take ji a can cikin k'asan zuciyarta. Wanda ta rasa na menene sannu a hankali ya dora hannunshi a tafin kafarta ta hagu yana mata tafiyar tsutsa, har cikin kwayar kanta take ji tafiyar tsutsa da yake mata dariya ta shiga yi tana jan k'afarta saida ya gaji don kanshi sannan ya saki k'afar ta ta, ya nemi kusa da ita ya kwanta tare da shigarta da ita cikin k'irjinshi yana shafar gadon bayanta a hankali cikin sanyi muryarta ta ce.

"Daddy kayi hak'uri Dan Allah ka dai-daita tsakaninka da mommy, in yaso ka kafa mata dokokin na tabbata a wannan karo ba za ta sa6a maka ba.

Har ta dasa aya a zancenta bai katseta ba, bai kuma furta uffan ba yai shiru tamkar yana nazarin maganganunta daga bisani ya ja numfashi ya sauke tare da cewa.

"Please prettyn Daddy karki k'ara 6ata min rai mana shin bana fad'a miki banaso kina min zancenta ba?"

"Amma Daddy ba shi zai sa nai shiru na zuba maka idanu ka cutarda iyalinka. Infact yaranka da matarka suna bukatarka Daddy please kada ka zama mai son kai...

"Ya isa pretty!

Ya katseta cikin kakkausar murya wacce ke nuna ya fara hasala da zantukanta, ya cire ta daga k'irjinshi ya dora kanta a pillow ya mik'e ya shige bathroom, Miyya ta bishi da kallo kafin ta gyada kai ta lumshe idanuwanta kafin ya fito har tayi barci ba k'aramin dadin hakan ya ji ba. Domin ya tsani ayi mishi zance Salima ko wane iri ne.
Madam Salima kasa barci tayi sai tufka da warwara take yi ta rasa mafita guda d'aya kwakwara har asuba bata rintse ba.
Da wuri Miyya ta tashi ta shiga kitchen da taimakon Nanny Lacey ta kammala had'a breakfast, ta bar Nanny tayi arranging dining table ita kuma ta wuce d'akinta ta fesa wanka, ta shirya cikin atamfar super Holland style din skirt and blouse dinki yai masifar kar6a jikinta, bata daure d'an kwali ba sai ta yane kanta da k'aramin mayafi. Jikinta na fidda k'amshin Arabian perfumes, ita da kanta sai da ta yabawa kanta da irin kyau da tayi d'akinsu Airah ta nufa koda ta shiga Airah ta shirya cikin school uniform d'inta tana zaune gefen gado tana sanya takalminta, fuskarta dauke da murmushi ta ce.

"Good morning my Airah!

"Morning our pretty.

Airah ta fad'a tare da d'agowa ita ma da murmushi akan fuskarta, kana ta cigaba da fad'in.

"Wai pretty yaushe za ki koma school ne?"

Ajiyar zuciya Miyya tayi kafin ta jingina bayanta a bango, jikinta a sanyaye ta ce.

"Bansani ba Airah don har yanzu Daddy bai yi maganar komawa ta ba, gashi next month za a fara exams.

"Kiyi mishi magana mana pretty kada karatunki ya koma baya.

"Shikenan zan yi mishi taso mu je kiyi breakfast kada ki yi latti.

Airah ta mik'e tare da daukar katuwar schoolbag d'inta ta bi bayan Miyya, saida ta raka Airah parking lot kana ta nufi d'akin Daddy tana tura k'ofa yana fitowa daga wanka, tsaye tayi a jikin k'ofa tana kallonshi tana murmushi cikin shagwa66iyar murya tayi magana.

"Good morning my Daddy!

"Morning prettyna kin yi matuk'ar kyau kamar na hadiye ki, amma miyasa kika gudu kinka bar Daddynki, bansan cewa kin tashi ba saida na lalla6oki naji wayam saura kiriss na fashe da kuka?"

Ya k'arasa magana cikin shagwa6e murya, kamar dai yadda take mishi. Hakan ba k'aramin burgeta ya yi ba, bata ta6a gani babba yana shagwa6a ba sai akan Daddy shiyasa tasa dariya tare da rufo k'ofa ta nufi wurinshi tana mai cigaba da dariya ta mik'a hannunta, ta kar6i towel din da yake goge dashin ruwan jikinshi.

"Wai Daddy ka manta ne ba mu kadai bane a gidanan ba?"

"Uhm...dama nasan da wannan za ki dogara idan kika ce ki dinga nuna min wariya launin fata zan kwashe yaranki na maida su idan suka fito.

Ya yi magana cikin zolaya tare da kallon cikin idanuwanta.

"Tuba nake yi my Daddy kai ma kasan kaine bugun zuciyata dai-dai da second d'aya banaso kayi nesa da ni, soyayyar da nake maka ce ta shafi yaranka.

Sosai kalamanta suka haifar mishi da farin ciki, hannunta ya riko ya sumbace tafin hannun nata.

"Ina sonki pretty so da bansan adadinsa ba kiyi min alqawali a duk yadda rayuwa ta zo mana ba za ki gujeni ba.

Murmushi tayi tare da dank'e hannunshi.

"Nayi alqawali Daddy har izuwa k'arshen numfashina Ina tare da kai ba kuma abin da zai sauya hakan.

"Nagode prettyna Allah ya ba ki ikon cika wannan alqawali.

"Amin thumma Amin!

Daga haka ta shiga taimaka mishi ya shirya cikin suit dark green colour, tana rike da briefcase d'inshi suka sauko k'asa gani ya nufi k'ofar fita tai sauri dakatar dashi.

"Daddy ya naga ka nufi k'ofar fita breakfast din fa?"

"I'm sorry my love na manta ban fad'a miki ba ina azumi.

"Azumi kuma Daddy?"

Ta fad'a da zallar mamaki akan kyakkyawar fuskarta, hannunta ya rike sannan ya sauke numfashi cikin sanyaya murya ya ce.

"Kwarai kuwa azumi nake yi my love kiyi k'ok'ari ki had'a min abinci bud'a baki.

"A iya sanina Daddy Monday and Thursday ake yi azumi yau kuma talata ko ka zaci yau Monday ne?"

Girgiza kai ya yi yayin da jikinshi yai masifar sanyi damuwa ta baiyana k'arara akan fuskarshi, yai saurin kauda fuskarshi gudun kada ta fahimci halin da yake ciki ya rintse idanuwanshi yana jin wani irin zafi a k'asan zuciyarshi.

"Daddy please ka answer me kana fad'ar azumi kake yi naji hankalina ya tashi...

Cikin hanzari ya katseta ta hanyar fad'ar.

"Karki damu prettyna azumin kaffara ne a shekaru baya na ta6a buge wani mutum har ya rasa ransa shine yau na fara azumi.

Cikin kaduwa ta zaro manyan idanuwanta muryarta yana rawa ta furta.

"Daddy mutum ka kashe azumi sittin fa za ka yi?"

Tayi magana tana dafe k'irji tare da zaro idanuwa ta kakkafe shi dasu.
Cike da rauni ya gyada kanshi, ya mik'a hannu ya kar6e briefcase d'inshi da ke hannunta ya juya cikin sauri ya bud'e k'ofa yana fadar.

"Na tafi prettyna sauri nake yi ina da meeting banaso nayi latti, ki had'a min abinci mai dad'i amma kada ki cika yaji sosai irin na jiya.

Ta bishi da kallo tsigar jikinta na tashi Sai kawai ta tsinci kanta cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa, da kyar ta iya jan k'afafuwanta ta nufi d'akinshi ta gyara mishi har ta kintsa d'akin batada natsuwar zuciya.
Azaad Junaid yana fita da direbanshi mr Richard basu yi tafiya mai nisa ba direban madam Salima ya fito daga ma6oyarshi ya bisu a baya, wanda madam ce tasaka shi duk wani shige da fice na Azaad Junaid ya binciko mata tun karfe 6 yake zaune a unguwar sai yanzu yaga fitarshi ya fito da wayarshi jikinshi har rawa yake yi ya kirata ya sanar mata fitarshi, nan ma umarni ta bashi ya ci gaba da binshi ita kuma ta wafci handbag d'inta ta fito direban yara ya dauke ta suka fice daga gidan.
Mr Richard yana cikin tafiya yaji mota ta fara jacking ya gangara gefen titi ya yi parking Azaad ya yi nisa a tunani shiyasa bai fahimci abin da yake faruwa ba saida ya ji saukar muryar mr Richard a dodon kunnenshi.

"Sir motar nan tana da matsala kuma ni kaina ban fahimci tana da matsala ba sai yanzu da ta fara mana jacking.

Shiru Azaad ya yi yana shafar sajenshi damuwa da yake ciki ba zata bashi damar dogon surutu ba, kafin yai nasarar bud'e baki yai magana mr Michael ya yi parking kusa da motarsu ya fito tare da knocking glass din k'ofa mr Richard ya saukarda glass din yana murmushi farin ciki saboda yasan matsalarsu ta ragu.

"Sir ga mr Michael ka fito ya k'arasa da kai company ni kuma zan jira zuwan engineer Bello ya wuce da motar garage.

Nan ma Azaad bai tanka ba Mr Richard ya fito da sauri ya bud'e masa k'ofa ya fito, suka nufi waje motar Mr Michael ya shiga kana Mr Richard ya ajiye masa briefcase din shi kusa dashi sai lokaci mr Michael ya gaidashi hannu kawai ya d'aga mishi suna cikin tafiya wayarshi tayi ringing jikinshi a sanyaye yai picking.

"Hakeem!

Ya furta cikin wani irin murya da jin sautinta kasan mai ita yana cikin zallar damuwa.

"Aj kana ina akwai kyakkyawan labari?"

"Ina bisa hanyar zuwa Aj gold company.

"Shikenan sai ka k'araso Amma ya naji muryarka wani iri?"

"Hakeem damuwa ce ta taru ta yi min yawa a duk lokaci da na tuna nine silar mutuwar mahaifin Aslamiyya sai naji wani iri matsananci tsoro ya lullu6eni. Hakeem ta wacce hanya zan fito na fad'a mata ni na kashe mata mahaifi?"

"Aj please ka natsuwa kasan abin da kake fad'a yadda kake magana tamkar da gangan ko da wata mummunan manufa ka kashe shi, idan ka kwatar da hankalinka sannu a hankali za mu nemo mafita in-sh-allah komai za tafi dai-dai.

"Ba za ka gane bane Hakeem al'amarinan fa babba ne domin na ragewa kaina nauyi yau na tashi da azumi yanzu kuma Ina neman ta yadda zan fad'awa Aslamiyya da kakarta ni na kashe Usman....

"Aj ya isa haka sai faman nanatawa kake yi kai ka kashe mahaifin Miyya wai kana jin dad'i fad'ar hakan ne?" Dan Allah mu aje wannan maganar har ka k'araso company bai kamata muna tattauna irin wannan maganar ba akan hanya.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da kashe wayar sai lokaci ya tuna da mr Michael yake tare ba amintattacesa ba mr Richard ba, a karo na biyu ya sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login