Showing 42001 words to 45000 words out of 91651 words
you already know that.
Har suka sauko downstairs parlor bai tsaya ba ita kuma bata fasa bin shi ba tana zubda ruwan rashin mutunci. Da gudu 'yan aikinsu suka watse Nanny Lacey ma d'akinta ta shige har da su murza key tana tsanmani, Azaad ya faɗawa madam zance aure da ya yi ne shine ta buɗe kwadon masifa da sanyi safiya.
"Dole ka dawo ka ji da matsalata first kafin ka fita, ko kana da abin da yafini muhimmanci ne?
Jin abin da ta faɗa yasa shi sakin handle ɗin k'ofa ya juyo a mugun fusace, cikin kakkausar murya ya ce.
"Me kika ce Salima?"
Yadda yai mata tambayar tasan ta reni ce da so gani k'arshenta, shiyasa ta kalleshi da murtuk'akk'iyar fuskarta.
"Duk abin da na faɗa ka ji ni sarai....so no need to repeat..
Ta faɗa tana irin mak'e kafad'a da watsi da hannuwanta da ke nuni da zallan reni.
"A tunanina Salima its over between us ko kin manta we're already divorce? Saboda haka ki fita harkana a hali yanzu kwata-kwata bana buk'atarki a rayuwata. Tun daga ranar da kika sa k'afa kika fita daga gidanan tare da yi fatali da umarni da rantsuwata ni kuma tun daga ranar I erased all the moment I'll have spend together....
"Ya isheka haka Azaad!
Ta faɗa sounding very angry idanuwanta suka firfito, ta kuma finciko towel ɗin kanta tai jifa dashi tasoma tattaki ta nufo shi tare da nuna k'irjinta da yatsa gaba ɗaya mamakin maganganunshi take yi ta kasa yarda daga bakinsa suke fitowa.
"Ni...ni Salima...Azaad kake gayyawa you erased all the moment I'll have spend together are you insane?"
"Lokaci ne za ban-bance mana tsakani ni da ke waye mahaukaci.
"To wallahi-tallahi bari ka ji Azaad ban amince da wannan saki ba saboda haka you have to cancel it, an gayamaka na shirya rabuwa da kaine?" You have to ask me first kafin ka yanke wannan banzar hukunci naka, saboda haka ni ban shiryawa rabuwa da kai ba because I want to spend the rest of my life with you so you better cancel that stupid divorce....
Cikin kad'uwa Azaad yake kallonta tare da waro idanuwanshi.
"Ashe duk tsawon shekaru nan da kidahumar jahila nake zaune ban ta6a sani Salima ke k'asurgumar mahaukaciya bace sai yau da kika fito min da 6oyayyen asalinki. Inaso ki buɗe kunnuwanki ki saurareni da kyau wallahi-azim idan duk duniya nan za taru akaina na gama aurenki.
Yana k'arasa magana ya juya cike da 6acin rai ya buɗe k'ofa da k'arfi ya fita yana bi sa hanyarshi ta zuwa kamfaninsa, na Gold Hakeem ya kirashi ya fesa mishi mummunan labari an har6en Hasheem a gidan gonar babban Yaya fasa zuwa company ya yi nufi prime hospital inda Hasheem yake likitoci sun duk'ufa ceto rayuwarshi, ana sa ran sai an cire mishi k'afa a dalili kwayoyin cuta sun shiga cikin raunin har sun ta6a naman k'afar tashi kasancewar har saida ya kwana ya yini kafin maigadi ya farga da hali da yake ciki.
Madam Salima ta fi minti goma a tsaye ko kwakkwaran motsi ta kasa da kyar ta iya jan kafafuwanta da suka yi mata mugun nauyi har kamar ba nata ba.
Har wani bishi-bishi take gani, ga zuciyarta dake mata mugun tuk'uk'i a haka ta soma tattaka matattak'alar bene duk lokaci da ta taka one stairs sai ta tsaya ta sauke wahalallen numfashi, kamar mai cutar asthma koda ta isa d'akinta ta jigata matuk'a, sai kawai ta kife akan tangamemen gadonta. Sai tayi yunk'uri yi kuka ko za ta ji sauk'i abin da take ji yana mata yawo a kahon zuciya, sai ta danne shi da k'arfin tsiya a ganinta zubda hawaye na rakwaye mata ne ba na iri-irinta jajirtattu bane.
Idan har ta bar hawayenta suka zuba akan kumatunta hakan na nufi ta faɗi, kwata-kwata a tsarinta babu faɗuwa sai zallan nasara. Tabbas Azaad ya taro match kamar yadda ya faɗa ne idan duk duniya za su taru akanshi ya gama aurenta. Ita ma abin haka yake a wurinta idan duk duniya za su taru akanta yanzu ta fara zaman aure dashi. Yayin da shed'aniyar zuciyarta ta ce da ita
"Haba Salima yaushe kika fara sakin jiki da har wani mahaluki zai haifar miki da damuwa?" Azaad ya k'ikk'iro wannan hanya ne domin ya sami lagonki ya rusa miki business career dinki idan kika bari yai nasara akanki shikenan babban company zai koma hannun 'yan uwanki, karki manta burinki ya ta'alak'a ne da son mallakarsa ke Kaɗai.
Babu shiri ta mik'e zubur a lokaci d'aya k'arfi da kuzarinta da rasa na wancan gadin suka dawo jikinta tamkar ba abin da ya faru da ita a cikin k'ankani lokaci ta shirya cikin Indonesia gown mai adon sequence sai kyali da daukar ido take. Ta fice abinta daga gidan kaitsaye gidan aminiyarta Hafsat Shinkafi direba ya sauke ta....
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Top Ten Takun Haske Batch:A
*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004
23....
Tun lokaci da ta fara labartawa Hafsat Shinkafi labari abin da ya faru, tai k'uru da idanuwa tana kallonta duk tsawon shekaru da tai da madam Salima batasan cewa bata da ilimin addini kwata-kwata ba. Ta zaci kawai dai bata yi zurfi a ciki ba ashe tunani da hasashenta ne ya bata hakan. Cabdijam.... lallai Salima jahila ce lamba d'aya wato ita tsabar ruwan boko da ta kwankwad'a da kuma cudanya da masu jajjaye kunnuwa ta kwashe dabi'unsu tsaf in banda hauka da jahilci a ina aka ta6a sakin mace har ta kusa gama iddah ta ce bata aminta da saki ba. Watakila bata ma san menene iddah ba.
Ajiyar zuciya Hafsat ta sauke kana ta cire tagumin da tayi cikin natsuwa ta fara magana.
"Gaskiya Salima kin tafka babban kuskure na 6oye min message ɗin da Azaad ya turo miki, da tun farko kin faɗa min da na wayar miki da kai.
"Mtsss....dallah ya isa Hafsa ni fa kwata-kwata ban d'auke message ɗin da muhimmanci ba. Azaad bai isa ya yanke alak'ar aurenmu ba...
"D'an dakata mana Salima!
Hafsat ta faɗa da sauri tare da tasowa ta zauna daff da Salima kana ta zarce da faɗin.
"Salima idan ke ba ki da ilmin addini ko tantama bana yi Azaad yana dashi. Kuma shi ɗin ba mahaukaci bane, a lissafi na saura kwanaki Kaɗan ki kammala iddarki idan har kika kammala ta batare da Azaad ya furta ya dawo dake ba. To ki sa aranki aure ke dashi hayatan-hayatan har sai ya sake biya sadaki an ɗora muku wani aure. Da Kuma saki uku ne ba za ki sake halatta agareshi ba har sai kin sake wani aure idan Allah ya kawo k'addarar rabuwarku da wancan mijin da kika aure sannan ne kike da damar sake aure Azaad Junaid. Salima babban abun da ya cuce ki rashin ilimin addini da kina dashi ko kusa ba za ki furta rashin amincewa da sakin da Azaad yai miki ba. Allah {S.W.T}ya halatta saki a hannun maza saboda mace tana da saurin fushi da saurin yanke hukunci. Mafi yawanci mata suna tafiyar da al'amuransu akan abinda zuciya ta raya musu. Amma shi namiji yana da zurfin tunani da hangen nesa, Kuma zai yi hasashe tare da yin aiki da hankali.
"Dallah....ya isa haka Hafsat kin wani tsareni da dogon sarhi in fact kwakwalwarta ba za ta d'auke shi ba. Gara kawai ki faɗa min hanyar da zan bi na dai-daita al'murrana.
Doguwar ajiyar zuciya Hafsat ta sauke tana girgiza kanta tabbas sai yau ta k'ara yarda da magana nan ta masu iya magana da ke cewa jahilci yafi hauka.
"Salima ni fa ina k'ok'ari na haska miki haske ko za ki fita daga mummunan duhu da kike ciki, ke kuma kina danganta ni da dogon sarhi. Wallahi-tallahi idan har kika ci gaba da tafiya a haka gaba ɗaya al-amurranki ba za su dai-daita ba. Saidai su ta6ar6are gwara tun wuri ki natsu na ɗora ki akan hanya.
"Na ji Hafsat amma ni wannan karatun naki zai shigeni ne bayan ki faɗi hanya da zai bi Azaad ya dawo da aurenmu.
"Mtsss....wai Salima meke damunki ne huh?" Sai nayi gabas kiyi yamma yanzu nan ma ba hanyar ce nake faɗa miki ba.
"Shikenan Hafsat ina sauraren ki.
Ta faɗa cike da izza tare da nuna k'osawarta. Yayin da Hafsat ta gyara zamanta ta cigaba da faɗin.
"Salima a halin yanzu dole sai kin sauke wannan girman kan naki da izza, ki bi hanyar maslaha ki karkato da hankali Azaad kafin iddarki ta cika ya dawo da aurenku karki sake iddarki ta cika bai dawo da ke ba. Idan har da gaske kina da burin ci gaba da zama matar Azaad Junaid dole ki sauke girman. Ki bashi hak'uri idan ta kama ki durkusa on your knees....
"Whats?" Hafsat kinsan abin da kike faɗa kuwa? No....no... Its can not be possible haba ki sake shawara ban da wannan na durkusa fa kika ce?
"To ai shikenan tun da ba za ki iya ba amma inaso ki fara lissafa kanki a jerin zauwarawa, ki kuma fara hango Azaad Junaid da tsaleliyar amaryarshi.
Zuciyar Madam Salima ta buga da k'arfi duk duniya ba abin da ta tsana irin ta ji an danganta Azaad ɗinta da wata mace ba ita ba.
Cike da 6acin rai ta kalli Hafsat ta ce.
"Hafsat zan dawo da Azaad gareni batare da na k'ask'antar da kaina ba, ki tuna ni mace ce mai k'arfin iko da izza ban ta6a yarda da faɗuwa ba sai nasara saboda haka Azaad zai dawo gareni ko yana so ko bayaso.
"Salima karki yi ganganci domin iddarki tana daff da cika, ki tuna aiki da hankali yafi aiki da agogo.
"Kai... Hafsat...kai! Gaba ɗaya kin isheni da zance iddah wai wacece wannan iddar da keso shiga tsakanina da mijina?"
"Innalillahi wa'aina illahim raji'un!
Hafsat ta faɗa tana tafa hannuwanta cike da kad'uwa take kallon madam Salima, kafin ta girgiza kai tana ta6e baki.
"Ni dama nasan za ayi haka hasashena kuwa ya tabbata gaskiya, Salima iddar ce ba ki sani ba anyya kuwa Salima kina gudanarda addininki yadda shari'a ta sharad'a?"
6ata fuska tayi cike da izgilanci ta ce.
"Banso maganar banza Hafsat za ki faɗa min wacece iddah ko na d'auki jakkata na bar miki gidanki?"
"Uhmm....jahili ya fi mahaukaci hauka.
Hafsat ta faɗa cikin zuciyarta a bayyane kuma sai ta ce.
"Yanzu kuwa zan faɗa miki wacece iddah? Iddah ba mutum bace kamar yadda kika zata.
"Idan har ba mutum bace to wacece ita ko aljana ce?"
Madam Salima ta watsa mata tambaya tare da yatsine fuska.
Hafsat bata bi ta kanta ba ta gyara zamanta ta tattaro natsuwa da dukkan hankalinta ta mayar dasu akan Salima.
"Iddah ita ce zaman jira da mata ke yi bayan sun rabu da mazajensu kafin su sake yi wani aure. Ita kanta iddar kala biyu ce akwai iddar rasuwa akwai iddar rabuwa.
"D'an dakata mana Hafsat ita iddar hadda ta mutuwa akwai? Cab.... gaskiya wannan iddar akwai rikitarwa.
"A wurin marar ilimin kan tana da matuk'ar wahala fahimta amma a gun mai wadattace sani ba abin da ya fi ta sauk'i.
"Ban fahimci ki ba Hafsat ki yi min magana da yare da hankali da tunanina zai d'auka?"
"Idan har kinaso hankali da tunanina su dauka sai kin daina katse ni kawai ki buɗe kunnuwanki ki saurare abin da nake faɗa domin ke zai amfana ba ni ba, saboda ni nasan da wannan babin tun ina da shekaru goma sha uku a duniya.
Sosai ran madam Salima ya fara 6aci tsakani da Allah ba don tanaso sani wacece iddar nan ba, da tuni ta wufce jakkarta tabar ma Hafsat Shinkafi gidanta.
Gani yadda take cika tana batsewa yasa Hafsat bata jira jin ta bakinta ba ta ci gaba da cewa.
"Iddar rasuwa ita ce bahaushe yake kira da takaba. Ita ɗin ma kala biyu ce akwai takabar mai ciki ita iddarta tana kammala ne daga lokaci da ta haihu. Wacce ba mai ciki ba Kuma zata zauna ne tsawon watani huɗu da kwanaki goma. Nau'in iddar rabuwa ta kasu kashi uku iddar mai ciki, da iddar mai jini haila sai Kuma mace da bata fara jini haila ba. Ko Kuma wacce ta fidda rai daga zuwan jini haila bima'ana tsohuwa. Iddar mace mai ciki za ta zauna ne har zuwa lokaci da ta haife ciki. Idan ta haihu to iddarta ta k'are Koda kuwa ranar da aka sake ta ɗin ne ta haihu.
Iddar mace mai jini haila, sai tayi jini uku. Da zarar tayi jini uku shikenan iddarta ta kammala kamar ke kenan tafiyar da muka yi kin yi menstruation sau biyu yanzu da zarar kin sake yin wani kin gama iddarki sai fatan samun wani miji idan kina da sha'awar sake aure. Sai Kuma iddar tsohuwa ko k'aramar yarinya......
"Ya isa Hafsat ai kin riga kin faɗi iya abin da nakeso ji ki bar saura kawai idan natsuwata ta dawo jikina Kya faɗa min.
Jikinta na rawa ta mik'e ta d'auki handbag ɗinta da ke aje akan center table, ta dubi Hafsat da idanuwanta da suka fara canza launi ta ce.
"Hafsat zan tafi gida tabbas a yau ɗinan zan kira ki da albishir ɗin Azaad ya dawo da aurenmu.
"Ina miki fatan haka Salima amma idan burinki ya cika ki nemi malamin addini, ya k'ara miki haske akan sha'ani addini kada ya zamana kina amsa suna musulunci ne kawai. Gaba ɗaya rayuwarki Salima neman duniya kawai kika sa gaba, kin manta da neman lahira al'hali lahira a duniya ake nemanta wallahi da zarar ka mutu shikenan....
"Nagode da shawara Hafsat.
Ta katseta cikin k'osawa da zancenta, ta juya cikin tafiyar sauri koda ta fito direbanta yana zaune a mota yana jiran fitowar yana d'aya ɗaga k'a'idojinta duk idan ya kaita bai isa ya tafi ba dole ya zauna har ta gama abin da ta je yi.
***** ***** *******
Duk wani shige da fice na asibiti Azaad ne ya yi hatta da jini da za a yi wa Hasheem surgery nashi aka d'iba, ko Kaɗan bai so a cirewa Hasheem k'afa ba so ya yi ya fitar da shi waje, saida doctors ɗin suka yi connecting ɗinshi da wani asibiti dake Germany suka turo musu bayyanai Hasheem su ma sun bada shawarar a cire k'afar kawai saboda ta riga ta fara lalacewa. Daga k'arshe sai yanke k'afar aka yi, lokaci da aka fito da Hasheem daga theatre room Azaad har dasu kuka saboda ba k'aramin tausaya mishi ya yi ba. Saida ya ga an kammala komai sannan ya wuce kamfaninshi koda ya iso tuni Hakeem ya wakilce shi meeting ɗin da za su yi.
Bayan sun Miyya sun dawo daga school suna zaune a downstairs parlor, Nanny Lacey ta fito daga kitchen sai lokaci take sanarda Aneesah da Airah dawowar Mommy. Nan take gaban Miyya ya faɗi duk wani annuri da ke kan fuskarta ya gushe, har wani zazza6i ta ji yana neman rufe ta. Daga Aneesah har Airah ba wanda ya nuna farin cikinshi da dawowar mommy ɗin, sai ma aikin gabansu da suka ci gaba da yi. bayan kamar minti goma da Nanny ta faɗa musu dawowar madam, suka ji karar buɗe k'ofa a zatonsu daddy ne ko wasu bak'i sai kawai suka yi tozali da madam Salima fuskarta a murtuk'e ko daga yanayi tafiyarta Kaɗai za ka gano irin zallan 6acin ran da take ciki. Miyya tana ɗago idanuwanta sai akan fuskarta kasa ci gaba da kallonta tayi shiyasa tai maza ta mayarda ganinta akan Ahlam da ke kwance a cinyoyinta tana barci.
"Welcome mommy!
Aneesah da Airah suka faɗa a tare yadda suka gaidata bai yi kama da gaisuwa irin ta uwa da 'ya'yanta ba. Daga haka ba wacce ta k'ara koda kallonta ne. Ita ma hannu kawai ta ɗaga musu ba wani kulawa balle ta nuna tayi kewarsu tana daff da fara taka matattak'alar bene idanuwanta suka hasko mata Miyya......
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Top Ten Takun Haske Batch:A
*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004
24...
Har ta buɗe baki da nufi yi magana sai kuma ta tuna da k'alubali da ke gabanta. Yanzu ba lokaci tambaya da neman sani wacece wannan bak'uwar fuska da ke hakince a falonta wacce ko arziki gaisuwa bata samu daga gareta ba. Ba komai ko ma wacce idan ta dawo natsuwarta za ta ji da ita. Tayi kwafa har da su cije le66e ta haura sama da shigarta d'aki tai wulgi da handbag tare da mayafinta kana ta cire kayan jikinta wani iri nauyinsu take ji.
Miyya tana gani madam Salima ta haura sama, ta tashi da sauri ta shige d'akinta.
Aneesah ta bi ta da kallo saboda ta lura da sauyawarta tun daga lokaci da tai arba da mommynsu.
Miyya ta kasa samun sukuni shigarta d'aki bai amfana mata komai ba. Sai ma k'ara mata fargaban zuci da ya yi zazza6i da take ji ya k'ara tasiri a jikinta ta haye gado tare da shigewa cikin duvet ita kanta tasan musanbabin zazza6inta ya samo asali ne daga tsorata da gani madam Salima da tayi a gefe d'aya tana ji radadin da za ta shiga idan ta daina tozali da kyakkyawar fuskar Daddy. Batasan dalili da yasa yanzu idan bata ganshi ba take rasa natsuwa da kwanciyar hankalinta ba.
Tun lokaci da Madam Salima ta baro gidan Hafsat Shinkafi bata sake samun natsuwa ba. Ta rasa wacce mafita za ta kama so take haɗa dabarorin da take ganin za su zama sanadiyar da Azaad zai dawo da aurensu ba tare da ta k'ask'antar da kanta agareshi ba.Tana ji a jikinta Azaad ba zai ta6a iya k'arasa rayuwarshi babu ita ba a dalilin mahaukaci so da yake mata. Har dare ya yi tana k'unshe a d'aki har zuwa lokaci bata ware d'aya daga cikin dabarar da take gani za tai amfani da ita da za ta karkato da hankalinshi.
Kiran