Showing 51001 words to 54000 words out of 91651 words
tambaya bai yi maka kallon girar ido ɗage ba which means ya amince da tambayar da ka yi mishi. Hakeem ya yi k'asa da murya ta yanda Azaad Kaɗai ne ke ji abin da yake faɗa tamkar dai mai rad'a ya ce.
"Aj kai ba k'aramin yaro bane balle ka ce ba kasan hanyoyin da za ka bi ka nemi soyayyar mace ba. Ko mace irin Miyya da batasan menene so ba, cikin ruwan sanyi za ka mallake zuciyarta. Aj Kana da matuk'ar buk'atar kulawar mace, shiyasa nakeso ka d'auki Miyya a matsayin babban kyauta daga Allah. Ubangiji ne ya dubi halin da kake ciki ya kawo Aslamiyya a rayuwarka domin ta zame maka waraka. ka zauna ka yi tunani da kyau za ka gano kai da Aslamiyya haɗin Allah ne bana mutum ba.
Azaad ya yi shiru yana sauraren bayani Hakeem shi da kanshi yasani ya kamu da son Miyya so ba na wasa ba. Amma muddin ya yi bincike ya gano shine silar jefata damuwa tabbas zai danne soyayyar da yake mata, ya saukewa mata aurenshi saboda yana so ta dauwama cikin farin ciki musanmman da yasan bak'ar wahala da tasha hannu kakarta da Baffanta.
Cikin karaya zuciya ya kalle Hakeem ya ce.
"Hakeem inasonta wallahi-azim Ina matuk'ar k'aunarta ina mata irin muguwar soyayya da fatar baki ba za ta iya faɗa ba. Ita ɗin ta kasance wani 6angare na jikina. Sai dai ba zan iya jure ganinta cikin damuwa ba balle har nayi sakaci da hawan jini zai kamata ba. Hakeem muddin na gano aurena shine matsalarta tabbas zan saukewa mata.
"Dan Allah Aj ka daina zance rabuwa tsakaninku babu rabuwa, ka d'aure ka sauke duk wani ji-ji da kai ka nemi soyayyarta wallahi za ta so ka watakila fiyye ma da yadda kake sonta.
"Da wuya ta soni koda rabin son da nake mata ne Hakeem. Ina gayamaka abokina sosai nayi zurfi a son kwailata.
Ya k'arasa magana da wani shegen blushing, Hakeem kan dariya ya yi tare da bugun shoulder ɗin Azaad yana faɗin.
"Keep fighting abokina in-sha-Allah nan da d'an lokaci zan d'auki second Azaad Junaid da hannuwa nan nawa"
"Allah ya kawo wannan ranar na rantse da Allah sai nai maka kyautar da za ta girgiza ka.
Azaad ya faɗa yana kallon Hakeem yana murmushi. Ihu Hakeem ya saki har da mik'ewa yana taka rawa, Azaad ya zabura da sauri ya rik'o shi yasa hannunshi ya rufe mishi baki.
"Kai fa ba kada hankali tana bathroom za ta iya jiyo ihunka dan Allah tafi kawai saboda kutse da kayi mana yasa ta ji kunya shiyasa ta mak'ale a bathroom, da zarar ka tafi zan fito da kayana.
Zaro idanu Hakeem ya yi sosai ya kadu da jin furuncin Azaad, kafin ya gama mamaki Azaad ya tura shi waje ya rufu kofa har da su murza key. Yana murmushi ya nufi k'ofar bathroom wani nishadi yake ji tamkar Miyya ce ya faɗawa sirri dake zuciyarshi. A hankali ya tura k'ofar ta buɗe ya shiga tare da sake rufe ta, Miyya da ke zaune akan tiles ta sunne kanta tsakanin gwiwoyinta biyu, ta ɗago a razane gani shine tasaki ajiyar zuciya kallo d'aya tai mishi ta kauda fuska cike da k'asaita ya iso gabanta yana kallon gefen fuskarta ya tsuguna tare da sa hannunshi ya rik'o ha6arta ya juyo da fuskarta ta su na haɗa ido ya saki mata k'ayatattace murmushi irin mai kashe sassan jiki. Ai kuwa ya yi nasarar tayar mata da tsigar jiki ta ji yarrrr....ta lumshe idanuwanta da sauri-sauri take sauke numfashi.
Gani yadda take fusgar numfashinta yasa shi rudewa cikin kidimewa ya ce.
"Ya aka yi ne pretty ina ke miki ciwo?"
Kusan a tare ya haɗa mata tambayoyi biyu a lokaci d'aya, ta sadda kanta k'asa cikin k'aramin sauti ta furta.
"Daddy kaina kawai ke ciwo shima ba sosai ba za mu ma iya tafiya gida"
Ajiyar zuciya ya yi tare da hamdallah wato ta ma gano asibiti suke tsabar yarinta ce yasa ta ce za ta bashi gado ya kwanta. "Uhm...kuruci dangin hauka"
Ya faɗa cikin zuciyarshi a bayyane kuma sai ya mik'a mata hannuwanshi ta ɗago a hankali ta kalli santa-santala hannuwan nashi masu d'auke da dogaye yatsu farare tass...a kunyace ta saka tafin hannuwanta cikin nashi wani irin taushi ta ji ya ratsata tamkar ta damk'i auduga, ya mik'e tare da ɗagota ta tashi tsaye ya sakala hannunshi na hagu a waist ɗinta, ya rungumeta a tsagin jikinsa tsintar kanta tayi da kwantar da kanta a dantse hannunshi saboda yafi ta tsayi shiyasa kanta ba zai kai ga shoulder ɗin shi ba.
Da suka iso wajen gado ya d'auke ta cakk...kamar ya d'auki Ahlam ya zaunar da ita ya nemi daff da waist ɗinta ya zauna cike da zallar kulawa ya rik'o hannunta ya dank'e cikin nashi.
"Pretty faɗa min gaskiya karki 6oye min meke damunki?"
"Babu komai Daddy na faɗa maka ciwon kaine kuma yanzu ba sosai yake min ciwo ba"
"Ba wannan nakeso ji ba pretty asalin abin da ke haifar miki da matsananci tunani, doc yace idan har ba ki rage damuwa ba za ki iya kamuwa da ciwon hawan jini. Ni kuma ba zan so hakan ta faru ba. Shiyasa nakeso ki faɗa min gaskiya idan har bakyaso aure nan zan saukewa miki.
Cikin tsananin firgita Miyya ta ɗago ta k'ura mishi idanuwanta, wanda har sun fara cikowa da hawaye sosai kalmar rabuwa ta dagi zuciyarta tamkar an halba mata kibiya ko mashi. Tana kifta idanuwanta sai ga hawaye sharrr...akan tattausan kumatunta biyu. Wani irin zafi Azaad ya ji a kahon zuciyarsa tamkar an watsa mishi tafasashe ruwan zafi. Yanzu ya tabbatar ashe ba hasashen banza ya yi ba. Da gaske ne shine silar damuwarta shikenan alk'awali da ya yi ba zai k'arya shi ba zai saukewa mata, dama can ba kalar aurenshi bace k'addara ce ta haɗa su haka zalika k'addara ce za ta zama silar rabuwarsu. Ya mik'e zubur jikinshi yana wani irin kerma da za ka tambaye shi da zai ce wannan ita ce rana da tafi kowace rana kunce a gareshi. Batare da kalleta ba ya ce.
"Zan tafi gida ki kwanta ki huta akwai nurses za ku kula da ke.
Daga haka ya juya cikin tafiyar sauri ya fice ta bi shi da kallo yayin da k'irjinta yake bugawa da k'arfi, ta kife kanta a pillow ta shiga rera kuka duk duniya idan akwai abin da zai rabata da farin ciki bai wuce kalmar rabuwa da Daddynta ba. Ita kanta a yanzu ta amince da shine cikon farin cikinta bugun zuciyarta rashinsa tamkar rusa duniyarta ne.
Madam Salima zaune a dining room ta ca6a ado na ban mamaki wanda ada bata yi kwata-kwacinsa ta zauna gida sai in za ta fita officer ko kuma in an gayyace ta dinner party. Yanzu ɗin ma tayi ne a bisa ga shawarar Hafsat Shinkafi ta yadda za ta karkato da hankali Azaad.
Lokaci zuwa lokaci take kallon wall clock da ke manne ga bangon dining room ɗin, can kuma ta ja tsaki ta rasa wacce duniya Azaad ya lula da sassafe muryar Nanny Lacey ta ji tana mishi sannu da zuwa da mugun sauri ta mik'e gari sauri taci d'an uban tuntu6e da ta faɗi, jikinta har rawa yake yi ta fito daga dining. Koda ta k'arasa fitowa har ya fara haura matattak'alar bene, ta bishi da sauri tana kiran sunanshi wanda sai in tana cikin nishadi take kiranshi dashi.
"Dattinaa!
Sometimes Jadda ke kiranshi da suna tun shine yaro Jadda ke kiranshi da Dattijo a dalilin sunan mahifinta ne dashi, sai ta gajarta suna take cewa Datti ko Dattinaa. Dai-dai yana haura last stairs ya ji ta kira shi ya tsaya cakk....tare da juyawa Azaad yana masifar son suna dalili Jaddarshi ce ta rad'a mishi yana kuma girmama hakan. Shiyasa a duk lokaci da Salima ta kira shi da suna ya kan tsinci kanshi cikin nishadi da walwala.
Yana nan tsaye har ta k'araso cikin izza ta ce.
"Dattinaa Ina ka je da sassafe Nanny ta faɗa min ko breakfast ba ka yi ba ka fita hope everything is alright?"
Kallon uku saura kwa6o ya yi mata da ada ne kwalliyarta ba k'aramin tafiyar da ruhinshi za ta yi ba, amma a yanzu da ya dube ta sai ya ga ta dawo mishi kamar fatalwa ko Kaɗan bata burge shi ba. Sai yake gani kamar a shekarunta ta wuce wannan kwalliyarta. California gown ce a jikinta brown colour tasaki gashin kanta, tasha red ɗin jan baki a takaice dai tayi simple makeup a zahiri tayi matuk'ar kyau a wurin Azaad ne abin yasha ban-ban.
"Mtss....ya ja siriri tsaki ya juya tare da buɗe k'ofar falonshi duk da haka ta danne zuciyarta ta bi shi a baya kusan a tare suka shiga master bedroom ɗinshi. Yana sane da tana bin shi amma ko ya nuna hakan.
"Dattinaa ba ka ce nayi kyau ba saboda kai nayi wannan Make up ɗin?"
Ya waiga ya kalleta up and down kafin ya ta6e baki a lalace ya ce.
"Tsakani da Allah Salima kin tsofa ya kamata ki daina abin k'anana yara irin wannan kwalliya bata dace da ke ba. Ki bar wa yara sabon jini su ne za su yi su burgeni amma kan kamar kurar wasa musanmman wannan eyes shadow da kika sa zallar k'yak'yami zuciyarta har tafara tashi fita Dan Allah kada nayi amai.
Ya k'arashe magana yana ya mutsar fuska kamar da gaske aman zai yi. Madam Salima tai mutuwar tsaye wannan shine karo na farko a tarihin rayuwarta da aka ta6a ci mata zarafi Kuma mutumin da take kira da shine jigon rayuwarta. Wani irin k'atoto k'ololo bak'in ciki ya taso ya tokare mata gadon zuciya, bata San lokaci da ta zube bisa tiles ta ratsa kuka mai k'arfin gaske.....
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Top Ten Takun Haske Batch:A
*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004
28....
Sosai Miyya tasha kuka kamar ba gobe da ta gaji da rera kuka ta rarrsshe kanta. Daga bisani tayi barci.
Hasheem ya dubi Ahmadu da fusatattun idanunshi, yana huci kamar bak'in kumurci.
"Na ratse da wanda rayuwata take hannunshi ba zan bar Azaad ba har sai naga bayanshi duk shu'umancinsa kuwa. mu zuba ni dashi shege kafasa.
"Hasheem ka hak'ura da wannan burin naka ka ji da hali da ka tsinci kanka mana. Ubangiji yana sonka da rahama shiyasa yabarka da numfashinka kayi amfani da raguwar lokaci da yai saura gareka wajen rokar gafarar ubangiji da Azaad wallahi kada ka bari shaidan ya ci gaba da buga maka gangarsa zai kai ka ne ya baro. Duk da muna da mugun son zuciya amma ba za mu so mu yi mutuwar kask'anci ba.
Hajiya Kubra ta faɗa tare da daukar jakkarta dama ta zo duba Hasheem ne ta tararda shi da Ahmadu suna sake shirya sabon shirinsu na gani bayan Azaad Junaid.
"Ni dai na hak'ura kamar yadda Alhaji Abdallah ya cire kanshi a cikin wannan tafiya ni ma ba dani ba na fita, kuma Ina mai ba ku shawara da ku dangana......
"Ya isa kubra ga k'ofa fita ki ba mu wuri muddin Ina raye da ikon Allah sai na cimma mummunan manufata akan Azaad koda ni Kaɗai nai saura a wannan tafiyar"
Hasheem ya k'arasa magana yana nuna mata k'ofar fita da yatsanshi, Hajiya Kubra ta kad'a kai batare da ta sake magana ba ta fice abinta. Ahmadu yana so ya hak'ura saidai mugun kwadayinsa ba zai bari ba domin yana tsoron kada Hasheem ya yi nasarar kashe Azaad shi Kaɗai. Da zarar sun kauda shi mallakar dukiyarshi ba zai musu wahala ba, idan ya hak'ura Hasheem ya yi nasara shi Kaɗai zai mallake dukiyar shiyasa tunaninsa ya rabu gida biyu. Sabon shiri suka shirya sosai wanda suke gani koda bala'i sai sun cimma manufarsu.
**** *** ******
Cike da takaici Azaad yake kallon Salima sosai takaicinta ya kamashi musanmman yadda ta yage baki tana 6arka kuka kamar wata k'aramar yarinya.
"Mtsss....!
Ya buga mugun tsaki ya shige bathroom abinsa har ya fito daga wanka tana rera kuka fiyye da yadda ya barta, ko Kaɗan bata bashi tausayi ba saima ji haushinta kamar ya rufe ta da duka in yaso tayi kuka da dalili. Ta ɗago idanuwanta da suka yi jajir mascara da kwali haɗi da eyes shadow da tasa suka ca6e wuri d'aya, sai ta dawo tamkar wacce tai kwalliyar wasan tashe. Tayi tozali da Azaad d'aure da blue towel iya waist ɗinshi cikinshi a shafe ga six packs a jere kwanin sha'awa. Ta bi gaba ɗaya jikinshi da kallo ta ja dogon numfashi sakamakon wata masiffafiyar sha'awarshi ta taso mata ya biyo ta gefenta yasa k'afarshi ta dama ya shure kafafuwanta cike da wulak'anci ya ce.
"Ke dallah.....jaye min kafafuwanki na wuce kin saki kafafu tula-tula kamar doya, ni ban masan haka kafafuwanki suke ba abu ba ko kyau gani"
Ya k'arashe magana yana tafiyar tak'ama yana hura hanci, ya nufi gaban mirror ya shiga shafe lallausar fatar jikinsa da lotion mai sanyi k'amshi. Madam Salima ta yunk'ura ta tashi da kyar saboda kasala da tsananin sha'awa da suka taso ta gaba. Azaad ya ajiye robar lotion yasake ra6awa gefenta ya wuce ko kallonta bai yi ba.
Ya nufi dressing room yana cikin buɗe closet hankalinsa ya raja'a da kallon kayan da zai saka, sam bai ji shigowarta ba sai kawai ya ji ta rungumeshi ta baya, da dukkan k'arfinta ta zagaye cikinshi da hannuwanta tana gunji kuka cikin muryar kuka take faɗin.
"I'm sorry Azaad please forgive me It’s never been easy for me to say “I’m sorry,�? but I’m saying that now. Please give me another chance...
Tana magana tana kuka tare da goga fuskarta a gadon bayanshi, yadda take mishi saura Kaɗan towel ɗin jikinsa ya zame saida ya gyara zaman towel ɗin kana ya daddage iya k'arfinshi da Allah ya albarkace shi dashi ya tureta ta goshinta ya buge bango kana ta faɗi k'asa, cikin gaggawa ya shirya cikin shadda getzner sky blue d'inki babbar riga yasa hula zanna bukar da ta dace da shaddar, faɗuwar da tayi ba k'aramin ciwo ta ji a goshinta ba. Amma ko ya bi ta kanta ya fice abinsa duk da haka ta sake tashi ta biyo shi a baya tana mai ci gaba da bashi hak'uri.
"Azaad!... Azaad Dan Allah ka yi hak'uri ka yafe min Azaad Please give me a chance to prove that I can change. I’m sorry, and I’ll take my punishment. Amma ka tsaya mu fahimce juna..
Ko waigawa bai yi ba. Balle tasa ran zai amsa kafin ta k'arasa saukowa har ya fice sani tayi idan ta bishi zai ci gaba da disga ta ne a gaban housemaids ita Kuma ba za ta yi sake da daraja da k'imarta su ragu ba. Sai kawai ta wuce 6angarenta ta ɗora Abaya akan tufafin jikinta, ta zari handbag ta fice kaitsaye gidan Hafsat Shinkafi direbanta Mr Michael ya sauke ta.
Azaad yana fitowa ya shiga 6angaren Jadda ya yi breakfast ya kuma umarce Mero mai aikinta ta zubawa Miyya. Sai lokaci ya faɗawa Jadda tana asibiti sosai Jadda ta tausaya mata har ta nuna za ta bishi asibiti ta dubata, ya k'i amincewa ya kuma kafa mata hujja yau ko gabo za a sallameta ba don ranta yaso ba, ta zauna tayi mata fatan samun sauk'i, Mero ta kai ma Mr Richard basket ɗin abinci yasa cikin mota. Dai-dai Mero tana kawowa k'ofar shiga, shi kuma yana fitowa ta janye ta bashi hanya ya wuce.
Koda suka isa asibiti sha biyu ta gota yana gaba Mr Richard yana biye dashi rik'e da food basket suna zuwa k'ofa Azaad ya tsayar dashi ya kar6i basket ɗin. Mr Richard ya koma gun mota, sannu a hankali ya tura k'ofa ta buɗe cikin k'aramin sauti duk da haka saida Miyya da ke kwance ta waigo da k'arfi karaff idanuwanta suka sark'e cikin nashi ya saki mata k'ayatatcen murmushi irin mai shiga jiki ya yi wa jini da bargo babbar illa, saboda tuni ya yi awon gaba da ruhi haɗi da gangar jikinta. Ta rausayar da kanta yayin da zuciyarta ke ta faman bugawa da k'arfin gaske. Cikin mutuwar jiki ta tashi zaune.
Ya k'araso tare da ajiye basket ɗin cike da kulawa mai d'auke da zallar wutar so da k'auna ya ce.
"Prettyn Daddy ya jikin naki hope ba inda yake miki ciwo?"
Sabon suna da ya kira ta dashi ba k'aramin farin ciki ya haifar mata ba. Tsabar dad'in da ta ji yasa tasaki murmushi mai sauti, ta tsare shi da idanuwanta da ke masifar burgeshi.
"Ni fa Daddy sumul nake. Yadda nake ji ma tamkar ban ta6a wani ciwo ba ko kaina dake ciwo yanzu ya daina gida kawai nakeso zuwa banaso Aneesah da Airah su dawo daga school ba su ganni ba za su tashin hankalinsu. Ga kuma baby Ahlam idan bata gani ba za ta iya kuka"
Yadda takevmagana cikin shagwa6a6iyar murya ya k'ara rura mishi wutar sonta, wani maganadisu ke yawo a jinin jikinshi tamkar electric shock, lumshe idanuwanshi ya yi kafin ya ware su tass...akan kyakkyawar fuskarta kana ya tattara babbar rigarshi yanda ba za tayi squeezing ba, ya zauna daff da waist ɗinta ya Kamo hannunta ya haɗe da nashi yasa ɗayan yana tatta6a gefen-gefen wuyanta ya ji ko da raguwar zafi, yadda yake shafa wuyanta yasa tsigar jikinta tashi yarrrr.....ya ji ko Kaɗan babu zafi kana janye hannun nashi daga wuyanta.
"Gaskiya kin ji sauk'i sosai babu zafi a jikinki amma sai in doc ne da kanshi ya yi discharge ɗinki sannan ne zan amince da tafiya gida.
Yayi magana yana massage ɗin tafin hannunta, hakan ba k'aramin k'ara mata mutuwar jiki ya yi ba, ta langwa6e Kai ta ce.
"Allah Daddy ni gida nakeso zuwa kaga ko d'azu da uncle Hakeem ya zo duba ni na tabbata sai ya faɗawa Amrah da Amal muddin suka zo suka sami ni anan hankalinsu zai tashi ba Kuma zan so haka ba. A wannan rayuwar su Kaɗai nake da su ɗin ma ni