Showing 66001 words to 69000 words out of 91651 words
farfasa abubuwa masu matuk'ar daraja da tsada. Ran Hafsat ya 6aci sosai saboda a ganinta ko Aneesah da take 'yar Salima ba za ta yi wannan haukar ba balle madam Salima da ta gama mallakar hankalin kanta. Wannan ai abin kunya ne da zubar da daraja da k'ima. Da kyar ta iya kamata suka shiga da ita d'akinta, ta zaunar da ita a gefen gado sai faman sauke wahallale numfashi take yi, Hafsat ta kai dubanta wurin Aneesah da ke tsaye a jikinta k'ofa tana faman goge hawaye da bayan hannunta, sosai tausayin yarinyar ya kamata cikin taushi murya ta ce.
"Aneesah ba mu wuri zan yi magana da Mommynki.
Ta juya batare da tayi magana ba.
*** ** *****
Shiru ya yi tare da lumsashe idanuwanshi, yana sauke mata numfashinsa mai d'an zafi-zafi a gefen wuyanta, jin shiru nashi yana neman ya yi yawa yasa ta shafo kwatatcen sajenshi cikin siriryar murya mai taushin gaske ta kira sunanshi.
"Daddy!"
"Uhm!
Ya amsa mata batare da ya bud'e idanuwanshi ba.
"Dan Allah ka yi hak'uri ka yafewa mommy nasani ita d'in mai girman laifi ce agareka, amma duk da haka ba zan kasa furta maka kayi hak'uri ka dawo da aurenku.....
"Ya isa pretty!
Ya katse ta cikin kakkausar murya alamar da ke nuna maganarta ta fara 6ata mishi rai, duk magana da za a yi da ta shafi Salima komai k'ank'antar harzuk'a shi take yi, ranshi a 6ace ya cireta daga jikinshi kana ya mik'e tsaye fuskarshi a had'e babu annuri ko kad'an ya sauke mata fusatattun idanuwanshi, ai kuwa ba k'aramin kad'awa hanjin cikinta ya yi ba.
"Pretty ba ki san wacece Salima bane shiyasa kike k'ok'arin dawo da ita cikin rayuwarmu. Salima mace ce mai mugun zafin kishi duk da batasan ta yadda ake kulawa da tattalin miji ba amma tana tsananin kishina ko kad'an bataso ta ga mace koda 'yar uwa ta jini ce ta ra6eni matuk'ar kika kafe sai na dawo da ita to ki sani ke ce za ki wahala domin ba za ta, ta6a barinki ki zauna gidanan lafiya ba. Aslamiyya ki rufe babin Salima kamar yadda na rufe hakan ne kadai rayuwarmu za ta inganta ni da ke.
Yana k'arashe magana ya shige bathroom ya barta tsaye, rungume da hannuwa a k'irji tana so Daddy bata tunani nan kusa da akwai abin da zai iya raba tsakaninsu, kana tana jin tausayin yaranshi har k'asan zuciyarta saboda tasan illa da ke tattare da rashin iyayye duk da tana da tabbaci, da wuya yaran Azaad su fuskanci irin rayuwar da tayi ita da siblings d'inta.
Za ta ci gaba da lurarda Daddy hadi da rarrashinshi har sai ya amince ya dawo da mommy ko don albarcin su Aneesah da take ji k'aunarsu sosai a cikin zuciyarta.
Saukar ruwa taji a fuskarta ta zabura a firgice Daddy ta gani tsaye a gabanta har ya yi wanka ya fito yana daure da brown towel, raguwar ruwan wanka da ke hannunshi ne ya yarfa mata a fuska. Shagwa6e fuska tayi tana turo baki hannunshi yasa kama hannunta ya ja ta zuwa ga dressing mirror ya mik'a mata k'aramin towel din da ke hannunshi.
"Da wannan tunani da kike da ma taimakawa mijinki kika yi ya shirya, kin tsaya kina tunani abin da bai shafe ki ba.
"Haka ma za ka ce Daddy yanzu abin da ya shafe ka bai shafe ni ba ko?"
Ta k'arasa magana tare da kar6a towel din ya ja stool ya zauna ta cikin mirror yake kallon kyakkyawar fuskarta, saida ya saki mata murmushi kafin ya ce.
"Ina sonki prettyn Daddy ke ce cikon farin cikina idan babu ke bansan ya rayuwata za ta kasance ba.
Ta k'ara matsawa ta tsaya bayanshi tare da dora towel din hannunta a shoulder shi, tana murmushi har farare hak'oranta suka baiyana.
"Daddy sarkin wayau wato so kake yi ka shashantar da tambayar da nai maka, ta hanyar bani wannan amsar ko?"
"A'a kawai dai inaso ki kore duk wani abu da zai yi yunk'uri kawo mana cikass a yayin zamanmu, musanmman akan abin da ya shafi Salima.
Shiru tayi tana kallonshi ta cikin mirror kafin ta girgiza kai ta shiga goge mishi jikinshi, ta ajiye towel din ta dauki robar lotion ta matsa a tafin hannunta, sannu a hankalin ta ke bin sassan jikinshi tana shafawa yayin da gogan naku ya lumshe idanuwa yana sauke numfashi akai-akai. Tuni ta fahimci yana yinsa yana sauyawa a duk lokaci da tafin hannunta ya sauka a fatar jikinshi, k'afadarshi ta d'an buga tana dariya ta ce.
"Kai Daddy daga shafa mai ka fara gyagyadi a zaune idan barci ka ke ji ka tashi ka je ka kwanta mana, ni kan kar ka yi min barci anan.
Murmushi ya yi tare da kar6a robar lotion ya ajiye ya jawo ta ta zauna akan cinyoyinshi, ya rungumeta gam har saida tayi 'yar k'ara. Cikin shagwa66iyar murya ta ce.
"Daddy wannan rungumar fa kada ka fasa min ciki mana?"
Kuncinta ya sumbata tare da kashe mata idonshi d'aya.
"Ba zan fasa ba my pretty ni da nakeso nan da nine months ki haifa min kyakkyawar baby girl mai kama da ke.
"Cab....gaskiya haihuwa ba yanzu ba Daddy sai na k'ara girma.
Tayi magana tana murguda baki, hakan da tayi tai masifar bashi dariya sosai ya ci dariya kafin ya mik'e dauke da ita ya nufi dressing room.
"Mu je ki saka min tufafina ta hakan ne girmanki zai k'aru, ki haifawa baby Ahlam k'anwa da wuri.
"Daddy please ka sauke ni sai faman koya min rashin kunya kala-kala kake yi, na fahimci idan ban yi da gaske ba zan nemi kunyata na rasa.
Kowane furuci da ke fitowa daga bakinta nishadi yake haifar mishi, shiyasa yake ta faman kwasar dariya duk yadda take mishi magiya ya sauke ta yak'i sai da ya shigar da ita dressing room d'inshi ya direta ya yi kamar zai cire towel din jikinshi, da sauri ta runtse idanuwanta.
Yana dariya ya matsa daff da ita ya kai bakinshi akan karan hancinta yasa hak'oranshi ya cije ta kad'an, babu shiri ta bude idanuwanta tana ihu tare da yarfe hannuwa ita a dole ta ji zafin cizon.
Shi kuma sai faman yi mata dariya yake yi ya nufi katuwar closet ta gilashi wacce ta cinye daga farkon bango d'akin zuwa karshensa cike tafff da tarin suturunsa kala daban-dabam gasu nan birjik ya zuge gefen da jallabiya's d'inshi suke ya ciro coffee colour ya saka, har ya kammala shiryawa Miyya tana tsalle-tsallenta dafe da hanci hannunta ya cire daga kan hancinta nata, ya kalli dai-dai gun da ya ciza ya ga shatin hak'oranshi a hankalin ya matsota jikinshi ya dora harshensa gun da shatin hak'oran nashi yake sannu a hankalin ya shiga yawo da harshensa a wurin kafin ya gangaro zuwa ga bakinta, bata yi gardama ta bude mishi bakinta ya zura harshensa idanuwanta suna rufe ruff ta shiga taya shi wannan shine karo na farko da ta mayar mishi da martani sosai hakan ya k'ayatar dashi, wata irin natsuwa suka ji tana saukar musu a cikin sassan jikinsu gaba d'aya ji suke yi kamar suna wata duniya ta daban ne ba wacce tun farko suke ciki ba.
Sun d'auki tsayin mintuna ahaka suna tsotsar bakin juna kafin Miyya ta d'an ture shi, kasancewar jikinshi ya mutu bashida wani k'arfi kirki ya yi baya kamar zai fad'i Allah ya taimake shi ya dafa bango, cikin zallar shauk'in so take kallonshi tana dariya, kafin ta shiga tafiya da baya-baya sai da takai ga k'ofar fita ta tsaya ta ce.
"Daddy ka ji tsoron Allah ka dinga sassautawa 'yar marainiya Allah kada soyayyarka ta lalatani gaba d'aya.
Tana k'arasa magana ta kwasa da gudu ta fice daga d'akin, a hankali ya k'arasa sulalewa k'asa ya zauna bai ta6a tsanmani zai ji irin manya-manyan maganganu iri wad'annan daga bakinta ba. Shi fa gaba d'aya kallon kwaila wacce bata da wayau yake mata ashe ta girmewa tunaninshi ya shiga shafa sumar kanshi yana fad'in.
"Alhamdullilah....ya Allah da ka albarkace ni da wannan babbar ni'ima, Allah nagode maka da wannan sauyi da ka yi min ya ubangiji ka bani ikon rike wannan yarinya bisa ga gaskiya da amana Allah ka kare min ita bisa ga kariyarka.
Koda Miyya ta dawo parlor bata tarar da Airah ba, kaitsaye d'akin da taga Nanny Lacey ta shigar musu da kayansu ta nufa.
*** **** ***
"Innalillahi wa'inna illaihim raji'um!....shikenan Salima kin 6ata komai garin haukar kishinki na wofi kin k'arasa lalata alak'arki da Azaad.
Hafsat tai magana cike da haushi da zallar takaici ji take tamkar ta rufe madam Salima da d'an banzan duka, ga mace har mace amma kwakwalwarta kamar ta dusa. Ta rasa wacce irin kwwaya ce a cikin kokon kanta, bata iya dai-daita komai ya koma a gun muhallinsa ba kawai dai ta kware ne wurin 6atawa ba gyarwa ba.
"Wallahi-azim Hafsat ba zan ta6a bari Azaad ya rayu da wata mace ba, ko ta halin yaya sai na raba tsakaninsu....
"Dallah ya isa Salima! Nace ya isa haka ke yanzu fissibilillah....ba ki ji kunyar fitar wannan maganar daga bakinki ba?"
"Kunya fa kika ce Hafsat wacce kunya zan ji?"
"Kunyar abin da kika aikata kunyar nunawa da kike yi a yanzu kin damu da Azaad har kina nuna kishinsa a fili alhali kece kika jawo ya tsinka igiyoyin aurenku ya kuma maye gurbinki da wata.
"Ki sa aranki Hafsat idan har akan Azaad ne banida kunya ko kad'an ba ma za kisan hakan ba sai kin ga irin abubuwan da zan aikata nan ba da dad'ewa ba sannan ne za ki tabbatar da rashin kunyata.
"Salima.... Salima please calm down nuna fushi a fili ko k'udurta mugun nufi ba naki bane,ki kore duk wani mugun zafin kishinki ki jinginar dashi gefe mu bi hanyar maslaha ko Allah zai sa Azaad ya ba ki dama ta biyu. Shi fa namiji da kike gani kulawa da soyayya hadi da tattali yake bukata a wurin mace matuk'ar ya sami wannan sauna yake komawa a gunta, da alama abin da kika kasa bashi na tsawon shekaru ya samu a wajen k'aramar yarinyar da kika gama renawa. Kuma da kike zance za ki raba tsakaninsu ta ina za ki fara?"
Ai Salima kin riga da kin 6ata rawarki da tsalle, tun da har kika ga Azaad ya tattara yaranshi kafff ya bar miki gida hakan yana nufi ya gama dake babu saura wani abu da yai saura a tsakaninku.
"Wayyo Allahna!
Madam Salima ta fad'a da k'arfi tare da fashewa da wani irin kuka, Hafsat bata hana ta kuka ba ko tayi yunk'uri rarrashinta kyaleta tayi taci kuka mai yawan gaske kafin ta dawo ta rarrashinta kanta, ashe ko kuka rahama ne saboda Salima ta ji bakin cikinta ya raguwa da kashe uku cikin d'ari ta tashi ta shiga bathroom ta watsa ruwa masu sanyi ko za ta ji sanyi a zuciyarta, ta dai ji sanyi a fatar jikinta amma zuciyarta ko kad'an bata sanyayya ba. Ta nemi riga mai karanci nauyi tasa, ta dawo kusa da Hafsat shinkafi ta zauna tare da zabga dank'areren tagumi ta zurawa Hafsat kumburarrin idanuwanta.
Saida Hafsat ta gyara zamanta kafin tayi k'asa da muryarta ta fara magana.
"Salima a yanzu dama d'aya ta rage miki wacce nake tunani da ita kadai za ki yi amfani, watakila Azaad ya saurare ki idan Allah yasa aka dace sai ki ga ta cikin ruwan sanyi ya gyara aurenku.
"Please Hafsat in za ki yi magana go straight to the point, zuciyata bata daukar noke-noke duk abin da za a yi na fiso ayi shi kaitsaye.
"Aneesah ita ce damarki ta k'arshe da ta rage miki saboda haka ta cikin hikima da dabara za mu yi amfani da ita Azaad ya dawo da aurenku.
*** ** ****
Ahamdu ya dawo tamkar mahaukaci ba shi da aiki sai surutu yana tonawa kansu asiri, iri mugaye abubuwa da suka dinga yi wa Azaad, Hasheem kuma k'afarshi tak'i warkewa kullum ba a gani sauki sai ca6ewa take yi tana fidda ruwa masu mugun doyi, dama in za ka gina ramin mugunta ki gina shi gajere ba ka sani ba watakila kaine za ka rufta a ciki. Allah ya kare mu da son zuciya yasa mu fi k'arfin zukatan mu.{Amin}
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_
Na
Jeeddah Aliyu
Top Ten Takun Haske Batch:A
*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004
35...
Hafsat shinkafi bata tafi ba sai da taga ta dora Madam Salima a hanyar da take gani za ta dai-daita mata al-amurrata, duk da tasan da matuk'ar wahala Salima ta bi shawarwari da ta bata tai aiki dasu d'aya bayan d'aya.
Tun daga lokaci da Aneesah ta shige d'akinta take kuka, zuciyarta ta kasa kar6a sabbabin k'addarori da suka kunnuwa rayuwar gidansu. Duk sanda ta tuna da yanzu fa iyayyenta sun rabu, sai ta ji wani irin kunci da 6acin rai babban takaicinta bai wuce auren Pretty da Daddy ya yi ba, da ta kasa jurewa fitowa tayi fuskarta tayi mata jajir saboda d'an uban kukan da taci. Kaitsaye 6angare Jadda ta nufa tana zuwa ta zube a jikinta tasa kuka, gaba d'aya ta tashin hankalin Jadda sai faman tambayarta take me yafaru, cikin shasshekar kuka take fad'i dalilin kukan nata shiru Jadda tayi tamkar batasan da labarin ba, daga bisani ta shiga yi mata nasiha cikin hikima irin ta tsofaffi ta dinga kawo mata misalai da ke haddasa mutuwar aure ta kuma kawo mata dalili kwarara da ke nuni da babu illa don Daddynsu ya auri sa'arta. Kasancewar Aneesah yarinya ce mai kaifin tunani tayi na'am da duk abin da Jadda ta fad'a mata, duk wani haushin Daddy da pretty da take ji sai ta ji ya ragu.
Azaad ya fito cikin shirin shi na fita a downstairs parlour ya tararda miyya da yaranshi, wani irin farin ciki ya ji ya kama shi, zuciyarsa tayi wasai a yanzu bai da saura damuwa fuskarshi ta cika da k'ayatattcen murmushi k'amshin turarenshi da Miyya ta shak'a yasa tai saurin kallon bene ta ganshi tsaye ya yi folding hannuwanshi a k'irji yana ta faman zabga murmushi, batasan lokaci da ta mayar mishi da martani murmushin nashi ba, ta bi shaddar jikinshi da kallo ya yi matuk'ar yi mata kyau, a kullum k'ara gani take yi yana zama yaro. Mik'ewa tayi dauke da Ahlam ya k'araso kusa da ita ya kar6i Ahlam yana mata wasa kafin ya dawo da ganinshi akan fuskarta.
"Zan fita!
Ya furta cikin k'aramin sauti.
"Allah ya tsare ya dawo mana da kai lafiya"
"Amin! Mu je ki raka ni koda a bakin k'ofa ne.
Murmushi tayi tare da bin bayanshi.
Airah ta d'ago daga game din da take yi a wayar Nanny Lacey, ta kalle shi tana murmushi tare da furta.
"Daddy Allah ya Tsare ya kai ka lafiya"
"Amin Mamana.
Suna zuwa k'ofar fita, ya tsaya ya tsareta da rikitattun idanuwanshi masu rikita mata kwakwalwa, yadda yake kallonta ya haddasawa tsigar jikinta tashi ta lumshe idanuwanta kana ta ware su tana kallonshi k'asa-k'asa tana murmushi.
"My pretty ba za a bani good-bye kiss bane?"
"Uhm....ni dai babu ruwana Daddy idan Airah ta ganka gara tun wuri ka kama gabanka, ka tafi gudun kada kayi abin kunya a gaban yara.
Tana rufe bakinta taji saukar bakinshi cikin nata, yana zare bakinshi ya mik'a mata Ahlam ya k'arasa bud'e k'ofa ya fita ta bishi da kallo tana murmushi.
Aneesah tana baro 6angare Jadda ta nufi d'akin mommy tana so ta duba ta, sannan ta k'ara kwantar mata da hankali tana shiri bud'e k'ofa ta ji sautin muryar Madam Salima tana waya, gudun kada ta katse ta sai kawai ta juya ta koma d'akinta ta nemi gefen gado ta zauna talla6e da kumatu sai tunanin mommy take yi, ta rasa wacce irin zuciya ce a k'irjinta ko sai yaushe za ta natsu ta soma gyara kurakuranta?"
Kiran sallar magarib ya tashi Aneesah daga tunani da ke yi, ta shiga bathroom tayo alwala da ta gama sallah tsawon lokaci ta dauka tana yi ma iyayyenta addu'a idan da akwai alkhairi a zamansu Allah ya dai-daita tsakaninsu.
Azaad yana fita kaitsaye farmhouse d'inshi ya nufa, tun kafin Mr Richard ya yi parking ya hango Hakeem tsaye ya jingina jikinshi a motarshi, tun kafin ya k'arasa wajenshi ya ga yana mishi dariya nan tashi ta shak'iyanci. Hannu Azaad ya mik'a masa suka yi musabaha kafin ya ce.
"Naga tun kafin na k'araso kana min dariya, me hakan ke nufi?"
"Ina dariya ne saboda naga kusan three days kenan ba ka zo office ba, ko d'azu da ka kirani ka ce mu hadu a gidan gonarka nayi mamaki saboda na dauka sai ka gama cin amarci kai da kwalarka kafin na iya ganinka.
Ta k'asan ido Azaad yake kallonshi yana tsotsar lower lips d'inshi, kafin yai murmushi tare da fad'in.
"Allah ya shirye ka Hakeem kadai ba ka rabu da iskaci, Aslamiyya fa 'yarka ce ni kuma sirikanka amma ka zauna kana sa mana ido.
Sosai Hakeem yasa dariya yana nuna k'irjinshi da yatsa.
"Lallai yau za a yi ruwan sama har da k'ank'ara Aj da bakinka ka amsa cewa ni sirikanka ne?"
"Kwarai kuwa saboda dadin da naji na aura min 'yarka da kayi yasa na nemi da mu hadu anan firstly nai maka godiya secondly inaso ka rakani gidan Baffanta inaso zan yi magana dashi akan mahaifiyarta.
Tsagaitawa da dariya Hakeem ya yi kafin ya ce.
"Babu godiya a tsakaninmu Aj ka manta ne we're brothers, duk abin da nai maka tamkar kaina nayi wa, saboda haka babu kalmar godiya a tsakaninmu.
Sai kuma batun zuwa gidan Baffa sani ko yanzu idan a shirye ka ke za mu iya tafiya.
Murmushi Azaad ya yi cike da farin ciki ya rungume Hakeem, kafin ya sake shi suka jera zuwa wajen mota inda Mr Richard ya fito da sauri ya bud'e musu k'ofa anan farmhouse Hakeem ya bar motarshi, koda suka isa unguwarsu Baffa Sani ana kiran sallar magarib saboda haka suka nemi masallaci mafi kusa da gidan suka yi sallah.
Bayan fitar Azaad daga gida Miyya ta goye Ahlam ta nufi kitchen da kanta ta girkawa Daddy abincinsa, ko kad'an bata wasa da darussa da aunty Zaliha ta dorata akai musanmman da ta fad'a