Showing 54001 words to 57000 words out of 91651 words

Chapter 19 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

816

Kaɗai suka sani nice uwa nice uba a garesu haɗuwarmu da uncle Hakeem ya kar6e wannan matsayin duk da haka ina tattalin
farin cikinsu. Dai-dai da kwarar zara banaso su shiga damuwa.

Cikin kalamanta Kaɗai ya fahimce muhimmancin da 'yan uwanta suke da a wurinta, nan take ya k'udurta aranshi ba zai sake bari su yi maraci ba daga na uwa har na uba. Da kanshi ya yi feeding ɗinta sai ya tabbata ta k'oshi sannan ya kyaleta.

"Nagode Daddy Allah ya saka maka da gidan ajanna firdausi"

Ta faɗa cikin k'aramar muryarta mai dad'in saurare, cheeks ɗin ya kama da hannuwanshi biyu yana dariya.

"Amin thumma amin Prettyn Daddy amma karki sake yi min godiya duk abin da nayi miki kin can-canci fiyye da hakan a wurina"

Dariya tasa mai ban sha'awa kana ta ce.

"Kamar yadda na can-cance fiyye da hakan a wurinka nima kana da babbar daraja da k'ima a idanuwana ba kuma zan gaji da gode maka ba har izuwa k'arshen numfashina.

Furuncinta ba k'aramin jifa shi farin ciki ya yi ba shiyasa ya saki kumatunta ya rik'o hannunta, ya matse cikin nashi ya ce.

"Ki yi min alk'awali ba za ki sake shiga damuwa ba balle ta shafi lafiyarki. Ki d'aukar min alk'awali Pretty za ki faɗa min asalin abin da ke damunki, ni kuma zan yi iya bakin k'ok'arina na magance miki damuwarki. Idan matsalarki ta kud'i ce Pretty ina da kudin da ni kaina bansan adadinsu ba. Idan kuma ta wannan aurena ne da yake kanki shima zan iya hak'ura na saukewa miki duk da hakan zai iya rabani da farin ciki da na fara samu, ni dai burina ki kasance cikin farin ciki.

Ta sadda kanta k'asa tana wasa da zip ɗin cardigan ɗin jikinta, duk lokaci da Daddy ya yi anbaci kalma rabuwa sai ta tsinci kanta cikin mugun yanayi sai ta ji tamkar ta ɗora hannu aka ta kwatsama ihu ta tsani jin wannan kalma tana fitowa daga bakinshi.

"Pretty yi magana mana so nake naji musanbabin damuwarki?"

Ta ɗago cikin rauni da karaya zuciya sai ta buɗe bakinta tayi magana sai kuma ta datse bakin nata, ta rasa abin faɗa. Sai musu-musu take da baki ga wani irin gumi da ya karyo mata. Hakan da Azaad ya gani sai zargi batason aure shiyasa tak'i magana k'ara matse hannunta ya yi zuciyarsa na bugawa da k'arfi kamar za ta fasa k'irjinshi ta faɗo k'asa sakamakon nauyi da girman maganar da zai furta.

"Pretty ba ki so aure nan ko?"

Shiru tayi ta kasa furta uffan sai ci gaba da wasa takebda zip ɗin yayin da ɗayan hannunta ke cikin nashi, shiru-shiru ba ta yi magana ba. Batasan cewa shirun nata yana barazana ga lafiyar Azaad ba.

"Please talk to me mana banaso shiru nan naki saboda yana jefa ni cikin tunani kala daban-dabam.

Tai ajiyar zuciya tare da ɗagowa ta kalleshi kafin ta kauda fuskarta cikin tattausan lafazi ta ce.

"Daddy ni Musulma ce na yarda da k'addara mai kyau da marar kyau. Tun daga ranar da uncle Hakeem ya kawo ni gidanka nasa araina zan zauna da kai da zuciya d'aya duk da a lokaci basan waye kai ba. Amma nasa araina mutuwa ce Kaɗai za ta rabani da kai. A lokaci da na gama sani waye kai sai na fahimci kafi k'arfina nesa ba kusa ba. Ni ba ajin aurenka bace amma duk da hakan ban fidda rai wata rana nima zan sami gur6i a gidanka koda ban sami gur6i a matsayin matarka ba. To Al-hamdu-lillah ko yanzu burina ya cika saboda irin kulawar da ka bani a yau ɗinan Kaɗai ta haska min irin muhimmanci da nake dashi a wurinka.

Tun daga lokaci da ta fara magana idanuwanshi suke bisa lips ɗinta, yana mamakin yadda take jeru kalamai cikin tsaftace halshe tamkar wata mai manya shekaru, alhali bata wuce 16-17 years ba.
Kalamanta sun haifar mishi da farin ciki da ya jima bai ji kanshi a cikin irinsa ba. Batare da wani dogon tunani ba ya jawo ta cikin jikinshi ya rungumeta tsaf....yana shafa gadon bayanta yayin da fuskarshi ke bayyana irin farin ciki da yake ciki. Ya kai bakinshi daff da kunneta ya rad'a mata.

"Thank you so much my pretty you're truly a blessing in my life. Ke ta dabance pretty kin fi lu'u lu'u tsada da daraja a wurina girmanki da k'imarki sun dad'a hauhawa a zuciyarta, in-sha-Allah ba za ki yi danasani aurena ba"

A hankali ya janye jikinshi daga nata ya mik'e tsaye, yana kallonta tare da murmushi akan fuskarshi kafin ya kalli agogon hannunshi kana ya dawo da ganinshi akanta idanuwanta na kafe akanshi.

"Lokaci zuwa masallaci ya karato banaso na rasa huɗuba ki kwanta ki huta kafin na dawo kin ji?"

Ta gyada kanta, ya rik'o kanta da hannuwanshi ya sumbace ta a for head runtse idanuwanta tayi, tana ji lokaci da ya gangaro bisa lips ɗinta tun kafin bakinsa ya sauka akan nata tayi wata ajiyar zuciya, iskar da ta fito daga k'ofufin hancinta biyu ta sauka akan fuskarshi hakan ya k'ara rura wutar abun da yake ji akanta. Cike da kwarewa ya yi connecting lips ɗinshi da nata. Cikin salo na burgewa tare da tafiyar da ruhi da gangar jiki yake tsotsar bakinta, ba don ya gaji ba ya cire bakinshi daga nata. Sai don yana gudun kada ya rasa sallar juma'a. Gaba ɗaya jikin Miyya ya mutu mutusss.... kasala da kunya suka lullu6e ta tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta. Ya yi dariya tare da faɗin.

"Ashe haka Prettyn Daddy take da kunya, Ki ce Daddy yana da aiki?"

Da sauri ta kwanta tasa pillow ta k'ududdune fuskarta sosai ta bashi dariya yasa dariya mai ban sha'awa tare da rik'o k'afarta da hagu yana mata tafiyar tsutsa can cikin pillow take kwasar dariya tana d'an shura k'afarta. Da kyar ta fizge k'afarta ta yana dariya ya ce.

"Shikenan na tafi tun da kin kore ni Nanny Lacey za ta zo tare da su princess su taya ki fira kafin na dawo. Bai tsaya jin amsar da za ta bashi ba ya buɗe k'ofa ya fita yana zagba fara'a da kalle shi sau ɗaya za ka fahimce duniya ta masa dad'i.
Tun bayan tafiyarsa lokaci zuwa lokaci Miyya take murmushi, wani irin farin ciki da take ji wanda ta rasa na menene. A haka su Aneesah suka tararda ita da gudu suka rungumeta. Aneesah ta shak'i k'amshin turaren Daddynta a jikin Miyya gaba ɗaya jikinta k'amshin turarenshi yake yi, a firgice ta janye jikinta daga jikin Miyya zuciyarta na bugawa da k'arfi yayin da tsoro ya lullu6e ta. Cikin rawar murya ta ce.

"Pretty ya na ji gaba ɗaya jikinki yana k'amshin turaren Daddy?"


*Afuwan please jiya ban samu nayi update ba throughout jiya ba mu da wuta transformer ɗin mu ya lalace.*
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004


29.....


Kamar wacce aka jefo daga sama haka Hafsat Shinkafi taga Salima ta faɗo mata cikin falo, tana zuwa ta durk'usa bisa center carpet tamkar mai rokon gafara ta rushe da matsanancin kuka. Hankali tashe Hafsat ta taso ta dafa kafad'arta tana tambayarta.

"Subhanalillah.....Salima lafiya ba dai mutuwa aka yi miki ba Kodai matsalarki ce da Azaad?"

Tsananin kuka da take yi yasa ta kasa magana gaba ɗaya ta birkitawa Hafsat tunani ta rasa yadda za ta yi da ita sai faman rarrashinta take yi kamar wata k'aramar yarinya.

"Haba Salima wannan fa ba girmanki bane koda mutuwa aka yi miki a wannan shekaru naki bai dace ki dinga rusa kuka haka ba. Balle ma nasan ba mutuwa bace matsalarki ce da Azaad ne ko?"
Hak'uri za ki yi duk abin da ya faru da bawa muk'addari ne daga Allah tun ran gini tun ran zane. Ba wanda ya isa ya sauya k'addararsa, asalima imanin mutum ba zai cika ba har sai ya yi imani da k'addara mai kyau da marar kyau. Salima ki yi hak'uri ki mik'awa ubangiji al-amurranki kuka ba zai miki magani komai ba. Ba kuma zai warware miki matsalolinki ba, sai ma ya k'ara jefa ki cikin mayuwaci hali.

Cikin shasshekar kuka da muryarta da bata fita sosai ta ce.

"Hafsat na shiga uku na lalace Ina zan tsoma raina, na ji sanyi ji nake tamkar hankalina zai gushe wayyo......ni Hafsat ki taimake ni banaso na rasa Azaad. Wallahi Ina matuk'ar son mijina.

Ta k'arashe magana tana sake rushewa da wani sabon kuka wanda yafi na farko. Hafsat tayi ajiyar zuciya jikinta ya yi sanyi lak'ass....dama tasan irin wannan ranar za ta zo da Salima za ta gir6i abin da ta shuka duk yadda take da ita da zarar ta fara bata shawara ta gyara zamantakewar aurenta, rufe idanu take yi ta ci mata mutunci sau dama sun sha faɗa akan ta bata shawara ta daina yi wa aurenta rik'on sakainiyar kashi.

"Salima kina da girman kai wallahi duk yadda na ba ki shawara ba ki amfani da ita.....

"Wallahi-tallahi Hafsat duk abin da kika faɗa min ba wanda na yar asalima shawararki da na d'auka ita ce silar kukan na nawa.

Tana kuka tana zayyanewa Hafsat irin wulak'anci da Azaad ya shuka mata, tun da ta fara magana Hafsat ta yi shiru hak'ik'a Azaad ya shammace su yadda yake shiru-shiru nan ga d'an banza hak'uri bata ta6a zaton zai iya zuba rashin mutunci irin wannan ba. Duk da tasan iskanci da Salima take mishi ba kowane namiji zai iya jure shi ba. Duk tsawon shekaru da suka yi da aure zaman hak'uri Azaad yake da ita bai isa ya faɗa ta ji ba, bashi da ra'ayi sai nata duk abin da ta faɗa ya zauna koda kuwa ranshi bayaso. Batasan darajarshi ba balle ta aurenshi da ke rataye a wuyanta kwata-kwata a rayuwarta ba abin da tasani ko ta iya daga neman kud'i sai izza da tak'ama.

"Kukan ya isa haka ki share hawayenki, ki natsu ki bani aron hankalinki dole ta inda aka hau tana ake sauka a yanzu kina da two options dole ki yi amfani da d'aya daga cikinsu"

Madam Salima ta ciro mayafin abayar jikinta ta goge fuskarta tare da fyace majina, tattaro dukkan natsuwarta ta kafe Hafsat da jajjaye idanuwanta.

"Salima tun farko kin ri ga da kin 6ata rawarki da tsalle ko ba a faɗa ba daga jin yadda Azaad yake ci miki fuska yana kushe halittarki, kin fice mishi a zuciya ko kaɗan a yanzu ba bu ke gabanshi. Kuma duk kece silar faruwar hakan saboda haka girman kai ba naki bane ki sauke duk wani jiji da kai naki, ki nemi Jadda ko Hakeem sune Kaɗai mutane da Azaad baya iya fatali da umarninsu. Su Kaɗai ne za su iya yi mishi magana ya dawo da aurenku. Ina ga wad'annan mutane guda biyu su kaɗa ne damar da suka rage miki.

Madam Salima ta rafka tagumi har ga Allah bataso maganar rabuwarsu ta yad'u a duniya shiyasa, za ta d'auki wannan shawarar ta Hafsat da ba don haka ba daga Hakeem har Jadda basu isa ta rok'i alfarma a wurinsu ba saidai su rok'a a wurinta.
*** **** *****
Gumi ne ya karyowa Miyya gaba ɗaya ta rud'e ta rasa amsar da za ta ba Aneesah, gashi ta kafe ta da idanuwanta ba ko kiftawa ba shakka Aneesah tana zargin wanzuwar wani abu tsakaninta da Daddy.

"Ke dai Aneey kina da shegiya mantuwa yanzu har kin manta d'azu da safe da Pretty ta suma Daddy ne ya d'auko ta zuwa hospital Kin ga kuwa dole tayi k'amshin turarenshi.

Airah ta faɗa tana kallon Aneesah da murmushi akan fuskarta.

Kusan a tare Miyya da Aneesah suka sauke ajiyar zuciya, duk abin da suke faɗa Nanny Lacey tana zaune a gefe rungume da Ahlam tana kallonsu.

"Al-hamdu-lillah.....Allah nagode ma da Airah ta yi sauri kar6e zance nan da batasan me zan ce da Aneesah ba.

Miyya ta faɗa cikin zuciyarta, daga haka su ci gaba da firar abu da ya wakana yau a school jefi-jefi take tsoma bakinta. Da ta gaji da sauraren surutunsu ta mik'e ta shiga bathroom tayi alwala ta kabarta sallar azhar tana raka'ar k'arshe sai ga Aunty Zaliha tare da Amrah, Amal da Rayhan tana sallamewa bata tsaya doguwar addu'a ba ta mik'e, Amrah da Amal suka rungumeta ta yi matuk'ar farin ciki da gani su. Ta saki jiki suka shiga fira tamkar ba ita bace marar lafiya ba.
Misali karfe biyar da minti goma Azaad ya tura k'ofar d'akin da Miyya take, tana zaune tsakiyar gado ta mi-mik'e kafafuwanta yayin da Ahlam take kwance akan cinyarta tana wasa da doll ɗinta, Miyya tana ɗagowa taga shine tai sauri sadda kanta k'asa gudu kada tayi abin da Aneesah za ta sake dasa mata alamar tambaya.
Yana shigowa gaba ɗayansu suka daina magana ka ji tsittt....kamar ruwa ya cinye su d'aya bayan d'aya suka dinga gaida shi can k'asan mak'oshi yake amsawa, sai kayi da gaske za ka iya jin abin da yake faɗa. Aunty Zaliha Kaɗai ya d'an sakewa fuska suka gaisa.

"Daddy manya ba dai miskilaci ba.

Miyya ta faɗa cikin zuciyarta.

"Nanny zo ki d'auki Ahlam direba yana jiranku a waje"

Ya yi magana batare da kalli gefen da Nanny Lacey take ba, ta taso da sauri ta d'auki Ahlam kuka Ahlam tasa alamar bata zuwa. Cikin sanyi murya Miyya ta ce.

"Nanny ki barta kawai tun da bataso in Daddy ya tashi tafiya ya wuce da ita.

Kallon da ya yi wa Nanny Lacey yasa bata bi ta kan Miyya ba ta wuce da sauri sa6e da Ahlam a kafad'a sai taratsin kuka take yi, yayin da sosai kukan nata ya ta6a Miyya shiyasa ta runtse idanuwanta. Aneesah ta ce.

"Get well soon our Pretty"

Murmushi kawai Miyya ta saki mata, kamar jira su Aunty Zaliha ke yi su Aneesah su fita suma suka mik'e. Miyya ta kallesu tamkar za ta rushe da kuka ta ce.

"Aunty Zaliha ba dai tafiya za ku yi ba?"

"Eh....tafiya za mu yi Aslamiyya mun baro gida ba kowa.

"Aunty ki barmin twins da Rayhan su tayani fira, bana ji dad'i zama ni Kaɗai, wallahi na gaji da zaman asibiti nan"

Murmushi Aunty Zaliha tayi saboda yadda taga Azaad Junaid ya kasa ya tsare so yake su bar mishi d'aki, ta dubi su Amrah ta ce.

"Ku tashi mu tafi mana"

"Aunty ba ki ji Miyya ta ce ki barmu anan ba?"

Cewar Rayhan tana turo baki, harara aunty Zaliha ta galla mata babu shiri suka mik'e, Miyya tana kallonsu suka fice.
Suna ficewa shima ya fice kaitsaye office ɗin doc Saheeb ya nufa, tare suka dawo d'akin doc ya sake dubata, ya ga tadawo normal kana ya yi 'yan rubuce-rubuce a cikin folder ɗinta kana ya mik'awa Azaad discharge papers yana murmushi.

"Al-hamdu-lillah....jikinta ya yi kyau za ku iya tafiya Yalla6ai saidai ta dinga kula da shan magani cikin lokaci, ta kuma daina sa kanta damuwa Allah ya k'ara bata lafiya.

"Amin Doc Saheeb thank you very much.

Azaad ya yi magana tare da mik'a masa hannu suka yi musabaha. Doc Saheeb ya buɗe k'ofa ya fita sai lokaci ya kalleta, ta sunyarda kai tana wasa da yantsun hannunta a natse yake yawo da idanuwanshi akanta, ta cire cardigan ɗin jikinta ta bar white t-shirt kasancewar rigar fara ce yasa ake iya gani shatin black colour bra ɗinta. Gashin kanta a buɗe tayi parking ɗinshi wurin d'aya a yadda take ɗinan ba zai iya barinta ta fita ba text ya turowa Mr Richard ya nemo mata wasu kaya.
Sannan ya nufi kusa da kafafuwanta ya zauna ta ɗago idanuwanta ta kalle shi, shima ɗin ita yake kallo duk bayan kowace dak'ik'a k'ara mishi sonta ake yi. Ya mik'a mata hannunshi na dama ta dubi tafin hannunshi sumul-sumul dashi alamar ba a aikin wahala dashi cikin mutuwar jiki ta ɗora hannunta cikin nashi.

"Daddy Dan Allah mu tafi gida haka nan wallahi na ji sauk'i.

Tayi magana cikin siriyar muryarta mai taushi, ya kalleta tare da maka mata harara da sauri ta kauda fuskarta.
Ya d'an gyara murya tare da matsawa kusa da ita ya ce.

"Prettyn Daddy ba ki so kasancewa tare da ni ko?"

Da sauri ta ce "ba haka bane Daddy kawai dai naji sauk'i babu amfani ci gaba da zamana anan.

Ya ja gwaron numfashi ya sumbace hannunta dake cikin nashi.

"Ki k'ara hak'uri kaɗan na aiki Mr Richard ya siyo miki kayan da za ki saka mu tafi gida.

"Kaya kuma Daddy bayan wannan da ke jikina ai Ina da wasu kaya a gida da zarar mu isa gida zan canza, ni dai ka tashi mu tafi.

Ta k'arasa magana tana cire hannunta daga nashi ta shiga k'ok'arin saukowa, Azaad ya kalleta da girar ido ɗage lallai yarinyar nan akwai zallan kurciya a cikinta, ai ko karen hauka ya cije shi ba zai barta ta fita da wannan kayan a jikinta ba.
Hannu yasa ya dawo da ita bisa gado ya d'aure fuska ta kalleshi sosai yai mata kwarjini da sauri ta sadda kanta k'asa. Mr Richard ya yi knocking on Azaad ya mik'e ya kar6o shopping bag ya buɗe ya ciro long hijab ya saka mata batare da ya tanka mata ba ya nufi k'ofar fita da sauri ta diro daga kan gado ta d'auki sneakers ɗinta a hannu ta bishi a baya kamar an ce ya waiga ya ganta tafe babu takalmi a k'afafuwanta. Ya ja tsaya har ta k'araso cikin d'aure fuska ya ce.

"Ke banaso shirme ki tsaya ki sa takalminki nan asibiti ne kina tafiya ba takalmi salon kuma wata cuta ta kama ki.
Cike da jin kunya tasa takalmin yana gaba tana bin shi suna daff da isa parking lot suka haɗu da Ahmadu sai lokaci Azaad ya tuna da Hasheem a asibitin yake cikin sakin fuska ya mik'awa Ahmadu hannu su gaisa a maimakon Ahmadu ya bashi hannu sai kawai ya ɗaga masa hannu cike da wulak'anci yake kallon Azaad. Miyya ta k'araso wajensu cikin sanyi murya ta gaida Ahmadu yana ganinta cikin dogon hijab har k'asa gabanshi ya yi mummunan faɗuwa nan take ya tuna da inda yasan fuskarta tabbas

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login