Showing 57001 words to 60000 words out of 91651 words

Chapter 20 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

629

ita ce aljana da ta fito cikin kwaryar zafi boka ta kasheshi tare da babban Yaya da Alhaji Buba.
Shima ta biyo shi ne domin ta kashe shi cikinshi yai masifar murd'awa, a tsorace ya dinga ja da baya yana furta.

"Innalillahi wa'aina illahim raji'un.....Ita ce wallahi ita ce aljana da ta kashe babban Yaya da Alhaji Buba ki duba girman Allah ki yi min rai karki kashe ni wallahi-tallahi babu hannuna a cikin wannan tafiya, gaba ɗaya shirrin Hasheem ne.
Ahmadu yana magana yana ja da baya da sauri Azaad ya rik'o shi ya buge mishi hannu ya kwasa da gudun bala'i ya nufi gate ɗin fita ko ta kan motarsa bai bi ba.
Azaad ya dawo wurin da Miyya take tsaye tayi folding hannuwanta a k'irji hankalinta kwace ba abin da ya razana ta.

"Daddy amma wannan mutumin motsatsi ne ko?"

Tsabar mamakin abinda ya ji Ahmadu ya faɗa ya hanawa Azaad bata amsa sai kawai ya kama hannunta suka nufi wajen mota, da sauri Mr Richard ya fito ya buɗe musu k'ofa suka shiga kana ya ja motar cike da kwarewa da driving.
A maimakon su nufi gida sai ta ga Mr Richard ya d'auki hanyar Nassarawa GRA a sultan road wani tangamemen gida ya tsaya horn guda ya yi security ya buɗe mishi gate.
Azaad ya fara fitowa kana ya taimaka mata ta fito, a fakace take kallon compound ɗin gida sosai ya burgeta yana rik'e da hannunta suka jera side by side bata k'ara tabbatar da gidan ya haɗu ba sai da suka shiga parlour anan taga matuk'ar haɗuwa za ka ci ba a Nigeria kake ba.
Da shigarsu parlour ya saki mata hannu ya nufi upstairs muryarta na rawa ta ce.

"Daddy me za mu yi anan ni fa gida nakeso zuwa?"

"Hutawa za mu yi gida Kuma ba yanzu ba.

Ya faɗa yana ci gaba da tatttaka matattak'alar bene, jin abin da ya faɗa yasa gabanta yai mugun faɗuwa cikin sauri ta bishi tana faɗin.

"Wane irin hutawa Kuma Daddy?" Ni dai Dan Allah ka maida ni gun su Aneesah ko Kuma gidan uncle Hakeem, wallahi kwata-kwata gidanan bai kwanta min arai ba.

Ya tsaya cakk.... batare da ya juyo ba ya ce.

"Wannan kuma matsalarki ce ki zo mu je na nuna miki bedroom ɗinki ki yi wanka tun safe kike sanye da kaya d'aya ke ko k'azantar su bakya ji.

Turo baki tayi tana gun-guni k'asa-kasa "ka ji min mutum haka kawai ka d'auko ni ka kawo inda bansani ba ka ce ba zan yi magana ba.

"Me kika ce?"

"Ban ce komai ba Daddy"

Ta faɗa cikin marairaice murya.

Ya ci gaba da haura staircase dole ta bi shi a baya, ya buɗe k'ofar d'aya daga cikin d'akuna uku da ta gani a jere, dai-dai k'ofa ta ja birki tana tunani ta shiga ko ta koma inda tafito. Bata gama tunani ba ta ji ya jawo tana jin saukar numfashinsa daff da fuskarta, ya cire mata hijabin jikinta idanuwanshi suka sauka akan boobs ɗinta da suke cike tabbb....a k'irjinta har sun so su rinjaye ta sauk'inta d'aya a tsaye suke cakkk kana ya jefa hijab ɗin nata bisa gado, ya ɗora hannuwanshi masu masifar taushi aKan kafad'arta ya mutsa da ita cikin jikinshi, kafin ta yi yunk'uri kwatar kanta ta ji ya sumbace ta a gefen wuya ya cigaba da shinshina gefe-gefen wuyanta yana zuba mata dafi kisses k'ok'arin tura hancinshi yake tsakiyar rigarta wacce rabin boobs ɗinta ke waje jikinta ya d'auki rawa kamar mazari batasan lokaci da ta ture shi ba ta falla da gudu ta nufi wata k'ofa da take tsanmani bathroom ne. Tana shiga ta datse k'ofar da key.
Sai da Azaad ya d'auki dogon lokaci yana dambe da numfashinsa kafin ya samu ya dai-daita, a kasalance ya buɗe k'ofa ya wuce d'akin da ya kasance mallakinshi a gida wanka ya yi ya shirya cikin milk colour ɗin jallabiya, yana cikin fesa turare Hakeem ya kira wayarsa, ya yi picking up ya kara a kunnenshi. Kafin ya yi magana Hakeem ya ri ga shi ta hanyar faɗin.

"Aj duk abin da ka ke yi ka aje shi ka zo yanzu-yanzu nan Jadda tana son ganinka"

"Lafiya Hakeem Jadda keso ganina da gaggawa?"

"To zan iya cewa lafiya Salima ce ta kawo kararka wajenta.

"Uhm... Salima!

Ya furta sunanta cike da takaici ko kaɗan bai so Jadda tasan ya saki Salima ba har sai ta gama iddarta gudun kada ta cilasta shi ya dawo da ita sai gashi an gudu ba a tsira ba.

"Shikenan Hakeem ka faɗa mata ganina zuwa.

Daga haka ya kashe wayar tsabar haushi da takaici yasa ya fita batare da ya lek'a Miyya ba. Koda ya iso ana kirar sallar magariba ya tsaya anan masallaci dake k'ofar gidanshi ya yi sallah k'a'idarshi ne in ya shiga sallar magarib sai ya yi isha yake fitowa daga masallaci. Bayan an kammala sallar Isha yana fitowa ya yi arba da Hakeem ya mik'a masa hannu suka yi musabaha suka jera zuwa cikin gida suna tafe suna tattaunawa dangane da kiran da Jadda take mishi.

"Aj miyasa ba ka faɗawa Jadda ka saki Salima ba?"

"Saboda banaso ta cilastani na dawo da ita har ga Allah naso ace iddarta ta cika kafin Jadda tasani, a zahirin gaskiya Hakeem banaso dangatakar aure ta sake haɗani da Salima. Musanmman a yanzu da na fara son kwailata.

Ya k'arashe magana da annuri akan fuskarshi, murmushi Hakeem ya yi kafin ya ce.

"Ai abokina ba k'aramar sa'a ka taka ba yarinya danya latsar sai yadda ka bi da abarka ba za ka faɗi ta faɗa ba. Saidai zance na gaskiya dole ka hak'ura ka dawo da Salima ko don albarkaci yaran dake tsakaninku. Kuma ga dukkan alama duniya ta fara yi mata atishawar tsaki, koda na fito sallah na baro su ita da k'awarta Hafsat Shinkafi Jadda tana wanke mata allonta tass....sai kuka take yi tana rokon Jadda Allah da Annabi ta sa baki ka dawo da ita......
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004


*SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣�?*

*SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣️🗣️*

*SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣️🗣️🗣�?*



*NUCEEYLUV😘 NA MUKU ALBISHIR DA DATA DINTA ME SAUKI AKAN FARASHI ME RAHUSA, MAZA KU GARZAYO SAUKI DATA A CANCARE KU DA DATA A BAGAS🤸🏻‍♀�?, TURAWA BABU BATA LOKACI 📤👌🏻*


*MTN*
50mb-50
150mb-100
500mb-200
1GB-300
2GB-600
3GB-900
5GB-1500
10GB-3k
20GB-5k

*Codes for check balance, *131*4#*
*1MONTH VALIDITY*


*AIRTEL*

100mb-150
300mb-250
500mb-300
1GB-600
2GB-1200
5GB-3k
11GB-4500

*Codes for check balance, *140#*
*1MONTH VALIDITY*

*GLO*
1.35GB-550
2.9GB-1200
4.1GB-1600
5.8GB-2200
7.7GB-2600
10GB-3200
14GB-4k

*Codes for check balance, *127*0#*
*1MONTH VALIDITY*

*9MOBILE*
1.5GB-1200
2GB-1500
3GB-2k
11GB-4k

*Codes for check balance, *228#*
*1MONTH VALIDITY*

CALL 09039118754 OR CHAT ME PRIVATE 09039118754�?

*YADDA ZAKI BIYA, ZAKI TURO KUDI TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 1445626295. NUSAIBA MUSTAPHA ACCESS BANK*


*IYA KUDIN SIYEN DATA IYA SHAGALIN KU🤸🏻‍♀�? BANA AMSAR KATI PLS😁👌🏻, KADA KU BARI AYI BA KU WANNAN GARABASAR😍, ZAKU IYA SAVING NUMBER NAN 09039118754 DOMIN SIYEN DATA KAI TSAYE BABU BATA LOKACI KO BANA ONLINE KU KIRA KAWAI MASOYA💃🏻*


30....


Miyya tayi tsaye gaban mirror tana kallon tsakiyar rigarta da Daddy ya gama tura kanshi a cikin, wata kunya ta sake lullu6e ta har tana rufe fuska tamkar tana a gabanshi.
Daga bisani ta cire kayan jikinta tayi wanka ta zari d'aya daga cikin jerin white towels da ta gani a bathroom ta d'aura, ta buɗe k'ofa a hankali saida ta fara lek'awa taga Azaad ya fita kana ta fito, agaggauce ta tsane jikinta ta shafa lotion da ta gani akan mirror. Shopping bag ɗin da ya aje mata bisa gado ta d'auka ta zazzage kayan da ke ciki. Ɗaga su sama ta dinga yi tana kallo tana yatsine fuska sakamakon babu ta kirki a ciki kusan seat biyar ne biyu sleeping dress ne, suma duk wasu fingilallu dasu. Ta ɗaga wata belted shift ga ta tayi kyau har ta gaji musanmman da ta kasance her favorite color saidai ba za ta wuce iya cinyoyinta ba. Tsaki ta ja ta aje ta, ta d'auki Indonesia gown ita kuma spaghetti hands ne da ita Kuma za ta iya wuce gwiwoyinta.

"Kai amma wallahi Daddy d'an duniya ne yanzu shi ko kunya ba ya ji ya siyo irin wad'annan kayan"

Miyya ta faɗa tana ta6e baki haka nan ta d'aure ta saka Indonesia gown ɗin ba don ranta yana so ba. D'aya daga cikin perfumes da take akan mirror ta fesa, kana tasa hijab ɗin da ya bata wanda ya sauka mata har k'asa tayi sallah.

Jahilin tsaki Azaad ya ja kamar zai gutsire harshensa "mtssss.!
Cikin 6acin rai ya kalli Hakeem don har idanuwanshi sun fara canza launi ya ce.

"Tuban mazuru ne kawai tayi ni nasan wacece Salima hawainiya ce a ko wane lokaci sauya launi take da zarar tayi nasara na dawo da ita za ta ci gaba da halinta ne, ba abin da za ta fasa. Ba zan 6oye maka ba Hakeem wallahi-azim Salima ta fita daga raina, kamar an yi ruwa an d'auke ji nake tamkar ban ta6a rayuwar aure da ita ba.

"Hak'uri za ka yi Aj tsakani da Allah kaima kana da naka laifi tun farko kaine ka bata damar da tayi yawa har ta zo tafi k'arfinka. Kuma tun farko ba ka duba nagarta da tarbiyya ba ka biyewa soyayya ka kwasowa kanka jangwa, ko a wancan lokaci ni da Jadda mun nuna maka illolin da ke tattare da auren Salima amma ka rufe idanunka.

Kafin Azaad ya bashi amsa suka iso k'ofar shiga falon Jadda, dole ya ja bakinshi ya yi shiru tun kafin ya k'arasa shiga falon ya d'aure fuska tamau alamar babu wargi a tare dashi, Salima tana ganinshi ta k'arawa kukanta armashi har wani shan majina take yi, kallo d'aya Azaad ya yi mata ya wulga mata harara ya kauda fuska. Hafsat shinkafi sai faman gaidashi take yi yak'i amsawa ya kalleta a ɗage ya watsar kana ya nufi cushion ɗin da Jadda take zaune ya zauna kusa da ita. Jadda kan sai kallonshi take yi ta kasa gasgata ya saki Salima gaba ɗaya gani abin take kamar al'mara.

"Gani Jadda"

Ya faɗa cikin dakakkiyar murya tare da sunkuyar da kai.

"Idonka kenan Datti wato da raina da lafiyata ka saki matarka shine ba ka faɗa min ba. tsabar baka d'auke ni a ba ki komai ba ko?"

Sosai ya ji ranshi ya k'ara 6aci musanmman da ya fahimce ran Jadda ya 6aci a dalilin rashin faɗa mata ɗin da ya yi sai duk ya ji wata sabuwar tsanar Salima ta kamashi. Ya fara magana rai 6ace.

"Da farko ina mai ba ki hak'uri Jadda, Allah ya huci zuciyarki. Inaso ki sani Jadda idan kika cire soyayyar Allah da manzonsa ke ce abu mafi soyuwa a zuciyata matsayinki a guna ya zarce na kowa a faɗin duniya, basan dad'in uwa ba balle na uba kece uwata kece ubana duk wani abu da na zama a rayuwa albarka ki ce take bina. Banso ko kaɗan ki saka bakinki a lamarin nan ba ke kanki sheda ce akan tsawon shekaru da na d'auka ina kunsar bak'in ciki Salima. Suna kawai Ina da aure ne amma a zahirin gaskiya banida ban-banci da gwaro. Ni da gidana ban isa na faɗa aji ba hakazalika yarana sai ta nuna tafi ni iko dasu, a takaice dai Jadda tafiya ta shirya nace ba da yawuna ba, saboda ba ta d'auke ni da daraja ba tasa k'afa takalmi tayi tafiyarta sai sanda ta ga gama gantalinta sannan ta dawo. Ba irin rok'on da ban mata ba akan ta fasa tafiyar nan amma ta murje idonta tak'i, daga k'arshe tayi abin da ranta yake so nima shine na nemawa kaina mafitar da ta dace da ni. Iya hak'uri nayi hak'uri yanzu kuma tura ta kai bango nagaji Jadda wallahi-azim na gaji da zama da Salima kwata-kwata ta fice min a rai, babu ko burbushin sonta a zuciyar nan tawa.

Ya k'arasa magana ya nuna saitin da zuciyarsa take, tun kafin ya dasa aya Salima ta d'aura hannu aka ta kwatsama ihu, tana kururuwa sam bata zaci jin wad'annan zafafan maganganu daga bakinshi ba.

"Dallah....kama mana bakinki ai duk kece silar faruwar komai, wallahi Salima kin yi girman wofi, kin yi faɗuwar bak'ar tasa ba nauyi.

Jadda ta daka mata tsawa tana zuzuba mata harara mai cike da takaici, ji take tamkar ta rufe ta da duka. Rufe idanuwa Jadda tayi tasake wanke mata allonta tass ta inda take shiga ba ta nan take fita, ta zage ta iya son ranta takaicinta na tsawon shekaru da take k'unshe dashi yau saida ta sauke mata shi. Kafin ta juya kan Azaad ta fara mishi nasiha haɗe da rarrashi.

"Datti hak'uri nan da ka saba yi ko yanzu shine zan ba ka, mai hak'uri yana tare da Allah kuma ba zai ta6ewa ba. Ubangiji da kanshi ya hallata saki amma kuma bayaso idan har kace ka gama zama da Salima, to yaranka fa duk da su ɗin ma ba dad'inta suka sani ba?"

"Uhm...har ga Allah Jadda banso maganar nan ta zo gunki ba, saboda ba zan iya Musa miki ba amma duk da haka ina neman alfarma a wurinki da ki cire bakinki tun da kema ba girmanki take gani ba, Kuna zaune a gida d'aya sai ta share shekara bata lek'o 6angarenki ba da suna ta zo duba lafiyarki duk da tasan matsayin da kike takawa a guna. Me Salima take nema a duniya indai ta fanni arziki ne Dai-dai gwargwado Allah ya azurtani da dukiya mai dinbin yawa amma tsabar rashin godiyar Allah irin nata a kullum burinta tayi building nata career na rasa gidan uban da za ta je da daud'ar duniya. Ni yanzu jira kawai nake ta gama iddarta ta tattara komaitsa ta ta barmin gidana.

Cikin muryar kuka Salima take faɗin.

"Azaad kayi hak'uri ka dawo dani wallahi-tallahi na daina duk wani abu da baka so daga yau ba zan sake fita ko nan da k'ofar gida sai da izzininka. A dalilin soyayyar da nake maka tun lokaci da Hafsat ta faɗamin da zarar naga menstruation ɗina iddata ta kammala wallahi pills nake sha na hana mishi zuwa da bana son zama da kai da ba zan hanawa period ɗina zuwa ba.

Gaba ɗayan falon in kacire Azaad salati da sallalame suke yi, ba tun yau ba Jadda tasan Salima kunsurgumar jahila ce amma bata zaci jahilcin nata ya kai haka ba. Tsabar takaici Azaad sai jan iska yake ta k'ofufin hancinsa yana fesarwa. Tsawon lokaci suka d'auka a falon aka rasa wanda zai yi magana gaba ɗayansu mamaki ya gama kashe su. Azaad ya yi k'arfin hali furta.

"Ban yi mamaki jin wannan magana daga bakinki ba saboda ke jahila ce Salima wacce ba abin da tasani akan addininta ni Kuma a yanzu mace mai wadattace ilmin addini nakeso, natsatsiya ba ballagaza irinki ba. Saboda haka idan har kinaso ci gaba da zama dani sai kin koma islamiyya kin zama kalar mace da nakeso to a lokaci zan d'an yi tunani ko zan iya sake aurenki.

Kuka sosai Salima take yi tsawon rayuwarta bata ta6a kuka irin wannan ba, muryata ta dusashe da rerafe ta isa wajen Jadda ta kama kafafuwanta ta ce.

"Dan girman Allah Jadda ki sa bakinki wallahi na tuba, zan nemo malamin addini ya dinga koyar da a gida.

"Shikenan tashi ki tafi zan yi magana dashi zan neme ki daga baya.

"To amma Jadda ban ji Azaad yace ya dawo dani cewa fa ya yi....

"Salima a halin yanzu Datti a fusace yake duk wata magana da za ta fito daga bakinsa ba mai dad'i bace, gara ki tafi har ya huce.

"Tam....Jadda nagode.... nagode Allah yasaka miki da alkhairi, Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana.

Jadda kam...kasa amsawa da Amin tayi saboda tun zamanta da Salima ko gaisuwa kirki bata ta6a haɗasu ba, sai gashi yau da wuya tayi wuya har fatan nisan kwana take mata. Duniya rawar 'yan mata na gaba ya koma baya.
Hafsat shinkafi ta taso daga gun zamanta ta kama kafand'un Salima, ta mik'ar da ita sakamakon gani yadda ta kasa tashi daga durk'uso da tayi. Kamar makaho da d'an jagora haka suka fice daga falon Azaad ya bi su da harara.
Jadda ta kalleshi a natse kafin ta ce.

"Datti inaso ka dubi girman Allah ka dawo da Salima gudun kada ta jefa kanta babbar masifa, ni ban ta6a jin inda aka sha magani dakatar da zuwan jini haila ba don kawai kada iddah ta kammala sai a wurinta.

Ajiyar zuciya Azaad ya yi tare da shafar sajenshi Wanda yin hakan ya zama mishi d'abi'a, ranshi a matuk'ar 6ace ya ce.

"Gaskiya Jadda ban da ra'ayi sake zama da Salima ni fa yanzu Prettyn Daddy ta ishe ni rayuwa ba ma buk'atar third party a zaman mu.

Zaro idanu Jadda tayi yayin da Hakeem ya tintsire da mahaukaciyar dariya.

"Abdul-hakeem me Datti yake faɗa ne kwata-kwata ban fahimci turancinsa kai kuma ka yage baki kana babbaka dariya?"

Hakeem ya tsagaita da dariya da yake yi ya mik'e tsaye ya ce.

"Ba za ki gane ba Jadda saboda Aj ya zurma a soyayyar kwailarshi, bai ji bai gani ita kaɗai yake gani a gabanshi a takaice dai ita ce tauraruwar da ta dusashe hasken madam Salima a zuciyarsa.

"Hoo.... ja'iri lallai Datti baka da kunya gotai-gotai da kai ace kana soyayya.

Jadda ta faɗa tana dariya sai lokaci Azaad ya saki fuskarshi hadda su murmushi yana sosa keya kana ya mik'e tare da nufar k'ofar fita.

"Datti ka dawo ba mu gama magana ba.

"Jadda na baro matata ita kaɗai a bakon wuri bai kamata na shantak'e a wurinki ba tun da kina da ra'ayi da Salima ga ki nan ga ta.

Ya k'arasa magana dai-dai yana kama handle Hakeem ya biyo shi da sauri yana faɗin.

"D'an tsaya mana Aj ina ka kai 'yar mutane da ko isasshiyar lafiya batada, kada kace min angwacewa za ka yi.

"To ko haramun ne?"

"A'a...amma ka yi duba da kasancewarta kwaila anya kuwa za ta iya d'aukarka ka tuna weight ɗin ka fa abokina?"

Ya k'arashe magana yana sake fashewa da dariya, tsaki kawai Azaad ya yi yana isa gun mota Mr Richard ya buɗe mishi k'ofa ya shiga duk iya shegen da Hakeem

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login