Showing 87001 words to 90000 words out of 91651 words

Chapter 30 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

624

naki?"

Dadda tai magana tare da mik'a mata hannunta, a maimakon ta kama hannu kamar yadda Dadda ta buk'ata sai kawai ta durk'usa k'asa tana kuka tana basu labari abin da ya faru.

"La'illaha illallahu muhammadu rasulillahi sallallahu alaihi wasalaam!

Dadda ta fad'a tana tafa hannuwa tare da zaro idanuwanta, nan take ta fara kuka yayin da fuskar Baffa Sani bata nuna ya razana da jin zance ba. Sai ma sadda kanshi k'asa da ya yi yana saurare kuka Miyya da Dadda. Tun washe gari ranar da Azaad ya fahimci mutume da ya ta6a kad'ewa mahaifin Aslamiyya ne shi da Hakeem suka zo wurin Baffa Sani basu 6oye masa komai ba. Da farko hauka ya dinga yi musu da sai daga bisani Hakeem ya shawo kanshi ya fahimce su, da suka nemi gani Dadda saboda ita ma bai kamata a 6oye mata ba. Yanayi rashin lafiyarta yasa Baffa Sani ya hanasu sai ya nuna masu zai fad'a mata da kanshi, tun daga ranar har izuwa yau nema yake hanyar da zai bi ya fad'a mata sai gashi Allah ya kawo Aslamiyya.
Ya sauke numfashi kana ya d'ago idanuwanshi ya kalli yanda Dadda ke ta faman zabga kuka kamar wata k'aramar yarinya cikin taushin murya ya shiga rarrashinta tare da fad'a mata, yadda suka yi da Azaad da Hakeem ya zarce da fad'in.

"Dadda ki yi hak'uri ki daina kuka komai muk'addari ne daga Allah...

Tun kafin ya k'arashe magana Dadda ta tsula mishi casbin hannunta.

"Rufe min baki dallah! Ban ta6a tsanmani sakarcinka Sani ya kai har haka ba, a kashe d'an uwanka kissan gilla ace da kai tsautsayi ne kuma ka hau ka zauna akai...

"Wallahi Dadda yadda kike tsanmani ba haka bane, Usman ya ri ga da ya mutu addu'armu kadai yake buk'ata idan ma nace zan kai k'arar Alhaji Azaad ga hukuma nine zan kwana a ciki, sannan kafin na furta na yafe masa saida nai kwakwaran bincike akansa. Aka tabbatar min da shi din mutume kirki ne. Dadda mu kanmu masu laifi ne a wani gefe ma Alhaji Azaad ya fi mu saboda ya rik'e yaranan amana sa6ani mu da muka dinga gallaza masu.

Kasa cewa komai Dadda tayi hakan ne ya ba wa Baffa Sani damar ci gaba da yi mata nasiha mai shiga ciki.
Aike da aka yi masa ana sallama dashi a k'ofar gida yasa ya fita yabar Dadda da Miyya suna shar6ar hawaye Dadda ta mik'awa Miyya hannunta a wannan karo bata yi gardamar kamawa ba, Dadda ta jawo ta jikinta tana shafar sumar kanta wacce garin kuka d'an kwali kanta ya zame.
Baffa Sani yana fita ya ci karo da Azaad Junaid tare da direbanshi mr Richard suna tsaye cirko-cirko, kallo d'aya yai ma Azaad ya gano irin zallar tashin hankali da yake ciki.
Ya mik'a mishi hannu suka yi musabaha kafin Azaad ya shiga zayyane masa abin da yake tafe dashi.

"Karka damu Yalla6ai in-sh-allah komai ya zo k'arshe zo mu shiga daga ciki mu yi magana a gaban Dadda.

Baffa ya juya ciki yayin da Azaad Junaid yake binsa a baya daga Miyya har Dadda ba wanda ya amsa masa sallama, ya zauna akan kujera cikin taushin murya ya shiga ba Dadda hak'uri har ya gaji da magana Dadda bata tanka masa ba. Saida ta gama shan k'amshinta kafin ta furta ta yafe masa.
Miyya ta mik'e zubur daga jikin Dadda ta ce.

"Kin yafa masa kika ce Dadda?"

"Kwarai kuwa Aslamiyya ubangiji muna masa laifi mu rok'e shi gafara mu sa ran zai yafe mana balle mu 'yan adam masu rauni, kema inaso ki yafewa mijinki kowa da irin tasa k'addara tashi k'addara ce ta zo da hakan.

"Cab! Ni dai gaskiya ba zan yafe masa ba idan har ba da wata manufa ya kad'esa ba miyasa ya 6oye bai sanar mini ba?"

Ta k'arasa magana tana harara Azaad da sauri ya mik'e da nufi ya rik'ota, ta rugu ta shige uwar d'akan Dadda har da su rufe k'ofa.
Duk yadda Azaad yaso ta saurare shi abin yaci turu, sai bore take masa Dadda ta rarrashinshi da kalamai masu dad'i.

"Kyaleta kawai wannan bore nata zallar kurciya ce ke damunta ba wani abu ba, ka barta zuwa gobe idan ta sauko sai ka dawo ka tafi da matarka.

Azaad ya gyada kai azahirin gaskiya ba haka yaso ba saidai ba shi da za6i, ya yi wa Dadda sallama suka fito tare da Baffa har zuwa k'ofar gida ya dauko magungunata ya ba Baffa tare da d'aya daga cikin wayoyinsa akai mata tashi dabara watakila idan ta waya ne za ta saurare shi.
Bayan tafiyar Azaad Dadda ta isko ta har cikin d'akin ta dinga bata magana, ba ta so ta tukura ta shiyasa da ta fara kuka ta kyaleta.
Baffa Sani yana bata wayar tai switch off d'inta, ta jefa ta k'asan pillow da take kwance akai magani ma bata sha ba sai zubarwa tayi.
Washe gari tun 8:00am dai-dai Azaad ya yi wa k'ofar gidansu Miyya tsinke, koda yaje tana barci haka yai ta zama a falon Dadda yana jiran ta falka sosai tausayinshi ya kama Dadda ta kawo mishi koko da k'osai saboda ko bai fad'a ba yadda yai wannan uban sammako bai karya kumallo ba.

"Nagode Dadda amma ina azumi.

Ya fad'a cikin taushin murya tare da sadda kanshi k'asa, addu'a sosai Dadda tai mishi a dai-dai lokaci Miyya ta falka jin Dadda tana zabga mishi addu'a haushi ya turnuk'e ta, ta sauko daga kan gado tasawa k'ofar sakata ta koma ta kwanta abinta.
Ba yanda Dadda bata yi da ita ba ta bud'e k'ofar amma tai biriss, jikin Azaad a sanyaye ya baro gidan kaitsaye gidan Hakeem ya nufa, ya kwashe abin da ya faru ya sanarda da zaliha matar Hakeem. Tai mishi alk'awali da zarar Amrah da Amal sun dawo daga school za ta d'ibesu su je gidan Dadda ta ba Miyya magana ko za a dace ta sauko daga dokin nak'i da ta hau..
6/2/22, 20:27 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004

43...

*K'ARSHEN LABARI...*


*Australian*

Cikin hukunci ubangiji Hakeem ya isa lafiya ya hau taxi ta kaishi hotel d'in da ya yi booking, sai a washe gari da ya sauka a garin ya fara processed d'in gani Miss Gambella kasancewar bai da appointment da ita shiyasa ya sha matuk'ar wahala don sai da ya kwana uku a garin kafin ya had'u da ita a katafare gidanta a guest room aka saukarda shi, bayan housemaid ta kawo mishi ruwa da lemo sannan Miss Gambella ta shigo suka gaisa a mutunce. Kafin Hakeem ya fito da envelope mai dauke da hotunan Miyya da twins ya mik'a mata, tana tozali da yaranta hankalinta ya tashi ta shiga rera kuka.
*Nigeria*
A washe gari ranar suka nufo Nigeria a cikin private jet d'inta, kwatsam Azaad ya gansu ba k'aramin farin ciki ya yi ba. Saboda tun tafiyar Hakeem sau d'aya suka yi waya. A gidan Hakeem suka yi mata masauki Bayan miss Roseline Yaqub Gambella ta huta Hakeem ya kira twins suna shigowa falon da take suka yi turuss suna kallonta, tun kafin a gabatar masu da ita suka ji a jikinsu suna da kyakkyawar alaqa da ita.
Miss Gambella tana gani yaranta da ta gudu ta barsu suna da watani a duniya a yanzu sun girma har sun zama 'yan mata cikin sauri ta iso gare su ta had'e su dukkansu biyu ta rungume tare da rushewa da kuka bayan sun gama koke-kokensu suka duguma duka zuwa gidan Dadda anan ma wani sabon shafi suka bud'e na kuka musanmman Miyya da ta tsinci kanta kwance yau a jikin mahaifiyarta tana jin d'uminta Bayan komai ya lafa Dadda da Baffa Sani suka sake neman gafarar Miyya da twins. Suka Kuma kar6i Miss Gambella da hannu bibbiyu babu kyama balle tozarci ba kamar yadda suka yi mata a shekaru baya ba.
Duk abin da ake yi Miyya bata ga Daddy ba tana so ta tambaye uncle Hakeem amma tana kunya abin da tai masa sai kawai ta hadiye abin da take ji. Har a washe gari bata ganshi ba daga nan ta fara shiga damuwa, Miss Gambella da kanta ta nemi Hakeem da ya kira mata manema labarai{press} ta gabatar da yaranta so take duniya tasan da zaman su.
Hafsat Shinkafi tana zaune a office d'inta newspaper d'in yau ce a hannunta shafi farko tai tozali da abin da ya hartsuna mata tunani, jikinta har rawa yake yi nan take ta fito, direbanta ya kawo ta hospital wurin Madam Salima tana zuwa ta jefa mata newspaper d'in tare da murmushin mugunta.

"Salima tayani gani yarinyar da kika rena kika ci wa zarafi a yanzu tai miki fintikau idan kuma kika yi wasa ba wai iya lafiyar jikinki da kika rasa saboda ita b. Hatta da dukiyar da kike tink'aho da za ki iya rasata, in takaici miki labari Aslamiyya 'ya ce ga Miss Gambella mace mafi rinjaye hannun jari a babban kamfaninki idan har ta sami labari irin wulak'anci da kika yi wa 'yarta to fa! K'aryarki ta k'are.

Jikin Madam Salima ya dauki rawa a tsorace take kallon hoton fuskokin miss Gambella da su Miyya, ji take kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu tabbas zance Hafsat shinkafi gaskiya ne tak'are mata.
Hafsat Shinkafi tana fita Mr Michael yana shigowa hankalinshi a tashe, yayin da hannunshi na hagu yake rik'e da bak'ar Jarida kamar yadda Madam Salima tai mata lakabi dashi.

"Mun shiga uku Madam asirinmu yana dabb da tonuwa idan har Yalla6ai Azaad yasan cewa nine na nunawa Pretty wannan video, kashina ya bushe a yanzu mafita guda d'aya ta rage mana ki bani kud'ad'e da kika yi min alk'awali idan da hali amaimakon 20 millions sai bani 30 millions na bar garinan shine kawai final decision.

Wani mugun kallo Madam Salima ta watsa masa kafin ta hayyako masa kamar za ta wanke masa fuska da mari.

"Lallai mr Michael ba kada hankali aiki me uban me kayi min da zan dauki wadannan makudan kud'i na ba ka?" To bari ka ji wallahi tallahi ko kwadalla ta ba zan ba ka ba d'an 419 kawai dallah fita ka bani wuri nace ka fita!

Ta k'arasa magana cikin shouting da sauri ya nufi k'ofar fita har ya bud'e sai kuma ya juyo ya kalleta da idanuwanshi da suka rikide zuwa jajayye yai mata kallon tausayi ya ce.

"I'm sorry madam k'arshen ki ya zo sai na nuna miki ba a ci amanata sannan Kuma a zauna lafiya, sai na rushe duk wani abu da kike tink'aho da shi. Sai nasaki kuka da babu hawaye.

Wani irin mashahurin tsoro ne ya kama madam Salima, tsawon rayuwarta bata ta6a jin irinsa ba cikin sauri ta bi bayanshi tana d'igishi da k'afa tare da kwada mishi kira yana juyowa ya cilla mata key d'in motarta a fuska, ya sake juyawa cikin sauri ya fice daga asibitin.
Yau kusan sati d'aya da zuwan Miss Gambella ta siye tangamemen gida a nassarawa GRA ta tare ita da yaranta har ma da Dadda wacce yanzu ta dawo mai matuk'ar sanyi hali da kirki kamar ba Dadda da mu ka sani a baya ba.
Yau tun safe da Miyya ta tashi take ji wani irin kewar Daddy ji take idan bata ganshi ba za ta iya zarewa, ta sha kiran layukanshi da wayar da ya bata amma baya picking kasancewar yau weekend ne Miss Gambella tana d'akinta haka ma Dadda 'yan biyu kuma tun jiya suka tafi gidan Uncle Hakeem.
Cikim sauri Miyya ta sauko daga gado, ta dauki hijab da 1k had'i da wayar da Daddy ya bata, ta fice daga gidan cikin sauri.
Masu gadi ne kawai suka ga fitarta.
Ta hau adaidaita a bakin gate d'in gidan Azaad Junaid aka sauke ta duka ta mik'awa d'an adaidaita 1k d'in, yai mata godiya kana ya kama gabanshi.
Bata wuce knocking d'in gate biyu zuwa uku ba, d'aya daga cikin securities d'in gidan ya bud'e k'aramar kofa ya lek'o da kanshi yana gani ita ce yai maza ya k'arasa bud'e k'ofar, ta shigo suka gaisa ta wuce cikin gida dai-dai main door ta hadu da Mr Richard yana ganinta ya fara zabga murmushi, ita kuma ta galla masa harara saboda shi ma fushin da take da Daddy ya shafe shi tun da ya ga hakan ya fahimce manufarta ya gaidata ta amsa tana kumbura baki. Tana shiga babban parlour tai tozali da Airah tana zaune rik'e da mug d'in tea.

"Pretty oyoyoyo! Ga prettyn Daddy ta dawo Nanny Lacey fito ki gani wallahi prettynmu ce ta dawo.

Airah ta fad'a cikin ihun farin ciki ta dire mug d'in tea akan center table ta rugu suka rungume juna, Nanny Lacey ta fito daga kitchen fuskarta lullu6e da farin ciki, Aneesah da ke d'akinta ta ji lokaci da Airah take ihu had'i da kiran sunan pretty, da sauri ta yaye duvet d'in jikinta ta fito da gudunta, ita ma tana zuwa ta had'e Miyya da Airah ta rungumesu. Gaba d'aya ihunsu ya cika parlour.

"Prettynmu kin dawo kenan ko?"

Airah ta tambaye Miyya a lokaci da suka zauna.
Murmushi kawai Miyya tayi saboda batasan amsar da za ta bata ba.
Sai kawai ta ce.

"Ina Baby Ahlam?"

"Tana barci.

Aneesah ta bata amsa.
Da Nanny Lacey ta kammala arranging table suka yi breakfast a tare, sai lokaci tai k'asa da murya tare da kallon gefen da Aneesah take ta ce.

"Aneey tun zuwana gidannan ban ji motsi Daddy ba ko baya gida ne?"

"Yana bedroom d'inshi kinsan azumi yake yi bai cika saukowa k'asa ba, sai lokaci bud'a baki yake saukowa.

Ajiyar zuciya Miyya tayi ko kusa ba za ta iya jure har zuwa lokaci bud'a baki ba sannan ta ganshi, da suka kammala breakfast Airah ta wuce d'akinta tayi wanka Aneesah da Miyya kuma suka shiga study room, Aneesah tana duba wani littafi tayi zurfi sosai yayin da Miyya kan tayi nisa a cikin tunanin Daddynta sai wasa take da bango littafin hannunta, sake kallon gefen da Aneesah take tayi sai taga hankalinta yana ga karatun da take yi, sai kawai ta mik'e ta fice daga room d'in koda ta fito babu kowa a falon k'asa, cikin sauri ta haura upstairs kaitaye apartment d'inshi ta nufa ta wuce falo na d'aya da na biyu ta kutse kai a Master bedroom d'inshi, tana tura k'ofa dai-dai yana fitowa daga wanka yana daure da towel.
Kamar wacce aka jefo daga sama haka ya ganta don shi har ta tsorata shi ko kusa bai yi zaton ganinta a dai-dai wannan lokaci ba. Shawarar Dadda ce ya dauka shine hana shi zuwa gunta dama Dadda ta gayamishi yana zaune zai ga Miyya ta kawo kanta da farko ya dauko zanceta ne kawai na tsofa ashe maganarta za ta zama gaskiya.
Kallo-kallo suka shiga yi wa junansu sosai ta ga ya yi rama sai d'an uban kyau da kwar jini da ya k'ara yi mata, da gudu ta rugu ta fad'a k'irjinshi kyakkyawar runguma tai mishi ya rasa tsakani ita da towel d'inshi wa zai kama, da kyar ya yi jaruntar rik'e su dukka biyun.
K'ok'arin cire ta yake yi daga jikinshi yana murmushi, ita kuma sai k'ara mak'alk'ale mishi take yi tana kukan shagwa6a cikin kunnenta ya rad'a mata.

"Pretty azumi nake yi kada ki 6ata min azumi mana, ni kaina rungumar nan bata isheni ba amma a duba yanayin da azumina zai shiga"

Da sauri ta janye jikinta tasa gefen hijabinta ta rufe fuskarta tana dariya sai da ya gyara d'aurin towel d'inshi kana ya rik'o hannunta suka zauna a gefen gado, kallonta yake yi fuskarshi ta cika da yalwatatce murmushi.

"Nayi mamaki ganinki a gidannan pretty ban yi zato za ki dawo gareni cikin sauki ba?"

"Nima ban yi zaton zan dawo cikin sauki ba sai gashi zazzafar soyayyarka ta hanani sukuni, basan lokaci da na saci jiki na zo gidanan ba.

Ta fad'a tana kallonshi tana dariya mai ban sha'awa, yai sauri kai mata kiss a kumatunta na dama kafin ya mik'e ya shiga dressing room ya shirya cikin White colour d'in jallabiya koda ya fito ta cire hijabin jikinta, tana tattara masa takardu da ya zubar ko ina a cikin d'akin.
Ganinta kawai da Azaad ya yi ya ji wani irin sauyi a jikinshi ya k'ara tabbatarwa da Miyya ita ce cikon farin cikinsa.
Tun shigarta d'akin bata sauko k'asa ba tana manne da Daddynta, shi Kuma lokaci zuwa lokaci yake tunatarda ita azuminshi ita kan abin dariya yake bata.
A can gidan kuma hankalin Miss Gambella ya tashi matuk'ar da ta nemi Miyya ta rasa, gudun kada tashi hankalin Dadda yasa bata yi saurin fad'a mata ba. Sai kawai ta kira Hakeem shi kuma Hakeem ya kira Azaad a lokaci ya yi matashin kai da ciyoyin Miyya ita kuma tana damuk'ar sumar kanshi wai kitso take yi mishi shi Kuma sai biye mata yake yi kamar wani k'aramin yaro. Yana gani Hakeem ya kira shi yasan kwanan zance yana yin picking up yasa dariya.

"Aslamiyya ta dawo kuma kuna tare kenan?"

Hakeem ya fad'a shi ma yana dariya.

"Ya aka yi kayi saurin ganowa, Hakeem kodai kana duba ne bansaniba?"

"Ba ko d'aya kawai dai wannan dariya nasan kana yi ta ne kadai idan kana tare da Aslamiyya.

"Lallai ka fahimce ni abokina fiyye da yadda na fahimci kaina, banida kalamar da zan furta wajen gode ma. Ina maka fatar alkhairi abokina ka yi addu'a Miyya ta sami ciki mu ka yi ma takwara.

Sosai Hakeem yake tintsirar dariya kafin ya ce.

"Ba shakka Aj abin naka ya girmama to kadai tuna da kana azumi gudun kada kayi abin ashar!

"Mtss! Ka dauka nima jarabbabe ne irinka?"

"Ai abokin barawo, barawo ne ni da kai kwayar sama ce ke dukan ta k'asa, ka kuma tabbatar ka kira Miss Gambella ka fad'a mata inda ka sakad'e mata 'ya ni dai ba ruwana.

Kafin Azaad ya sake yin magana Hakeem ya datse kiran, ya kalli Miyya ya ga ta turo baki cikin shagwa6a ta ce.

"Ni ma ba ruwana ka kirata ka fad'a mata na dawo gidan mijina kenan ba kuma abin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login