Showing 69001 words to 72000 words out of 91651 words

Chapter 24 - Azaaj Junaid Book 1 Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

623

mata Azaad yana masifar so abinci gargajiya shiyasa ta duk'a masa tuwo semolina da miyar agusi, hadi da farfesu kayan ciki. Gani an fara Kiran sallar magarib yasa ta barma Nanny Lacey ta zuba a warmers ita kuma ta koma d'akinta ta shinfid'e Ahlam da tai barci sannan ta shiga wanka, ta shirya cikin Australian gown mai dauke da spaghetti hands ta zura dogon hijab tayi sallar magarib da isha'i, da ta kammala sallah ta zauna ta tsantsara kwalliya ta dauk'ar hankali bakinta ya sha pink colour din lipstick ta tattara gashinta ta daure da katon hairband tayi mishi style din doughnut. Jikinta na fitar da k'amshin Arabian perfumes, ta k'ara gyarawa Ahlam kwanciyarta kafin ta bud'e k'ofa ta fito zuwa downstairs parlour.
Madam Salima ta fito daga d'akinta ta nufi na Aneesah tana turo k'ofa Aneesah da ke zaune akan praymat din da tayi sallah, ta zabga tagumi ta juya a razane tana kallonta da idanuwanta da suka cika da zallar tsoro da fargaban zuwan nata d'akinta, gefen gadonta Madam Salima ta nema ta zauna.

"Taso ki zauna anan Princess inaso nai magana dake"

Madam tayi magana tare da pointing kusa da ita, 6oyayyiyar ajiyar zuciya Aneesah tayi, ta mik'e jiki ba lakka ta zauna inda madam ta nuna mata.
Saida ta riko hannu Aneesah cikin nata kafin ta marairace murya ta hanyar cewa.

"Princess kin ga irin butulci da Daddynku ya yi min ko?"

"Uhm!

Aneesah ta fad'a tamkar za ta fashe da kuka, har ga Allah bataso mommy ta ji haushinta bata kuma tunani za ta iya supporting d'inta ko ta furta wata mummunar kalma akan Daddynta ba. Saboda yanzu ta fahimci mommy ce mai laifi duk ita ce ta janyo sanadin rabuwarsu.

"Princess!

Ta kira sunanta gani kamar hankali da tunaninta sun karkata wani gun daban, ba a wurinta ba.

"Na'am mommy!

Aneesah ta amsa cikin taushin murya yayin da hawaye da take 6oyewa suka silalo a kumatunta, kallon hawaye da ke bin fuskarta Madam Salima tayi tasa hannunta ta d'ago ha6arta.

"Princess ba kuka nakeso ki tayani dashi ba so nake ki kira Daddynku ki fad'a mishi za ki zauna a wurinshi sauran bayani kuma sai kin je can gida zan sanar miki.

Cikin tsananin razana Aneesah ta d'ago da idanuwanta tana kallon mommy, zuciyarta har tana wani irin bugawa. Wato wata manufa take so ta cimma shiyasa za ta tura ta can gidan.

"Ni kuma mommy miyasa zan je can d'in ni bana da ra'ayi zama dasu?"

Ta fad'a cikin rawar murya tare da sark'ewar lafazi, zare mata idanuwa Madam Salima tayi kafin ta bata amsa ta hanyar cewa.

"Saboda ki dai-daita tsakanina da Daddynku ko bakyaso ya dawo gareni ne?"

"Inaso mommy amma Dan Allah kada ki cilastani zuwa can gidan banaso na fiso na zauna kusa dake.

"Ke!

Madam Salima ta katse ta hanyar daka mata tsawa tare da fizgo k'afadarta tamkar za ta 6alla mata ita.

"Banaso shanshanci banza da na wofi princess idan kika zauna anan uban me za ki tsanana min?"

"Mommy ki yi hak'uri wallahi ba zan iya abin da kike so sakani ba, duk da bansan menene shi ba, kisani Mommy Ina sonki, burina a kullum ki kasance cikin farin ciki sakoni a sha'ani zamantakewarku da Daddy ba dai-dai bane, idan har Daddy yana da ra'ayi sake zama dake ba sai kin yi amfani dani ba ta wata siga da bata dace ba.....

"Ya isa princess nace miki ya isa haka wad'annan maganganu da suke fitowa daga bakinki, uban waye ya koyar da ke su fad'a min uban waye ya dora ki akansu domin ba su yi kama da tunaninki ba?"

Kuka Aneesah ta fashe dashi sai faman girgiza kai take yi, yadda kuka ya ci k'arfinta yasa ta kasa magana. Cike da zallar 6acin rai Madam Salima ta tureta ta fad'i kwance akan gado ta mik'e tsaye ta nuna ta da yatsa.

"Muddin ba ki yi abin da nasaka ki ba ki manta da kina da uwa daga yau sai ki fara tunani wannan k'aramar yarinyar sa'arki da ubanki yake kirarin matarsa ce ta maye miki gurbina"

"Mommy please karki fad'i haka ke mahaifiyata ce ba wacce za ta iya cike min gurbinki a wurina, mommy Dan Allah ki saurareni saboda na faranta miki rai na k'i bin Daddy kin kuma san halinsa sarai baya daukar reni, idan har naje mishi da zancenki Allah ne kadai yasan irin hukunci da zai dauka akaina. Dan Allah mommy ki cire ni cikin wannan lamarin.

Cewar Aneesah cikin muryar kuka ta taso da nufin ta riko Madam Salima, kafin ta iso wurinta ta bud'e k'ofa ta fita abinta.
Komawa Aneesah tayi ta kwanta ta ci gaba da shasshekar kuka, a k'asan zuciyarta tana mamakin wacce irin mahaifiya ce garesu mai masifar so kanta da yawa ita kwata-kwata damuwarta ita ce damuwa duk wanda zai shiga damuwa bai shafe ta ba.
Bayan su Azaad sun kammala sallah suka fito daga masallaci kaitsaye k'ofar gidansu Miyya suka nufa, gidan nan yadda Azaad yasan shi duk da sau d'aya ya ta6a zuwa gida sai yaga ya lalace fiye da farkon ganinsa dashi. D'aya daya daga cikin yaran Baffa Sani ne ya fito daga cikin gida, suka aika shi yai musu sallama da Baffa bai dauki dogon lokaci ba sai ga shi ya fito tare da Baffa.
Kallo guda Baffa Sani yai musu ya sheda su daure fuska ya yi don yana tunani ko wani abu ne yafaru da su Miyya yadda suka rabuda yaran ko kad'an baya fatar su sake dawo mishi gida.
Bayan su mik'a mishi hannu suka yi musabaha, kana Hakeem ya zarce da cewa.

"Baffa wata muhimmiyar magana ce ta kawo mu gunka idan da hali ka ba mu damar shiga daga ciki mu tattauna saboda bai dace mu yi ta tsayuwa a k'ofar gida ba.

Ba don ran Baffa Sani yaso ba yai musu iso zuwa 6angare Dadda, ita kanta Dadda ta sheda su shiyasa tai sauri tashi daga kishingid'e da take batada wadatattaciya lafiya kwananan ciwo ya sako ta gaba, sai kuma ga Azaad da Hakeem fatanta Allah yasa ba dawo mata da 'ya'yan arniya nan za su yi ba. Duk sai tayi kici-kici da fuska ta kalli Baffa Sani ta ce.

"Sani lafiya ka shigo min da k'artti a tsakar dare nan?"

"Dadda ba ki sheda su bane mijin Aslamiyya ne tare da abokinshi?"

"Mijin Aslamiyya k'ani ubana ne da za ka shigo min dashi falo kaitsaye batare da neman izzina ba?"

Kafin Baffa ya bata amsa Hakeem ya riga shi ta hanyar furta.

"Allah ya ba ki hak'uri Dadda ba wani abin tashin hankalin bane ya kawo mu, ki taimaka ki ba mu aron lokacinki kad'an magana mai matuk'ar muhimmanci ce ta kawo mu.

Sai da Dadda ta galla-galla musu harara kafin ta ce.

"Ku yi gaggawa fad'ar abin da ya kawo ku ni barci nake ji.

Murmushi Hakeem ya yi yayin da Azaad sai faman bin ta da idanuwa yake yi, dattijuwa ce mai cikar kamala ya rasa dalilinta na dorawa su Miyya karan tsana.

"Dadda Dan Allah ki taimaka ki ba mu cikkake tarihi iyayye Aslamiyya.

Shiru Dadda tayi kafin idanuwanta su ciciko da hawaye, cikin sanyi murya ta ce.

"Mijina margayi malam Abubakar ladan shahararen malamin addini ne, mun yi aure saurayi da budurwa na yi haihuwa kusan sau biyar suna mutuwa sai Usman mahaifin Aslamiyya ne ya rayu, sai da ya shekara goma kafin na sake haifar Sani daga kansu Allah bai sake bani haihuwa ba.
Daga Usman har Sani sun taso cikin nagartattaciya, tarbiyya Allah ya yi wa Usman fasaha da baiwa ta zane tun shi na yaro yake zane-zane musanmman motaci da gidaje, usmanu yaro ne natsatsi gashi da hak'uri da matuk'ar wahala ka ga abokin fad'ar shi. Shiyasa malam ya dauke soyayyar duniya ya dora akanshi, Cikin hukunci na ubangiji yana kammala karatun sakandire d'aya daga cikin masu kud'i da ke zuwa neman addu'a wuri malam ya nema mishi scholarship ya sami gurbin karatu a London. Bayan ya kammala karatunshi yai nasarar samun aiki a wani kamfani k'era motoci a can London da farko malam bai so ya kar6i aikin ba, amma gani usman yana da sha'awa yasa ya amince mishi.
Duk bayan shekara guda Usman yake kawo mana ziyara wani zuwa da ya yi sai gashi ya taho mana da babban tashin hankali, wanda ya rusa farin cikin ahalinmu ya jefa mu cikin k'unci. Arniya ya zo mana da ita har da 'ya a matsayin matarshi da 'yar da suka haifa mai shekaru uku da haihuwa, ashe tsawon shekaru hudu kenan da ya yi aure bai fad'a mana ba. Karka so ka ga yadda muka tashi hankula mu ta sanadiyar hakan ne malam ya yanke jiki ya fad'i ya had'u shanyewar 6arin jiki, wata malam uku yana jinya kafin Allah ya kar6i ranshi. A gaskiya tun lokaci naso Usman ya datse duk wata alak'a da ke tsakaninshi da wannan kafira yarinya amma yak'i duk da kuwa yadda nakai da nuna mishi 6acin raina. Haka na hak'ura na zuba mishi ido saidai daga matar tashi har 'yarshi Aslamiyya na tsane su kiyayya nake nuna musu ba ta wasa ba. Bayan wasu shekaru matar Usman ta sake haifar tagwaye duka mata saidai guda d'aya ta zo da matsala a zuciyarta, hakan bai sa na tausaya musu ba sai ma fatan mutuwa nake yi wa yarinya.
Amrah da Amal suna da shekaru hudu a duniya Usman ya had'u da ajali ciwon Amal ne ya tashi cikin dare kuma maganinta ya k'are, gashi ana shek'a ruwan sama, don ba zan manta ranar talata ne uku ga watan hudu shekara ta dubu biyu da takwas yadda ya ga ciwon nata ya yi tsanani yasa ya fita ya siyo mata magani ana ya had'u da wani direba marar imani ya buge shi da mota kuma ya gudu, tun anan wuri Allah ya kar6i ranshi, bayan kwana uku da rasuwarsa matarsa ta zube mana yaranshi ta gudu har yau ba mu sake jin labarinta ba.

Azaad yana jin date din da Dadda ta anbata hankalinshi yai mugun tashi, wani irin gumi ke feso mishi a sassan jiki, ya runtse idanuwanshi gam yana jin maganganu Dadda suna mishi kai komo a cikin kwakwalwarshi.
Kusan a tare Hakeem da Baffa Sani suka sauke ajiyar zuciya, a wannan karon ma Hakeem ne ya yi k'arfin halin fad'ar.

"Dadda a labarinki ba mu ji kin kira sunanta ba ko suna kasar da take, ko a can London din take?"

Shiru Dadda tayi tana sharar hawaye da ke bin kumatunta, saboda mutuwar Usman ta dawo mata sabuwa fil, ji take tamkar yanzu ne al'amarin ya faru, gani ba za ta yi magana ba yasa Baffa Sani ya dubi Hakeem ya ce.

"Sunanta Roseline 'yar asalin k'asar Ethiopia ce....
5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004


36...


Duk dogon bayani da Baffa Sani yake yi Azaad bai fahimci ko d'aya ba, saboda hankali da tunaninshi sun karkata wani gun daban.
Magana Hakeem yake mishi bai amsa ba saboda ya yi zurfi a tunani, saida Hakeem ya zugure shi
a k'afa sannan ya yi firgigit kamar wanda ke barci aka watsa mishi ruwan sanyi a fuska, numfashi ya ja tare da rintse idanuwa yana dafe goshi. Koda ya bud'e idanuwanshi har Hakeem ya mik'e tsaye, yana kallonshi da alama yana karatar sauyawarshi a lokaci guda ne. Jiki ba lakka ya mik'e suka yi ma Dadda sallama, Baffa kuma ya rako su har zuwa k'ofar gida kana yai musu sallama ya juya cikin gida. Har suka shiga mota Mr Richard ya ja motar ya dauki hanyar farmhouse inda Hakeem ya baro motarshi, Azaad ya kasa dawowa cikin natsuwarshi.
Sannu a hankali Hakeem yake yawo da idanuwanshi akan fuskar Azaad, kafin ya yi gyaran murya ya ce.

"Ya aka yi ne Aj tun d'azu na fahimci sauyawarka a lokaci d'aya kalli yadda zufa yake karyo maka duk da ac da ke cikin motar nan a kunne yake, jikina ya bani akwai abin da ke damunka?"

Azaad ya ja dogon fasali yayin da bugun zuciyarsa ya tsananta. Ya bud'e bakinshi da ya yi matuk'ar yi mishi nauyi ya ce.

"Hakeem akwai matsala kuskure da na aikata a baya ne yake shirin dawo min a dai-dai lokaci da na fara sabuwar rayuwa.

"Ban fahimci abin da kake k'ok'arin fad'a ba, Aj kayi min magana da yare mafi sauki fahimta.

"Shin za ka tuna mutumi da na ta6a bugewa da mota shekaru goma sha hudu da suka gabata, wanda na bi shawararka na barshi kwace cikin jini, wanda har yanzu na kasa goge hoton al'amarin a cikin zuciyarta,?"

"Innalillahi wa'inna illaihim raji'um.....Aj kada ka ce min wannan mutumi shine Usman mahaifin Aslamiyya?"

"Shine Hakeem domin date din da Dadda ta fad'a da kuma lokaci da al'amarin ya faru, ya yi dai-dai da faruwar wancan al-amari ko shakka babu ni na kashe mahaifin Aslamiyya.

"Daina fad'ar haka Aj ba da gangan kayi ba tsautsayi ne kuma ko a wancan lokaci mun koma wuri da hatsarin ya faru, aka ce mana bai mutu ba har an kai shi hospital ba irin neman da ba mu yi shi mishi ba kusan duk wata asibiti da ke kusa da wuri mun je nemanshi har wacce ke nesa da wuri mun je amma ba mu yi nasarar ganinsa ba. Daga k'arshe dole muka hak'ura.

Idanuwan Azaad ya suka yi jajir gaba d'aya jijiyoyin kanshi suka tashi, ya dafe goshi sai faman furgar numfashinsa yake yi, ya shiga tashin hankali marar misaltuwa, duk yadda Hakeem yake kwantar mishi da hankali ta hanyar dad'ad'd'an kalamai hakan bai rage radadin da yake ji a zuciyarshi ba.

"Aj please ka manta da wannan a....

"Ya isa Hakeem!

Ya dakawa Hakeem tsawa ya nuna shi da yatsa, tare da zazzare manyan idanuwanshi zuciyarshi na tuk'uk'i ya ci gaba da fad'in.

"Na sani Hakeem tsautsayi ne amma akwai gangaci domin da a wancan ranar ban bi shawararka ba, na kai shi hospital da watakila ya rayu da rayuwar 'ya'yanshi bata tagyara ba. Duk abin da ya faru dasu Aslamiyya hakkinsu yana rataye a wuyana, me kake tunani zai faru idan Aslamiyya tasan cewa nine na kashe musu mahaifi nine sanadi shigarsu kunci da maraici?"

"Aj nasani mun aikata babban kuskure a baya kuma har gobe kana nadama akan hakan, ni fa tun farko haduwa ta da Amrah na ji a jikina akwai wani 6oyayyen al'amari a tsakaninmu. Saboda haka yanzu ba lokaci dorawa juna laifi bane ka natsu mu nemo mafita.

Murmushi takaici Azaad ya yi saboda gani yake yi muddin labari nan ya fita, Miyya za ta guje shi, abin da baya fatar faruwar shi.
Duk yadda Hakeem yake kwantar mishi da hankali ji shi kawai yake yi ba don maganganu shi sun yi tasiri a wurinshi ba. Da suka iso farmhouse kasa fita daga mota Hakeem ya yi sai ci gaba da rarrashinshi Azaad yake yi.

"Dare ya yi Hakeem ka tafi gida mu jira zuwa wayewar gari, kafin mu san abin yi.

Azaad ya fad'a ba tare da ya kalli gefen da Hakeem yake ba, bud'e k'ofar mota Hakeem ya yi ya fita jikinshi ya yi matuk'ar sanyi shi kanshi yana kwantar wa da Azaad hankali ne kawai amma yasan akwai gagarumar matsala ba kad'an ba.
Miyya ta kasa zaune ta kasa tsayi lokaci-lokaci take janye curtains din window bedroom din Azaad ta leka compound ko za ta hango motarshi ta shigo ta rasa dalili da yasa take jin matsananci fad'uwar gaba, a wannan karo da ta janye curtain din kasa sakewa tayi sai kawai tayi tsaye, tana kallon securities din gida dake kai komo domin tabbatar da tsaron gidan.
Tana gani an bud'e gate tun kafin ta hango motarshi ta sauke ajiyar zuciya, domin jikinta ya bata shi din ne. Kasa dauke idanuwanta tayi da barin kallon gate din har sanda Mr Richard ya yi parking ya fito ya bud'e mishi k'ofa, kafeshi da idanuwanta tayi yana 6acewa ganinta tai maza ta saki curtain ta 6oya a ciki, cike da rashin kuzari ya turo k'ofar d'akin nashi. A can k'asan makoshi ya yi sallama duk da yana da tabbaci babu kowa a d'akin.
Saida ta ga ya zauna a resting chair yana cire takalmin k'afarshi kasancewar su rufaffi cikin sand'a ta fito daga ma6oyarta, tana zuwa ta rufe mishi idanuwa da tafin hannunta tare da kwantar da k'irjinta a gadon bayanshi, wani irin gundari sanyi dad'i ya ji yana bin sassan jikinshi, ya ja dogon numfashi tare da saukewa cikin taushin murya ya furta.

"Prettyn Daddy!"

"Uhm...Daddy ya aka yi ka gano ni nan take?"

Ta fad'a cikin shagwa66iyar muryarta tare da cire tafin hannun nata daga idanuwanshi, ta sakala su a wuyanshi ta turo fuskarta ta gefen wuyanshi kumatunta yana gogar nashi. Yatsanshi yasa yana zagaye tattausan lips d'inta, kafin ya bata amsa ta hanyar cewa.

"A duk lokaci da prettyna ta zo kusa dani koda idanuwana ba su yi tozali da ita ba bugun zuciyata zai tsananta hakan zai tabbatar min da tana kusa dani balle kuma tattausan tafin hannunta ya sauka akan fatar idanuwana, pretty ke ta daban ce a cikin zuciyar Daddynki.

'Yar k'aramar dariya tayi mai ban sha'awa tare da fad'in.

"Daddy wai Ina ka shiga ne Allah ba ga yadda na tashi hankalina ba da naga 10 o'clock ya yi ba ka dawo gida ba, ka ga yadda gabana ya dinga fad'uwa kuwa?"

Saida ya yi murmushi mai sauti tare da jawo ta ta fad'o kanshi, ta saki ihu saboda ya yi mata bazata sam bata zaci zai iya jawota ba, rungumeta ya yi ya tura hancinshi cikin gashinta yana shakar k'amshin man gashi da tai amfani dashi, sai wani lum-lumshe idanuwa yake yi kamar mai jin barci.

"Miyasa za ki tashi hankalinki prettyna bayan kinsa duk nisan da nayi kina cikin zuciyata?"

"Ba za ka gane bane Daddy na damu da kai sosai da son samu ne ko nan da k'ofar gida banaso ka fita, na fiso ka zauna nai ta kallon wannan kyakkyawar fuskar taka da bana gajiya da kallonta.

D'ago ta ya yi ya zuba mata rikitattun idanuwanshi, yana kallon cikin idanuwanta, tai saurin kawar da kanta tare da yunk'urawa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login