Showing 33001 words to 36000 words out of 93107 words

Chapter 12 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete

friends nasa girki"yanata mun masifa nayi nagama da k'arfe 12 zasu iso"kinga so nake zuwa 10 am mu shiga kitchen"idan da matemaki zanyi sauri"Amma ni kad'ai zan iya kai 1 pm ma ban gama ba"okay insha Allah zuwa 10 d'in zan iso Allah yasa masu gadi su barni na shigo"yaya bilal yakawoki mana"to shikenan"ummu na k'ok'arin kashe wayar sa'ada ta shigo parlourn"tasha gayunta cikin doguwar riga ta lace lemon green"ta yafa siririn mayafi"duk wanda yasan big man yakalleta yasan jininsa ce ita sbd yanayin da sukeyi kuma itama tanada kyau"baby kin dawo?"Eh Anty"yaya sadeeq yana gaidaki"waye haka nan?"yayan Anty leemart ne"okay ina Amsawa"kinsan ko Anty? yaya sadeeq yana ji dani"dana nuna bana son Abu zai dena"kuma yace nice babbar k'anwarsa"murmushi ummu tayi tace"ya kyauta sosai"Amma kamata yayi gabansa ki rage surutu"shima yayanki kinsan besan yawan surutu"balle kin fara zama budurwa"ita kuma budurwa nuna Aji da kamun kai aka santa dashi"komai kiyi cikin nutsuwa kina jina?"sa'ada tayi shiru Alamar tunani sai kuma tace to Anty zanyi duk Abinda kikace"yauwa babyn mu"yanzun ki had'a tea ki zuba Abinda kikeso saiki ci ko?"kona had'a miki?"ah ah Anty zan had'a da kaina"to shikenan"dg haka sukayi shiru" sa'ada ta had'a tea ta zuba Abinda zata buk'ata ta zauna tana break fast"big man yasakko down stairs d'in da Alamar rashin mutunci samqn fuskarsa"yana sanye da kayan data fiddo masa"Amma ganin sa'ada saiya had'iye masifar daya fito da ita"ummu na lura dashi murmushi yasub'uce mata ta kauda kanta"yakafeta da ido yana jifarta da kallon zamu had'u...my hand some harka gama saka kayan?"ta fad'a tana kallon dagayen k'afafuwansa jajir kamar baya taka k'asa"baki gogemun takalmin ba"sannan.... kidai taso muje ciki! gabanta yafad'i"ta marairaice fuska gun cewa "gafa baby nan tana break fast na barta ita kad'ai??"yana k'ok'arin mgn sa'ada tace"bbu komai Anty kije wajen yayan mana"big man yasaki murmushin mugunta yace"hakane baby tazo tayi Aikin yayanki ko?"murmushi tayi batace komaiba"dama be Ida sakkowa k'asan ba saiya juya ya koma"ummu kuwa kamar tayi kuka ta tashi ta haye upstairs d'in"Atsorace ta bud'e k'ofar parlourn ta lek'o kanta"bbu kowa hakan yasa ta shigo.....hucin numfashinsa taji Abayanta"Ashe labewa yayi"Atsorace taja da baya"yaja tsaki yana nufota"ta zaro ido tana fad'in dan Allah kayi hak'uri nadena wlh"sbd ganin gadan gadan yana biyota"ke Ai marar mutunci sbd ganin sa'ada harda yimun dariya ko?"ah ah wlh"kafad'amun me zanyi? sai nayi"yatab'e baki yana fad'in ki biyoni inkin gadama"dg haka yabud'e k'ofar bed room d'in yashiga"jikinta Asanyaye ta biyosa Abaya"kin fito mun da kaya bbu handkcheef"sannan baki goge takalmi ba"kayan babu turare"baki fitomun da vest da boxer ba"tana dg tsaye jikin k'ofar yayinda shi kuma yana zaune gefen bed yana dannah waya"ina Abinda zan goge takalmin?"sannan gaskiya bazan fito da vest d'in da wancan ba"dariya taso tabashi"Afili saiya koma had'e rai yana fad'in shiyasa nace ke bak'auya ce"ni bbu Abinda zan baki ki goge kisaka d'an kwalinki mana"and last one karki yarda na koma yimiki mgn"batace komaiba sbd itama surutun ya isheta"gefen mirror d'in ta tsaya jikinta nata kirma sbd bata saba kad'aicewa itada namiji ba"shiyasa duk sai tajita Atakure"turaruka kusan kala 3 ta d'akko tazo ta duk'a ina zan fesa??"na riga na saka ki mayarmun da kaya"sannan dallah kimun sauri"batace komaiba ta duk'a gefen takalmin ta zare d'an kwalin kanta tafara gogesu dg sama"Azuciyarta tana jin zafin irin wannan wulak'anci dayake mata"big man kamar Ance yad'ago kansa ya kalleta"idanuwansa suka sauka samqn dogon farin wuyan ta dake jajir har zuwa saman kanta"cikin second 5 yak'are ma gashin kanta kallo yana mamakin tsayinsa"domin yadda ya kallesa ya tabbatar masa da cewa ba attached bane nata ne"sai kuma yaja tsaki sbd ganin to ina ruwansa?"juyowa tayi ta Ajiye masa takalmin tana yafa d'an kwalinta"saida ta nufi k'ofa kafin tace"Anyi maka Abu bbu godiya"sannan ni nayi break fast d'ina sbd ban Ari Ak'idar turawa na Azama kaina ba"idan katashi kayi Abinka kai kad....ganin yana k'ok'arin zai tashi Azatonta biyota zaiyi saita zunduma da gudu"yaja tsaki yana fad'in matsoraciyar banza"dani kike zancen sai kinsan kin gayan magana"yana fad'in hakan yazura takaminsa sawu ciki bak'ak'e"kafin ya tsaya gaban mirror d'in yana taje suman kansa zuwa lallausan zagayayyen sajensa"yad'an yatsina fuska sbd office zai d'an je sai kuma yaje masaukin da bak'insa suke yatafo dasu nan"wayarsa k'arama ya d'auka ya lalubo number d'in kamal yakira"saidai data fara ringing sai Akashe" kusan sau biyu ana kashewa"wata iriyar tsuka yaja yana fad'in ni kamal zai kashewa waya sbd yarinyar nan?"kwafa yaja yabaro d'akin"koda ya sakko down stairs"bbu kowa sai motsin sa'ada da ummu dayaji A kitchen"bebi takan suba yafita"be jima da fitaba tafara bak'i y'an zuwa biki dabasu kaiga tafiya gidaba"kasancewar sa'ada na nan duk wanda yazo zata sanarwa ummu wanene shi"kuma zata cika gabansa da drinks da Abin motsa baki"sbd cikin kayan garan datazo dasu gidan harda "dubulan ,cincin,Alkaki da nakiya"Ahaka itama lawisa ta iso"bata jima ba innah uwani me Aiki itama ta iso"danda nan suka kwab'a cake sukayi"sannan Akayi meat pie da dambun kaji"sai wajen sha biyu saura Aka Aza friend rice d'in"lokacin sun jera komai dining area"har coslow An had'a"an kuma k'ara gyara parlourn"lawisa ta dubi ummu tace"kije sharp sharp ki watsa ruwa ki canza kaya ko dubai Abaya kisaka tunda bak'in turawane"kuma idan yazo zai d'aukeki me tsabta"bawai yadawo yasameki da kayan daya fita yabarki dasu ba"ni zan tsaya nan harta ida"ita kuma baby naga Ai tana parlour ko?"Eh tana can"bara naje d'in to"dg haka ta fita"cikin mintina 15 ummu ta shiga wanka ta fito"tana sakq kaya wayarta tayi ringing"tana dubawa taga sunan *Azzalimu* tayi d'an murmushi ta d'aga wayar"K ! kina nufin saina shigo na kiraki ne sannan kizo ku gaisa?"kun shigo ne ?"bansani ba"kaifa matsalata dakai kenan komai fad'a fad'a"to bazan zoba d'in"Ai na Ajiye muku komai samqn dining table"tana fad'in hakan takashe wayar"Abdallah da tun 12:10 pm suka shigo gidan shida Abokansa" kusan su 12 in hardashi da kamal su 14 kenan"shine yatafi bed room nasa ya d'auki wayarsa yayi kiranta"ransa ab'ace ya sakko down stairs d'in"ga yunwa yanaji sbd beyi break fast ba"Aikuwa yasamu kamal nata seving nasu suna shagwali"turawan cikinsu na magana da turanci"sa'ada kuma na'ajiye musu tray data jero ruwa da lemummuka na kwali A sama"Abokina Amarya ta iya girki sosai kayi dace"cewar wani bature cikin harshen turanci"big man yayi murmushi yaje yaduba basket d'in yazuba Abinda zai butak'ata"yayi zamansa gefe yana break fast nasa"suna hararan juna shida kamal"yayinda sauran ke fira suna cin snacks da drinks"can kuma sa'ada ta shigo da dray d'in Abinci ta Ajiye musu"cikin mintina 30 duk suka yi han'ian suna yaba girkin ummu"sai surutunsu Akeji"lawisa dai da sa'ada suna kitchen d'in suna zaune suna fira"inna uwani na wanke wanke"suna kuma jiyo muryar mazan"sai cewa suke Abdallah yaje ya fiddo musu Amarya"gashi ummu tak'i zuwa"can yadubesu yana fad'in kattin banza kuyi k'asa da murya karku furgitamun mata da wannan muryoyin naku"suka dinga masa dariya"dg k'arshe Abdallah ya mik'e tsaye yanufi bed room d'in ummu sbd yanuna mata bata isa tak'i zuwa kiran saba"zaije yafito da ita ta k'arfin tsiya.....tura k'ofar yayi yashiga"tana zaune gefen bed tana mgn ta chat da shugabar makarantar datake koyawa"d'ago kanta tayi suka had'a ido dashi"gabanta yafad'i tayi k'asa da kanta tana neman mayafin dubai Abayar dake jikinta"saidai ganin yatun karota yasaka tayi saurin mik'ewa tsaye"kanta bbu d'an kwali"gashin kanta datayi parking dg tsakkiyar kanta yanata raito"wai dan Allah meyasa kakemun haka?"bansaniba k'aramar marar kunya"dama kinsan d'azun inada haushinki shine yanzun kika koma wani?"yafad'a yana zare mata manyan idanuwansa"ita kuwa kauda kanta tayi ta matsa jekin window tana fad'in ni bbu ruwana dakai da bak'in naka"haka kikace ?"Eh d'in"d'an murmushi yayi yanufeta"tasaki k'aramar k'ara"ya yatsina fuska be fasa nufotaba"pls zanje wlh"banza yamata ya Ida isowa gabanta"ya rik'e hannun ta guda"saidai tak'i yarda su had'a Ido"kin rainani k'arshe ko?"to zanyi maganinki "zuwa ku gaisa kuma ki d'auka kinma riga kinje"yak'are maganar yana jan tsaki ya fisgo hannun nata daya rik'e"tafara turjewa"tsaki yaja yana fad'in bazakije ba?"toni kacikani mana fisabilillahi"bazan cika d'inba"yafad'a yana fisgota da k'arfi"tasaki k'ara"ya duk'a ya d'auki mayafin rigar jikinta ungo yafa muje"hararar hannunsa da yamik'o mayafin tayi"ki tabbatar saina saki kuka Anjima da dare bayan tafiyar kowa"yak'are maganar yana yafa mata mayafin da hannunsa guda"ita kuma tanata turashi"saida yagama yafa mata mayafin sannan yaja hannunta suka fito dg cikin d'akin"suna fitowa taji muryar su"nutsuwa tayi kanta ak'asa"Abdallah yak'ak'aro fara'ar dole yana yasak'alo hannunsa gefen k'ugunta ta kwanto da kanta agefen kafad'arsa"kamal yabisu da kallo sbd ba k'aramin kyau suka masa ba"saiya gansu kamar masoya"Abdallah yamatso da fuskarsa saitin tata yana fad'in wlh kika mun k'auyanci sai kin sani"rintse idanuwanta tayi da k'arfi sbd jin tsikar jikinta na tashi sakamakon gemunsa daya shafo k'asan wuyanta da gefen fuskarta"ga hucin numfashinsa na sauka gefen hancinta irin wannan soyewa haka Abokina?"cewar kamal da gayya"Abdallah ya janye fuskarsa suka k'araso cikin parlourn"tana d'an murmushi ta musu sannu da zuwa"kafin su zauna kan kujera yana rik'e da hannun ta ta gaidasu tana kallon yadda duk suka b'ata parlourn"sai godiya suke mata da yaba girkin nata"can Abdallah yamata rad'a da cewa"k'arya sukeyi girkin naki beyi wani dad'i ba"murmushi tayi itama tamasa rad'a da cewa"fad'i gaskiya dai malam kaji girki ya maka dad'i.....Amm big man da Alama Amatse kake bara mu wuce kawai"cewar kamal yana dariya sbd yasan yashak'ar da Abdallah"Aikuwa yashak'a d'in"saidai gaba d'aya kuma duk yaji wani iri sadda ummu ke masa mgn cikin kunne"gaba d'aya tashi tsaye duk sukayi"ummu ta musu fatan Alkhairi"Abdallah yatashi zai bisu"ta rik'e masa hannu tana shagwab'e fuska ita inaje yabarta?"duk ta fad'a cikin harshen turanci"bazan jimaba fa zan dawo my heart beat"miye na damuwa?"rakasu zanyi fa"zokiji wata mgn"yafad'a zai janyota jikinsa sai tak'i yarda k'irjinta na bugawa tazura Aguje zuwa bed room d'in ta"kamal nata kallonsu ya fahimci Abdallah bazaima ummu wuyar kamawa ba muddin tasan Abubuwan jan hankali kuma tana masa"Abdallah kuwa harara yasakarma kamal yana fad'in yaka mata kadena gulma sbd mata aka sani da ita"Abin Ayi gulmar taka kayi shiyasa nayi"yafad'a yana yin gaba"duk suka fita"saida ummu taji fitarsu sannan ta fito dg cikin d'akin tana sakin Ajiyar zuciya"dan gaba d'aya tsoron Abdallah yatab'a ko hannunta takeyi"saima taji har k'amshin turarensa tanayi..... k'awata! taji muryar lauwisa Abayan ta"hararanta ummu tayi tace"shine sai kukak'i fitowa kukayi zaune kitchen?"ina babyn?"tana can kitchen d'in"nidai bara na kwashe kayan n kaima mai Aiki a wanke su"saina gyara miki parlourn natafi gida"lallaima tafiya gida bbu Inda zakije saida yamma"wlh ummah fad'a zatayi ummu ki gane mana"batace komaiba" Atare suka kwashe kayan suka kai kitchen"sannan suka gyara parlourn suka zauna suna cin Abincin"bayan sun gama sa'ada ta tafi gida"lawisa kuwa sai bayan sallar la'asar ta tafi gida....

Da dare.....✍️


wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

❤‍🔥❤‍🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤‍🔥❤‍🔥

*27&28*


.........da dare wajen k'arfe 8:16 pm"ummu ce zaune A parlourn tana kallon TV"tana sanye da doguwar riga ta bacci Ajikinta pink colour"saita sakq hijab milk iya gwiwa marar nauyi...Azahiri zaka d'auka hankalinta na wajen kallon"Amma A bad'ini tana duniyar tunanin zuwan da goggo murja tayi d'azun da yamma"Ankawo mata duka kayan lefenta harda motarta"hjy yaya nata masifa ta raina Abinda Aka bata" wai turmin zani guda kad'ai Aka bata Acikin kayan kala 100 na jikarta"....k'aramin tsaki ummu tasaki"tana jin tsanar kakar tata Azuciyar ta"Afili tace"ni kaina bazan tab'a masa kayan lefe ba"zqn barsu Ajiye sbd gudun yace Abiyashi wata ran ....shiru tayi k'irjinta na bugawa sakamakon jin motsin big man dake bud'e k'ofar da key"nutsuwa tayi ta maida hankalinta wajen kallo"sanyayyan k'amshin turarensa yafara yimata sallama kafin shi uban gayyar ya shigo"cike da shan k'amshi ya shigo yana yin sallamar adak'ile"sai cin magani yakeyi"yana sanye da jallabiya dark brown"da Alama dg masjeed yake"ummu na lura dashi ta wutsiyar ido"saidai tayi bala'in d'auke masa kai"da nuna kamarma batasan dashi ba"dining area yasaci kallo yatab'e baki"saidai yaji haushin yadda ta masa banza"sbd koma miye k'asa dashi take"dining area d'in yanufa yaja kujerah ya zauna"itama saita taso tazo ta zauna"Ahankali tace"sannu da zuwa! be Amsaba saima tsaki yaja yana fad'in ke karki koma samun hijab d'in gulma Agidana"miye zaki b'oyemun a wannan k'azamin jikin naki?"yak'are maganar yana bud'e warmers d'in Abincin"wasu tsakin yakoma ja yana had'e rai"kusan second 5 yana kallon Abincin kafin yadubeta yace"shiyasa nace ke y'ar k'auye ce"waya ce ki dafamun tuwo Amatsayin dinner??"ummu dai kanta Ak'asa tama kasa mgn"bakiji ne??"yafad'a cikin daka tsawa"kayi hak'uri bansan baka soba"kije ki had'amun coffee idan kin gadama"ki kamun ina d'akina"sauran ki cikamun sugar"batayi mgn ba ta mik'e tsaye ta nufi kitchen"ya girgiza kansa yana tab'e baki"kafin ya mik'e tsaye ya haura upstart"kai tsaye bed d'insa yanufa"yana shigowa yafara dube duben Inda ya Ajiye kayan shaye shayensa"can kuma saiya zauna gefen bed sbd ransa yabashi ummu ta gansu ta d'auke"idan kuwa ta salwantar dasu shine kawai yasan miye zai mata....yana wannan tunanin ta turo k'ofar ta shigo cikin sanyin jiki da sallama Ahankali"had'e girar sama data k'asa yayi be Amsa sallamar ba"wanda sosai ummu ta tsorata da yanayinsa data saci kallonsa"hakan yasa bata koma gigin yadda ta kallesaba"gefen dogayen yatsun k'afarsa ta duk'a ta Ajiye cup d'in ta mik'e tsaye da nufin ta fita! ke! dallah zauna na gama koda Akwai Aikin dazaki mun"nanma batayi musu ba ta rakub'e gefen bango tayi k'asa da kanta....K bana son munafurci! zaki d'ago kanki ki zauna kan sofa ko kuwa??"nidai nan yamun Ai"baraki tashi ba?"batayi mgn ba ta koma samqn sofa ta zauna"yaja tsaki afusace yace"ina kayan shaye shayen dana Ajiye samqn bed side drower?"yafad'a ko Ajikinsa yana tsareta da Golden Eyes nasa dayake yawan lumshesu"d'ago kanta tayi da mamaki tana tsurawa saman kyakykyawar fuskarsa ido"kallona zakiyi ko tambayata zaki Amsa??"banga Abinda zan kallah ba Anan"saidai kuma kafin na Amsa dan Allah kasanar mun kaine ke sha??..... what??"yafad'a da k'arfi"yaushe kika rainani har haka?"okay bara kiji da hujja nike sha"ko Akwai Abinda kika isa kimun ko kuwa kin isa ki hanani shane??"ko kuwa kin d'auka b'oye miki zanyi?"bana munafurci ina fad'in gaskiya ko A gaban waye"tashi ki fiddomun su Inda kika mayar mun dasu kona tattakaki Anan.... yafad'abbu Alamar wasa yana k'ok'arin tashi tsaye"jikinta na b'ari itama tafara k'ok'arin tashi cikin rawar murya tace"kayi hak'uri na zubar das....kin zubar kikace??"sbd bakisan zafin neman kud'i ba shine kika zubar mun da kaya?"to bari kiji bazan yi Asara ba"jikinki zai gaya miki kuma zakiyi Aikin kud'insu gobe"yak'are maganar yana shan gabanta"tayi baya da sauri"yabiyota yana binta da mugun kallo ya d'aure fuska sosai"tana ja da bata tana fad'in dan Allah kayi hak'uri na tuba"sannan kaji tsoron Allah be kamata kana shaye shaye ba da mutuncinta da komai"idan mutane suka san kana shaye shaye to meye.....K! kin isa ki nunamun yadda zanyi ne,ko Anfad'a miki ina neman shawaranki y'ar haka dake ne??"yak'are maganar yana Ida biyota ta dangane jikin gini"ya matsota sosai har jikinsu na gugar juna"yasa hannunsa ko wane gefe datake tsaye yakare sbd karta gudu"ita kuwa jikinta ne ke kirma"ina zakije?"yafad'a cikin cool voice yana lura da yadda ta tsorata"dan Allah kay..... shiiiiittt! yafad'a cikin tsawa"da sauri ta nutsu"ya fisgo hannayenta duka biyun yarik'e gam"ya d'auki kusan mintina 2 kafin yace"kin gayamun magana son ranki d'azun sbd nace kizo ki gaisa da friends d'ina ko?"da safe ma kin mun yanzun kuma kinmun karambani"to duk zanyi maganinki yanzun"yafad'a cikin taushin muryarsa"ta rintse ido da sauri"yasaka hannunsa guda yafara d'allar mata lips da dogon hancinta"tanata k'ok'arin kauda kanta da juye juye"Amma yamata ruk'o bana wasa ba"gabanta fad'uwa kawai yakeyi sbd har hucin numfashinsa tana ji "tun tana k'ok'arin kaucewa da juye juye harta daina"sai hawaye da keta zubowa samqn baby face nata ta kama ido ta rufe"cikin y'an mintina lips nata sukayi jawur suka kumbura"shima hancin nata yana mata zugi"saida yagaji dan kansa yacika mata hannunta"yana jan tsaki kamar zai huda harshensa yace"ya turata da farki yace"get out! Da sauri ta bud'e idanuwanta tanata kuka gwanin ban tausayi ko kallonsa bata yiba ta fita da gudu dg cikin d'akin"yaja tsaki ya zauna gefen bed d'in ya fara shan coffee d'in"sai bayan yagama sannan yafito yaje yabawa masu gadi Abincin data girka musu"yakashe hasken main parlour yaje yayi shirin kwanciya bacci.....
Ummu kuwa tasha kuka sosai sannan tayi wankan wajibi sbd bak'onta yatafi"shafa'i da wuturi tayi sannan ta kwanta ranta ab'ace"tana tunanin wane irin mugun mutum ne Abdallah"Ahaka bacci ya d'auketa.....washe gari tana idar da sallah ta nufi b'angaren sa tafara gyarawa"saidai gaba d'aya fuskarta bbu walwala ko kad'an"idanuwanta sunyi jajir sunyi kumburi"hakama lips nata"tanata tuna y'an gidansu tana Aikin"bayan ta gama da part nasa ta fito tana gyara main parlour kafin me Aikinta tazo ta k'ara gyarawa"tana turare parlourn big man yashigo"saidai yayi sallama"ita kuma Azuciyarta ta Amsa"ta d'auke kanta kamarma bata ganshiba"shima be kulataba ya haye saman"d'akin daya keyin exercise d'insa"Anan ya shiga yafara exercise tsawon mintina 30 kafin ya fito yanata zufa"main parlour d'in ya sakko"ummu na kwance samqn 3seeter kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin damuwa"yatab'e baki ya zauna kan kujera"yana sanye da singleti da wondo 3 quarter"wuyansa da goshinsa duk zuface"handkcheef k'arami na hannunsa yana share zufar"ummu kuwa da sauri ta tashi da nufin tabar masa parlourn dan ta tsorata data tagansa bbu kayan kirki Ajikinsa...sai sannan ya shirya yin mgn"tamkar bayaso yamotsa brown lips nasa wajen fad'in ki kamun ruwan lipton"to"shine Abinda ta fad'a dg haka ta nufi kitchen d'in"batafi mintina 5 Aciki ba ta fito da cup d'in shayin"Ajiye masa samqn center table tayi ta juya ta koma kitchen d'in"lokacin k'arfe 7 daidai"cikin Awa guda ta had'a chips da farfesun kayan ciki"ta dafa ruwan zafi"ta fito da nufin ta jera komai A dining area ta sami Abdallah kwance yana bacci"hararar kyakykyawar fuskarsa tayi Aranta tace"harma yana baccin saida yayi kyau"afili kuwa tab'e baki tayi tace"shine sbd iyayi zai kama yimun bacci a parlour?"tak'are maganar tana Ajiye kayan hannunta"ta koma kitchen d'in ta fito da sauran.... Abin mamaki tasami big man zaune yana canza channel d'in tv"gabanta yafad'i Amma saita dake"tana fatan Allah yasa beji me tace d'azun ba"shi kuwa daman neman hanyar da zata kulashi yakeyi"saiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login