Showing 45001 words to 48000 words out of 93107 words

Chapter 16 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete

ta gefen ido yanata turiri"hak'uri zakayi ka d'aure kasha" maganin asibiti na mura bacci kawai yake sakawa"bece komaiba sbd kan nasa har ciwo yakeyi kuma be sami baccin kirkiba da k'yar yayi sallar Asuba ya koma ya kwanta"gefen bed d'in ta zauna tana janye bargon daya rufe jikinsa dashi.....saidai da sauri ta cika bargon sbd ganinsa datayi dg shi sai boxer Ajikinsa"body building d'insa ba k'aramin tsoro yabata ba"ta sunku yadda da kanta k'asa gabanta nata fad'uwa"shi kuwa sakkowa dg samqn bed d'in yayi har yakai bak'in k'ofar bath room d'in yace"ki fiddomun jallabiya"dato ta Amsa"bayan ta fiddo masa ta d'auki shayin ta koma parlourn sa tana shashshek'a masa"saida taga yayi daidai yanda zai iya sha"sannan ta tashi ta nufi d'akin"Ahankali ta tura k'ofar ta lek'o kanta"yana zaune samqn bed side drower yasaka jallabiyar"ya kama ido ya rufe"sallama ta amsa ya bud'e idon ya kalleta sau d'aya ya kauda kansa"gashi kasha kaji?"beyi mgn ba ya Amsa yayi bissimilah yafara kurb'a"dg farko yaso yadena sha"sbd yaji d'aci ga yaji yaji sosai"Amma saiya daure kodan sbd yadda yaga ta damu"shi Azatonsa bazama ta damu sbd beda lafiya ba.....yana wannan tunanin yaga tanufi k'ofa zata fita"ina zuwa?"yafad'a iya lab'b'ansa"zanje sbd kar baby tayita knocking"kansa kawai yagyad'a mata"yaci gaba da sha"yana idarwa yafara zufa da atishawa sai kuma yaji wani irin bacci"magani na ruwa na bature dake Ajiye samqn bed side drower ya d'auka yasha marfi biyu ya kwanta"wani nauyayan bacci yayi Awon gaba dashi"sai wajen k'arfe 11 na safe yatashi"saidai Ahankali kansa yadena ciwo"kuma mak'oshinsa yayi sauk'i"wanda Aransa yayi mamakin tayaya ummu tasan irin yadda ake had'a wannan maganin?"yana wannan tunanin yashige bath room yazuba ruwan zafi cikin ruwan data had'a masa yayi wanka"sosai yaji dad'in jikin nasa"bayan ya fito ya shirya cikin yellow d'in t shirt da jeans dark green"fuskarsa tayi haske hancinsa yarage jan"saidai har yanzun idanuwansa Akwai sauran ja cikin su"plate shoes yasaka yana rik'e da wayoyinsa yasakko k'asan da nufin yaje ya gaido Ammi kar taji shiru.....ummu kuwa bayan fitarta dg b'angaren nasa kitchen ta koma ta aza masa farfesun naman kan rago"ta zuba kayan yaji sosai"tana Aikin sa'ada ta shigo"Atare sukayi break fast"sai wajen k'arfe 11 ta idar da farfesun"sbd ta barshi ya dahu yayi ligub"bayan ta gama jera komai taje ta wanke hannunta tadawo parlourn suna fira sama sama da sa'ada"wacce rabi firan duk kan karatune sbd yanzun itace ke mata lesson"can dai ta tashi sbd ta dubosa"tana k'ok'arin hawa stars na biyu shi kuma yana sakkowa"hakan yasa ummu ta dakata"saidai bata yadda ta kallesaba"shi kuma ita yake kallo"saida yazo gab da ita kawai taji yakama hannunta"Ajiyar zuciya tasaki Ab'oye ta saci kallonsa suka had'a ido"ya jikin?"da sauk'i"yanzun nake cewa naje na maka mgn kazo kayi break fast"d'an shiru yayi sai kuma taji yace"sai 12 kema kin sani"yafad'a Ahankali yana d'an tari"hak'uri zakayi yaya Abdallah kodan sbd lafiyarka kayi yanzun "ko yanzun maganine zaka koma sha"zakaji dad'i, muryanka zai daidaita"ta k'are maganar suna jerawa suka iso cikin parlourn"sa'ada na kallonsa tace"yaya sannu ya jikin?"nifa naji sauk'i wama yafad'a miki?"Anty ummu ce tacemun baka jin dad'i"beyi mgn ba yacika hannun ummu yanufi dining area"biyosa Abaya tayi ta zuba masa farfesun a cikin plate ta zuba roman sosai"tana fad'in roman zakafi yawan sha"dg haka ta zuba masa doya da k'wai da soyayyar planten"sannan ta zuba masa irin shayin dayasha d'azun"shidai yana Aikin kallonta da Abinda ta zuba masa"cike da rarrashi tace"kaci komai zaka ji normal fa"Amma kuma naga kamar kin cika yaji ko?"ba sosai na sakq ba"to ki zauna mana"tayi mamakin maganar tasa ta k'arshe" saidai batayi mgn ba ta zauna "shi kuma tea d'in yafara sha"tas ya shanye sannan yafara shan roman da naman"yanata Atishawa da dari tana masa sannu"da bashi k'arfin gwiwar yaci lafiya tafi komai"kafin ya idar yayi zufa" hancinsa na zuba"ummu ta d'auki handcheef d'insa dake Ajiye samqn table d'in tana goge masa"can ya kalleta yace"pls ki barni haka na k'oshi"shikenan kabada gab d'in mintina 5 sai nabaka ruwa marar sanyi kasha....yana k'ok'arin mgn yaji sa'ada na waya da Ammi tana fad'in bafa sosai kebeda lafiya ba Ammi"kuma Anty ummu ta shareni ta yaya kawai takeyi ni tafiyata zanyi"Abdallah yatab'e baki yana fad'in maza kitashi kifi ruwa gudu"ummu ta kama dariya k'asa k'asa"sa'ada ta turo baki tana fad'in" Ammi kin gansu shida Anty ko?"sai takashe wayar ta mik'e tsaye zata fita"ummu ta dinga kiranta tak'i kulata....ki k'yaleta ko kema na b'ata miki rai"dama na lura kwana biyun nan kina shagwab'ata ko?"to yaya Abdallah idan bamu shagwab'ata nida kaiba waye zai mata haka"?kasan dai matar daddy bata damu da itaba"hakane"ni yanzun fita zanyi"haba dan Allah! kabari sai zuwa k'arfe 2 kad'an huta kasami sauk'i"barama na rage iskan fanka"ta k'are maganar tana tashi tsaye taje ta rage iskan fankan"sannan taje kitchen ta d'akko masa ruwa marar sanyi da cup tadawo tasamesa yakoma kan 2 seeter ya zauna"gefensa ta zauna ta zuba masa ruwan"sai bayan yagama sha yaduba time 12:10 pm"cikin sanyayyar muryanshi yace" *khairee*!.........har cikin jini da jijiyarta taji sunan"kafin ta kallesa zuciyarta na bugawa sbd mamaki dan wannan ne karon farko dataji sunanta Abakinsa"yana kallon ta ya girgiza kansa yace"ki hak'ura da rigimar bazan fitaba yanxun"zan je naduba Ammi saina dawo yau ai week end ne"gaba d'aya ummu jinta takeyi wata iri"kanta kawai ta gyad'a masa bata koma mgn ba"gashi yau sai taji muryansa yafi na kullum dad'i.....motsin mik'ewarsa tsaye yasaka tadawo tunaninta"har yakai bak'in k'ofa tace"Allah yatsare"da Ameen ya Amsa ya murd'a k'ofar ya fita"tasaki ajiyar zuciya tana maida numfashi kamar wacce tayi wani Aikin wahala"tafi mintina 10 zaune Anan "kafin dg bisani ta tashi ta tattara komai dake samqn dining table takai kitchen"inna uwani dake goge kitchen d'in bayan ta idar taci gaba da wanke wanke" ummu kuwa faten dankali da bushashshen kifi da Alaiyahu tayiwa Abdallah"sai wajen k'arfe 1:30 pm ta gama"bayan ta gama sallar Azahar ta d'aura towel da nufin ta shiga wanka wayarta dake samqn bed tayi ringing"ta nufi gefen bed d'in ta d'auki wayar ta duba"d'an murmushi tayi ta d'auka tana cewa"tuba nakeyi k'awata nasan kinji shiru banzoba ko?"dg d'ayan b'angaren lawisa tace"Eh wlh harma nafara zaton ko wannan miskilin mjin naki ya hanaki zuwa?ah ah wlh"to meyasa baki zoba har biyu saura ? wlh lausy yaya Abdallah ne bashida lafiya shiyasa datun 12 nama iso"yanzun haka yama d'an fita shi nake jira yadawo idan naga jikin nasa da sauk'i saina zo"lallai k'awata"idan bbu sauk'i fa??"ummu na k'ok'arin mgn taji mayataccen k'amshin turaren big man"ta juyo bayanta da sauri ta gansa tsaye gefen k'ofa yatsareta da rinannun idanuwansa da yake yawan lumshewa"kashe wayar tayi da sauri"sam bataji motsin shigowarsa ba"gashi k'aramin towel ne Ajikinta.......✍️✍️


wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤‍🔥❤‍🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤‍🔥❤‍🔥

*35&36*


.......Da sauri ummu taja da baya tare da k'ank'ame jikinta gabanta na wani irin bugawa"gefen zuciyarta kuma wata iriyar kunyarsa ce na ganinta da yayi haka......big man kuwa jikinsa na jingine da bango"hannunsa guda cikin Aljihun wondonsa"gudan hannunsa kuma yana shafa kansa dashi"yayinda lip nasa na k'asa yaturashi cikin bakinsa yana tauna tamkar zai hudashi"kallon k'asan ido yake binta dashi tun daga fararen k'afafuwanta datayima jan lalle na biki har zuwa samqn fuskarta"saidai yafahimci tana jin tsoro ko kunyar ya dinga ganinta irin haka....kusan second 5 bbu wanda yayi mgn cikinsu"shi dama yadawo ne daga masjeed kuma yajisa normal sai Abinda ba'a rasaba shine daya shigo yaga be gantaba"dalilin da yazo nan dan yafad'a mata ta koma dafa masa irin shayin d'azun"yasamu tana waya kuma duk Abinda take fad'a yanaji"saidai miskilin yama kasa mgn"ummu kuwa da sauri ta shige bath room banko k'ofar ta murza key"Abdallah kuwa takalmin k'afarsa cover shoes yacire yaje ya haye samqn bed d'in ta ya kwanta yana kallon sillin d'in d'akin"hankalinsa kwance tamkar yana cikin d'akinsa...tsawon mintina 15 ummu ta fito dg cikin bath room d'in"saidai ta yafo wani towel d'in samqn kafad'arta da nufin idan ta fito ta tsane ruwan jikinta dashi"saidai turus tayi dataga mutum kwance kan bed d'in ta"tamkar ta koma cikin bath room d'in haka taji"dan ita Azatonta yama jima da fita"d'aure fuska tayi tana kauda kanta tace"kaji sauk'i da Alama shine zaka fara da jan mgn ko?"kallonta yayi yaga tayi tsaye"yatsareta da ido be furta komai ba"dakai fa nake yaya Abdallah"ni katashi kaje d'akinka zan shirya"kawai saidai ka dinga shigowa bbu ko neman izini fisabilillahi"na gyara maka bed d'inka ka tafi can mana....ta k'are maganar tana nufar gefen mirror"Abdallah yatashi zaune yana fad'in ank'i atafi d'in"dama me gida da gidansa Ana masa shamaki da wani wajen?"juyowa tayi ta kallesa dariya na sub'uce mata"har fararen jerarrun hakoranta suka bayyana"shidai Abdallah yana kallonta bbu yabo bbu fallasa saman fuskarsa"saida ta gama dariyarta sannan tace"malam kadena kallonah dan Allah"kai yanzun bakaji nauyin furta me gida ba?"ka manta Auren dakayi ne?"gaba d'aya saima ya rasa me zai mata na kare kansa"ita kuwa bata koma mgn ba tana jiran yafita tafara shiryawa"sakkowa yayi dg samqn bed d'in yafara tunkaro Inda take"Atsorace taja baya tana fad'in toni mena maka fisabilillahi?"dan Allah kajira mana"banza yamata yana cigaba da nufar Inda take"da sauri tayi k'ok'arin nufar k'ofa yasha gabanta yana tab'e baki yace"matsalata dake gaddama"sannan baki iya k'watar kanki wajena"sannan ga tsoro ga jan fad'a ko?"nidai dan Allah kaje zan shirya"okay fita Anguwar yafi miki lafiya ta mahinmanci?"to Amma bakaji sauk'i ba?"ta tambayesa tana ja da baya"bbu laifi da sauk'i"kona koma dafa maka shayin?"kansa ya gyad'a mata"dama na dafa kamar nasan zaka buk'ata"kaje kasha sai kayi lunch pls"menene kika girkamun"tana nufar gaban mirror tace"faten dankali ne sbd kana mura nayi maka"saidai na sakq bushashshen kifi naga kuma bakacika son kifi ba"wai kinfi k'arfin ki juyo kimun mgn shine zaki juyamun baya?"wlh zanzo na fisge towel d'in naga yanda zakiyi....dan girman Allah kayi hak'uri nidai kaje ka zauna ka huta"bazan jeba har Abincin bazan ciba"Azatonsa zata rarrashesa sai yaji tace"shikenan Ai"bece komaiba yasaka takalminsa yafita dg cikin d'akin yabuga k'ofar da k'arfi"ummu ta tab'e baki taci gaba da shirinta"wajen k'arfe 3 ta fito"tayi kyau cikin Ankon Atamfa lemon green me zanen bak'i da fari"siket d'in me tsaga dg baya yaka mata sosai"ta yafa mayafi samqn kafad'arta bak'i"hand bag da takalmi masu tsini duk bak'ak'e tasaka"tasha make up gwanin kyau tanata k'amshi"Abdallah na zaune samqn kujera yanata cin magani"bbu yanda ya iya yaci Abincin da shayin"ummu ta k'araso tana cafe key d'in motarta ta zauna gefensa yakoma had'e rai"ita dariya ma yabata dan yanzun ta saba da halayensa"sannu da hutawa y'allabai"harara ya banko mata yak'i mgn"nidai pls zanje na zuba mai a mota kuma banida...sai kuma tayi shiru"tab'e baki yayi cikin cool voice yace"maganar bata dameki ba shiyasa bazaki fad'a ba"yak'are maganar yana binta da kallon k'asan ido....batayi mgn ba ta mik'e tsaye da nufin kawai ta tafi samqn nafef"Abdallah yayi saurin finciko hannunta tajuyo kamar zata fad'i"ya zaunar da ita gab dashi"murya bbu Alamar wasa yace"fad'amun menene ?"nidai dan Allah kabarni natafi bbu komai fa"koma matsowa gab da ita yayi har jikinsu na gugar juna"still yana rik'e da hannun ta"yadubi idanuwanta tayi saurin yin k'asa da kanta tana son k'wace hannun ta daya rik'e"bazan cikakiba saikin fad'amun ko kuwa ki fasa zuwa Anguwar"dama zance maka ne banida kud'in zuba mai shine fa"kuma ATM d'ina yayi espire"hmm! tunda nake dake kin tab'a cemun kinason na siya miki Abu kaza?"kokin tab'a cemun kina son na baki kud'i?"duk bakya cewa sbd kina ganin kinfi k'arfin Amsar Abin hannun mak'iyinki ko?"shiru tayi tanata kiciniyar k'wace hannunta"yatab'e baki yace"kitashi kije d'akina cikin lokar gado ki d'akko ko nawa kike so?"nidai takalmin nan sun cika tsini kaje ka kamun man....sai kuma tayi shiru data tuna waye big man ta isama ta Aikesa?"idan barakije da kankiba ki bari"murmushi ummu tayi Aranta tace wlh sai kaje ta hanya me sauk'i"Afili kuwa kukan shagwab'a tasaka ta kwantar da kanta gefen kafad'arsa murya can k'asa tace"zanfa iya fad'uwa kan stairs d'in can pls yaya Abdallah kaje kaji?.....da farko haushin yadda tayi masa yaji Aransa"Amma kuma ajikinsa sai yaji kamarma karta dena mgn"yana wannan tunanin yaji ta janye kanta tana fad'in ka cikamun hannuna"bakyaso naje na d'akko miki?"inaso mana"beyi mgn ba saidai gaba d'aya yajishi wani iri"tashi tsaye yayi cikin nutsuwa ya nufi samqn"be jimaba ya sakko da kud'i masu yawa Ahannunsa"Amamakin ummu sai taga rafar y'an d'ari biyar guda hud'u ya Aza mata samqn cinyarta" yana fad'in gashi nan saiki k'yaleni da wata rigima"kallon kud'in tayi ta kuma kallesa yana k'ok'arin zama gefenta"Ahankali tace"yaya Abdallah duk kana nufin da wannan kud'in zan zuba man?"kanki akeji idan zaki d'auka kije to idan bakyaso ke kika sani"nifa wlh ko 5k kabani nagode sunyi yawa zan d'auki dubu 50 nagode Allah yak'ara bud'i"haka nan yaji ya tsintsi kansa dajin dad'in Addu'ar tata"saidai beyi mgn ba ya fisge hand bag nata yabud'e yasaka kud'in ciki"ido cikin ido ya kalleta yana fad'in idan Abdallah yayi kyauta ba'a mayar masa"ki tashi da sadeeq zaku fita azuba miki man"shiya dawo ke ki wuce yana bakin get"tsabar mamakin big man kasa mgn ummu tayi ta mik'e tsaye ta tafi ,shi kuma yabi bayanta da kallo harta b'acewa ganinsa.... Agefen motarta ta sami sadeeq tsaye yana jiranta"kamar yadda yasaba ya gaisheta da ladabi ta Amsa tana bud'e motar suka shiga.....duk Abinda yaka mata Ayi saida sadeeq yaga Anyi sannan yabar ummu ta wucewarta Anguwa"wanda duk wani motsinta da bugun zuciyarta Abdallah take tunani.......
misalin k'arfe 8:5 pm ummu ta turo k'ofar parlourn ta shigo da sallama"kasancewar saida ta tsaya ta bama Aminu 150k yaje yasiyo kayan Abinci yakaima baba injita sannan ta tafo gida"shiyasa har isha'i tayi mata waje"Abdallah na zaune kan kujera yunwa yakeji sbd ko dinner bata aza ba"yana jin sallamarta yamata banza"ta k'araso cikin parlourn tana fad'in yaya Abdallah ya jikin ?"bansaniba"sai yanzun kikaga damar dawowa ko?"wlh nad'an...bana son ji! yakatse mata mgn Atsawace"batare daya kalletaba"dan Allah kayi hak'uri"baran yiba"zancen fita kuma kingama"batace komaiba ta wuce cikin d'akinta"magrib da isha'i kawai tayi ta fito parlourn da hijab har k'asa d'inkin jalbab ajikinta"big man na zaune yana danne danne Awaya"kitchen ta shiga ta fara tunanin meye zata girka masa?...."shayin d'azun ta dafa masa sannan ta Aza indomie da k'wai"bayan ta zuba indomie d'in ta fito rik'e da cup d'in shayin Ahannunta"fuskarta bbu walwala sbd bataji dad'in disgin daya mata ba"gabansa ta duk'a ta Ajiye cup d'in saman center table tana fad'in kafara shan shayin kafin indomie d'in ta ida"banasha ! ki d'auki kayanki"shima indomie d'in bana ci"kije kiyi Abinda kika gadama"shiru tayi batace komaiba ta d'auki cup d'in shayin taje kitchen ta zubar"indomie d'in ta juyota cikin tray ta nufi d'akin ta"zama tayi ta kira sa'ada ta waya"ta sanar mata tazo suci Abinci"bbu jumawa ta shigo d'akin sukaci tare"saidai cikin zuciyarta ta damu da fushin da Abdallah keyi da ita"tana tunanin sbd takai dare ne yake fushi"bayan sun gama sa'ada ta fita da tray d'in takai kitchen tayiwa Abdallah sallama ta fita"shi kuwa gaba d'aya yarasa meyasa yakejin zafin fitar datayi takai dare?"sai tsaki yake ja jefi jefi"dg bisani ya tashi yakoma part nasa"kayan wanka yasaka yashige bath room"yafi mintina 20 sannan yafito ya shirya cikin guntun boxer ya kwanta"saidai yarage iskan fanka ,yakashe AC"kuma Alhamdllh yasami sauk'in murar bisa kulawar da ummu ta bashi yau"saidai kuma yana rufe ido zuciyarsa ta dinga hasko masa ita sadda take d'aure da towel da kuma jiya da dare daya ganta da kayan bacci"tsaki yaketa jaa"kamar zai huda harshensa"sbd haushin tunata dayakeji"sai wajen 11 pm bacci ya kwasheshi"washe gari da safe yaje masjeed koda ummu taje gyara d'akin be nan"har vests da jallaboyinsa guda 3 ta wanke masa da taga yajika su da klin a bath room"tana jera Abin break fast yashigo da milk d'in jallabiya Ajikinsa"yana ganinta ya had'e rai"da sauri ta duk'a ta gaishesa"bana so ki rik'e Abinki"mgn ta kikeji ne?"yafad'a cikin shan k'amshi yarab'a gefenta ya wuce"ummu ranta yab'aci matuk'a"tasha Alwashin fita harkansa"Abdallah kuwa daya shigo yaga ta gyara d'akin yaji sanyi Azuciyarsa"lokacin daya shiga bath room yaga ta wanke masa jallabiyoyinsa sai yaji dama d'azun be disgata ba"da wannan tunanin yayi wanka"saidai yayi niyar idan ta masa mgn yayi break fast zaiyi"lokacin daya gama shiryawa ya sakko down stairs d'in"bbu kowa a parlourn"fita yayi ya rufe k'ofar da key.....
kimanin kwana 2 kenan ummu na wasar b'uya da Abdallah"tun ranar data gaishesa be Amsa ba ta dena girki dashi"gyaran d'akin ma ta dena yi masa"idan tasan yana gidan bata zama parlourn"idan kuwa suna tare da sa'ada ya shigo ko kallo be ishetaba"ita kanta sa'ada tana mamakinsu wata ran"dg ita sai sa'ada da mai Aikinta take musu girki"Abdallah kuwa ba k'aramin b'aci ransa yayiba da Abinda take masa"musammun yasaba itake gyara masa d'aki dan beson k'azanta"data dena saidai yanzun shine ke Ajiye Abinda yakeyi ya gyara Abinsa"saidai yasha Alwashin shima fita harkanta"Aganinsa sai me idan ta fita harkansa?"idan yaga dama saiya saketa su rabu da juna ba wata tsiya bace awajensa??"dama mutum ne shi dabai cika yawon mgn ba"kuma beda fara'a"sai yanzun Abin yamasa yawa"yanzun ko sa'ada be fira da ita sai y'ar mgn d'aya biyu shikenan....Ayau kuma laraba ya shirya tafiya k'asar malesia sbd dama duk k'arshen shekara yana zuwa can k'asar Abinciki lafiyarsa"tun wajen k'arfe 10 na safe yagama shiryawarsa be mayi break fast ba"ya bari saiya shiga jirgi tukum yayi can"sakkowa yayi downstairs da troley nasa yana jiran sadeeq yazo yafita dashi yakai masa mota"ya shirya cikin suit farare k'al ga sabon Aski da gyaran fuskan da aka masa jiya"sai yayi kamar irin black America d'in nan"masha Allah ! yayi kyau bana wasa ba"duk macen dataga big man indai bbu igiya ukku kanta dole ta kyasa...lolx"bayan ya ajiye troley d'in bakin k'ofa" ya nufi gefen kujera ya zauna yana tunanin yasanarwa wannan matsiwaciyar tafiyar tasa ko kuwa??"yana wannan tunanin ummu ta fito dg cikin d'akin ta Azatonta bema gidan"tana sanye da wondo pencil bak'i da riga bak'a me dogon hannu"kanta bbu d'an kwali"kayan sunyi bala'in fito mata da suran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login