Showing 66001 words to 69000 words out of 93107 words

Chapter 23 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete

wani yanayi ya Amshi takardar sbd yaje yabiya kud'in afara yimata Abinda yadace"kallonsa ya maida wajen mutuniyar tasa"tayi k'asa da kanta ta had'e rai"gaba d'aya Abinda yafaru ne cikin ranta tana ganin Abin kamar a mafarki"saidai yadda Abdallah yadamu da ita yanata nan nan da ita tanata wanashi Abin yamata dad'i Aranta"yanzun damuwarta guda shine yace"yana SONTA..... khairee zanje wajen biyan kud'in nadawo"ko zaki bini ne?"ya tambaya k'asa k'asa yadda ita ce kawai zataji"dg doctor d'in mace har namijin sai kallonsu sukeyi"dan sun fahimci Abdallah na mugun jida ita"ita kanta baturiyar likitar bata tab'a jin bakak'en fata sun burgetaba sai Akansu..... mik'ewa tsaye yyi sbd ganin batada Alamar yi masa mgn"yasaki Ajiyar zuciya Ahankali sbd ganin doctor d'in yafita"dama da Alama wani abu yazo d'auka cikin office d'in"shima saiya fita"ummu tabi bayan sa da kallo harya b'acewa ganinta"doctor d'in ta dinga kwantar mata da hankali da sanar mata bbu zafin da zataji nan Asibitin tayi banban da sauran Asibitocin data sani"kuma idan Akayi d'inkin sati 1 zai warke inde tabi k'a'idarsu"tana cikin yimata bayanin Abdallah yashigo office d'in yabata takardan biyan kud'in"yadubi ummu dake zaune tak'i kallonsa"ya matso gefen kujerar datake zaune ya duk'a ya Aza kansa samqn cinyoyinta"idanuwansa a lumshe ya kama gudan hannunta ya sumbata"yana fad'in ki daure khairee kinjiko? ta d'auki kusan second 10 kafin tana b'ata fuska tace" to kaje dg waje mana"bece komaiba yafita kamar yadda ta buk'ata"saidai daya fitan ya tsaya dg bakin k'ofar shifa office d'in" lokacin k'arfe sha biyu saura"Ammi yakira"tana d'auka tafara tambayarsa yamai jiki?"sai sannan yatuna d'azun fa yayima sa'ada k'aryar kan ummu na ciwo"da sauri yace"da sauk'i muna Asibiti ne Ammi"kodai laulayi takeyi ne Abdallah?"bashi bane Ammi"zazzab'i ne kawai"zanzo nanda mintina 30 na Amshi break fast"bamuci komai ba"dato ta Amsa yanajin surutun sa'ada yakashe wayar"saidai yaji wani iri dayaji rakin ummu"yasan d'inkin Akeyi"duk sai yaji dama yabarta saida yardarta ya Amshi hakk'insa"wani tsananin sonta da tausayinta yaji na bin jini da jijiya na jikinsa"yana cikin wannan yanayin kiran kamal ya shigo wayarsa sbd yaji Abinda su junuid da tj suka masa Agari"cikin rashin walwala ya d'aga kiran"yanayin yadda ya Amsa sallamar kamal d'in"ya tabbatar wa kamal yanada damuwa"hakan yasashi fad'in Abokina da fatan kuna lafiya?"Alhamdllh ina Asibiti khairee ce bbu lafiya kamal"subahanallahi wane Asibiti ne?muna A&M INTERNATIONAL HOSPITAL! Ayya Allah yabata lafiya" kasan dokar Asibitin basu bari Azo dubiya dana zo ai"hakane saidai idan mun koma gida"Amma Anjima zanzo gidan zamuyi mgn"cewar Abdallah yana yanke wayar"yayi shiru yana jin tausayin y'ay'a mata"yatuna ko bayan wannan wahalar da mace tasha adaren farko zata d'auki ciki tayi nak'uda ta haihu"sosai yaji k'imar ummu Aransa data kasance me tarbiyya har takawo masa mutuncinta....yana wannan tunanin wata nurse tazo zata shiga"had'e rai yayi yak'i matsawa"shan jinin jikinta tayi sbd fuskar big man ba b'oyayya bace"shi kansa doctor d'in d'azun dayake d'an nigeria ne yaganesa"cikin sigar jan hankali tace"pls zan wuce doctor ce keson ganina"yatsina fuska yayi yana kauda kansa yace"matata na ciki idan ta fito kin shiga"yafad'a yana duba wrist watch d'in dake d'aure a hannunsa"ganin bbu fuskar dazai bari ta shiga yasaka batayi mgn ba ta wucewarta....yayinda ummu da doctor sunga komai ta tv da aka saita da CTV camera Acikin office d'in"wanda ummu Abinda Abdallah yayi yamata dad'i sosai Aranta"ta tabbatar kobe sonta yadamu da ita"doctor d'in data gani take tambayarta sbd itace ta kira nurse d'in ta waya zata tura ummu zuwa room d'in da aka bata"An kammala d'inkin"wanda taji zafi tasha raki"bayani ummu ta mata da nuna mata mijin nata na kishinta sosai"itadai doctor murmushi tayi taje ta bud'e k'ofar big man na tsaye ya juyo suka had'a ido"cikin harshen turanci sukayi mgn tasanar masa yaje room 5 yanzun za'a kamasa matarsa"Amma sun mata Alluran bacci"zata d'auki kusan Awa 2 tana bacci"dato ya Amsa yayi gaba"Ahankali yashiga d'akin"fes d'akin yake"saman bed d'in An shimfid'a bed sheet"ga fridge da tv manne jikin bango"ga dust bin Aciki da sink agefe na wanke hannu"da alama cleaners na kulawa da komai"yafad'a yana tura k'ofar toilet d'in shima fes yake"gefen bed d'in yaje ya zauna yafara danna waya"Ahaka nurses biyu suka turo ummu samqn wani bed suka shigo"Idonta biyu baccin nason d'aukarta"tunda suka shigo yatsurawa baby face nata ido yanata kallonta kamar yaune yafara ganin ta"ta gallah masa harara"shi kuma ya maido mata da murmushi yana mik'ewa tsaye yanufo gefen d'an gadon da deep husky voice d'insa yace"my khairee sannu! yak'are maganar yana matsowa dab da ita yafara k'ok'arin d'aukarta"sudai nurses d'in nata kallonsu"batayi musu ba sbd ganin basu kad'ai bane Acikin d'akin"samqn bed d'in ya Azata"yamata matashin kai da cinyarsa"yana janye hular samqn kanta"ta doke masa hannu"thank you tawan"ina Alfahari dake khairee nah"naji dad'in yadda kika rik'e marta...kukan data saka yasanya yyi shiru be koma mgn ba"ita kuma ta rufe ido sbd baccin dake fusgarta"Acikin mintina 5 bacci yayi Awon gaba da ita"Abdallah yaja Ajiyar zuciya Afili yana furta Allah yabaki lfy khairee nah kona goge kuskurena na baya"lallai na yarda da zancen kamal dayace SO baya shawara yake shiga"yak'are maganar yana shafa gashin kanta ya gyara mata kanta ya Aza samqn pillow d'in dake kan d'an gadon"yaduba time k'arfe 12:15 pm"Ahankali ya sumbaci goshinta da lips nata"ya rad'a mata Agefen kunnanta kalmar I LOVE YOU" ya mik'e tsaye yafita yana waiwayon ta"batare data san yana yiba"kai tsaye office d'in ganin likitan yashiga yasanar masa su kula masa da motsinta nanda mintina 30 zaije yadawo"dato ta Amsa shi kuma yafita"kai tsaye gida yakoma"duk Abinda yasan zata buk'ata yabud'e d'akinta ya d'akko ya shirya cikin k'aramin troley nasa daya d'akko d'akinsa"sannan ya d'auki blanket duk yafito dasu da kansa yasaka cikin mota ya d'auki hanyar gidan Ammi"batare daya tsaya jiran driver ko body guards d'in saba.... lokacin daya iso gidan Ammi har Anfara kiran k'arfe d'aya saura"Ammi da sa'ada na zaune a parlourn"kan sa'ada na samqn cinyar Ammin"big man yashigo da sallama Ahankali"kallo d'aya Ammi ta masa ta kasa gane Awane yanayi yake"saidai yau taga yayi haske sosai"ta kumayi mamakin ganinsa da manyan kaya"dama kuma tana masa fad'an nacewa saka k'ananun kaya dayayi Arayuwarsa....ina wuni Ammi?"Abdallah ya katse mata tunaninta"lafiya qlau Alhamdllh"yaya ya Antyn da jiki?"da sauk'i baby tayi bacci ma"to zan bika dan Allah naganota"wannan Asibitin ba'a zuwa dubiya saita dawo kin dubata"ki tashi ki shiga ciki zamuyi mgn da Ammi"batace komaiba fuska bbu walwala tanata turo baki ta tashi"Ammi tace"meke damun ummulkhairi d'in?"d'an sosa k'eya yayi yana fad'in zazzab'i ne"Allah yabata lafiya"yau ka tuna kayan Al'ada kenan?"d'an murmushi yasaki yana fad'in cikin satin nan yawanci da yamma sune nake sakawa sbd khairee su tafiso na sakq"sai tayita rigima wai manyan kaya sunfimun kyau"ta kyauta Ai"dama haka Akeso macen k'warai itace wacce mijinta idan yayi ba daidaiba zata Ankarar dashibisa hanyar daya dace" Allah yayi mata Albarka yabata lafiya"cikin jin dad'i ya Amsa harda yin murmushi"wanda Ammi tayi mamaki"ga basket can na shirya komai sai kaje dashi dukda dai ranama tayi"shi lunch d'in kabari da yamma sai kazo ka amsa"to Ammi Amma kar a Ajiye mana dinner"to shikenan"shiru na mintina 10 ya ratsa tsakani"fuskar Ammi bbu walwala tace"sa'ada tasanar mun Abinda matsiyaciyar matar daddynku ta Aikata da irin hukuncin daya yanke mata"sai yanzun zaice zai maidani dayaga bbu ita?"to bbu Inda zan koma, y'ata kuma na rik'e ka kwaso mun kayanta ka kamun nan.... ganin tayi shiru yasaka Abdallah cewa" dan Allah Ammi kiyi hak'uri ki koma kodan sbd zuri'arki"idan kink'i komawa kinsan wacece kuma daddy zai koma yayibo mana"kuma kinsan bayin kansa bane meyasa bazaki masa uzuriba??"ko khairee wlh banji dad'iba datasan baku tare da daddy"dan Allah kiyi hak'uri Ammi"shikenan Abdallah bbu yadda zanyi zan hak'ura na koma Amma wlh shima saiya gane kuransa na wahalar dashi sannan zan koma.... murmushi yasub'uce masa"Aransa yace"oh mata basu girma Awajen mazajensu"yanzun ita Ammi tsofai tsofai da ita wane Aji zata jama daddy?"sai kuma yatuna da ummu yace"nima tawa rigimammiyar nacan na jirana"mik'ewa tsaye yyi yana fad'in zan wuce Ammi"batace komaiba ta k'walama sa'ada kira"ta fito tana b'ata rai"jeki d'akko jug d'in lemon cittan nan da lemon tsami yaje mata dashi za taji dad'in bakinta"dato ta Amsa Abdallah cikin jin dad'i yaketa zubama Ammi godiya"itadai tana murmushi kawai batace komaiba"ranta yabata yanzun yafara son ummu kenan?"kasancewar sa'ada tasanar mata komai"ta kuma kira kamal ta tsaresa da tambaya yamata bayanin sanadin Auren da had'uwarsa da ummu ta farko da Abinda ya had'asu"Ada taso ta masa mgn kuma araba AUREN"saidai kamal daya nuna mata nagartattun halayen ummu yasaka ta fasa"sbd itama shedace kan ummu nada hankali da tarbiyya"hakan yasa tabarshi sai ranar daya kamata wani zance dake nuna yafara sonta zata masa tas"takumasha Alwashin bazai Auri preety ba.....gashi Ammi"muryar sa'ada ta katse mata tunani"kije ki bisa dashi mana yana bakin get"batace komaiba taje tasami big man tsaye yana saka basket d'in a back sit"Autar Ammi sbd bazanje dake wajen khaireen ba shine kike fushi?"Eh mana yaya Abdallah"hak'uri zakiyi zuwa gobe mun dawo"kuma ita dukta damu dabaki kusa da ita"murmushi sa'ada tayi tace"dama nasan Anty zatayi kewata kai kuma shine kace nazo nan ko?"shiru kawai yayi sbd yasan bazata gane komai ba"ya Amshi jug d'in yasaka ciki yarufe"tana tsaye tana kallon sa tace"Allah yatsare Agaida ita"ya Amsa da Ameen ya shiga mota yatafi....
saida yatsaya masallacin dake cikin Asibitin yayi sallah sannan yanufo ciki"basket d'in ne da jug a hannunsa"Ahankali yaturo k'ofar yashigo da sallama"tanata baccinta ta kwanta gefen damarta"Ajiye kayan yayi yanufi gefen bed yaje ya sumbaci goshinta sannan yafita"be jimaba yadawo da sauran kayan ya Ajiye"shi kuma ya matsa samqn bed d'in ya zauna ya janyota samqn jikinsa ya matseta sosai kamar zai maida ita ciki"yana lissafin nanda mintina 30 zuwa 40 zata iya farkawa dg baccin ta...yayi shiru yana bin farar kyakykyawar fuskarta da kallo yana tuna yadda ya risketa d'azun da safe"sai yaji inama kar lokacin ya wuce"wata zuciyar tace"kanada tabbas idan ta warke zata cigaba da zama da kaine bayan kasan bata sonka??"wani irin fargaba yaji Azuciyarsa"yana jin tsananin zafin mubashshir acikin zuciyarsa"gashi shi besan kowa na ummu ba balle ya tambayesa samari nawa ta tab'a yi??"dan yanzun ya fahimci ba k'aramin zafin kishinta yakeyi ba...yajima yana zaune yana tunani yana kallon ummu"wanda komai nata yamasa kyau"musammun lips nata da gashin girrar ta dana saman kanta"yana wannan tunanin tafara motsi Ajikinsa"yatsareta da ido kamar yana kallon TV"hamma tayi ta bud'e idanuwanta tana salati....saidai ganinta datayi Ajikinsa yasaka ta had'e rai"tana kiciniyar k'wacewa"dukda bbu k'arfi ajikin nata"da irin wannan rigimar kuma kika tashi khairee??"yanzun wajen yadena miki ciwon ko?"kuka ta fashe dashi tana turashi dason ta k'wace"Ahaka doctor d'in ta turo k'ofar d'akin ta shigo da wasu ledoji a hannunta"big man yacikata badan yaso ba"ta sakko dg samqn bed d'in ta jingina jikinta da bango tana tsuke bakinta"doctor d'in ta mata sannu tana fad'in zamuje toilet kiyi sit bath"kanta ummu ta gyad'a mata"Abdallah dai bece komaiba yana kallo suka shiga toilet d'in"bbu jumawa doctor d'in ta fito tabarta ciki"tafi mintina 15 sannan ta fito dg cikin toilet"jikinta da ruwa da Alama Alwalah tayi"kuma jikin Alhamdllh da sauk'i sosai dan har tafiyarma normal takeyi"saidai wata irin muguwar yunwa ke damunta"ranta yabata kallonta yakeyi"hakan yasa bata kallesaba"sai taga yatashi yabud'e troley d'in ya d'akko mata hijab da prayer mate ya shimfid'a mata"saima sannan ta lura da kayan dake cikin d'akin daya kawo"kallonta yayi yana fad'in zokiyi sallar saiki karya ko?"nanma shiru tayi ta matsa ta d'auki hijab d'inta ta sakq ta kabbara sallar"shi kuma blanket d'in ya shimfid'a samqn bed d'in"sannan ya had'a mata tea me kauri"yazuba mata farfesun naman kaji da ships dayaji kayan had'i"duk ya Ajiye gefen bed d'in yazauna yana kallonta tana Addu'a tana hawaye"wanda hankalinsa yatashi matuk'a yafara zaton ko rabuwa dashi take addu'ar yi???.....,...✍️

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
*AUREN YARJEJENIYA*

*53&54*



.......tunda Abdallah yatafi ummu ta gama waya da lawisa take tunanin ina yaje?saidai kuma zuciyarta na wasi wasi da irin yadda suka tsara itada lawisa tayi" dan ta k'ara tabbatar da cewa Abdallah na sonta yakuma damu da ita"saidai data tuna y'an gidansu da mama sai taji shakku Aranta game da Abinda take k'ok'arin yi idan ta sami sauk'i"wanda ta yadda wannan Asibitin tanada bambamci da sauran Asibitoci"tunda gashi jikin nata Alhamdllh"tana wannan tunanin big man yaturo k'ofar cikin nutsuwa ya shigo"bakinsa d'auke da sallama cikin k'asaitacciyar muryarsa"yana rik'e da ledoji manya guda biyu Ahannun"fuskarsa bbu walwala"yayi y'ar rama"lips nasa sun bushe...ido hud'u sukayi shida mutuniyar tasa"yatsura mata ido yana Aiko mata da wani irin kallon daya sakar mata kasala Ajiki"ta turo masa baki ta d'auke kanta da sauri"shi kuwa Ajiye ledojin hannunsa k'asa yayi yanufi wajen fridge ya d'akko goran ruwa yadawo ya zauna saman farar kujerar dake kallon gadon"still idanuwansa nakan ummu"b'alle murfin yayi yakafa Abakinsa"be Ajiye ba saida ya shanye tas ya jefa roban cikin dustbin dg Inda yake zaune"ummu kuwa jikinta yabata kallonta yakeyi saidai ta maida hankalinta wajen waya.... khairee kin hak'ura dan Allah?"d'ago kanta tayi ta zabga masa harara tana fad'in ban hak'ura ba kuma bazan tab'a hak'ura ba"ka manta irin wulak'ancin dakamun ranar danazo gidan ka?"nace ka manta?"ta k'are maganar cikin masifa tana sakin kuka....kinga pls kiyi shiru khairee"yaka mata ki manta Abinda ya wuce"ki d'auka bada wancan Abdallah d'in kikeba da wanine sabo"kefa kikace bbu wanda bayayin kuskure ko khairee?"to meyasa ni baraki yafemun kuskuran dana miki Abaya ba?"karki manta kemafa kinmun"saidai nawa yafi yawa"zan iya komai sbd ke !;zan iya sadaukar da raina Akanki "yaka mata ki yadda dani ki kwantar da hankalinki ko nawa hankalin zai kwanta pls...."dakin san yadda na shiga damuwa dakin tausayamun"pls kidena cewa bakya sona ina jin zafin Abin Araina"ni dama can ba irin wannan Auren nayi dake ba"kece dama can dai kikayi irin wannan Auren da irin wannan niyar ,yaka mata ki tuba" Amma wlh bazan iya rabuwa dake ba.....iya nan yafad'a yayi shiru yana jiran jin meye zatace??"ta d'auki kusan mintina ukku kafin tace"ka gama dogon sharhin naka?"ta fad'a batare data kallesaba"shiru yayi yanata kallon d'an bakinta yana jin kamar yaje yakama kissing nata... ganin tayi shiru yasaka Ahankali cewa"ga wannan ki duba ko Akwai Abinda bakyaso saina canzo miki ko?"yafad'a yana tashi tsaye ya d'akko ledojin ya aza samqn bed d'in gefenta"hararar ledojin tayi"shi kuma yayi murmushi yana fad'in kinyi kyau sosai"ni meyasa baraki harareniba?"banza ta masa tak'i mgn"khairee! yakirata cikin wata iriyar murya"ak'ule tace"dan Allah ka k'yaleni banaso kaje kabayar dasu mana"sannan wannan Abincin yayi yawa tunda Anan babu wanda za'a bamawa"kazuba kaci mana kar Ayi Asaransa"kinaso naci ne?"k'in kulasa tayi ta zame ta kwanta samqn bed d'in"jikinsa asanyaye yaje yazuba Abinda yakeda buk'ata ya zauna kan kujera yana ci kamar magani yana kallonta"ba wani sosai yaciba ya had'e komai yasaka cikin basket d'in ya d'auka yana kallon bayanta"sbd ta bashi baya"Ahankali yace"khairee zanje wajen Ammin saina biya dg nan nayi sallah"shiru tayi tak'i mgn kuma bata juyo ta kallesa ba"cikin damuwa yanufi k'ofa yafita"ummu ta tashi zaune tafara duba ledojin shopping d'in"chacoolates ne dasu biscuits, Sweet,cakes da ice cream da sauransu"ice cream d'in da cakes d'in kawai ta d'auka ta zauna tana ci"tana tunani"bayan ta idar takomayin sit bath sannan tayi sallar la'asar...big man kuwa gida yakoma yayi wanka da sallah ya shirya cikin sabuwar shadda giznah light green"saidai yasaka hula"ba k'aramin kyau yayi ba"sai wajen k'arfe 5:14 pm ya iso Asibitin sbd yabiya gidan Ammi"sadda ya shigo room d'in doctor d'in na koma duba ummu wacce har tayi wanka ta canza kaya"Acikin kayanta kala 2 daya d'akko mata d'azun"saida taji k'irjinta yabuga dataji Amon tattausan muryanshi yana tambayar doctor d'in yaya yanayin jikin nata??"tasanar masa gobe za'a iya basu sallama tunda da sauk'i jikin nata"gaba d'aya k'amshin turarensa yacika mata k'ofofin hancinta"yana tsaye tunda ya shigo ya jingina bayansa Ajikin bango"hannunsa guda cikin Aljihun wondonsa gudan hannun yana rik'e da waya yana dannawa"ummu ta bishi da kallo tana yaba baiwar kyawun halittar tasa Aranta"tana jin dad'in mallakarsa Amatsayin mijin Aurenta"har yanzun zuciyarta tak'i Aminta data Aikata shawaran da lawisa ta bata"sai ranta yadinga bata kar garin jan aji kuma ta b'allo ma kanta ruwa??....tana wannan tunanin doctor d'in ta fita"sai sannan big man ya maida duka hankalinsa wajenta murya can k'asa yace"kin fara jin yunwa ko?"shiru tayi tak'i mgn"bece komaiba yaduba warmers d'in Abincin daya shigo dashi"tuwon shinkafa ne fara miyar danyar kubewa"ta wadatu da man shanu da naman saniya"sai farfesun kifi dayaji kayan k'amshi"bayan yazuba ya matso ya Ajiye mata yana fad'in pls kici kinjiko?"ni bazan ciba"d'an jim yayi"saiya saki Ajiyar zuciya yana kallonta cikin muryar rarrashi yace"kiyi hak'uri kar laifina yasaka kiyi gaba da Abinci khairee"ki daure kici kisha magani"idan kuma Abincin ne be miki ba"fad'amun me kikeso sai naje nasamo miki??" ko?"yafad'a yana tasowa ya zauna gefenta ya Amshe wayarta datake game da ita"bata kulashiba sai k'ok'arin matsawa dg kusa dashi takeyi"gabanta nata fad'uwa"sbd sak Abinda yafaru d'azun yadawo mata a k'wanya"Abdallah kuwa rik'e hannunta guda yayi ya janyota jikinsa ya rungumeta yana fad'in"sai yaushe zaki dena wannan fushin dani khairee? fad'amun yaushe ne pls kona samu nutsuwa?"nida nakeso ki koma zama y'ar lukuta shine bakyason cin Abinci?..batayi mgn ba sai mutsu mutsun son ta k'wace jikinta dg cikin nasa takeyi"shi kuwa kansa ya aza gefen kafad'arta"ya cire hular samqn kansa ya aza mata samqn gashinta yana murmushi"har fararen jerarrun hakoransa suka bayyana"saima Asannan ummu ta lura da wushiryar dake tsakkiyar hakoransa"wanda tayi masa bala'in kyau"sosai yanayin da suke ciki ya musu dad'i Arai dg ita harshi"hannunsa ta kama ta gartsa masa cizo"yakama dariya yana fad'in koda jini wajen zaiyi bazan cikakiba khairee"kawai inason mu kasance Ahaka"ke kuma kina guduna ko? yak'are maganar yana sinsinar gefen wuyanta yana manna mata kiss gefen wuyan da kumatunta"ita kuma ta k'ak'aro kuka"adole yacikata yana rarrashinta taci Abinci"wanda saida ta bashi muguwar wahala sannan taci Abincin"shi kuwa yakasa jin haushinta balle ko zuciya yayi"gashi Anyi sa'a week end ne"gaba d'aya Anan ya yini"be fitaba sai gab da sallar magrib....bayan sallar isha'i ya shigo d'akin"kuma daya dawo da tsarabar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login