Showing 90001 words to 93000 words out of 93107 words

Chapter 31 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete

sukaje Asibiti Aka gano ta kamu da ciwon b'arin jiki"gashi basuda halin biyan kud'i Afita da ita waje"ga hafsat harta fara gajiya da kulawa da ita"wannan kenan" Allah yasa muyi kyakykyawan k'arshe.....
Ayau yakama week end"Amma Abdallah baya gida be jima da fitaba da yamma"bayan ya samu ummu ya gama tumurmusa sbd Anjima ba'a had'u ba"fitowa tayi cikin lambun gidan tana tafiya sbd tayi exercise"cikin yayo k'asa"kuma dama tun safe sai Ahankali jikin daurewa kawai takeyi"sai yatsina fuska takeyi tana shafa k'asan cikin"Ahaka wayarta tayi ringing"tana dubawa tayi d'an murmushi ta d'auka tana fad'in baby nayi fushi"dg d'ayan b'angaren sa'ada tace"sorry Anty nah"kinsan exams mukeyi wlh shiyasa"yauma naga week end ne nace bara nazo dai na ganki naji lafiyar baby nah"kin kyauta baby"saidai wlh yadameni da motsi sai y'an ciwace ciwace nakeji"wayyo Anty Ai kin kusa sbd jiya gabana yaya yace ma Ammi befi saura 1week ki haihu ba"hakane baby saikin iso"dg haka sukayi sallama"ummu da taji Abin yak'i lafawa saita wuce cikin gidan"da k'yar ta iso main parlour ta zauna kan carpet tayi zaman masu ciki"masu Aiki dake jera Abincin da kuku yagama sunata yimata sannu tana dai gyad'a musu kanta"batayi zaman mintina 10 ba Awajen sa'ada da sadeeq suka shigo cikin parlourn"daurewa tayi suka gaisa dashi ta lallab'a ta tashi tsaye tana fad'in baby zo muje ciki"dato ta Amsa ta kalli sadeeq ya langab'e mata kansa"tayi murmushi tana fad'in ka jirani pls"dato ya Amsa tabi bayan ummu data haye up stairs"turus sa'ada tayi data shigo cikin d'akin tana kallon ummu dake tsaye dafe da mararta tace"yaya dai Anty?"baby inaga haihuwar tazo, kinga ga troleys can guda 2 fita dasu sadeeq yasaka a mota muje Asibitin danake Awo"zan kira yaya Abdallah yanzun nasanar masa sai yasamemu can"Amma karki sanarwa Ammi idan An sauka sun sani sbd karsu damu"ta k'are maganar cikin k'arfin hali"jikin sa'ada Asanyaye ta jawo manyan troleys d'in ta fita"ummu ta saka hijab ta d'auki wayar ta da hand bag nata ta fito da k'yar"sbd har ta fara zubda ruwan nak'uda"Downstars ta tsaya ta sallami masu Aiki a gaggauce sannan ta rufe k'ofar ta wuce parking lot tana tunanin ta yaya zata sanarwa Abdallah ta fara labour?"ta sanshi zai damu gashi shi kad'ai yafita bada driver ba"gefen motar sadeeq ta tsaya ta fara k'ok'arin kiran Abdallah"kashewa yayi ya maido kiran"tayi murmushin k'arfin hali tana d'auka sbd duk sadda zata kirashi be bari Aci mata credit saidai shi Aci nasa"my heart beat! tattausan muryanshi ta katse mata tunani"Ahankali tace"yaya Abdallah gani nan nida baby zamuje Asibiti su Aunani baby ya cure waje guda"kai my khairee dama ba yana yin hakaba kuma sunce is normal?"nidai pls zanje kasameni Acan"okay yafad'a"ita kuma ta yanke wayar ta bud'e back sit ta shiga"sadeeq yaja motar yana yimata sannu shida sa'ada"cikin y'an mintina suka iso Asibitin"kasancewar komai nasu a k'a'idance ne ko sa'ada basu bari ta shigaba"ummu kawai suka bari ta wuce da kayan haihuwar"suka nufi labour room da ita"kasancewar Asibitin batada banbanci data k'asar waje cikin k'ank'anin lokaci suka fara Aikinsu"sai gashi nakud'ar tayi nisa harta kai kusan 7cm"komai ya rikice Abdallah ya fad'o cikin labour room d'in"kasancewar A haraban Asibitin ya samu sadeeq da sa'ada suka masa bayanin haihuwace"ummu na ganinsa ta fashe da kuka tana mik'a masa hannunta guda da rok'onsa gafara mutuwa zatayi"gaba d'aya big man yarikice yana k'ok'arin nufarta wata doctor ta girgiza kanta tana fad'in yayi hak'uri yafita dg ciki"saidai kafin yayi mata mgn"ummu tasaki wani Azabebben nishi Atake baby girl ta fad'o duniya tana tantsara kuka"jajir da ita me gashi"saidai sak kamannin mahaifinta ne da ita" farin ne da gashin kawai na ummu"Abdallah yayi hamdala yana kallon ummu data sume"nurses na k'ok'arin yanke cibi"yakalli yanda jini ke fita Ajikinta ya d'auke kansa cikin tsananin jin tausayinta da k'aunarta"k'asan ransa kuma yana k'ara ganin k'ok'arin mata dasuke haihuwa sbd ya tabbatar ta wuce wasa....duk yadda doctors suka tabbatar masa matarsa da y'arsa normal suke cikin k'oshi lafiya yatafi"Amma yak'i tafiya har Aka gama shirya babyn Aka dawo kan ummu"sai sannan big man yafara kiran sa'ada dake tsaye haraban Asibitin yasanar musu An sauka"sannan yakira Ammi da kamal da Aminu duk ya sanar musu"lokacin kuma ummu ta farko"ya kalleta yana murmushi ta sunkuyar da kanta"khairee nah sannu kinjiko?"bbu Inda ke miki ciwo ko?"kanta ta kawai gyad'a masa"yana murmushi ya Amshi babyn yana fad'in nakawota ki ganta?"nok'e kafard'arta tayi tak'i mgn"yayi murmushi kawai"suka Amshi babyn da sanar masa idan be fitaba zasu bashi matarsa da y'arsa yabar musu Asibiti, sannan ya hak'ura yafita"wani d'aki na bincikar lafiya Aka kai babyn"ummu kuwa saida suka saka ta d'auraye jikinta da ruwan zafi ta canza kaya sannan suka turata d'akin hutu suka d'aura mata drip da mata Alluran bacci..... Acikin y'an mintina mutane da yawa suka sami labarin k'aruwar da family d'in Alh mohd jibo suka samu....bayan sallar magrib Abdallah yadawo suka nuna masa d'akin da ummu ke ciki"had'e da sanar masa sai gobe zasu basu sallama idan sun gama bincikar lafiyar uwar da y'ar"dan babyn tanama wajensu"dato ya Amsa yana rik'e da kaya nik'i nik'i Ahannunsa yatura k'ofar ya shiga ciki"ummu na zaune kan bed d'in ta jingina bayanta Ajikin pillow tana waya da mama"tana jin sallamar gwanin nata tayi murmushi had'e da yiwa mama sallama ta Ajiye wayar"suka had'a ido"tayi murmushi ta rufe fuskarta"shima murmushin yayi ya Ajiye kayan hannunsa ya zauna gefenta"yana fad'in my khairee nah yau kuma kunyar habeebin Akeji ne?"uhmm! kinji?"yafad'a murya can k'asa yana koma matsota jikinsa"ta saki kukan shagwab'a"menene?"da fatan normal kike ko?"bbu wata matsala fa yaya Abdallah yanzun nanma na farka"nasan babyn tana wajensu ko?"Eh tana can"Ammi na gaisheki da baby da Abokina"bbu halin kowa yazo kinsan yanayin tsarin Asibitin nan"sannu khairee nah"bansan miye zan miki ba sbd farin cikin da kikayi sanadin shigata Aciki?"bbu Abinda zaka mun face nuna k'auna"kuma kanuna mun yaya Abdallah meye zan buk'ata Aduniya?"saidai fatan mu cika da kyau da imani"ina sonka mijina ina kuma Alfahari dakai"wanda ban tab'a zaton zanyi farin ciki ta sanadin AUREN YARJEJENIYA ba"sai gashi nayi kuma cikin yi nake"ta k'are maganar tana k'ank'amesa"Abdallah na murmushi cikin jin dad'i yana furta I love you so much my lovely wife"I love you too habeebi....bata rufe bakiba taji bakinsa cikin nata"bbu musu ta tallabe kansa tana tayashi"saida yagaji dan kansa yacikata suna murmushi"murya can k'asa yace"khairee nah bazakije wankan gida bako?"Eh yaya Abdallah banaso naje sbd kar nayi nisa dakai"yauwa tawan dama munyi mgn da babah d'azun danaje gidan bayan nabar nan"goggo luba zatazo da safe acan zata zauna har Ayi suna kafin me saka ruwa ta dinga Aikinta"to shikenan Allah yakaimu"ya Amsa da Ameen"da kansa ya had'a mata tea me kauri yazuba mata uban Abinci da namomi"tasaka rigimar tare zasuci Abincin"beyi musu ba sukaci Abincin sannan yatafi yayi sallar isha'i"ita kuma tasha magunguna ta shige bath room ta k'ara gyara jikinta tazo ta kwanta"Ahaka Abdallah ya shigo yana waya da Ammi"ya nufi kusada ummu yana fad'in gata Ammi"ummu na murmushi ta karb'i wayar tayi sallama"Akunyace suka gaisa da Ammin tana tambayarta ya jikin nata?"ta sanar mata da sauk'i"sannan sukayi sallama"Abdallah na kallonta yace"khairee nah nanfa zan kwana"to dama yaya Abdallah inba kai d'in ba bbu wanda zai kwana Ai"hakane kinsan mena tuna?"turo baki tayi tace"ah ah kuma banaso naji"yayi murmushi yana zama gefenta ta kwanto Ajikinsa tanata shagwab'a"Ahankali yace"last time damuka zo nan natuna"Anata wahalar dani ko?"shiru tayi yakama dariya yana fad'in pls kayafemun mutuw....kukan shagwab'a tasaka ya rungumeta yana dariya"sun jima suna firansu sai wajen 10 pm suka kwanta bacci rungume da juna.....

Washe gari....✍️

mu had'e last page da dare insha Allah
❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯ *AUREN YARJEJENIYA* ❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯

*73&74*


Washe gari misalin k'arfe 7:35 am Aka bama ummu da babyn sallama"sbd Antabbatar da suna cikin k'oshin lafiya"Abdallah ne sab'e da babyn"sai ummu na gefensa kanta Asaman kafad'arsa"tanata murmushin jin dad'i"kai tsaye haraban Asibitin suka nufa"kasancewar dama saida yakai kayansu yasaka cikin boot sannan yadawo suka tafo atare"da kansa ya bud'e mata gefen me zaman banza ta shiga ta zauna"kafin yaza gayo yana murmushi ya shigo ya mik'a mata babyn"wacce Idonta biyu tanata y'an kalle kallenta"saida ya tashi motar kafin yace"second me jego nacan fa my khairee itada goggo luba ke kawai suke jira"wai kana nufin baby na can?"Eh mana tun 7 am ta kirani suna can na Aika musu da key"saina tura driver yakai musu"yanzun haka tana can tana had'a miki break fast itada kuku"nasan ita kuma goggo nacan najiran mu ta mana wanka"ni wlh tsoron ruwan zafin ma nakeyi sai naga kamar zan k'one ne....bazaki k'one ba khairee nah"data miki safe da yamma shikenan zaki iya da kanki"banaso Ayita kallemunke Atub'e"kuma idan zaki shayar da ita banaso ki fitomun da Abuna mutane su gani"yafad'a yana kashe mata ido guda"murmushi yasub'uce mata ta kwanto Ajikinsa tana fad'in yaya Abdallah bakaji Allah yagyara mun kai"indai Akanki ne my hear beat bbu Abinda bazan iyaba Ai"to Amma yaya Abdallah wajen shayarwarfa Ance da zafi ko?"bafa sosai bane karki damu daurewa zakiyi"idan kuma bakya son shayarwar sai Abata madara"ah ah zan daure kawai"to yanzun nida dare ya zakiyi dani?"wajen me?"hararan wasa yamata yana fad'in kin fini sani"ta saki kukan shagwab'a tana masa rad'a atgefen kunne.... Atake yaji kasala da mutuwar jiki"murya Akasale yake fad'in my khairee kinsan banida wuyar kamuwa ta wannan fannin ko?shine kike mun Abinda zaki tayarmun da hankali gashi kuma kina jini....nadena yaya Abdallah"yanda nake jinka Araina komai kakeso zan maka"insha Allah da jinin ya d'auke zan baka kaina koda ban warkeba"yayi murmushin jin dad'i yana fad'in kota hanyar romance ma kina gamsar dani khairee nah"nasan kina k'ok'ari sosai zan hak'ura iya romance d'in har kiyi 40days d'in"dukda dai nafison wancan"Allah yataimakeni d'azun nayi na ban kwana"yak'are maganar yana yin parking"itadai tana murmushi ta bud'e k'ofar suka fito Atare"ya mairarai ce murya wajen fad'in karfa bak'i y'an barka su saka ki manta dani my khairee"bazaka iya tab'a mantuwa ba Acikin zuciyar khaireenka koda daidai da second d'aya ne Aduniya yaya Abdallah"karka damu muje ciki kaima kayi wanka na kamaka break fast ko?"bece komaiba saidai kawai taji yayi hugging nata ya matsesu itada babyn yana furta ina sonku my family"ta dinga dariya tana fad'in yaya Abdallah kar wani ya gammu fa"ko babah ne ke tsaye bazanji kunyaba khairee nah"zan iya nuna soyayyar danake miki Agaban idon kowa"yanzun kuje ciki bara na shigo da kayan dake cikin boot nida security"dato ta Amsa tana tafiya cikin farin ciki da jin tsananin k'aunar mijin nata na k'aruwa Aranta....da sallama ta shigo cikin parlourn"Anty wasilah da goggo luba da sa'ada na zaune sai masu Aiki dake shirya Abin break fast saman dining table"ihun murna sa'ada tayi taje ta rungume ummu da babyn su duka tana fad'in Alhamdllh my doughter da sweet heart take kama"ta k'are maganar tana kallon babyn"Anty wasilah ta taso itama tana kallon baby"Abdallah ya shigo da kaya Ahannunsa shida wasu yana fad'in khairee nah kinji dai dani take kama ko?"turo baki tayi ta kallesa yamata murmushi"goggo Luba tabisu da kallo tana mamakin yadda Abdallah keson ummu dashi da danginsa....ni kuwa nace kyawawan halayen ta da hak'urinta yakaita wannan matakin"ina kwana goggo?"cewar Abdallah"ta Amsa fuska Asake ta masa barka"kafin ummu ta matso ta zauna suka gaisa"ta Amsa da tambayarta ya jikinta?"ta fad'a mata da sauk'i "ummul khairy kuje kiyi wanka yaka mata ace kinyi wanka yanxun ko?"dan nidai nice zan yiwa kishiyata"cewar Anty wasilah"dato ummu ta Amsa suna dariya"Abdallah ya wuce part nasa"goggo luba da ummu suka wuce d'akinta dake nan down stairs"babyn kuwa d'akinta da aka shirya mata komai Anan Anty wasilah da sa'ada suka nufa....cikin mintina 45 Anty wasilah tayima babyn wanka na Asali ta gashe mata jikinta ta shiryata cikin kayan sanyi ta goyata"danda nan tayi bacci"ummu ma hakan ne"sosai taji dad'in jikinta da aka mata wanka"bayan ta fito ta shirya cikin sabuwar Atamfa super exclusive lemon green me zanen blue da fari"sai gashi ta fito sak a Amaryar jegonta"dandanan Anty wasilah ta cika gaban ummu da Abinciccika,irinsu kunun kanwa ,farfesun kaji,Anta gasassa"tuwon semonvita da sauransu"tana fad'in kici ki k'oshi ba'ason me jego na zama da yunwa"sosai taci ta k'oshi tasha magani"sai bayan ta tura sa'ada takaima big man Abin break fast sannan ta kwanta bacci me dad'i ya d'auketa.....wajen k'arfe 2 pm lawisa da leemart dasu Asiya duk suka bayyana"
Ahaka Aka cigaba da zaman barka ummu da baby girl na samun kulawa sosai wajen mutane"gefe guda kuma bbu ruwan Abdallah ko gaban wa nuna mata soyayya yakeyi"saidai ita tayita jin kunya"duk dare saita sace jiki taje d'akinsa sun soye sannan ta dawo su kwanta"Aranar kwana biyar Aka kawo kayan barka"fad'in dukiyar da Abdallah yakashewa ummu da babyn b'ata bakine"kowa fad'in masha Allah yakeyi"ranar suna y'a taci *Jamila* Ana mata Alkunya da *Amaan* wanda ranar sunan a hotel Akayi taron suna sbd kar Ab'ata musu gida"yayinda duk wanda yaje wajen taron sunan yasan nera tayi kuka ta zauna"shiga kala 7 ummu tayi duk itada Abdallah"marok'a wajen kam ba'a mgn"sa'ada da lawisa sune k'irjin suna"da haka taro yatashi lafiya kowa ya watse"ummu da Abdallah da babyn suka wuce gida Agajiye"goggo luba da sa'ada kuwa Anan suka kwana da wasu mutum biyu cikin dangin mama.....awashe garin suna Abdallah yayima ummu Albishir yabiya ma mama da baba saudiya"tsabar farin ciki rungumesa tayi tanata kukan farin ciki dayi masa godiya har saida yace"godiyar tayi yawa"Aranar ummu sun soye da big man kamar bbu gobe....

*bayan shekara ukku*
Ahankali wata had'add'iyar mota bak'a tayi parking gefen wani shago da Akeyin lalle da retouching"dg bayanta wata motace itama ta tsaya"da sauri driver ya fito ya bud'e back sit"Abdallah da ummu suka fito cikin shiga ta Alfarma"sunyi kyau cikin shigar shadda sky blue iri d'aya"ummu na rik'e da hannun Amaan"Abdallah kuma na sab'e da baby boy d'in da suka Haifa last 3 month"sun k'ara kyau da k'iba"ummu ta k'ara zama hamshak'iyar mace"dan yanzun har dubai take fita sarin kaya"shaguna Abdallah ya bud'e mata"tana siyarda hand bags da dogayen riguna Abayas irin na y'an gayu"wanda umar k'anin ta ke kula da komai...cikin tattausan muryanshi da har yau bata canzaba ya kalleta yana fad'in mommy kin cika rigimar sai kinyi lallen nan"banaso ajemun da yaro cikin mata Anata hayaniya kinsan besan hayaniya yanxun saiya fara kuka ko?"kai yaya Abdallah idan banyi lalleba bikin baby sunkutum Ai ban kyauta ba"Amatsayina na k'irjin biki ko?"ta fad'a suna dg tsaye gefen motar"Abdallah na murmushi yace"hakane kuma khairee"Ai gara kimata Aure komun sarara da zaryar da sadeeq ke mana Agida"kai yaya Abdallah?"ta fad'a tana dariya"Adaidai lokacin da nahni d'in Amaan ta fito dg cikin motar dake bayansu ta iso gefensu"ummu ta cika hannun Amaan tana fad'in kuje ciki ki rik'eta Afara yimata lallen gani nan zuwa"cikin ladabi ta Amsa dato"ummu ta kalli Abdallah tana fad'in to Habeebi bani babanah mu wuce"da An idar zan maka waya pls"Amma Allah nidai baza kaje wajen dinner ba"kawai y'an mata suyita kallemun kai"bayan inaji dakai kamar k'wai...yasaki k'asaitaccen murmushi yana k'ok'arin mgn sukaji sallamar wata mata Abayan su"juyowa Abdallah yayi sukayi ido hud'u da umma balki dake zaune cikin keken guragu wani yaro na turata"kasancewar da k'yar tasamu lafiya"saidai b'arin jikinta ya mutu baya Aiki"kasancewar Abdallah beda mantuwa Atake yaganeta"ummu ce bata ganetaba kawai"Amma sai bai nuna yagane taba"kuka ta fashe dashi tana fad'in Abdallah nice balki"wucewa zamuyi naga kamar kune,sai nace bara nazo naduba"kaga yadda rayuwa tayi juyin waina dani sbd Alhakin ku ko?"innalillahi wa inna ilaihir raju'un"ummu ke furtawa Aranta tana k'ara jin tsoron duniya"Abdallah ya saki Ajiyar zuciya bece komaiba yabud'e k'ofar motar yashiga"kud'i ne rafar y'an dubu guda ukku ya d'akko ya mik'a mata"hannunta na kirma ta Amsa tana hawaye had'e da neman gafaransa"yace"suje ya yafe mata"kuma zai rok'i daddy Alfarma da Ammi su yafe mata"tanata godiya ta wuce bayan ta rok'i yafiyar ummu"wacce tasanar mata Ai ita bata mata komai ba"sai bayan ta wuce jiki Asanyaye ummu tace"tabbas habeebi duniya Abin tsoro ce"kar bawa yaga yasamu wata dama ya tsula tsiya"dan idan ta tashi juyin waina da mutum sai sunansa sory"bari kawai khairee"kinsan kwanaki nasanar miki su junuid har office nawa sukaje neman yafiyata bisa jagorancin kamal"na hak'ura na yafe musu kodan sbd kamal kuma Allah nason masu yafiya"sai dg baya wata rana ina cikin mota na hangosu bakin titi suna goge gaban glass d'in mota ana basu nera 50"nayi mamaki sai kawai nasaka Aka tsaya Aka kirasu na basu kowa dubu d'ari biyar biyar suje suja jari"ka kyauta habeebi"shiyasa kaketa yin gaba Aduniya"domin duk me saurin yafiya dayin sadaka Ab'oye" yana kuma kyautatama iyali da iyayensa zaita ganin gaba Arayuwarsa"Ajiyar zuciya Abdallah yasaki yana murmushi yace"hakane musammun idan kadace da mace ta gari irinki me d'ora miji turban data dace"har gobe ina Alfahari dake Ummul khairee Amatsayin matata"ta lumshe idanuwanta cikin jin dad'in kalamansa tana fad'in nima haka habeebi"yau zan baka mamaki samqn bed sbd jin dad'in kalaman nan naka"ta fad'a murya can k'asa k'asa"yana dariya yace"da gaske?" Eh mana "to shikenan bara nakoma office inkin gama sai nazo mu wuce gida ko?"dato ta Amsa tana murmushi ta Amshi babyn"ta bud'e masa back sit da kanta ya shiva" tana masa addu'ar sauka lafiya"driver yaja motar yana jin koda yaushe uban gidan nasa da matarsa ba k'aramin burgesa sukeyiba"sbd ya fahimci suna zama na so da Amana da ganin mutuncin juna.......

Tamat Bi hamdilillahiπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Anan nakawo k'arshen wannan litttafi me taken AUREN YARJEJENIYA"kuskuran dana Aikata Aciki yah Allah kayafemun ka bani ladar Abinda nayi wanda ke daidai....

Ina mik'a godiyata ga Allah SWT daya bani ikon farawa zuwa kammala wannan book lafiya"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login