Showing 36001 words to 39000 words out of 93107 words

Chapter 13 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete

fiddo wata takarda dg cikin Aljihun wondonsa ya Ajiye remote d'in kan center table yafara ketata takardan gutsi gutsi yana watsasu samqn carpet...ummu data gama Ajiye komai zata juya da nufin taje tayi wanka ta lura da Abinda yakeyi....wannan Abun dakayi kana ganin daidai ne ??"d'ago kansa yayi yajefa k'wayar idonsa cikin tata"beyi mgn ba fuskarsa kuma bbu Annuri"wani irin mugun shakkarsa da fad'uwar gaba taji duk lokaci guda"da sauri ta d'auke kanta" cikin rainin wayo yace"Abinda nayi daidai ne idan kin isa ki hana mana"na lura kina buk'atar koma yin kuka yanzun ko?"tunda gashi kin jima jiya kina kuka"an fad'a miki Akwai wanda nake shakkar yasan kinyi kukan ne?"Abinda kawai zakiyi ki burgeni shine kiyi kukan jini"uhmm bazanyi kukan jini ba"nayi dai na hawaye saidai kai idan katashi na zuci zakayi"kuma banyefa maka muguntar daka....ganin zai taso yasaka ta fashe da kuka zata gudu"hakan yayi daidai da shigowar sa'ada cikin parlourn"kasancewar yau sunday bbu skul"da kallo tabi ummu Atake ta fahimci tana cikin b'acin rai ga kuma kuka tanayi"Abdallah kuwa koma had'e rai yayi ya wurgoma sa'ada harara yace"ke koma Inda kika fito"yak'are maganar yana tun karo Inda ummu take"saidai batayi k'ok'arin guduwa ba"hannunta guda yake k'ok'arin kamawa ta janye da sauri tana fad'in karka tab'amun hannuna"wai yaya meke faruwa ne dan Allah??"kidena kuka Anty ummu"cewar sa'ada"wai baby baraki tafi ba?"bbu Inda zanje yaya"in kuwa ka tursasani natafi nida part d'in nan har Abada"ta k'are maganar cikin jin haushi"ni kike gayama mgn?"kayi hak'uri yaya laifin me Anty ummu ta maka ne?"bansaniba ina ruwanki?"ummu bata koma mgn ba tana jan Ajiyar zuciya ta wuce d'akinta"itama sa'ada bata koma mgn ba yana kiranta ta masa banza ta fita"damuwarsa kawai karta sanarwa Ammi da wani abu"hakan yasa ya wuce ciki ya sakko jallabiya yabi bayan ta"ummu kuwa wankanta tayi ta shirya cikin riga da siket na lace ta fito ta nufi dining area ta zauna kan kujera ta kife kanta samqn center table"Ahaka inna uwani me Aiki ta turo k'ofar ta shigo"gaisawa sukayi ta rok'eta Alfarmar taje ta kira mata sa'ada"bbu musu ta tafi"ba'a jimaba suka dawo tare da sa'adan"ummu na kallonta tace"kiyi hak'uri baby kizo muyi break fast kinji?"turo baki tayi tazo ta zauna tana fad'in da har nace kema bbu ruwana dake Amma mun shirya dake"kiyi hak'uri da halin yaya wlh haka yake Anty ummu Amma zai daina"kuma saina sanarwa da Ammi"damun b'ata dake baby in har kika same maya "karki sake ki sanar mata da komai koda wasa kina jina?"dato ta Amsa"dg nan suka cigaba da break fast d'insu sunata fira...."Abdallah kuwa duk Abinda ke faruwa yana ganin su ta laptop d'insa daya jona ta CTV camera"yatab'e baki yana rufe lap top d'in"sbd yau bema nemi ummu ta fiddo masa kayan sawa ba"shiyayi komai da kansa sbd haushinta yakeji"cikin jarket orange da black d'in trouser ya shirya"yanata k'amshi hannunsa guda cikin Aljihun wondonsa"yayinda gudan hannunsa ke rik'e da phones nasa"ya sakko down stairs d'in"dg ummu har sa'ada d'in bbu wanda yabi takansa"wanda sa'ada tabashi haushi sosai otama....muryarsa bbu wasa yace"sa'ada zo nan! batayi musu ba tabiyosa Abaya"suna fitowa dg parlourn yaja tsaki yana fad'in Ammin dana miki warning karki sake ki kai mata wata mgn shine naji kina cewa zaki sanar mata??"ah ah yaya kayi hak'uri"ni banceba"ki rantse baki ceba"nidai bbu kyau yawan rantsuwa haka Anty ummu tacemun"shiru yayi kamar me tunani sai kuma yace"jiya da yau sadeeq bakuyi karatu dashi ba?"Eh kusan 4 days ma sbd hidimar biki da Akayi"jiya yace mun zaizo na rakoshi su gaisa da Anty ummu"Amma ni yanzun yaya Anty ummu zata dinga koyamun karatu"tasanar mun nadinga kama kaina gaban ko wane namiji na rage surutu saiya kama nayi mgn"dama kuma ina jin kunyar yaya sadeeq"kaga ita zata dinga koyamun shi kuma yaya sadeeq saimu dinga gaisawa dashi....nanma shiru big man yayi yana danna waya"sai kuma yad'ago kansa ya kalleta yace"hakan ya miki ne?"Eh yaya yayi"Amma dan Allah kadena saka Anty ummu kuka tanada kirki wlh....kallon daya mata yasaka tayi shiru"zo muje kimun rakkiya"ita Anty ummu meyasa barak..... sa'ada yaushe nafara wasa dake?"yakatseta cikin zafin rai"Allah yabaka hak'uri yaya"Amma kwana 2 da Aure har zaka fara fita?"banza yamata"tana k'ok'arin koma mgn tj da junuid suka iso wajen"tab'e baki sa'ada tayi sbd haka nan haushi suke bata"badan tasoba ta gaida su"big man yabasu hannu sukayi musabuha"tj yace"munzo gaida madam ne"banza Abdallah yamusu yacigaba da tafiyarsa ta isa da gadara"ita kanta sa'ada kallonsa takeyi har yayi gaba su tj suna biye dashi"sa'ada kuwa part nasu ta koma ta shirya ta tafi islamiya....ummu kuwa wajen 10 ta kwanta bacci sai 12:30 pm ta farka"ta fito main parlour ta duba taga Abdallah yadawo yayi break fast har yakoma fitama"kitchen ta koma ta Aza farar taliya super getting da miyar kifi"sannan ta had'a masa lemon Abarba ta gasa masa naman rago"sai wajen k'arfe 2 tagama"taje tayi wanka"bayan tayi sallah ta shirya cikin riga da wondo na kanti"wondon coffee brown ne"saita sakq t shirt dg ciki fara"dg sama ta saka riga me bud'add'en gaba milk"ta shafa jam baki red"ba k'aramin kyau tayiba"fitowa tayi parlourn ta zauna tana jiran shigowar sa'ada sbd suyi lunch tare"wayarta ta d'auka ta kira lawisa"sun jima suna fira"sannan takira Aminu da umar tana musu mitar sunk'i zuwa su ganta"tana wayar ne sa'ada ta shigo da sallama...."wow masha Allah!"kinyi kyau sosai kamar baturiya Anty ummu"kinsan fa yaya Abdallah kayanmu na gargajiya basu burgesa yafison mace ko namiji suyita saka k'ananun kaya"yanzun haka baya d'in kamun shadda ko lace saidai daddy ke d'inkamun"shi saidai yayita jibgomun manyan kaya"shima Ai baya son saka manyan kayan"cewar ummu data Ajiye wayar"tana tashi tsaye tace"muje muci Abinci"daga haka suka nufi dining area d'in.... k'at suka yima cikinsu sa'ada nata santi"bayan sun gama suka zauna ummu na k'ara koya mata Abinda bata gane ba"sbd yanzun har taje SS1"kasancewar sa'adan nada k'ok'ari"jumping Abdallah keson yamata shiyasa yabar sadeeq na k'ara koya mata Abinda bata ganeba"sai sa'ada d'in taga ummu tama fi sadeeq iyawa"ni kuwa nace to ai ita malama ce....saida aka kira sallar la'asar sannan suka tashi sukayi sallar"bayan sun idar suka dawo parlourn"ummu na duba Agogon dake manne jikin bango tace"hud'u saura kije kiyi shirin islamiya baby"kai Anty ki idamu koyamun yadda zanyi Assignment d'ina mana"ummu na k'ok'arin mgn Abdallah ya murd'a handle d'in k'ofar ya shigo"da Alama dg office yake yana rik'e da wasu takardu da jakarsa"can k'asan mak'oshi yayi sallamar"ummu ta kallesa ta Amsa tana fad'in sannu da zuwa"be Amsaba saima ya d'aure fuskarsa"dukda haka ta taso ta Amshi jakar daya rik'e tana fad'in zakayi wankan??"saida yagama hura hancinsa sannan yayi lokacin kulata yana fad'in uhm"tayi d'an murmushi kawai ta wuce upstairs"sweet heart sannu da zuwa"harara ya ballama sa'ada takama dariya ta taso ta rungumesa"ya dungure mata kai yana fad'in boarding skul zan kaiki"daka kasheni yaya"Akanme?"yo idan Anty ummu ta haihu wace uwar d'an ko y'ar idan bani nan??"haka nan yaji fad'uwar gaba"saidai be kaiga mgn ba ummu ta sakko down stairs d'in tana fad'in na gama komai"shiru yayi ya janye sa'ada dg jikinsa yana fad'in kije islamiya"dg haka yanufi dining Area"kujera yaja ya zauna yana jin sa'ada nayiwa ummu sallama ta fita"warmers d'in Abincin yaduba....wasu irin dogayen tsuka yadinga ja"ya juyo ya hango ummu na zaune tana murmushi tana danna waya"saima sannan ya lura da irin dreesing d'in dake jikinta....K ! d'ago kanta tayi suka had'a ido"d'aure fuska tayi tace"wai bakasan sunana ba malam dazaka dinga cemun K? Da hakan da gadamar kiranki in na kiraki karki Amsa dan Allah"yak'are maganar cikin zafin rai"Allah yabaka hak'uri ni bana neman fad'a"yatab'e baki yana fad'in to dama tunda kinga Anfi karfinki Ai dole ki Ajiye wani zafin kai yarinya"batace komaiba taje gefen k'afafuwan sa ta duk'a tace gani"shiru yayi yana danna waya"k'amshin humran da kulaccan dake jikinta nata kaiwa hancinsa ziyara"kanafa jina ina mgn?"nanma banza yamata" *yayan sa'ada* murmushi yaso ya sub'uce masa saiya dake yak'i yi"yasha Alwashin muddin bata kira shi da sunan saba zatasha wahala" sbd rainin wayo shine zatace wani yayan sa'ada....duk yake zancen Acikin zuciyarsa"saidai Azahiri danna waya yakeyi kamarma besan da zamanta ba Awajen.....✍️

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤‍🔥❤‍🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤‍🔥❤‍🔥

*29&30*


........Girgiza kansa big man yayi ya kalleta sama da k'asa yatab'e baki"yaja k'aramin tsaki yana fad'in bazan sake kiba tunda sakin kike da buk'ata"saidai zan baki zab'i biyu ko kizo ta Arzik'i ki canzo mun kayan nan ko kuwa wlh na miki Abinda harki rabu dani bazaki manta ba" zab'i yarage naki"Ada nace zan fisge towel naki"saidai na fasa sbd bazan iya bak'in gani ba"ummu bata tankashiba tana share hawayenta"shi kuwa wayarsa yad'aga da preety keta faman kiransa tun d'azun"hands free yasaka wayar beyi mgn ba"cikin k'asa da murya had'e da karairaya preety ke fad'in hellow baby nah"d'an yamutsa fuska yayi yace"my preety ykk ?"lafiya qlau Amma kewarka yamun yawa"tunda kayi Auren nan shikenan ka manta dani ko?"shiru yayi yana sauraron ta idanuwansa Alumshe ya kwantar da kansa jikin bango"baby kamun shiru ko kuna tare da matar taka ne??"tsaki yaja ya bud'e lumsassun idanuwansa yakashe wayar"yanufi k'ofa "ummu ta kece da dariya tana fad'in na tausayawa wannan wahalallliyar yarinyar wlh, da take wannan rawar kan da zumud'in Akanka"bayan Banga Alamar ka cika namiji ba"yana jinta be tankataba yabar d'akin da nufin zasu had'u"ita kuma tasaki Ajiyar zuciya ta tashi ta nufi wajen ward rope ta d'akko sabuwar Atamfa riga da siket tasaka"tana rik'e da d'an kwalin ta fito da nufin taje ta canzo masa kayan sbd tsoron masifarsa"tana k'ok'arin shiga bed room d'in nasa shi kuma yana k'ok'arin fitowa harda belt hannunsa.....kusan cin karo sukayi"tayi baya da sauri tana d'aure fuska"shi kuma yaja tsaki yana binta da kallon k'asan ido yace"k'aramar marar kunyar k'arya"aida kin bari nazo ta haka kawai zan tabbar ke babbar marar kunya ce"karka koma jifata da irin wannan kalmar"idan nakoma fa?"yafad'a Afusace yana tunkarota"sai sannan ta lura da belt d'in dake hannunsa"gabanta yafad'i Amma saita dake tana fad'in koma miye zan iyayi akan jifata da irin wannan kalmar da kakeyi"dan Allah ki d'auki matafin yanzun kinjiko?"zakizo ki wuce kosai kinja na makara??"kana bani mamaki wl.... k'aramar k'ara tasaki sbd ganin yakoma nufota"Aguje ta shige cikin bed room d'in"saidai ashe ya zuba shower jall k'asa kan tiles sbd idan tashigo ta taka"Aikuwa tana Aza k'afarta ta tafi suuuuuuuuuu! jikake timmmm"k'ururummm.....ta saki k'arar Azaba tana dafe kanta"big man daya biyo bayanta yasaki wata iriyar dariyar mugunta wacce bata tab'a ganin yayi irin taba"sannu ko?"yanzun kin yadda na cika namijin ko kuwa sai nayi reping naki sannan zaki yarda??"yafad'a cikin rainin hankali yana d'age kafad'a irin ko Ajikinsa da fad'uwar da tayi"ummu na dafe da gefen goshinta"hawaye na zuba samqn fuskarta"babban yatsan k'afarta na mata zugi"ga goshin yayi fushi daga gefe"saidai dataji ya Ambaci kalmar reping tsoro yaka mata"da k'yar ta samu ta tashi tsaye"batace masa komai ba ta rab'a gefen da bbu shower jall d'in ta fita"shi kuma ransa fari k'ar ya duba ya matsa jikin ward rope ya d'akko wasu k'ananun kayan yasaka"bayan yagama yima jikinsa wanka da turare yagyara lallausan suman saman kansa"saidai yarasa meyasa zuciyarsa ke ganin be kyautaba ga Abinda yayima ummu"duk sadda zaici zalin nata saiyayi tunanin be kyau taba"kuma gashi ita bata tab'a cutar dashi ba"da wannan tunanin ya sakko down stairs"yasami inna uwani da ummu zaune kan carpet tana ja mata babban d'an yatsanta na k'afa da Alama targad'e tayi"kallo d'aya yamusu ya d'auke kansa"yanufi k'ofa"inna uwani ta gaishesa ya maido mata gaisuwar"dukda tsohuwar ta d'an fahimci Akwai wata y'ar matsala tsakanin ummu da Abdallah Amma bata tambaya ba sbd ganin ba huruminta bane"sai sannu takema ummu harta gama fidda mata targad'en"Ahankali ummun tayi mata kwatancen gidan Ammi"inna uwani tace tasan gidan"500 na nafef tabata ta had'a mata komai tace"taje takaima Ammi"bayan fitar inna uwanin"ta zauna tayi shiru"kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin damuwa"saidai tasha Alwashin insha Allah zata fita harkansa" bazata dinga biye masa ba"yafitar mata da jini kwanaki yanzun yayi sanadin datayi targad'e....tana wannan tunanin sa'ada ta shigo parlourn"tasha gayunta cikin leshi d'inkin fited gownt pink colour"tanata k'amshi harda make up saman fuskarta"da fara'a ta shigo cikin parlourn saidai yanda taga ummu da yanda goshinta yayi fushi yasaka jikinta yin sanyi"Anty lafiya?"bigewa kikayi ne?"Eh sa'ada harda targad'e Amma an kamamun"wayyo Allah sannu Anty ummu"ta fad'a tana kallon idanuwanta ta fahimci kuka tayi"yauwa sai ina irin wannan gayu haka?"bbu ko ina Anty nan dai nazo"zan Aikeki gidanmu dan Allah?"to shikenan Ai nasan gidan"Inda kika sani gidansu lawisa ne"mu layi na gaba gida me dakali da fenti brown colour shine gidan mu"to shikenan bara ataso masjeed sai driver yakaini"wane driver d'in?"wanda yaya Abdallah ya d'aukar mun duk Inda zanje yana kaini da motata daya siyamun"inafa so na dinga driving Amma wai yaya yace nayi k'aranta sai nayi SSCE"kinyi k'aranta yanzun gsky gara dai nan gaba"yanzun tashi muyi sallah naga k'arfe 1:45 pm Antaso masallaci"dato sa'ada ta Amsa"kasancewar tanada Alwalah sai kawai tasaka hijab tayi sallarta"bayan sun gama sa'ada ta fito bakin get tasanarwa me gadi Inda zasuje"ya Amsa dato"ita kuma tadawo ciki ta Amshi sak'on"bayan fitarta inna uwani tadawo da fara'a tana fad'in hjy tana gaidaki sai godiya da sakq miki Albarka takeyi"tabani dubu 2 wlh"gaskiya kinyi sa'ar sarkuwa me kirki"murmushi ummu tayi batace komaiba"sbd ita dai tunda taga Ammi taji sonta da k'aunarta"tasan Abdallah ba halin ta bane yabiyo"can yakwaso mugun hakinsa...tashi tayi ta had'ama inna uwani Abincinta ta bata ta tafi gida"ita kuwa damuwa tasaka bata iya cin Abincin..... Abdallah kuwa yana fita a parking lot suka had'u da daddy" kowa zai shiga mota yatafi masjeed sallar juma'a"dukda sun gaisa d'azun da safe saida Abdallah yaje gefensa yakoma gaishesa"daddyn ya Amsa fuska bbu walwala yana fad'in Abdallah meyasa baka jin maganata?"subahanallahi! Daddy menayi?"kusan kwana7 kenan da zuwan iyalin taka gidan nan baka tab'a cewa tazo ta gaida bilkiba"kayi hak'uri daddy gobe zan rakota saita gaisheku dama inada niyar idan tacika sati saita fito"shikenan Allah yayi muku Albarka yabaku zuri'a ta gari"kasa mgn yayi domin itama Ammi duk idan yaje gaisheta irin wannan addu'ar take musu"da wannan tunanin yanufi motarsa driver ya bud'e masa back sit ya shiga aka nufi babban masallacin juma'a dashi....koda Aka taso dg masjeed d'in kamal yabiyosa wai zaizo yaci girkin Amarya"Abdallah dai bai tankashiba sbd shi office zaima je"koda suka shigo mota kamal yaga hanyar da sukayi be damu ba"saidai Abin mamaki da suka iso comparny d'in Abdallah"suka sami su junuid cikin office d'in Abdallah zazzaune"dukda Anan cikin camparny d'in suke Aiki Amma hakan ba daidai bane ga doka"Abdallah kuwa ko a fuska bema nuna musu komai ba"saidai sun kama kansu sunata rawar jiki"shi kuwa zama yayi kan kujera yakira mutanan da zasuyi mgn dasu dama sbd su yazo yanzun"babu jumawa suka iso"bayan sunzo sun gama mgn da mutanan ya kira sakatarensa da cleaner d'in dake gyara office d'in yagoge duk yabasu takardar sallama"sosai kamal yaji dad'in hakan"dama ka'idar Abdallah ce idan kayi laifi bazai sanar maka laifin dakayi ba, zai koreka kaine da kanka zaka gano laifinka"idan kuma yayi kora ko sama da k'asa zasu had'u baya maida mutum"junuid da tj sun tsorata sosai da korar mutum biyu da Abdallah yayi wanda sunsan suma danasu laifin"saidai suna ganin kamar bazai iya korar suba sbd suna Abokansa.....kamal be gama mamaki ba saida Abdallah yagama zamansa zasu tafi sai cewa sukayi zasu biyosu suje suci girkin Amarya"nanma be tanka musu ba"suka nufo gidan atare dasu.....
mama na zaune tsakar gidan tayi shimfid'a k'ofar d'akinta"tana lazimi sbd tana gama salla ta fito tsakar gidan"ta shirya cikin jar Atamfa Riga da zani"yayinda goggo luba ke zaune Riga daban zani daban duk sun k'ode"ga tsohon ciki"itama Asiyar tana kwance samqn tabarma da Alama yunwa ke damunta"uwar na daka kanzo da Alama shine zasuci"dan yau mlm rufa'i"500 ce yabama luba yace"suyi kalaci ita kad'ai ta rage masa"saida ta gama yada masa mgn kan cewa"wai sunan ya Aurar da diya gidan me kud'i Amma bbu kama bbu Alama" kud'in kashewa ya gagaresa da Abincin dazai ciyar da iyalansa"mama najinta ga lokacin tayi dai murmushi bata tanka musu ba"ita bema bata komai ba dukda girkintane yabata hak'uri"ita kuwa bata damu ba"tanada kayan Abinci da Aminu yasiya mata iya k'arfinsa"sannan umar yasiya mata kayan tea batada damuwa"shiyasa idan kazo gidan yanzun zaka d'auka Luba itace gora"idan ka jerasu kuwa tofa za'a d'auka Luba ta girmi mama"sbd duk lubar ta lalace jiki bbu gyara"kimanin kwana 7 kenan da Auren ummu kullum sai goggo luba ta yadawa mama haibaici"basuga Alamar y'arta na Auren me kud'i ba"ita tayi nata habaicin hjy yaya ma idan ta shigo tayi nata habaicin"mama dai bata tankasu hidimar gabanta takeyi....mamar nata lazimi tana jiran shigowar mahmood Autah sbd ta Aikesa yayo mata cefane tayi musu girkinsu.... Ahaka sa'ada tayi sallama cikin nutsuwa ta shigo tsakar gidan"tana rik'e da babban kwandon a hannunta guda"gudan hannun nata kuma kular da Aka zubo kunun Ayar ne"Amsa sallamar tata mama tayi"su goggo luba kuwa kallon sa'ada da kamshinta ke kai musu ziyara sukeyi bbu ko k'iftawa"ina wuninku?"lafiya qlau y'an mata"dama dan Allah ina mama ?"Anty ummu ce ta Aiko ni"mama na murmushi tace"gani nan taso muje dg ciki"bbu musu sa'ada ta d'akko kayan ta cire takalminta tabiyo mama parlourn ta"sosai ta yaba da tsabtar mamasbd parlourn fes yake yanata k'amshin turarukan wuta"zama tayi suka gaisa tabata sak'on inji ummu"mama tayi godiya ta d'auka ta wuce ciki ta juye"humra da turaren kaya masu kyau na y'an meduguri ta had'o ma sa'ada ta dawo parlourn ta bata"Aikuwa ta Amsa tanata zuba godiya"saadar ta Amshi kwandon sukayi sallama ta fita...goggo luba idan ranta yayi dubu bace yake ,domin boka yasanar mata Ai ummu zata manta da mahaifiyarta bazata dinga taimaka mata ba"Amma gashi taga An shigo da Abin duniya An wuce d'aka....bata gama wannan tunanin ba taji muryar mama na fad'in kai Alhamdllh! Allah Abin godiya"yau na tabbatar da y'ata na Aure cikin kwanciyar hankali" masu wani korafi batayi Aike ba kuma sai Acigaba dayi kar Afasa"iya Abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login