Showing 39001 words to 42000 words out of 93107 words
Chapter 14 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete
nasani idan fitsari banzane kaza tayi mugani.....sosai maganganun mama suka soki zuciyar goggo luba"Ahaka babah yashigo gidan yadawo dg masallaci"bakinsa duk yabushe"da Alama ba k'aramar yunwa yakejiba"mama ta fito tsakar gidan tana fad'in mlm kadawo?"nadawo hajara"sannu da zuwa"ga tabarma nan zauna naka maka Abinci"kinyi girki kenan?"ah ah dg gidan ummu dai aka kamana Abincin Amarya"to to masha Allah"yafad'a yana k'ok'arin zama"goggo luba ta tab'e baki tana cigaba da dakan k'anzonta"yayinda Asiya dake kwance tasaka rai da cin Abincin gidan ummun"plate ne me kyau mama ta zubo masa Abincin ciki"sannan ta zubo masa miyar daban tacika uban naman kaji"tazo gabansa ta Ajiye"take k'amshin miyar yakaima Asiya da goggo luba ziyara"mama kuwa d'akin ta koma ta zubo kunun Ayar cup guda babba tazo ta Ajiye masa"sannan ta koma tazuba Abincin cikin plate na roba da miya gefe da kunun Ayar cup guda ta fito tana kiran mariya"tana isowa gabanta ta mik'a mata tana fad'in kaima ummanku na gidan yayarkune ummu"jikin mariya na kirma ta Amshe"mlm rufa'i kuwa ba baka sai kunne lodawa cikinsa kawai yakeyi yana cizge k'ashi....lolx"mama kuwa d'akin ta koma ta zuba a plate tabama mahmood yakaima hjy yaya sbd tasan muddin ba'a kaiba sai tayi tsogumi.....goggo luba kuwa bbu kunya ta Amshe ta d'an ciccirama yara ta zubawa Asiya A marfin kwano ta tasa sauran gabanta tanaci hannu baka hannu k'warya"Asiya nata surutai ta Amsa sbd ta raina kason da uwar tasu tayi"kije mlm yak'ara miki mana"cewar goggo luba tana kallon Asiya dake sid'e marfin kwanon"mlm kuwa yakusan gamawa"saidai kafin Asiya tayi mgn mama ta fito rik'e da wani d'an bowl data zubo soyen naman ragon ciki ta Ajiye masa gabansa tana fad'in ga wannan mlm"kice abu dai dayawa hajara?"to Allah ya Amfana yamata Albarka"Allah yabasu zaman lafiya"mama na murmushi ta Amsa da Ameen"goggo luba Aranta tace"wato harda soye shine mu munafukar bata bamu ba??"Allah kad'ai yasan me y'ar ta Aiko mata dashi kenan.....mama dai batasan tanayiba ,wandama tabasu sbd Allah da hakk'in ganin ido yasaka tabasu Amma badan sbd halin suba"mlm dan Allah sammin tsoka biyu na sama bakina"kasan me ciki da....tsaki baba yaja yana fad'in bazan bayarba y'ar bak'in ciki"dg haka yace"hajara zoki kwashe kayan nan"yafad'a yana zaro leda bak'a dg cikin Aljihun rigarsa yajuye naman ya d'aure yamayar Aljihu"ya mik'e tsaye yanufi d'akinsa yana gyatsa"mama kuwa na murmushi ta kwashe kayan ta shige d'aki"Jim kad'an saiga mariya wai Asiya tace"dan Allah tabata tsokar nama 2"mama ta kalleta tace"yak'are"dg haka mariyar ta fita dg cikin d'akin.....
Ummu na zaune a parlourn tana kallon Arewa 24"sa'ada tayi knocking"ta tashi tana tambayar waye?"bayan taji muryar sa'ada ta bud'e mata k'ofar"da murna ta shigo parlourn tana nunawa ummu kyautar da mama tayi mata"d'an murmushi tayi tace"kin gode baby"kije kimayar da kayan kitchen kixo kici Abinci"dato ta Amsa ita kuma ta zauna kan kujera tana tunanin tabbas sai goggo luba taji zafin Abincin datakai gidan"bayan kuma da ita za'a ci"ta girgiza kanta kawai"sa'ada kuwa bayan ta zubo Abincin da kunun Ayar tadawo k'asa kan carpet ta zauna suna fira da ummu tana ci.... Ahaka Abdallah yasaka key yabud'e k'ofar yashigo"su kamal na dg waje"kamal yakafe saiya shigo yasanarwa ummu zasu shigo sbd haka shari'a tace"fuskarsa Ad'aure yashigo"Atake ummu tadena dariyar datakeyi ta kauda kanta gefe tana jin fad'uwar gaba"saidai sa'ada ce kawai ta Amsa sallamarsa tayi masa sannu da zuwa"wanda rashin tankasa da ummu tayi yatabbatar ma da sa'ada Abdallah nada Alak'a da bigewar datayi"baby tashi kije kicema su kamal su shigo"dato ta Amsa"shi kuma ya haye upstars"batare daya bi takan ummu datayi bala'in d'auke masa kai ba"ummu kuwa d'an kwalinta ta gyara ta mik'e tsaye da k'yar zata tafi kenan taji sallamar su kamal"sunkuyadda da kanta k'asa tayi ta Amsa sallamar tasu"kamal na murmushi yace"ranki yadad'e Amaryar mu"tana murmushi tace"yaya kamal ka koma nayi fushi"tuba nakeyi hjy ummu"Abubuwan ne sai Ahankali kuma ina bama Abokina sak'on ya gaida mun ke"hakane yana fad'amun" ina wuni yasu hjy??"lafiya qlau suke"yafad'a yana lura da k'urman dake samqn goshinta da idanuwanta da sukayi jaa"ya girgiza kansa yana tunanin yaushe Abdallah zai dena cutar da ita??"sai kuma yatab'e baki sbd ganin su tj sun nufi dining area"wanda basu tanka ummu ba sbd ganin yadda ta nuna bata damu dasu ba ta kamal kawai takeyi"to yanzun dai nazo naci girkinki kuma na goge laifina ko?ka kyauta sosai"hakan yayi daidai da sakkowar big man down stairs d'in"kamal yajefesa da kallon tuhuma"shi kuwa koma had'e rai yayi yaja kujerah ya zauna"ummu kuwa d'akinta ta shige sa'ada ta biyota"hakan yasa kamal dake tsaye shima yanufi dining area d'in yaja kujera ya zauna"kaine zakayi seving namu"cewar tj yana kallon big man"saida ya d'auki kusan second 10 yana yamutsa fuska yace"dabaku ci Abincin ba"dg haka yayi shiru yana duba warmers d'in"sam irin wannan Abincin na gargajiya be burgesa"dandai gasu zaune yakejin zaici ko kad'an ne"Amma in bacin suna wajen da saita sani....wow! Ina son Alkubus sosai"cewar kamal"Abdallah beyi mgn ba"Alkubus biyu wainar farar shinkafa biyu yazuba da miya Agefe"yayi bissimilah yafara ci kuma da cokali"yayinda su kuma kowane da kansa yazu bama kansa"sai gashi su ukkun sunata santi"Abdallah kuwa besan lokacin daya k'ara zubawa ba"kunnansa be tsinkeba saida yasha kunun Ayar dayaji kayan had'i"k'at sukayiwa cikinsu lokacin Anata kiran sallar la'asar"kamal nata yabama ummu da mata godiya"yayinda su tj kejin inama kullum Anan suke cin Abinci"kasancewar disgi halin Abdallah ne bbu wani kunya ya kalli su tj yace"kattin banza sai ku tashi kuje kuyi sallah"dukda nasan kai junuid bakayinta kan lokaci"dg haka yamik'e tsaye yana kallon kamal yace"jirani na fito mu wuce"dato ya Amsa duk suka fita Atare"wanda junuid yaji haushin maganar da Abdallah ya gaya masa gabansu kamal…....✍️
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤🔥❤🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤🔥❤🔥
*31&32*
....... cike da mugunta Abdallah ke rik'e da hannun ummun"sun jero idan kagansu zaka d'auka irin masoyan nan ne su masu bala'in son junan su"gashi hijab d'in jikin nata yamata kyau sosai"tsayinta iya kafad'arsa ne"suna k'ok'arin shiga babban parlourn gidan ummu tace"yaya Abdallah ka cikani kasan da kunya ko?"shiyasa nace ke bak'auya ce Ai"Eh naji d'an birni"ka cikani kona had'aka da daddy d'in yasin"murmushi yasub'uce masa yana fad'in kurarin banza kamar zata iya"nasan ko had'a ido dashi bazaki iyaba"canza topic d'in tayi da cewa wai jiya kaci d'an waken??"ta fad'a tana sakin murmushi me sauti"hmm! nidai ko?"dani kike zancen"Ai nasan sbd dama ki b'ata mun rai kikayi mun Abinci da mai da yaji"ummu bata sami damar mgn ba suka shigo cikin parlourn"umma balki da hafsat na hakimce samqn kujeru na Alfarma"sai masu Aiki dake jera break fast a dining area"ummu tayi sallama cikin siririyar muryarta"umma balki ta d'ago kanta ta kallesu gabanta na fad'uwa"saidai ta kasa d'auke idanuwanta kan hannayensu dake rik'e da juna"sai yau tak'ara kallon ummu sosai"ta tabbatar dama Abdallah sai mace me kyau irinsa zai iya Aure...lura da yayi ummu zata iya d'ukawa ta gaishe da wannan makiran matar yasaka ya sanya gudan hannunsa yadafa gefen kafad'arta ya manna bakinsa saitin kunnanta yana fad'in kinsan Allah kika duk'a kika gaisheta saina b'ata miki rai"itadai batayi mgn ba d'an murmushi tasaki"hafsat ta tab'e baki tana kauda kanta dg barin kallon su"umma balki kuwa murmushin yak'e tayi tana Amsa sallamar tasu"tana fad'in maraba da y'ata"ummu ta Amsa suka zauna gefen kujera ga k'ugunta gana Abdallah"kan ummu Ak'asa tace"umma ina kwana?"lafiya qlau y'ata yakuke?"Alhmdllh"batare daya kalletaba yace"ina kwana?"lafiya qlau Abdallah ya office d'in?"Alhmdllh"sai sannan hafsat tace"ina kwananku?"ummu ce kawai ta Amsa"Abdallah yajata suka mik'e tsaye suke nufi part d'in daddy"daddy na sanye da jallabiya yana zaune kan kujera da farin glass Asaman fuskarsa yana karanta jarida"ya Amsa sallamar tasu yana murmushi"ummu ta duk'a har k'asa ta gaishesa"ya Amsa mata cike da kulawa yana tambayarta bbu dai wata matsala?"ta Amsa da Eh"sai sannan shima Abdallah ya gaishesa"dg bisani daddy yace"masha Allah! Ayita hak'uri da yanayin zaman tare y'ata kuma kiyita biyayya dan Allah"kaima Abdallah ka kasance me Adalci da kyautata mata"duk suka Amsa da insha Allah"suna k'ok'arin tashi daddy yajawo wani kwali gefensa ya zaro rafar y'an 1k ya mik'ama Abdallah yana fad'in gashi ka rik'e mata"juyowa ummu tayi ta girgiza kanta tana fad'in dan Allah daddy Abars.... ba'a mayar da Alkhairi y'ata"daddy yakatseta yana bama Abdallah kud'in"Atare suka masa godiya suka fita"sbd umma balki taga kud'in yasaka Abdallah barinsu a hannunsa be bata ba"dan yasan data gani tasan kyauta daddy yayima ummu"yana wannan tunanin ummu tace"yaya Abdallah inane d'akin baby ka rakani??"ta fad'a Ahankali sadda suke isowa main parlour"shirin office zanyi ki bari tazo Ai"nidai dan Allah ka nunamun in baraka jirani ba"ta fad'a tana b'ata fuska"beyi mgn ba yanuna mata k'ofar d'akin sa'ada da hannunsa"zare hannunta dg cikin nasa tayi ta nufi bakin k'ofar d'akin tana yimata knocking"shi kuma ya zauna gefen kujera"sa'ada tazo ta bud'e k'ofar tana d'aure da towel da Alama dg wanka ta fito"ihun murna tayi ta rungume ummu suna dariya"Abdallah yabisu da kallo yana mamakin irin shakuwar tasu"yana jin sa'ada na cewa"Anty ina zakije?"ni dake shirin zuwa na gaidoku keda yaya??"nan muka zo baby"ko yanzun bata b'aci ba inkin gama shiryawa saiki zo ko?"tunda week end"to Anty zakimun kitson ?"zan miki mana"to ki shigo kiga d'akina mana"yaya Abdallah gaya can yana jirana zamu wuce"sai sannan sa'ada ta lek'o tana fad'in sweet heart"harara ya ballah mata yana fad'in sai yanzun kika tuna dani?"kai yaya mgn mukeyi fa da Anty"baby kyalesa jeki shirya ina jiranki"dg haka ummu tabaro k'ofar d'akin"ta kalli gefen dasu umma balki suke taga gaba d'aya su suke kallo"d'an murmushi tayi tace"sai Anjimanku"madallah mungode"dg haka ummu ta nufi k'ofa sbd har Abdallah yatashi yafita"sadda ta fito yamata nisa ta tab'e baki tana fad'in saime dan baka jirani ba?"da wannan tunanin ta iso part d'in nasu"ta sami big man yayi d'aid'aya saman 3seeter yana danna waya ga TV na Aiki"be Amsa sallamar taba yana danna waya fuskarsa Ad'aure yadubeta zata wuce d'aki sai cewa"yayi yaka mata kidinga tsafta"na lura ba kullum kike wanka ba"hmm! naji banayi kai tunda kanayi me ruwanka da bana yi malam?"sannan ni bana gayya dan Allah ka tashi ka koma sashenka"tunda dai kanada parlourn ka"zamanka nan wajen inba fitinah ba bbu Abinda zaka tado"ta k'are maganar zata shiga d'aki"bazan tashiba kizo ki maidani idan zaki iya y'ar rainin hankali"juyowa tayi ta banko masa harara tana fad'in Allah yakiyaye na d'auki k'ato kamar ka....ke waye k'aton?"yafad'a Aharzuk'e yana tashi tsaye"ummu ta masa gwalo tana fad'in kai mana"beyi mgn ba yabiyota"ta zura Aguje"saidai tana banko k'ofar taga bbu key Ajiki"asukwane ta shige bath room ta banko k'ofar ta murza key"Abdallah daya shigo yaja tsaki yana fad'in banza matsoraciya"yak'are maganar yana zaro kud'inta da daddy yabata ya Ajiye mata gefen bed yafita dg cikin d'akin"key yasakawa k'ofar main parlour ya wuce samansa....ummu kuwa wanka tayi ta fito"haka nan taji yau tana jinta cikin nishad'i"kud'in ta lura dasu daya Ajiye mata"saita d'auka tajawo lokar bed side drower tasaka"tana k'ok'arin nufar gaban mirror taji knocking"Ajiyar zuciya tasaki sbd dama Atsorace take sbd tsoron kar Abdallah yashigo yamata wata mugunta"ranta yabata kuma sa'ada ce"hijab tasaka samqn jikinta ta fito tazo ta bud'e mata k'ofar tana fad'in sai yanzun?"wlh waya mukayi da yaya sadeeq shiyasa"murmushi kawai ummu tayi ta gyara sa'ada ta shigo "ita kuma ta rufe k'ofar tana fad'in bara na sakq kaya sai muyi break fast d'in"dato ta Amsa ta nufi bed room d'in ta.....
zaune suke suna break fast d'in gaba d'aya ummu ta shagala sunata firansu itada sa'ada suna dariya"sam bataji ko motsin sakkowar Abdallah k'asan ba"saidai kawai taji mayataccen k'amshin turarensa"tayi saurin d'aure fuska"big man dake lura da ita yatab'e baki yana fad'in magulmaciya! sa'ada ta kallesa Azatonta da ita yake"cikin shagwab'a tace"yaya gulmar me nayi maka?"bayan ni dama can bana gulmar kowa kuma Anty ummu ta nunamun illar yi da mutane"wanda nake dashi yasan kansa"yafad'a cikin cool voice yana d'aukar wayarsa da kamal ke kira"ya shirya cikin k'ananun kayan da sukayi mugun karb'an choco skin nashi"Allah yatsare! cewar sa'ada"ya gyad'a mata kansa ya fita"ummu kuwa be isheta kallo ba sbd tasan maganar da yayi da ita yake"be jima da fitaba suna zaune a parlourn sadeeq yayi knocking aka bashi izinin shigowa"sa'ada dai nutsuwa tayi koma kallonsa batayi ba"ummu ce ta Amsa sallamar tasa suka gaisa yana satar kallon gefen da sa'ada ke zaune yace"dama Anty yaya yace"ki bada key d'in motarki za'a mata service Azuba mai"kuma zan dinga koya miki driving duk week end"cike da mamaki ummu ta Amsa dato"ta mik'e tsaye ta wuce d'aki"dama motar na haraban gidan a Ajiye"parlourn yayi saura dg baby sai sadeeq"Ahankali sa'ada tace"nima zan bita Akoya dani pls yaya sadeeq?"na zata baby bakima lura dani ba?"nafa ganka kuma d'azun Ai mun gaisa ko?"wancan gaisawar ta waya daban itama wannan daban"saidai idan jan Ajinku na mata zakimun ko?"tana k'ok'arin mgn ummu ta fito dg cikin d'akin ta mik'a masa key d'in ya Amsa yafita....
***********
haka rayuwar ummu da Abdallah taci gaba da wakana Acikin wannan gida"idan yaga dama yasakata kuka da muguntar daya saba yimata"idan kuma yaga dama ya k'yaleta"tana k'ok'arin kyautata masa dashi da sa'ada harma da Ammi"kamal kuwa tana jimawa bata ganshiba"part d'in umma balki kuma duk bayan sati 1 Abdallah na rakata suje su gaisheta"Aminu da umar da mahmood wata juma'a sun kawo mata ziyara"saidai har sukazo suka tafi basuga Abdallah ba"Ahaka ummu ta kwashi wata ukku Agidan"wanda tunda tazo bata tab'a fita ko ina ba"ba kuma sbd Abdallah ya hanata ba"tanayin waya da mama taji lafiyarta"yayinda jama'ar gidansu ke yada mgn wai ummu tak'i zuwa taga mahaifiyarta"itadai mama saidai tayi murmushi"domin tasan iyawa mutum sai Allah"kwanaki sunce batayin Aike miye miye"taci gaba da yi musu Aike da duk Abinda take da Hali"yanzun kuma ana cewa tak'i zuwa"wanda ta tabbatar idan yawan zuwan takeyi sai wata ran Ance yaji tayi ko kuma mijin yagaji da ita...yanzun haka bikin lawisa da nura yaga bato"naira dubu d'ari d'in da daddy yabama ummu kwanaki sune ta Aiki sa'ada da saitin jug me kyau da tsada takaima lawisa har gida wai gudunmuwarta"Anko kuma dayake tana samun kud'i wajen daddy duk idan sunje gaishesa sai yabata kud'i"sune ciki ta siya musu Anko na yini itada mama"sannan tayi musu na ranar dinner itada sa'ada"sosai ummu ke yiwa mama Aike da duk Abinda take da hali"Abdallah kuwa tunda tazo gidan sisinshi bata tab'a rik'ewa ba"saidai komai na Amfani dajin dad'in rayuwa zai jibge mata akitchen.... ummu ta k'ara kyau"haske,da shek'i da y'ar k'iba Acikin wata ukku kacal....jiya laraba Akayi wa'azi, yau Alhamis kuma Akeyin dinner"sai gobe kuma Ake yin yini"to jiyan ummu batajeba sbd meyiwa sa'ada lalle tazo tayi mata"yau kuma tun wajen 12:0 pm ta gama girkinta sbd sa'ada zata rakata shagon da ake mata kitso"idan tadawo sai su shirya su tafi wajen dinner d'in da babyn"dukda sa'ada na skul sai k'arfe 1 :30 take dawowa"ummu nata jera komai samqn dining table"ga break fast d'in Abdallah dabaiyiba tasan yana hanya tunda Abin yazamar masa ibada dole sai 12 yakeyin break fast"bata gama wannan tunanin ba yashigo cikin parlourn"Agadarence yayi sallamar yanata wani shan k'amshi"ummu ta dubesa tana cewa" yauwa yaya Abdallah dan Allah bani number d'in sadeeq"banza yamata yawuce ta gabanta ya zauna kan kujerun dake gaban dining table d'in"tanama k'ok'arin tafiya taji Amon muryarsa yana fad'in kiyi me da ita?"kanta ak'asa tace"dama zan bashi key d'in motata ne Azuba mata mai"ina zakije?"yak'are maganar yana kallon hannayenta da suka sha lalle ja da bak'i"tamkar ta gaya masa bak'ar mgn saita fasa tace"wajen bikin lawisa kasan yau dinner gobe yini"wajen kitso yanzun idan na shirya zan fara zuwa saina dawo muyi shir...duk da izinin waye zaki fita?"yakatseta cikin daka tsawa"gabanta yafad'i ta kallesa suka had'a ido ya wurgo mata harara"ta d'auke kanta tace"kaifa kace mun bakada damuwa duk Inda nakeso naje"kuma wlh tunda nazo gidan nan ban tab'a zuwa ko inaba"harda gida nakeso dg nan naje na gaida su mama....Ada kenan yanzun na janye wannan zancen saida Amincewa ta zaki fita"dan girman Allah karkamun haka yaya Abdallah lawisa ta wuce komai Awajena kaima ka sani"ban kyautaba idan nak'i zuwa bikinta dan Allah ka....kina wahalar da kanki ne Amma bbu Inda zakije"idan kuma zaki iya fita ga hanya nan"wai ka manta irin AUREN da mukayi dakai ne?"tsaki yaja yana fad'in bansaniba"ko kin d'auka bansan menakeyi ba ko kuwa jahili kika d'aukeni?"Allah bbu ruwansa da irin Auren da mukayi"tunda dai na biya sadaki An shafa fatiha zance yak'are dole kimun biyayya"idan kuma tsinuwar mala'iku da b'acin ranki ta hanyar hukuntaki kikafi buk'ata kije ga hanya nan"yak'are maganar yana bud'e warmers d'in"ummu kuwa Aguje ta nufi d'aki tana gunjin kuka"shed'an na tunzurata kawai taje ta kwana gidansu lawisa idan Antaso dg wajen dinner"washe gari Akayi yini ta kwana gidansu"saita kirashi yabata takardarta"tuna kuma yadda iyayenta da mutane zasu fassara rabuwarta dashi wata ukku da aure yasaka taji fad'uwar gaba"gaba d'aya ta rasa mafita"tafi Awa guda tana kuka"idanuwanta sunyi jajir"dg k'arshe ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta kabbara sallar Azahar"bayan ta gama ta shirya cikin sabuwar dubai Abaya"ta fito parlourn ta zauna tayi tagumi"Ahaka sa'ada tayi knocking"batare data tambayi waye ba ta bud'e k'ofar"kallo d'aya sa'ada tayiwa idanuwanta gabanta yafad'i"ta shigo tana fad'in Anty harkin shirya??"bbu zancen tafiya sa'ada yayanki ya hanani zuwa bikin Aminiyata, wacce nakashe na rufe da ita bbu me ji"wacce ta fiyemun wasu dg cikin y'an uwana na jini....sai kuma ta fashe da wani irin kuka me cin rai"innalillahi wa inna ilaihir raju'un"gaskiya yaya Abdallah be kyautaba"me kika masa dazaiyi miki haka?"ni kaina asanina dake nasan kuna Abota sosai da ita"dan Allah ki dena kukan nan"bara na kira Ammi nasanar mata nasan zata mishi mgn"ah ah baby ki rufan Asiri dan Allah karki sanar mata"nasan bazai bari ba"shiru sa'ada tayi tana jin tausayin ummu Aranta"can kuma sa'adan ta fara janta da fira har k'arfe 3:16 tayi"sa'ada ce kawai tayi lunch ita cewa tayi ta k'oshi"wajen k'arfe 3:30 pm Abdallah da kamal suka