Showing 42001 words to 45000 words out of 93107 words

Chapter 15 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete

shigo cikin parlourn"sa'ada ce ta Amsa sallamar kamal ta gaidashi"ummu kanta Ak'asa itama ta gaidashi"yanayin yadda yaji muryar ta da yanda tak'i yarda ta d'ago kanta ta kallesa ya tabbar masa da cewa Akwai Abinda yafaru"dining area suka wuce suka zauna shida Abdallah"sa'ada kuwa tanaji kamar taje ta yiwa Abdallah mgn kozai bar ummu taje"lura da hakan da ummu tayi yasakata cewa baby zanje ciki na kwanta kafin la'asar ta ida"kema kije wancan d'akin ki kwanta"zanje dai gida Anty Anjiman zan dawo"kanta kawai ummu ta gyad'a mata ta tashi ta nufi d'aki"itama sa'ada ta fita"wanda Abdallah yayi mamakin k'in kulasa da sa'ada tayi"Aransa yace"wato sbd ta gaya mata na hanata fita shine itama takejin haushina kenan??.... Abdallah! kamal yakira sunansa bbu Alamar wasa ko zolaya samqn fuskarsa"d'aure fuska yayi yadubesa beyi mgn ba"kaji tsoron Allah! kaji tsoron Allah!! Ai kasan kai nake tsoro ba Allah ba?"ni bance ba Abokina"ina gaya maka gaskiya sbd bakasan me gobe zata haifar ba"look kamal! Akanme zaka dinga mun irin wannan zaurancen?ka fito fili kayi mgn ba nok'e nok'e ba"yafad'a yana k'ok'arin
zuba Abincin"me kayiwa ummu??"cikin zafin rai yace"ban saniba" dama kallonta kakeyi idan kazo harka lura tanada damuwa ne ko kuwa kiranka tayi ta kamaka k'arata???"Allah yabaka hak'uri miye Abin tada jijiyar wuya?"tun ranar dinner naku rabon danayi waya da ita kenan baka isa na maka k'arya ba"kallo dakake mgn bana yimata kallon da shari'a bata yadda dashi ba"nasan duk idan nazo gidan cikin raha muke gaisawa Amma yanzun banga hakaba"nasan kuma halinka ba dad'in zama dakai takeji ba"shiyasa na tambaya"tab'e baki big man yayi yace"to meye damuwar ka ko ruwanka da idan tana cikin damuwa??"d'an murmushi kamal yasaki domin wani abu daya fara hangowa"Amma Afili sai yace"karka fassaramun mgn idan bazaka fad'i me kamataba shikenan"tsaki Abdallah yaja cikin gadara yace"Anguwa zataje na hanata zuwa"Akanme?"Akan nina gadama"wai kamanta irin AUREN da kukayi ne?"bansaniba"koma miye na hana"shine taketa wannan fushi da koke koke"kasan k'awartata d'in na itace zatayi Aure....wai lawisa?"oho musu"gaskiya bakada kirki big man kuma baka kyautaba"kai kamanta yadda Akayita hidima da ita wajen bikinku??"d'age kafad'a yayi yace"su yadama Amma baratajeba"to meyasa ka hanata zuwa??"kaga kamal ka k'yaleni da surutun nan naka naci Abinci"kwantar da murya kamal yayi yana rok'onsa Alfarma da had'ashi da Allah da nuna masa idan batajeba batayima Abotarsu Adalciba"yaduba yaga idan shine yatashi Aure sai big man yak'i shiga hidimar komai kuma lafiyarsa qlau bbu wani uzuri me girma" Ai dole yaji zafin Abin Aransa"sai bayan yagama jan Ajinsa sannan yace"shikenan na Amince taje yau da kuma gobe d'in"kuma baby barata rakata taba"to shikenan kaje kasanar mata tunda kagama cin Abincin dan Allah"cewar kamal shima yana zuba nasa Abincin"big man bece komaiba ya mik'e tsaye yanata wani ciccin magani yanufi bed room d'in ummu"kamal yayi murmushi yana fad'in mace kawai ce zatayi mana maganinka big man"saidai jikina yayi sanyi danaga sauyi kad'an Atare dakai"naso naga sauyin fin haka tsawon wata ukku da Aurenku"Allah yasa hasashena gaskiya ne..... Ahankali yatura k'ofar d'akin ya shiga"ummu dake kwance samqn bed tana tunani ta juyo suka had'a ido"d'auke kanta tayi batace komaiba"kwanciyar ta mecece yanzun da la'asar??"iya Abinda yafad'a kenan kamar an masa tilas yanata kallonta"cikin fusata ta juyo tana fad'in ina ruwanka da kwanciyata??"okay shikenan dama nazo nace miki ki shirya zan baki Aron motata kije da ita"(motar million 40)"Amma na fasa yafad'a yana juyawa zai fita"da sauri ta diro dg samqn bed d'in cikin second 2 takai bakin k'ofar d'akin ta rik'e gefen rigar sa"murya a marairaice tace"dan Allah kayi hak'uri yaya Abdallah zanje"kuma nidai da motata zan tafi"juyowa yayi suka had'a ido"sunku yadda kanta k'asa tayi bata cika rigarsa data rik'e ba"yatab'e baki yace"ke kika sani koma Ak'afa zakije dama taimaka miki nayi tunda sadeeq na skul exams yakeyi"yau da kuma gobe"kawai na Amince kije"to shikenan nagode kabani key d'in na fita da ita pls"bece komaiba yazaro key d'in dg Aljihun wondonsa yamik'a mata yafita"lokacin kuma harma kamal yagama cin Abincin yana waje yana jiransa"shima saiya fita sbd Anata kiran sallar la'asar"ummu kuwa cikin farin ciki tayi sallah tafara shiri"d'inkin material ne pink tasaka gownt"ta d'aura d'an kwalin"tasaka mayafi da hand bag da takalmi duk pink"ba k'aramin kyau tayiba"wayarta ta d'auka ta kira sa'ada tasanar mata tasaka nata Ankon ta fito su wuce"bayan sun gama wayar ta d'an fesa turare"ta tsurawa kyakykyawar fuskarta ido ta cikin mirror d'in"ita kanta masha Allah take fad'i"tasan yau tabani da kallo wajen y'an gidansu musammun idan sukaga yanda ta sauya"key d'in motar ta d'auka ta fito main parlour hakan yayi daidai da shigowar sa'ada"ta kalleta tana dariya tace"Anya Anty yaya idan yaganki zai bari ki fita wasu su kalle masa ke??"irin wannan kyau haka masha Allah"kema ba dg baya ba baby"mutafi kar muyi latti"to Amma sai namiki photo awayarki ta snapchat"ummu batayi mgn ba suka fita"tasaka key ta rufe k'ofar" kafin ta mik'ama sa'ada wayarta"tana k'ok'arin yi mata mgn ta hango Abdallah dake nufo sashen......✍️

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤‍🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤‍🔥

*33&34*


........wani irin fad'uwar gaba ummu taji wanda batasan dalilin jinsaba"haka dai ta mik'ama sa'ada wayar"batare data koma kallon big man dake nufo suba....tunda yadoso Inda suke ya tsurawa saman farar kyakykyawar fuskar ummu ido zuwa kan k'afafuwanta"saidai fuskar nan tasa bbu fara'a ko kad'an"sa'ada na ganinsa ta nufesa tana fad'in yaya! yatsina fuska yayi ya kauda kansa" sbd fushi yakeyi da ita d'azun batayi masa mgn ba"bakin k'ofar yanufa bayan ya wuce ta gefen ummu datayi k'asa da kanta"sa'ada ta biyosa tana fad'in wayyo sweet heart menayi maka?"tafad'a tana k'ok'arin hugging nasa"saidai kallon daya Aiko mata dashi yasaka ta dakata tana turo baki"sai kuma ta kallesa tace"bansan laifin menayi maka ba yaya Abdallah"Amma nidai kayi hak'uri tafiya zamuyi kuma banida kud'in lik'i....muje ciki ki Amsa"iya Abinda yafad'a kenan yana bud'e k'ofar da key ya shiga"itadai ummu na tsaye gefe tana jinsu"Anty muje wajen yaya Abdallah"yanzun Ai ya kyauta tunda yabarki ko?"kije ke kad'ai zan jiraki Anan....bata rufe bakiba Abdallah yaturo k'ofar yafito"rafar y'an d'ari biyar guda 2 ya mik'o ma sa'ada yana kallon gefen da ummu take cikin nutsatstsiyar muryarsa yace"karki bari ku wuce 8 pm"bejira cewar taba yashige ciki"sa'ada kuwa duka kud'in ta mik'ama ummu tana fad'in gashi Anty inji yaya"banganeba baby?"kefa kad'ai yaba"ah ah wlh mu biyu ne yaba mawa ki Amsa dan Allah Anty kar muyi jayayya dake"ummu batayi mgn ba sbd dama bata fito da wasu kud'i ba"rafa guda ta Amsa ta saka jaka"ita kuma sa'ada tasaka gudar a hand bag nata"kafin tafara yiwa ummu zafafan pics kuma style's masu kyau"tana fad'in kinyi post a status"bana aza pics nawa a status baby"muje kinga biyar saura"kuma ta sanar mun k'arfe 6 za'a tafi zuwa 8 Antashi"ta k'are maganar suna jerawa suka nufi parking lot"da mamaki sa'ada ke kallon ummu dake k'ok'arin sqka key ta bud'e k'ofar motar Abdallah"Anty Amotar yaya zamuje??"Eh Aramun yayi sbd tawa bbu mai"lallai yaya Abdallah naji dake"iya sanina baya bada Aron motarsa ga kowa"murmushi ummu tayi tana fad'in nifa matarsa ce baby"dan yabani Ai ba Abin mamaki bane"tunda tawa d'in ma shine yasiyamun ko"hakane Anty"dg haka suka shige ciki"ummu na driving d'in cikin nutsuwa da nishad'i"tana ganin Abin kamar a mafarki"wai itace ke driving, kuma cikin wannan zuk'ekiyar mota haka"kasancewar dama tunda sadeeq ke koya mata motar bata tab'a fita ko inaba iyakarta cikin gidan tad'an zagaya shikenan"sunata firansu da sa'ada har suka iso Anguwar tudun wada"wanda kai tsaye ta layin gidan su lausy suka biyo.....lahhhh Anty ji wata can y'ar Ajinmu ce da Ankon jikinta"k'ilan cikin dangin mijin lausyn take"pls Anty ki tsaya mana"okay bara na tsaya ki sauka ni gida zan fara biyawa"kicewa lausyn gani nan zuwa yanxun"ta k'are maganar tana yin parking"sa'ada ta fito cikin nutsuwa ta wuce cikin gidansu lawisa...ummu kuwa tayi gaba"Adaidai layin gidansu ta tsaya"bayan ta gama parking ta bud'e k'ofar motar ta fito"tana k'ok'arin rufe k'ofar Asiya na fitowa dg cikin gidan da uban tsohon cikinta da Alama Aiken kanta zataje"kallo d'aya Asiyar tayiwa ummu ta d'auke kanta"ita kuwa murmushi tayi tace"Asiya kenan! kina ganina zaki wuce kamar ba yayarki bace nu?"tsaki Asiyar taja tayi gaba"ummu tace"Allah ya kyauta ta nufi soron gidan nasu"tun dg soro takejin kakarin Amai na goggo luba dake bayi "tana shigowa cikin tsakar gidan"ta sami babah zaune gefen tabarma yayi shiru"humairah k'aramar y'ar goggo luba na gefensa zaune da plate a hannunta tana kuka"da Alama yunwa takeji"yayinda mama na gidan su lawisa Anata hidima da ita"babah na ganin ummu ya fad'ad'a fuskarsa da fara'a yana Amsa sallamar ta"sosai ummu tayi mamaki"sbd ta saba dg zagi sai hantara ke had'ata da mahaifin nata"tana murmushi tace"baba sannu da gida"yauwa ummul khairy"har k'asa ta duk'a tana gaishesa"ya Amsa cike da kulawa da tambayarta yasuke"kafin yace"wajen bikin kika zone?"Eh baba"to Ai hajara ma tana can"Ai dama ban biyaba nan nafara zuwa"ke humaira kukan me kikeyi ne?"ummu ta tambaya"kukan yunwa takeyi wlh"to Abata Abincin babah"bbu ne shiyasa"subahanallahi! wlh kuwa Abubuwan sai Ahankali ummulkhairy"mamanki tayi girki tabasu uwarsu ta hanasu Amsa"dama yanzun Aminu ne k'arfin gidan idan yasamu"ni yanzun Aikin sai Ahankali"hand bag nata ummu ta bud'e ta zaro rafar y'an d'ari biyar d'in nan da big man yabasu na lik'e ta Ajiye gabansa tana fad'in ga wannan babah asiyi cefane insha Allah zan Aiko da kayan Abincin"ah ah y'ar nan karki roki mijinki komai"wannan ma nagode Allah yayi miki Albarka"Ameen babah tafad'a cikin jin dad'in Addu'ar tasa"wanda tunda take bata tab'a jin yasaka mata Albarka ba sai yau"babah ya d'auki kud'in yana niyar sakawa Aljihu goggo luba ta fito dg cikin bayi"itama da k'aton cikinta yayi k'asa"kallo d'aya zaka mata kasan batajin dad'i"dukda haka had'e rai tayi dataga ummu tsugunne gefen mahaifinta"ta kalli kud'in tana fad'in mlm sai muje Asibiti ko tunda ga kud'i ka samu ina zaton haihuwa ce zanyi....bbu Inda zamuje ki haihu a gida mana kamar yadda kukeyi"zancen kuma ki koma haihuwa na sokeshi Agidan nan ta kaina nakeyi nima.... mik'ewa tsaye ummu tayi tana fad'in goggo ina wuni?lfy qlau ta fad'a tana binta da wani irin mugun kallo na tsantsar hassada dajin zafi"har baba yalura da ita"to baba zan tafi can d'in na sami mamar Acan mu gaisa"to shikenan Allah yayi miki Albarka kya gaida mai gidan naki"dato ummu ta Amsa ta fita"goggo luba ta tab'e baki tace"su yaran nawa saika tsine musu Albarka ko?"tunda kaga kud'i da Abin duniya Ai dole kayita rawar jiki"tsaki baba yaja yatashi yafita yabar mata gidan"ummu kuwa tana fitowa zata shiga mota ta hango hjy yaya"da sauri ta ida shigewa cikin motar"tana hango hjy yaya ta glass tana tsaidata tayi gaba Aguje tabar wajen"har cikin get d'in gidan su lawisa ta shiga da motar"ta sami sa'ada cikin friends nasu Anata fira da ita"kowa kallon ummu yakeyi sbd yadda tayi wata irin canzawa"lawisa data had'e cikin gownt d'in material ta harareta tana fad'in ki koma Inda kika fito"hak'uri zakiyi k'awata"saida nasamu na rarrashi my hand some sannan na fito"duk k'awayen sukayi shewa"dg bisani ummu ta wuce cikin gidan wajen mama"bbu wata kunya ta rungume mama cikin farin ciki da tsantsar kewarta"umman lawisa nata kallonta tana fad'in masha Allah"ita kanta maman taji dad'in yadda taga ummu cikin kamala da shigar mutunci"sai taji hankalinta ya kwanta tasan tana samun zaman lafiya Agidan Auren nata.....sai wajen k'arfe 5:45 pm Anguna suka iso Aka fara jidar y'an mata"itadai ummu motarsu suka shiga itada sa'ada"sai k'awayen ta mutum biyu dake back sit"sunata santin motar"koda suka iso hotel d'in haka wasu suka dinga pics gefen motar"kowa na ganin ummu na cikin daula tunda take hawa irin wannan tsadaddar motar....koda zasu shiga ciki saida tasaka wani security ya kula mata da motar sannan suka wuce ciki"komai ana gudanar dashi yanda yaka mata"can sa'ada ta kalli ummu tana fad'in Anty muje muyi lik'i mana"kije kiyi ke baby"ke baraki yiba?"wlh kyauta nayi da kud'in nan"bbu damuwa ga nawa mu raba"be kamata kik'i yin lik'i ba kodan sbd yadda kuke da ita"ta fad'a tana zaro rafar kud'in ta ibi kad'an tabama ummu sauran"cikin nutsuwa suka shigo cikin filin rawar suka fara yiwa Amarya da Ango lik'i"Abin mamaki maza 3 suka rufu kan ummu sunata yi mata lik'i"lura datayi da hakan yasa ta fito dg wajen rawar"da hanzari wani had'add'en guy Acikin su yabiyota yana yimata sallama Abayanta"banza ta masa sai sa'ada ce ta sanar masa tanada Aure"sai yabasu hak'uri ya wuce"su kuma suka koma wajen zamansu"sa'ada ta zuba ruwa tasha"kafin ta tashi taje ta d'auki plate tabi layin Inda ake zuba gashashshen naman rago aka zubo mata"ummu tayi murmushi tana kallon ta bayan ta zauna sbd ita batajin zatama iya cin wani abu Awajen sbd idon mutane yamata yawa"bata gama wannan tunanin ba wayarta tayi ringing.....k'irjinta yayi wani irin bugawa sbd ganin *Azzalimu* ne ke kiranta"sanin halinsa idan tak'i d'auka k'ilan gobe ya hanata zuwa wajen yini saita d'auka"sa'ada dai nacin naman tana kallonta"tun kafin ta kaiga mgn big man cikin muryarsa data shak'e yace"K! kuna ina?"muna can mana"okay nanda 15 minit zuwa 20 minit ki tabbatar kun dawo gida"yanzun bakwai da rabi"Inda ke kad'ai ce bazan kiraki ba Amma yanzun sbd kinja baby shiyasa na kira"Allah ko?"bansani ba"to shikenan karka damu yanzun babyn zata dawo ni sai zuwa anji....baki isa ba"yakatseta a zafafe"kafin yaci gaba da cewa"muddin kika bari raina yab'aci har goben baraki jeba"yana fad'in hakan ya yanke wayar"sa'ada ta Ajiye cup d'in hannunta data sha lemo tace"halan yayan cewa yayi mutaho?"Eh baby bama zan yiwa lawisa sallama ba"muje kawai "dato ta Amsa suka tashi suka fita....sadda suka iso gidan Anata kiraye kirayen sallar isha'i"sa'ada part nasu ta wuce"ita kuma ummu ta nufo b'angaren su"key tasaka ta bud'e k'ofar ta shigo da sallama"uban gayyar na hakimce samqn kujera yana danna laptop dake samqn ruwan cikinsa"ya mik'e dogayen k'afafuwan sa samqn center table"yana sanye da Quarter d'in wando bak'i da farar t shirt"k'wayar idonsa tayi d'an ja"sbd yau da mura yatashi"yasha magunguna Amma sai Ahankali"dama shi itace ke wahalar dashi"da yayita gara yayi zazzab'in kwana 2 Aganinsa"sbd yana jumawa kafin ya warke idan yana yinta"muryarsa harta fara shak'ewa"beko kalletaba Ahankali tace"sannu da hutawa"be Amsaba saima yajeho mata tambaya da cewa "ina baby?"ta wuce cikin gida"ta k'are maganar tana isowa gefen k'afafuwan sa ta Ajiye masa key d'in tana fad'in nagode"dg haka ta nufi k'ofar d'akinta ta bud'e ta shiga"sallolinta tayi sannan tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta bacci me hannun best"tsayinta rabin cinya"kuma bayanta Abud'e yake sosai"wani irin kyau tayi kamar y'ar yarinya"turaruka ta shafa, ta fesa na fesawa"kafin ta fito parlourn sbd tasami Abinda zataci"sam ta d'auka Abdallah yakoma sashensa shiyasa gaba gad'i ta fito kanta ko d'an kwali bbu"tayi parking d'in gashin kanta da ba'a samu damar yimata kitson dataso taje yau ba......saidai tana fitowa tasami Abdallah zaune"shi kuma motsin bud'e k'ofar datayi yasaka yad'ago kansa"saidai baiga fuskar taba bayanta kawai yagani"so yakeyi ya kauda kansa Amma yarasa meyasa yakasa dena kallonta harta koma shigewa cikin d'akin?"yaja tsaki ya mik'e tsaye ya tattare inasa inasa ya wuce samansa"ummu kuwa hijab doguwa tasaka ta fito parlourn taga big man d'in ma yatashi"kai tsaye dining area ta wuce"ta duba warmers d'in Abincin"tuwan farar shinkafa malmala biyu yarage da miyar shuwaka dataji bushashshen kifi da ganda" cikin nutsuwa ta zuba ta fara ci da bissimilah".......k'at tayiwa cikinta"sannan ta koma d'aki tayi brush ta kwanta baccinta......
washe gari da safe da ummu ta tafi part nasa sbd ta gyara tayi mamakin ganin Abdallah kwance yana bacci a bed room nasa"tasan kuma irin wannan lokacin baya gida yana masjeed"idan yadawo kuma sai wajen 7:30 am yake shigowa"bata koma kallonsa ko gigin mishi mgn ba"sbd fuskar sama A rufe take" bath room ta wanke ta had'a masa ruwan wanka sannan ta fito ta d'an gyara d'akin"ta koma parlourn sa ta gyara"dg nan ta koma kitchen ta had'a musu break fast"sannan taje ta shirya"saidai koda ta fito main parlour wajen k'arfe 8:35 am sbd tayi break fast"sai kawai taji tanaso ta duba taga yatashi"itama kuma sa'ada shiru bata shigo ba"da wannan tunanin ta nufi sashen nasa"saidai still yana kwance rub da ciki yana bacci"saidai fuskarsa Abud'e take"Amma ba'a ganinta sai suman kansa kawai akegani ya cusa fuskar tasa cikin pillows.....gefen bed side drower ta zauna Ahankali ta d'an bubbigi pillow d'in daya aza kansa tana fad'in yaya Abdallah kana kuwa duba time??"shiru beyi mgn ba" da mamaki ka koma cewa"yaya Abdallah! da k'yar ya iya furta menene?"in bacin tana gab dashi da bazataji mema yake fad'a ba"cikin da burcewa tace"dama naga shiru baka fito ba"kuma ko wanka bakayiba shine nazo naga lafiya???"saida yad'an muskuta yana furzan da wani zazzafan huci dg cikin bakinsa"ya juyo zuwa rigingine yana yin Atishawa A wahalce yace"mura nakeyi"dg haka yayi shiru yana lalubar tissue dake samqn bed side drower"saidai idanuwansa lumshe suke"hancinsa yayi jajir....saidai ita ummu bata lura da laluben daya keyiba sai kawai taji tafin hannunsa samqn cinyarta.... Azabure ta kalli hannun nasa tana jin wani iri Ajikinta"be janyeba saidai taji yace"bani tissue"batayi mgn ba ta duba gefenta taganta"cira tayi ta saka masa cikin hannun nasa"sai ya janye yadora samqn hancin nasa yana bud'e idanuwansa da sukayi jajir ya azasu samqn baby face nata"sunku yadda da kanta k'asa tayi cikin y'ar siririyar muryarta tace"sannu ya jikin?"kansa kawai ya gyad'a mata yana maida idon nasa ya lumshe"ta mik'e tsaye ta fita dg cikin d'akin"kitchen ta nufa ta fara Aza ruwan zafi ta zuba kayan yaji irinsu karamfani citta,masoro,na'ana'a , tafarnuwa da lipton da sauransu"ta tsaya tsawon mintina 8 sunata dahuwa kafin ta kwashe cikin cup me d'an girma"ta zuba sugar kad'an ta d'akko wani cup d'in ta fito ta nufi samqn"yadda ta fita tabarsa haka tasamesa"saman bed side drower ta Aza shayin kafin ta duk'a gefen inda kansa yake" murya A tausashe me nuna tsantsar tausayi tace"Ayya yaya Abdallah katashi kayi brush kad'an sha shayi irin wannan zakaji sauk'i insha Allah....ya d'auki kusan second 10 kafin yabud'e lumsassun idanuwansa ya kalleta tana duk'en"sannan ya kalli shayin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login