Showing 69001 words to 72000 words out of 93107 words

Chapter 24 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete

ummu Ahannun sa"saidai jallabiyace fara gogagga Ajikinsa"da Alama wanka yakoma gd yayi"bata cikin d'akin tana toilet"da alama wanka takeyi sbd yaji k'arar ruwa"sanin halinta da kunya bazata iya shiryawa ba Agabansa" zatayi rigima idan ta fito ta samesa"sai kawai yafita ya nufi wajen doctor d'in sbd yaji ta koma dubata...be jima da fitaba ummu ta fito dg cikin bath room d'in"Abinda tasan zata buk'ata ta d'auka ta koma ciki"sbd taji motsin shigowar sa da fitarsa"sannan ta lura da ledar daya Ajiye gefen bed"koda ta shiga toilet d'in kayan bacci tasaka da k'aramin mayafi ta fito"tana fitowa big man naturo k'ofar"ta b'ata fuska ta juya masa baya tana fad'in wai malam wannan zaryan na meye?"hmm! khairee bakya gajiya da neman mgn"ni wajen matata nazo shine nayi zarya?hmm! matarka kuma?"saidai ko wannan banzar marar zuciyar ita kake nufi ko?"sarai ya fahimci preety take nufi"saiya basar yana fad'in naji dad'i dakikamun mgn"dama ko masifar ne inaso Amun"bata kulashiba sbd wani irin zafin kishin preety taji yataso mata"kawai saita nufi samqn bed d'in ta zauna tana kallon tv"shi kuma ya zauna kan kujera fara"shiru na mintina 5 ya ratsa"can ya kalleta yana fad'in kamal na gaisheki da jiki"kamar tana jira ta fashe da kuka tana fad'in bana son gaisuwar tashi ina ruwana daku?"shiru yayi jikinsa yayi mugun yin sanyi"ya fahimci ba k'aramar k'iyayya khairee ke masa ba"wato shima kamal laifinsa ya shafesa kenan?"ya tambayi kansa"saiya canza topic d'in da cewa" to ki daure kici wancan naman kinji dad'in bakinki ko?"bana buk'ata"tana fad'in hakan ta kwanta ta juya masa baya"shi kuwa be koma mgn ba"sai wajen k'arfe 10 ya d'auki naman yafita bakin titi yabayar"shi kuwa tsabar damuwa bayajin sha'awar cin komai"saidai ruwa kawai yake sha"bayan yabayar yadawo ya shimfid'a blanket k'asa kan tiles ya Aza pillow"yazo gefenta ya dinga yimata Addu'oi yana tofeta dasu"tayi bulum kamar tana bacci"bayan ya gama yamatso ya sumbaci goshinta yana fad'in I love you so much my sweet khairee"dg haka yaje yayi bissimilah ya kwanta"bayan yagama Addu'a yafad'a tunani.....

*bayan kwana 5*
kimanin sati 1 kenan da faruwar wannan babban al'amari tsakanin big man da ummu"tunda Aka basu sallama ta dawo gidan take wanashi da sakashi cikin damuwa"gaba d'aya dukya zabge ya rame baya Aikin komai a office sai tunani"gashi da dare rufe d'akinta takeyi"da safe kuma ko Inda yake bata kallo"tanadai yin girki dashi"Amma bata kulashi tana sharesa sosai"gashi sa'ada bata gidan balle kodan sbd ganin Idonta tarage wani abu"sosai big man yakoma halinsa na miskilanci da k'in son mgn"tun kamal baya tausaya masa har yafara bashi tausayi"yana tunanin zuwa gidan yabama ummu hak'uri kan ta janye komai su zauna lafiya"Ayau friday misalin k'arfe 8:11 am "ummu na zaune tasha gayunta cikin k'ananun kaya riga da wondo kanta bbu d'an kwali"tanata chats da lawisa tana smiling"dan yanzun ta warke harma d'inkin ya warware"saidai har yanzun tana shiga ruwan zafi....tunda big man yasakko down stairs d'in yatsareta da ido bbu ko k'iftawa"ba k'aramin kyau da burgesa tayiba"danshi dama baya son ganinta da kayan Al'ada sai k'ananun kaya"Ajikinta taji kamar Ana kallonta Akeyi"ta d'ago kanta da sauri....tsab kyawawan idanuwansu suka sark'e da juna"Abdallah be dena kallon nataba saima doso Inda take yayi"ya wanku cikin farar shadda y'ar ciki da malun malun" kamar Ango sbd tsabar kyawun da yayi"ummu kuwa kallon second 5 ta masa ta d'auke kanta tana jin zafin kishin sa Aranta"sbd ji tayi kamar taje ta rungumesa"ta tuna jiya yadda yadinga yimata knocking da rok'onta ta bud'e masa k'ofa ya shigo ko k'asa ne ya kwanta"shidai baya son nesa da ita.... good morning beauty! d'aure fuska tayi tak'i Amsa gaisuwar tasa"gefenta ya zauna jikinsu na gugar juna"Ahankali yace"khairee yau za'a maida Auren daddy da Ammi bayan sallar juma'a.... Amamakinsa sai yaga tana murmushi had'e da fad'in Alhmdllh"Allah yasa Alkhairi"Ameen khairee nah"dama fita zanyi tare da daddy"break fast d'in saina dawo nayi"shiru tayi tak'i mgn"ko zaki mun rakkiya ne?"cikin k'osawa tace"dan Allah kaje kar daddyn yagaji da jiranka"bece komaiba ya mik'e tsaye zuciyarsa na wani irin turiri yafita"ita kuwa tashi tayi cikin sauri ta had'a kayanta kala 5 da Abinda zata buk'ata cikin k'aramin troley d'inta"sannan ta saka hijab saman kayanta ta d'auki hand bag da wayar ta da key d'in motarta"gabanta nata fad'uwa ta rufe ko ina ta fito rik'e da troley d'in ta nufi parking lot"dukda motar nada k'ura haka ta bud'e back sit ta ajiye troley d'in ta shige driver sit taja motar"tana fitowa ta tsaya bakin titi tasha mai sannan ta d'auki hanyar me duguri wajen k'arfe 8:35 am"tana driving d'in takashe wayar ta....tun tana driving d'in cikin dad'in rai harta fara gajiya"sbd rashin sabo"bata iso mai duguri ba sai wajen k'arfe 3 na rana"gajiya da yunwa na damunta"kai tsaye Aguwar da kakarta take ta dosa"gidan hjy innah"bayan ta gama parking Abakin k'ofar gidan ta fito tana janye da troley d'inta ta doshi cikin gidan.....tun dg soro har zuwa madaidai cin tsakar gidan share k'al yake goge kamar ba gidan tsohuwa ba"da sallama ummu ta shigo"bbu kowa tsakar gidan sai tabarma dake shimfid'e da redio Ajiye Agefe"troley d'in ta Ajiye ta cire hijab ta kwanta samqn tabarmar tana maida numfashi"Ahaka tsohuwar y'ar kimanin shekara 67 aduniya ta fito dg cikin wani d'aki da goro Ahannunta"turuz tayi tana fad'in wacece nake gani kamar ummulkhairy?"nice innah"ikon Allah kece tafe haka?"ko waya bakimun ba cewar kina hanya"ta fad'a tana k'ok'arin zama gefenta tanata kallon ta"sbd yadda ta canza mata"ummu dai batayi mgn ba ta tashi zaune suka fara gaisawa....
da yamma bayan ummu tayi wanka tayi sallah taci Abinci suna zaune parlourn innah sbd ankawo nefa"inna ta dubeta tana fad'in wai nan kikazo ko kuwa wata hidima Akeyi??dukda dai bbu wata hidimar dana san akeyi"dan Allah inna ki k'yaleni da tambaya"banaso nidai ki sanarwa kowa ina nan"zancen banza kenan"kamar yaya karna sanarwa kowa kina nan?"kodai yaji kikayi ?"sai gidana yazama mafaka bazakije gidan mugun ubankuba?"kai innah Ai yanzun zaman lafiya suke da mama"Eh mana tunda yaga me kud'i kike Aure"gashi ke kuma kina son bada matsala"inna bazaki ganeba Adena zancen kawai"ke kika sani Ai"duk tsiyarki dai dole asan kina nan ko?"tunda ba haka zaki tabbataba da zama nanba babu wanda yasani"shiru ummu tayi tak'i mgn"hankalinta na wajen waya tana gama turawa lawisa text d'in ta sauka lafiya"shima Abdallah ta fara tura masa text kamar haka....*na barka na fita dg rayuwarka Aganina shine daidai"baka sona ka rabani da martabata kuma kak'i cikamun alk'awarin da mukayi dakai na rabuwa da juna"sbd haka ina jiran takardar sakina bazaka koma ganina gidan kaba har Abada* tana gama sending ta kashe wayar gaba d'aya...
Ab'angaren big man....✍️

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤‍🔥❤‍🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤‍🔥❤‍🔥

*55&56*


....... Ab'angaren big man kuwa yayi busy ko gidan be dawoba balle yayi break fast d'in daya ce zai dawo yayi"Ana tasowa dg masjeed Aka maida Auren Ammi da daddy"wanda dg daddyn har Abdallah suna cikin farin ciki"dukda Ammin ta kafe ba yau zata koma ba"Amma yayanta da daddy sunce yau zata tare"sbd An kwashe komai na gidan Anzuba sabbi tun kwana 2 da suka wuce"duk irin farin cikin da big man yake ciki"zuciyarsa da tunaninsa na wajen mutum guda"wato khairee"sai wajen k'arfe 4:35 pm yanufi gidan"saidai yarasa meyasa tunda yadoshi side nasu gabansa ke fad'uwa?...kasancewar yanada key koda yaga k'ofar rufe be damuba saiya saka key yabud'e ya shiga"samqn 3 seeter yaje ya zauna yacire malin malin d'in jikinsa"yana k'arema cikin parlourn kallo"saima sannan yatuna da phones nasa daya saka silent"zaro babbar wayar yayi yafara dubawa.....wata iriyar bugawa zuciyarsa tayi"saidai yakasa yadda da Abinda yagani rubuce a text message d'in"da wani irin hanzari ya mike tsaye ya nufi d'akin baccinta"yana murd'a handle d'in k'ofar yajishi Arufe"yazaro ido ya nufi gudan d'akin"Abud'e yake saidai bbu kowa ciki"har toilet d'in dake cikin d'akin yaduba bbu kowa"ya fito Arikice ya duba kitchen da toilet d'in dake cikin parlourn duk bbu ummu"innalillahi wa inna ilaihir raju'un! ya furta da k'arfi zufa na keto masa"yadafe kansa dake sarawa"yayinda zuciyarsa ke wani irin had'ewa tana harbawa da sauri da sauri"dab'as ya zauna gefen kujera yana kallon fuskar wayarsa kamar yanason fito da wani Abu Acikinta.....never wlh! yafad'a da k'arfi yana yamutsa lallausan bak'in gashin kansa"yana girgiza kansa yace"bazai yuyuba khairee wasa kikeyi... yak'are maganar yana dealing number d'in ummu yajita is sweech up"ko malun malun d'in be mayarba ya mik'e tsaye yafita dg cikin parlourn da wani irin mugun sauri"cikin y'an second ya iso parking lot ya shiga mota"yajata a haukace"ikon Allah ne kawai ya iso dashi gidan Ammi"dg waje yayi parking yafito ya wuce ciki"k'awayen Ammi biyune da Ammin da Anty wasilah"sai matar yayan Ammin a parlourn suna zaune"kamar Anjehosa haka ya shigo bbu ko sallama"gaban Ammin yafad'i",kallo d'aya ta masa ta fahimci yana cikin tsantsar damuwa"sai tayi k'arfin halin cewa"kai lafiya zaka shigo bbu ko sallama??"da sauri yace"kuyi hak'uri Ammi"ina yininku?"yaduk'a ya gaishesu"suka Amsa da masa murnan maida Auren iyayen nasa"ya kalli Ammin yana fad'in baby fa?"sun fita da sadeeq zai kaita lalle da wankin kai"to Ammi kizo zan baki sak'o"yafad'a yana nufar d'akinta"Ammi ta mik'e tsaye tabi bayan sa...lokacin data shigo yana tsaye yanata safa da marwa Acikin d'akin yana ganinta yanufeta kamar k'aramin yaro yakama hannunta tun kafin tayi mgn cikin wani yanayi yace"dan Allah Ammi ki taimakamun khairee tadawo guna!wlh ta tafi gidansu inaga... Akan me ta tafi?"kasa mgn yayi yana sosa k'eya"d'aure fuska tayi tana fad'in kamata wani abun kenan ,ko kuwa sonta ne kafara shiyasa kadamu da tafiyar tata,ko kuwa ta gaji da AUREN YARJEJENIYAR da kukayi ko????".....sosai tambayoyin Ammin suka d'aure masa kai"yama kasa bata Amsar koda guda d'aya"ransa na bashi kamal ne yasanar mata kenan??...."sa'ada ta fad'amun irin yanayin zaman da kukeyi"hakan yasa na zurfafa bincike ta hanyar kamal nasan komai"kayi kuma daidai"saidai inaso kasani bbu ruwana da tafiyarta, sbd bansan meka mataba ta gaji da hak'uri dakai ta tafi"dan haka sai kasan yadda zakayi tadawo wajenka"saidai muddin ka bari ummulkhairy ta sub'uce maka na tabbatar ba zaka tab'a samun mace kamarta ba"yarinyar Arzik'i me kirki da girmama mutane da sanin yaka mata..... Ajiyar zuciya yasaki yana kallon Ammi idanuwansa jajir yace"Ammi dan Allah ki fahimceni"wlh ina sonta bazan iya rabuwa da itaba"sbd Abu kad'an shine dukta damu"kuma ni Araina da zuciya guda na aur.....kaga Abdallah nifa bbu Abinda zan iyayi"ban tab'a zuwa muka gaisa da iyayentaba sai sbd tayi yaji zan kwashi jiki naje?...shiru yayi sbd shima sai sannan yatuna be tab'a zuwa ya gaida iyayentaba"Asali kofa y'an gidansu da maifinta be saniba"lawisa kawai yasani Acikin friends nata....fitar Ammi dg cikin d'akin yadawo dashi tunaninsa"cikin sanyi jiki shima yafita"gaba d'aya hankalinsa da tunaninsa na wajen ummu"ransa yabashi sbd shi takashe wayar ta"driving yakeyi yana tunani yana kuma gwada kiranta saidai maganar gudace is sweech up"kai tsaye gidansu kamal yanufa"yana isowa bakin get dg waje yayi parking"be fitoba dg cikin motar yayi dealing d'in number kamal"yana d'auka ko sallamarsa be Amsaba yace"ina waje kasameni yanzun ina jiranka"bejira cewar saba ya yanke wayar ya kife kansa samqn sitiyarin d'in motar ya lumshe idanuwansa yana tunani"bbu Abinda k'irjinsa keyi sai bugawa"yasha Alwashin ko sama da k'asa zasu had'u bazai iya rabuwa da itaba"kuma bbu shegen daya isa ya Aureta muddin yana numfashi....cak tunaninsa yatsaya daya tuna da mubashshir"kodai wajensa ta tafi??wata zuciyar ta tambayesa"it can wlh! bazai tab'a yuyuwaba"yafad'a da k'arfi"hakan yayi daidai da shigowar kamal cikin motar"kallo d'aya yayiwa big man yace"subahanallahi! Allah yasa ba matsala kuka samu da ummulkhairy ba?"itace kuwa kamal"kuma babbar matsala"ta tafi tabarni kamal saidai ta turomun message tana jiran takardar sakinta"na kirata wayarta kashe"naje wajen Ammi sbd ta taimakamun ta koreni kamal"bansan ya zanyi da raina ba?"muddin narasa khairee mutuwa zanyi kamal"pls & pls kabani mafita"yanzun haka banda tabbacin tana gidansu d'in"raina yana bani ko wajen wannan d'an iskan ta tafi"idan kuwa zargina ya tabbata wlh tallahi sainaga bayansa.... yak'are maganar yana furzar da wani zazzafan huci dg bakinsa"jijiyoyin kansa da gaban goshinsa duk sun tashi....da farko dai inaso kayi hak'uri ka bama kanka nutsuwa Ayi Abinda yadace"dukda dama komai yafaru laifin kane Abinda na hango maka kenan tuni"zancen taje wajen wani dan Allah kadena karka b'ata Aurenku"zan iya maka rantsuwa da alk'ur'ani ummu baza tayi hakan ba"kaima ka sani"da Iliminta da komai da hankalinta"haba Abdallah! kar kishi ya rufe maka ido kayi Abinda ba daidai ba"Abinda yaka mata Ayi shine ka hak'ura zuwa gobe muje gidan k'awarta lawisa d'in nan nasan ita zata san Inda take ko?"nauyayyar Ajiyar zuciya big man yasaki yana fad'in k'warai da gaske"ni nama manta da ita sai yanzun"muje gidan nata kawai yanzun ko?"yanzun fa kace?"Ankusan kiran magrib fa"sannan niban san gidan taba saidai k'ilan baby tasani saita kaimu"kuma sai idan mijinta yabamu izinin shiga muyi mgn da ita ko??"Ajiyar zuciya Abdallah yasaki yana taunanin yaushe matsalar zatazo k'arshe??"kayi shiru big man"me zance kamal?"nazo sbd kataimakamun ne Amma naga ka d'auki matsayin da ummu take dashi Awajena da wasa"ba haka bane kayi hak'uri mana zuwa gobe sai ayi komai tunda yau ta tafi"nasan itama zatayi kewarka"hmm! kamal kenan" ba kasan yadda ta tsaneniba ne da bakace haka ba"haba big man daurewa zakayi sai kace ba Abdallah d'in dana saniba?"Aina canza kamal"ummu ta canza ni matuk'a ,muma dena wannan zancen"ni yanzun burinah matata tadawo hannuna"to ita preety kayi yaya da ita?"ta dameni da zafin waya da yimun zarya a office"wai na baka hak'uri iyayenta sunce ta fiddo miji"kuma kaine ta zab.....doguwar tsuka big man yaja yana fad'in ina cikin damuwa shine zaka k'ara mun da wata kamal?"wacece kuma preety?"kama dena kulata wlh"idan ta koma maka zancena kasanar mata ni mijin mace d'aya ne wato *ummul khairy*" haka kawai ana zaman lafiya zaka kamun zancen wata y'ar iska"y'ar dariya kawai kamal yayi sbd yasan zancen yayi tsawo zasu iya samun matsala da uban gayyar"yana kallon sa yace"rashin lafiya kayi duk kayi rama haka?"banza Abdallah yamasa sbd ya fahimci watama tsokana kamal keson yamasa"ak'ule yace"malama fitarmun dg cikin mota"goben ma idan bazaka rakaniba zanje da kaina"dg haka yayi shiru yatashi motar"kamal ya girgiza kansa yafita bece maka.... Awannan dare na yau big man yayi shi cikin damuwa da tunani"dukda yayi nafilfili na neman yardar Allah da kuma cikar muradin sa na dawowa da matarsa sannan ya kwanta"Amma tunani ya hanashi baccin kirki"sai wajen 2 am bacci ya kwasheshi yayi mafarkin ummu tanata kuka wai bazata koma wajensaba....cikin damuwa ya farka yaga har 7 am tama wuce"da hanzari yatashi yashige bath room yayi wanka da Alwalah yafito"bayan yagama sallah"yakoma gwada kiran ummu Amma Akashe"cikin sanyin jiki ya shirya cikin manyan kaya"shadda ce yasaka kalar sararin samaniya"ba k'aramin kyau yayiba"dukda yarame"lipton kawai ya had'a da kansa ya zauna parlourn ya d'an sha"kafin ya kira sa'ada bugu biyu ta d'auka"tun kafin tayi mgn yace"kinyi wanka?"eh yaya break fast zanyima"okay nanda 20 minit ki tabbar kin gama ki sameni part d'in mu"to yaya zanzo d'in"nakira Anty bata shiga"baby Antyn ki fushi takeyi dani"ta tafi ta barni yanzun so nakeyi tadawo guna"kai yaya meka mata da zafi haka? ta k'are maganar kamar zatayi kuka"idan kinzo munyi mgn"kinsan Ai gidan wannan k'awar tata lawisa ko?"Eh nasani"Ajiyar zuciya yasaki yace ina jiranki pls"dg haka ya yanke wayar"yana tunanin Allah yasa kar Ammin ta hanata zuwa"kasancewar Ammin tun jiya ta dawo da dare sbd tursasawar yayanta"yana kashe wayar yakira kamal"bugu 3 ya d'auka ko gaisawa basuyiba yace"na shirya kai nake jira"haba big man kasan kuwa k'arfe nawa yanzun? sakko zamuyi gidan mutane?pls kamal idan bazaks jeba zanje nika d'ai" yana fad'in hakan yakashe wayar ya mik'e tsaye Afusace yabar side d'in nasu"cikin gidan ya shiga"Ammi da daddy da baby suna dining area suna break fast"wanda baby gaba d'aya tana cikin damuwar tafiyar ummu"yayinda daddy keta nan nan da Ammi tanata sha masa k'amshi....lolx"cikin nitsuwa Abdallah yashigo da sallama"sosai Ammi taji tausayin d'an nata da taga duk ya zabge ga damuwa Atare dashi"saidai bataso ta goyi bayansa tunda batasan meya faru ba"bayan ya gaidasu sa'ada ta tafi d'akinta ta d'akko mayafi ta fito big man na tsaye"ina zakuje da safe haka?"cewar daddy"zata rakani wani wajene daddy"cewar Abdallah yana kama hannun sa'ada suka fita"bbu me mgn cikinsu har suka iso parking lot"body guards nasa na ganinsa suka taso ya tsaidasu"bayan sun shiga motar sa'ada tace"yanzun Antyn tana gidan su yaya?" bansan Inda ta tafiba sai munje wajen lawisan tukum maji"ko gidansu taje k'ilan"Amma nidai inajin kunyar zuwa gidansu yaya"sbd mamansu tanada kirki bazanso tasanar mata laifin kaba mutuncinka ya zube"bazata fad'i ba baby"sbd nasan halin khairee nah tanada hangen nesa"koke sau nawa tana miki warning karki sanarwa da Ammi sirrinmu shine kika sanar mata ko?"turo baki tayi tak'i mgn"Abdallah ya d'auki wayarsa ya kira kamal yana fad'in idan kaga dama ka fito mu wuce"dg haka yakashe wayar yana gyara parking ak'ofar gidan su kamal d'in"sa'ada ta fito dg front sit tadawo back sit"hakan yayi daidai da wayarta tayi ringing"waye ke kiranki?"yaya sadeeq nefa"bance ki d'auka ba"haka kawai ku damemu da surutu"Abarni naji da damuwata mana"dan Allah yaya kayi hak'uri na d'auka "wlh sbd ban d'auka ba zai iya shiga damuwa..... had'e rai Abdallah yayi yana mamakin yaushe baby ta fitsare har haka?"wato sadeeq da k'arfi da yaji ya cusa mata soyayyarsa Azuciya.....wayar ta katse wani kiran yakoma shigowa"big man yaja tsaki yana fad'in ke bani wayar"me zaka yi yaya pls?"bazaki bani ba?"tana turo baki ta mik'a masa"ya d'auka yana fad'in wai meye haka sadeeq?"ina tare da ita zamuje wani waje idan tadawo zata kiraka"dg haka yakashe wayar ya cillo mata ita"Alokacin kuma kamal ya shigo cikin motar"sa'ada ta gaidashi,ya Amsa da kulawa"yayinda uban gayyar keta cin magani yana driving d'in"Abokina Antashi lafiya?"Alhamdllh"cewar big man Atak'aice"yana fad'in ke inane Anguwar?"suna Ali Ak'ilu road"beyi mgn ba suka d'auki hanyar gidan lawisa"sa'ada na kwatanta masa har suka iso"Abdallah na kallon sa'ada yace"jeki sanar mata gani nan zan shigo muyi mgn"ko kuma idan mijinta na nan kimun sallama dashi"dato sa'ada ta Amsa ta fito dg cikin motar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login