Showing 21001 words to 24000 words out of 93107 words
Chapter 8 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete
kansa Adaidai saitin gefen fuskarta"k'irjinta ya buga! sbd har hucin numfashinsa da k'amshin mouth frishner d'insa tanaji murya can k'asa yace"K! wlh ki tashi kona b'ata miki rai"kinji dad'in kujera me laushi kinyi zaune ko?"dallah malam ka matsa ko wlh nayi maka Abinda baka tunani"to bissimilah idan zaki iya"yafad'a yana kamo hannunta yafara murd'e mata shi da k'arfi"duk yadda taso ta d'aure kar tayi Ihu saida tasaki k'aramar k'ara"gashi sunyi gab da juna"motsi kad'an idan tayi jikinsu zai iya gugar juna"dan girman Allah ka matsa"beyi mgn yaja tsaki yana d'ago kansa"hakan yasa ta mik'e tsaye"Ashe duk sunma fita"wlh kaida Allah cin zalin nawa da kakeyi"sannan rik'emun hannu.....maganar ta mak'ale mata sbd ganin ya juyo Afusace"ta rintse ido sbd ta zata marinta zaiyi"bazan miki komai ba yanzun sai lokaci me zuwa"banganeba?"ta fad'a tana bud'e ido"beyi mgn ba yanufi k'ofa"hakan yasa itama tabiyosa Abaya"saida ta fito sannan ya rufe k'ofar ya fisgi hannunta batace masa komai ba suka jero suna tafiya"suna fitowa waje bakin titi suka sami tj da junuid tsaye gefen motocin Abdallah"da wani irin mugun mamaki suke kallon Abdallah da ummu da kuma hannayensu"sannan suka kalli junansu"ummu Aranta tace"banzaye zan nuna muku ni macece yanzun"tj ne yayi k'arfin halin mgn wajen cewa"big man dama kana ciki ne?munzo d'azun Akace ka fita" yatsina fuska yayi yace"Eh yanzun ma zamu koma fita"to shikenan Ai saimu yi rakkiya ko? b'ata fuska ummu tayi ta dubi Abdallah dake k'ok'arin musu mgn cikin sanyin muryarta tace"nidai bana buk'atar wasu su rakamu mu kad'ai nakeso muje"kuma ka bud'emun k'ofar na shiga mana"ta k'are maganar tana kallonsa tana juya idanuwanta"kasa mgn Abdallah yayi gashi kan idon mutanene harda body guards nasa"Amamakin su tj sukaga yace"shikenan muje na bud'e miki"dg haka yabud'e k'ofar back sit ta shiga"yana k'ok'arin yayiwa su tj mgn tajawo hannunta dake cikin nasa"kawai saiya shigo be kulasu tj ba"yana shigowa ya rufe k'ofar ya ballah mata harara yana fad'in wlh sai kinsan kinsani Aiki"d'an murmushi tayi ta tab'e baki tace"zan koma saka wanima Akaro na biyu"kak'iyi nima wlh na baka mamaki.....βοΈ
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
β€βπ₯β€βπ₯ *AUREN YARJEJENIYA* β€βπ₯β€βπ₯
*17&18*
.......Wani irin kallo yaj efeta dashi wanda ta ita kanta ta kasa fassara wane iri ne?"yana tab'e baki cike da shan k'amshi yace"bana zaton ke y'ar haka dake har zaki iya bani wani mamaki"saidai muddin kika koma k'ok'arin yin makamancin Abinda kikayi yanzun nine kawai nasan meye zan miki"yak'are maganar yana rejecting d'in kiran junuid yaja tsaki"ummu ta tab'e baki tak'i yin mgn"Aranta kuma tasha Alwashin sai tayi sanadin rabashi dasu tj tunda ba mutanan Arzik'i bane su....tana wannan tunanin driver ya shigo yafara jan motar"ita kuma tana wasa da yatsun hannunta"yayinda uban gayyar yayi shiru yana tunani miye Amfanin kiransa da junuid yayi,bayan yanzun sun ganshi??.... ringing d'in wayar ummu yakatse masa tunani"ya yamutsa fuska yana fad'in karki d'agamun waya Anan Adameni da surutu marar Amfani"bata kulashiba ta d'aga sbd ganin lawisa ce"da mamaki yake kallonta tana wayar"beyi mgn ba yamatso sosai dab da ita"sam ummu bata Ankaraba saida taji yasaka k'afarsa me takalmi sawu ciki yatake mata yatsun k'afa da k'arfi"cike da Azaba ta saki wayar tana kallon k'afar"ta dubesa"da sauri ta d'auke kanta tana takure jikinta Awaje guda"gashi dama can k'arshe take zaune bbu sauran space d'in da zata matsa"big man kuwa ko Ajikinsa be janye k'afar saba"kashe wayarta tayi tana rintse ido sbd zafin dakeji yana ratsata"Ahankali ta yadda shine kawai zai iya jin Abinda take fad'a batare data bud'e idon ba tace"duk zalin nawa da kakeci na barka da All....bata k'arasa mgn ba"taji yatsunsa biyu saman lips nata yanata d'allarsu"ta doke masa hannu da sauri sadda ta bud'e idanuwanta"batasan sadda hawaye suka zubo mata ba....duk ranar da kikamun laifi na hukuntaki kikace kin barni da Allah zakiga Abinda yafi wannan"yak'are maganar tamkar meyin rad'a yana janye k'afar sa dg samqn tata"shiru tayi tak'i mgn ta b'oye fuskarta da mayafinta tana shashshekar kuka Ahankali"kimun shiru tun kafin ranki yab'aci"ko kuwa kinaso idan munje Ammi ta fahimci kinyi kuka?"nanma shiru tayi"ta share hawayenta"motar ta d'auki shiru"suna isowa get man yabud'e musu get suka shiga"Amma motar da body guards nasa suke ciki dg waje sukayi parking"bayan driver yafita ta d'ago kanta batare data kallesaba ta fita dg cikin motar"ta tsaya ta k'ara gyara rolling d'in dake samqn kanta"shikuwa fuska ad'aure ya fito ya tsaya gefenta"Adak'ile yace"Atsarina bana maimaita mgn"idan kunne yaji gangar jiki ya tsira"daga haka yayi gaba cikin basarwa yana tafiya cike da kasaita"me gadi da masu bawa flowers ruwa nata d'ago masa hannu"ummu kuwa gabanta keta fad'uwa"Aranta tana fatan Allah yasa y'an gidan nasu sunada kirki ba irin halinsa gare suba"sbd Azatonta gidansu ne sukazo"da hanzari tabi bayan sa"ta samesa tsaye bakin k'ofar shiga parlourn gidan"ya zura hannunsa guda cikin Aljihun wondonsa"kyakykyawar fuskar nan tasa Ad'aure....sosai taji ta daburce"ga wani uban kwarjini daya mata"sai taji kamar ta koma"saidai bata yarda takoma kallon saba"zo muje!"yafad'a yana mik'a mata hannunsa Alamar tazo"togewa tayi cikin marairaice murya tana fad'in"bbu kyaufa dan Allah"sannan idan muka shiga kana rik'e da hannuna dame za'a fassara hakan??kuma bayan haka ni ina jin kunya ko?"wai yaushe zaki dena mun musu ne?"iye?"sai kuma yaja tsaki yanufi k'ofa"ta biyosa tana magana k'asa k'asa bemajin me take fad'a"murd'a handle d'in k'ofar yayi yashigo da sallama Ahankali"Ammi dake zaune kan kujera bata Amsaba saima harara data tarbesa da ita"yasaki d'an murmushi domin hakan ya tabbatar masa da cewar taji Abinda yafaru"fuskarta ta fad'ad'a da fara'a tana Amsa sallamar ummul khairy"Aranta tana maimaita kalmar masha Allah! sosai taji yarinyar ta burgeta sosai data nuna ita me tarbiyya ce" sbd duk Abinda suke fad'a yanzun taji tunda gefen taga take zaune... sannunki da zuwa y'ata"maraba dake"ummu na murmushi kanta Ak'asa ta k'araso ciki ta duk'a k'asa kan carpet Ahankali tace"Ammi ina wuni??"lafiya qlau ya mutan gidan?"suna nan lafiya"masha Allah tashi ki zauna kinjiko?"bbu musu ta tashi ta zauna gefen kujera tana rissinar da kanta k'asa"yayinda uban gayyar yayi zaune yana danna waya tamkar babushi cikin parlourn" dama yau zatazo shine baka sanarmun ba"kuma zuwan marece Abdallah??" tamkar yak'i mgn sai kuma yace"nida bakiyi maraba daniba Ammi sai ita kawai kika damu da ita" hmm! kishi kakeyi da ita kenan?"to bari kaji"yanzun Andena yayinka"yayinta Akeyi itada sa'ada"ummu kuwa takama murmushi har fararen jerarrun hakoranta suka bayyana"tana mamakinsa ta d'auka ko Agidan ma baya sakewa da kowa"Ammi na dariya tace"kin ganshi yana kishi daku ko?"d'ago kanta ummu tayi ta kallesa ya zabga mata harara yana nuna mata kansa"wai dashi take?"da sauri ta gyad'a masa kanta tana murgud'a masa baki"yaja kwafa kawai"Ammi dake lura dasu ta tashi tsaye ta nufi cikin kitchen tana murmushi"K! bakiji warning d'in dana miki ba ko?"wai dan Allah miye na wani damuwa?"kaida ba'a maraba dakai fa"kaje kawai dg waje idan nagama zamana ka maidani gida"sosai yake kallonta da mamaki"Aransa yace"sbd kinga Ammi kike mun haka kamar wani driver naki?"Afili kuwa sai gimtse fuska yayi yace"kiyi yadda kikeso yanzun kafin mu fita ki Amshi hukuncin laifinki"shiru tayi dan tasha Alwashin bazata bisaba nafef zata hau"dan bata shirya jurewa mugunyarsa Akantaba.....zabura tayi zata tashi sbd ganin ya zauna gefenta"gashi batasan wace kalar mugunta zai mataba"saidai tana k'ok'arin tashin Ammi ta fito rik'e da tray Ahannunta" da sauri ummu ta mik'e tsaye tana fad'in sannu Ammi dakin kirani na d'akko miki"ta fad'a tana Amsar tray d'in batare data yadda ta kallo Ammin ba"Ammi na murmushi ta mik'a mata tace"kusha ruwa y'ata kinjiko?"Abdallah kuwa har ransa Abinda ummu tayi yaji dad'i"Amma miskilin ko'a fuska be nuna ba saima danna waya yakeyi kamar besan meke faruwa ba"lemo ne da ruwa da snacks"ruwan kawai ummu ta zuba tasha tana duba time shidda saura kwata"Ammi kuwa d'akinta ta wuce"batare data kallesaba tace"shidda saura yanzun dan Allah zan tafi"tashi ki tafi yafad'a cikin gatse"Aikuwa ta tashi tsaye da nufin ta tafi d'in"dukda taso tayiwa Ammin sallama"saidai tana tashi Ammin na fitowa dg cikin bed room nata tana rik'e da ledar shopping"badai tafiyaba?"kan ummu Ak'asa tace"Eh magrib ta kusane"hakane gsky"Amma ruwa kawai zakisha?"Ak'oshe nake"shikenan y'ata ina godiya da ziyara kinji?"d'an murmushi tayi"ungo kai ka rik'e mata"harda wata d'awainiya?"dan Allah Abar....kar muyi haka dake ummulkhairy"ki Amsa kinjiko?"Agaida mutanan gidan"ta Amsa dato tanata zuba godiya"Abdallah ya mik'e tsaye yanata cin magani yace"Ammi ita ta Amshi kayanta mana"kallon da Ammin ta masa yasaka ba shiri ya matso zai Amshi ledar"tamkar zaiyi kuka yace"kinafa gani Ammi dariya takemun"ummu kuwa rufe bakinta tayi ta dena masa dariyar"Ammi na murmushi ta mik'a masa ledar tana fad'in miye Amfanin ka inba ka rik'e mata d'inba?"Amsar ledar yayi ya gallah mata harara yana fad'in zaki sani yarinya"dg haka yayi bakin k'ofar da sauri"Ammi ta girgiza kanta tana tunanin yaushe Abdallah zai canza?"kiyita hak'uri da halayensa ummul khairy Ahankali zaki canzashi kinjiko?"Agaida mutanan gidan"dato ta Amsa jikinta Asanyaye ta fita"domin ta fahimci mahaifiyarsa mutuniyar Arzik'i ce kuma batasan wane irin Aure zasuyi ba?"duk sai taji wani iri"bata san ta fitoba saida taji motsin mutum gefenta" Atsorace ta kallesa"yayi bala'in had'e rai yana yatsina fuska ya mik'o mata ledar yak'i mgn"itama batayi mgn ba ta Amsa"sai kawai yaja tsaki ya nufi wajen da sukayi parking"ita kuwa bakin get directly ta nufa da sauri"sai bayan ta fita sannan big man da har yashiga mota ya lura bata biyosa ba"tsaki yaja yana dubawa kozai hangota"driver yasanar masa Aita fita ta get"shigo muje"iya Abinda Abdallah yafad'a kenan"tare da jan kwafa Aransa sbd shine yasan irin hukuncin dazai yanke mata idan tashigo gidansa"dan yafahimci raini ya shiga tsakaninsu da ita"dole kuma yayi maganin fidda rainin daya shiga tsakaninsu.....ummu kuwa tana fitowa taga wani me Adaidai da wata Aciki"ta tsaidashi da sauri"bayan ya tsaya ta sanar masa Inda zai kaita"yace nan gaba kad'an zaima sauke matar"da sauri ta shigo ciki tana sakin Ajiyar zuciya"saida suka fara tafiya sannan ta duba cikin ledar taga turaruka ne masu kyau da tsada na jiki dana kaya"tayi murmushin jin dad'i"sai wajen shidda da rabi ta iso gida.....
big man kuwa suna isowa gida yafito dg cikin mota"Amamakinsa ya hango su tj zaune kan resting chairs a compound d'in gidan da Alama shi suke jira"tsaki yaja dama cikin haushi yake sbd Abinda ummu ta masa"saidai yarasa meyasa suketa son bibiyarsa kodai kud'i suke sone?? yatambayi kansa yana cigaba da tafiya"driver na biye dashi da brief case nasa daya d'akko masa....tj yadubi junuid yana fad'in gashi nan ma yadawo"sonake naji Abinda mukaji gaskiya ne dg bakinsa"in kuwa gaskiya ne to Aljannar yarinyar nan Asiri ta masa"junuid yace"tabbas Asiri ne tj"kanafa gani y'ar iskar yarinyar nan ta hanashi kulamu"sannan tasaka yabud'e mata k'ofar mota ta shiga" kasanfa yadda ya tsaneta"yadda nasan halinsa inba iyayensaba waye ya isa yasakashi koya hanashi...shiru sukayi sbd ganin zai wuce ta gefensu"big man wajenka fa mukazo"tamkar bazai kula suba"sai kuma yatsaya yana fad'in menene?"Agajiye nake kunsan bansan takura ko?"pls kazo ka zauna muyi mgn"bece komaiba yanufi wajensu"yayinda driver ya mik'a masa brief case nasa yabar wajen"cikin gundura big man yace"5 minit na baku kuyi maganarku inada Abinyi! yafad'a cikin shan k'amshi....dama wani labari mukaji me ban mamaki"wai An saka maka rana kusan sati 2 kenan Amma bamuda labari duk yadda muke dakai"sannan yarinyar nan data maka rashin kunya kwanaki da ita Aka saka muku ranar???"mik'ewa tsaye yyi yana tab'e baki yace"kunyi tambaya kun bama kanku Amsa to me yarage kuma?"wai kana nufin sonta kakeyi?"tsaki yaja yace"kaga junuid ? bansan irin wa'annan maganganun banzan kafi kowa sani"Abinda nasani kawai zanyi Aure"ina sonta bani sonta bakuda damuwa da hakan"daga yayi gaba yabar musu k'amshin turarensa.....Ajiyar zuciya junuid yayi yace"garama ya Auri preety da wannan yarinyar"sbd preety batada wayo"wannan kuwa tanada wayo zata iya rabamu dashi mudena Amfana da dukiyarsa"nima dai Abinda nake tunani kenan"saidai mudena masa zancen kasan shi beda kyau idan Aka tab'osa"cewar tj suna tashi suka bar gidan...
**********
Duk'e take gaban wani mushurikin boka"yanata bugun k'asa"can yad'ago kansa yana kallon ta da jajayen idanuwansa yace"wannan Aure bbu gudu bbu ja da baya sai Anyi shi"matsawar zaki hana tofa har ranki zaki iya rasawa..... innalillahi wa....ke dakata! ba'a kira mana sunan Allah Anan"to Amma boka bbu yadda zakayi?"babufa yarinya"ko ina zakije zasuci kud'inki ne"saidai yanzun idan kin koma gida zaki tarar da Abin mamaki"muma nan dakika gani munsan gaskiya Amma muke dannewa"idan kinga munyi Aiki Ansamu nassara dama can haka Allah yarubuta"bana yin Aiki sai nayi duba naga za'aci nassara ko kuwa???"jikin goggo Luba Asanyaye ta tashi ta nufi gida....saidai Abin tashin hankali tana zuwa tasami Asiya nasir yakorota da cewar be sonta be k'aunarta, shi ummulkhairy yakeso"ta yayama harta zama matarsa?"gashi saki 2 yamata harda yaron ciki Ajikinta na wata biyu"sai Amaye Amaye takeyi...hankalin goggo Luba idan yayi dubu tashe yake"saidai dayake bak'ar zuciya ce da ita bata sadudaba "saima tunanin take gobe taje wajen wani boka Ayi Aikin da Asiya zata koma d'akinta"gashi nasir bbu kunya yazo har tsakar gidan yayi rashin mutunci da jefa mata takardar saki yace"sun cucesa Allah ya isa shi ummulkhairy yakeso"ummu da mama na d'aki suna jin komai"hjy yaya na tsakar gidan tana tsinewa nasir Albarka"lokacin goggo luba na yawon bin bokaye"bayan lafawar komai ne tadawo gidan......
haka rayuwar taci gaba da lulawa "kwanci tashi da dare yayi dandanan sai gari ya waye" tunda ummu da Abdallah sukaje gidan Ammi basu koma had'uwa ba"ko waya basuyi"tun sauran sati 3 biki goggo murja takai ummu maiduguri"Aka fara yimata gyaran jiki dana fata da gashi"da koya mata dubarun iya zama da miji"sati biyu kacal tayi Acan tafara k'ok'arin dawowa sbd biki yarage saura kwana8"kuma kamal yakirata zaizo ranar friday yaka mata invitation cards da Abinda zata buk'ata itada k'awayenta"dan ya tambayeta ta waya dame dame zasuyi?"tace itafa bbu komai sbd ba Auren dindin bane"saida taga beji dad'i ba sannan tace"yini da wa'azi kad'ai zasuyi "dama lawisa ta fiddo Anko tun sauran wata d'aya tanata nunawa friends nasu"dukda ummu bataso fito da Ankon ba haka dai ta hak'ura tabarta sbd lawisa ta wuce komai Awajenta"gyaran jiki aka mata na Asali"wanda ya zauna Ajikinta sosai"fatarta ta k'ara haske da yellow da taushi da sulb'i"gashinta yak'ara tsawo da bak'i"duk Inda ta zauna ta tashi sai Anji k'amshin jikinta"gaba d'aya ummu tausayin kanta takeyi sbd ganin Anata wahalar da ita da wani gyare gyare"bayan tasan irin kalar Auren daza tayi..... Ayau Friday tun wajen k'arfe 7na safe ummu da k'anwar mama suka baro garin maiduguri da dumbun kayan gyaran jiki da turarukan wuta da ummu zatayi Amfani dasu Agidanta"tayi kamar Aljannah sbd kyau"yayinda kuma Anan yau za'a kawo lefen ummu"mama da umman lawisa da goggo murja sunyi busy Anata shirye shiryen tarban bak'i"wanda gidansu lawisa ma za'a tarbesu.... Ango kuwa tamkar bashine Angon ba"zaka d'auka kamal shine Angon"sbd hidimar dayakeyi"dashi da Ammi da Anty wasilah suka shirya lefe"kuma Ammi tace"bbu taron da za'a yi kamal da Abdallah da sa'ada zasuje su kai lefen"wanda Abdallah yasha Alwashin bbu Inda zashi"kayan Angunci ma saida sukayi fad'a da kamal daya d'inko masa kala 10 sbd yana gaba da kayanmu na al'ada"zai iya shekara be saka shadda ba"dan dg sallar idi sai sallar idi yake saka manyan kaya"ga preety da k'awayenta keta zugata datayi sake zai Auri wata duk ta tashi hankalinta"tun yana biris da ita har yafara jin tausayinta yana bata baki"yanzun haka kamal yatsara harda dinner za'a yi yyinda Abdallah besani ba"umma balki kuwa taso Ace itace zata had'a lefe sbd ta yagi rabonta cikin kud'in had'o lefen sai hakan be faruba"kuma Akace Abdallah da kansa zai kai lefe ba'a taro"saidai dukda haka dama tayi kutu kutun data bama daddy shawara Ai su fara zama Anan gidan kar Abdallah yayi nisa da gida"idan sun haihu suka yaye Abinda suka Haifa saisu Amsa su kuma su koma gidansu"kasancewar tasan daddy nada son yara Aikuwa ya Amsa da shawaranta cikin jin dad'i....
wajen k'arfe 3 na yamma su ummu suka iso gida....βοΈ
Adinga sharhi gaskiya ko arage yawan pagesπ©π
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
β€βπ₯β€βπ₯ *AUREN YARJEJENIYA* β€βπ₯β€βπ₯
*19&20*
........wajen k'arfe 3 na yamma su ummu suka iso gida"tun daga soro sukejin k'amshi na girki na tashi Agidan"ga sabon fenti Ana tayi tun dg k'ofar gidan har cikin soro"ummu taji wani irin tausayin iyayen nata"gaba d'aya yanzun sai taji Auren yafitar mata Arai....goggo luba da Asiya na zaune tsakar gidan ko wace da cikinta"uwar cikinta wata na biyar yake"y'ar kuma ukku garesa har yafara turowa"ummu daketa kwad'a sallama ta dubesu taji sun bata tausayi" saidai tasan son zuciya ne yakawosu ga hakan"mahmood Autah yayi ihun murna yazo ya rungume ummu"umma da mama suka fito dg cikin d'akin suna musu sannu da zuwa"yayinda goggo luba kejin kamar ta had'iyi zuciya ta mutu sbd bak'in ciki"gashi mlm rufa'i yayi bala'in juya mata baya yanzun Agidan"goggo ina wuni??"cewar ummu tana rik'e da hannun mahmood"da k'yar ta Amsa da lafiya qlau tana binta da wani irin kallo kamar zata cinyeta" sbd ganin yadda ta canza cikin k'ank'anin lokaci"tubarakallah masha Allah y'ata"lallai kin fito sak Amaryar ki"yanzun kuwa k'awarki ta fita tazo baku isoba"cewar umman lawisa"Eh umma munyi waya da ita muna cikin nafef yanzun zatazo Ai"ina yininku umma ??"lafiya qlau ya hanya?"Alhmdllh"muje ciki ko?"umma tafad'a duk suna shiga d'akin mama"shima parlourn yayi gwanin kyau An canza yadin kujeru da sabbin labulaye"zama ummu tayi sukaci Abinci suka huta"umma da goggo murja duk suka d'auki Abinda Aka had'a suka tafi dashi gidansu lawisa"lokacin Anata kiran sallar la'asar"d'akin yarage daga ummu sai mama sai bak'uwa Anty Aysha da sukazo tare da ummu"mama ta kalleta tace"dukda sunce basu buk'atar komai munyi miki kayan kitchen"sannan zamu shirya miki d'aki guda sbd gudun gori wata ran"ummu na k'ok'arin mgn wayarta tayi ringing"saida taji fad'uwar gaba dataga kamal ne"jikinta Asanyaye ta d'auka tana