Showing 60001 words to 63000 words out of 93107 words

Chapter 21 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete

wannan shegiyar yarinyar me kama da Aljannu da Abdallah"junuid kuwa Ahankali yace"dama dan Allah wani hannun jarine zamu k'afa muna buk'atar million 4 shine mukeso dan Allah ka Ara mana"d'an murmushi big man yayi wanda iyakacinsa fatar bakinsa"dama yayi zaton kud'i suke so"kuma ransa yabashi k'arya sukeyi"k'ilan y'an matan su na bariki zasuje suyima sharholiya"kuma sunsan baya basu rance saidai yabasu kyauta....yana wannan tunanin ummu ta katsesa da cewa"gaskiya yaya Abdallah niban Amince kabasu Aron irin wa'annan kud'in har haka ba"shi hannun jari idan za'a zuba mutane da yawa ke had'awa Ayi aga me za'a samu riba?"wannan wane irin jarine daza'a zuba har 4 millions Acikin sa??"kinga bewar Allah ina ruwanki Anan?"ke mukazo mukace ki bamu ne?"balle k.....you are very stupid! Abdallah ya katse junuid Afusace yana binsa da wani irin shegen kallo yace"ita matar tawa kake gayama mgn haka junuid?"ina ruwanka da ita?"yafad'a Aharzuk'e yana kama ummu suka mik'e tsaye"ta saka kuka"ya rungumeta Ajikinsa yana fad'in menene kike kuka?nidai bana son tarayyarka dasu.....tabbas big man ruwa baya tsami banza"wannan matar taka Asiri ne ta maka"cewar tj cikin wani yanayi suna mik'ewa tsaye"Abdallah beyi mgn yafara danna waya"hakan yatabbatar musu da cewa security zai kira amusu koran kare"da hanzari sukayi gaba"ummu ta b'oye dariyarta ranta fari k'ar"Abdallah kuwa tsaki yaja yana kama hannunta suka wuce ciki"Atare sukayi break fast"sannan ta rakashi yaje yayi wanka"yauma manyan kaya tasaka rigimar saiya saka...dg ita harshi idan suna tare suna zuba soyayya da bama juna kulawa zaka d'auka sun manta irin AUREN da sukayi ne"Aranar sai k'arfe 12 na rana Abdallah yafita....
Da yamma ummu na zaune kan kujera tana sanye da mini siket red da bak'ar t shirt me dogon hannu"ta d'aure gashinta da red d'in bant"tanata tunanin ina sa'ada taje koda safe bata shigo tayi break fast ba"kuma takira wayarta yafi sau 5 bata d'auka ba"tana cikin wannan damuwar Abdallah yashigo parlourn"sadeeq na biye dashi da ledoji Ahannunsa daya ruk'o masa"ummu ta Amsa sallamar su tana fad'in sannu da dawowa"yauwa my khairee"sadeeq ya Ajiye lodijin yana gaisheta yafita"Abdallah dake kallonta sai yaji dama be shigo da sadeeq ba yagantaba"sbd sosai ta masa kyau....yaya Abdallah dan Allah zanje cikin gida na duba baby nagani ko lafiya?"kaga yau Alhamis bbu islamiya kuma koda safe bata zoba na kirata shiru"ta k'are maganar kamar zatayi kuka tana mik'ewa tsaye"Abdallah dai yana tsaye yana kallon ta"yana tuna shimafa duk yau baiga baby ba"Ahankali yace"zo muje ki rakani nayi fitsari sai muje na rakaki ki dubata ko?"gaban ummu yafad'i tana tunanin shifa besan miye wani abu kunya ba"Amma Afili kuka tasaka masa itadai yabari taje ta duba yanzun"shikenan ya isa" jeki ki sako hijab d'inki"da gudu ta nufi d'akinta ta sako hijab har k'asa red me hannu"tana fitowa suka had'a ido da Abdallah dake tsaye ya jingina bayansa Ajikin bango "yazura hannunsa guda cikin Aljihun wondon shaddar dake jikinsa sky blue"ganin zata fita da gudu yasakasa saurin fad'in miye haka khairee?"so kikeyi ki fad'i ne?"kije Ahankali mana"dato ta Amsa ta fita"shi kuma saiya shige bed room d'in ta"Acikin toilet nata yayi buk'atar sa da hanzari yafito yarufe k'ofar parlourn ya nufi cikin gidan"sbd ransa yabashi umma balki zata iya yiwa ummu Abinda ta gadama marar dad'i...ummu kuwa da sallama ta shigo main parlour d'in"umma balki na zaune itada wata k'awarta suna mgn k'asa k'asa"sai mai Aiki dake jera dinner saman dining table"Amamakin ummu taga umma balki na jifarta da mugun kallo basu Amsa sallamar tata ba"sai mai Aikin ta Amsa mata"d'ukawa k'asa tayi tana fad'in umma ina wuninku??"daba'a wuniba da kin gammu tsohuwar munafukar Allah"ubanme yakawoki nan??"ummu batace komaiba ta mik'e tsaye ta nufi k'ofar d'akin sa'ada"ke wai dan ubanki bakiji ina miki mgn ba?"ubanme kike nema ne?"cewar umma balki afusace"sosai ran ummu yab'aci da irin zagin datake yi mata"tajuyo da nufin tayi mgn suka had'a ido da hafsat data fito dg cikin d'akin ta"ke banza kin isa uwata na miki mgn kimata banza! ta fad'a tana nufo Inda ummu take"cikin fushi ummu ta matso kamar zata wuce ta gefenta" ta d'auketa da wani gigitaccen mari tana fad'in ni kike kira da banza ban girmekiba??....ki k'ara mata wani marin nace khairee! cewar big man daya shigo cikin parlourn Agadarence"umma balki takama salati tana fad'in dama kaine katurota tazo ta gayamun mgn taci mutuncin y'ata?"hafsat kuwa kuka ta fashe dashi tana ja da baya sbd ganin Abdallah yana nufo Inda take cikin fushi"da sauri ummu ta fad'a jikinsa ta fashe da kuka itama"sbd tasan halinsa karyaje yayi Abinda daddy zaiyi fushi dashi"me Aikinsu dake tsaye da k'awar umma balki sai bada hak'uri sukeyi"Abdallah ya d'ago kansa ya kalli me Aikin sbd yana ganin girmanta yace"ina baby taje?"tana wajen hjy tun d'azun ta sanar mun dg boko zata wuce"Abdallah bece komaiba ya d'ago kan ummu yana share mata hawayenta da tafikan hannayensa"kafin yaja hannunta suka fita batare daya tanka umma balki dake b'ab'atun k'arya da sharri ba"suna fitowa ummu tace"yaya Abdallah ina jin tsoron kar matarcan ta had'aka da daddy fa? kamar bazaiyi mgn ba sai kuma ya girgiza mata kansa yana fad'in muje karki damu khairee"bata isa tayi Abinda Allah beyi ba"yafad'a yana rik'e da hannun ta suna tafiya"itadai bata koma mgn ba har suka iso sashen nasu"Abdallah yajata suka zauna kan kujera yana fad'in to kicire hijab d'in mana"batayi mgn ba ta cire kamar yadda ya buk'ata"shi kuwa wayarsa ya zaro yakira Ammi"tana d'auka yayi sallama yana fad'in Ammi baby na nan?"dg d'ayan b'angaren ta Amsa da Eh gata nan tanata Aikin nata wato shagwab'a"ga sadeeq yazo d'aukarta tak'i binsa"yarinyar nan bafa cikakken hankaline da itaba Ammi"ta tashi tazo nan bata sanar mana ba"duk khairee ta tashi hankalinta dataga bata gantaba duk yau"kuma ta kirata bata d'auka ba"wai dama bata sanar maka ba?"Allah ya kyauta ma Auta"Abdallah beyi mgn ba yakashe wayar"shine bazaka bani mu gaisa ba?"cewar ummu zata tashi"ya rik'e hannun ta guda yana fad'in Ai nasan kullum sai kunyi waya"kin daiji baby tana can zamu had'u da ita idan tadawo"dan Allah kayi hak'uri ka k'yaleta"ai dama goyon bayanta kikeyi ko?"yanzun tashi muje kayi lunch"bece komaiba yana rik'e da hannun ta suka wuce dining area...

Bayan kwana 2✍️

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤‍🔥❤‍🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤‍🔥❤‍🔥

*47&48*


*Bayan kwana biyu*
kimanin kwana 2 kenan Abdallah na fama da matsalar ciwon mara da tsananin feeling d'in ummu"duk dare idan ya kwanta sai yaji inama Atare suke"office ko a gida bashida Aiki sai tunani"yayinda ummu keta baya dashi "shi kuma yana manne mata"sau dayawa tana masa Abubuwan dake sosa ransa"haka zaiyi fushinsa ya bama kansa hak'uri ya huce"ita kuwa ko Ajikinta da fushinsa"Ajiya friday sukaje shida ita gidan Ammi ta gaisheta"Amma bece su biya su gaida nata iyayen ba"tana zaton kodan sbd iyayenta na talakawa shiyasa be damu daya sansuba har yaje ya gaishesu ?"kimanin wata 5 kenan da Aurensu dashi Amma besan kowa nata ba"dukda ga yanayin yadda AUREN nasu yakasance Amma koma miye yaka mata Ace yasan wani nata"Ayinin ranar da wannan tunanin ummu ta wuni wanda Abin yamata ciwo sosai Aranta.....
Ayau yakama satday misalin k'arfe 6:11 pm"ummu na kitchen tsaye gaban gas cooker tana juyo Abinci Acikin warmer"bayan ta idar ta rufe"d'ago kan da zatayi hancinta yashak'o mata k'amshin turaren gwanin nata"saida taji k'irjinta yabuga"ta d'ago kanta da sauri suka had'a ido"yana tsaye da k'ananun kaya Ajikinsa"hannayensa na rungume ak'irjinsa yatsareta da mayun idanuwansa yana kallo kamar yaune yafara ganin ta"ummu kuwa suna had'a Ido dashi ta d'aure fuska sbd ganin irin kallon dayake binta dashi"shi kuwa d'an shafa kansa yayi yana d'age gira yace"madam yaya?"haba yaya Abdallah bbu ko sallama fisabilillahi ni har kabani tsoro ko?"ta k'are maganar cikin shagwab'a"dama can mecece ke inba matsoraciyar ba khairee?" bata kulashiba ta nufi wajen sink tana wanke hannunta"saidai kawai taji motsin takunsa Abayanta"ta juyo da sauri suka kusan cin karo da juna"tayi baya hanzari tana b'ata rai tace"kaje dan Allah kayi Alwalah ka tafi masjeed lokacin sallah yayi"ta k'are maganar tana yarfo masa ruwan hannunta Asaman kyakykyawar fuskarsa"yad'an saki guntun murmushi yana fad'in ke fin fara yin sallar ne?"girgiza kanta tayi tak'i mgn"hmm ! to jiya kika fara sallah nasan jinin ya d'auke"tsabar kunyar maganarsa kamar ta zura Aguje haka taji"yayinda shiko Ajikinsa"bata koma kulashiba tayi k'ok'arin tafiya ta gabansa ya ruk'o hannayenta tak'i kallonsa tana son k'wacewa"ya janyota jikinsa ya rungumeta yana fad'in meyasa kikemun haka khairee?"shiru tayi"ya zuro kansa gefen wuyanta ya fara sinsinar ta yana goga mata lallausan sajensa yana sakar mata hucin numfashinsa......sumar wucin gadi ummu tayi"gaba d'aya jikinta ya mutu murus"saidai tayi jarumtar son k'wacewa dg jikinsa"shi kuma ya matseta sosai"ita kanta yanayin da suke ciki yamata dad'i"kasancewar shekarunta sunkai label d'in da zata buk'aci namiji akusa da ita....ganin big man beda niyar cikata yasaka tayi lamo Ajikinsa"saida yasaki jikinsa sannan ta tureshi tayi wuf zata gudu"yakoma ruk'ota tana turjewa yajata jikin bango"ya ware mata hannayenta ya rik'esu da kyau"ita kuwa rufe Idonta tayi tana mamakin meyasa idanuwansa sukayi jajir??"binta yayi jikin bangon yana sinsinarta dg bisani ya had'e fuskarsa da tata yana son yayi kissing nata"tanata janyewa ga yarik'e hannayenta da gudan hannunsa"gudan hannun nasa kuma sai shafa mazaunanta yakeyi....dan Allah yaya Abdal....shiru tayi sbd nassarar cafkar bakinta da Abdallah yayi yana tsotsa tamkar zai cinyesa"sai juye juye takeyi yak'i barinta"har saida yayi nassarar kama harshenta yatsotse tas sannan yacikata"Aguje tabar cikin kitchen d'in"shi kuwa jingina bayansa Ajikin bango yayi ya rufe ido yana maida numfashi kamar wanda yayi wani Aiki"yayinda yadafe saitin zuciyarsa da gudan hannunsa" yafi mintina 10 Ahaka kafin dg bisani ya bud'e lumsassun idanuwansa yafita dg cikin kitchen d'in jikinsa bbu k'arfi ko kad'an"ya kalli cikin parlourn bbu ummu"d'an murmushi yasub'uce masa daya tuna yadda dukta tsorata da abinda yamata yanzun"toilet d'in dake parlourn yashiga yayi Alwalah yatafi masjeed"be dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i"ya shigo da ledoji Ahannunsa"saidai bbu ummu bbu Alamarta Acikin parlourn"k'ofar d'akinta ya kallah sannan yanufi kitchen yasaka mata ice cream d'in daya shigo mata dashi a fridge"shi kuma ya had'a coffee yafito yazo ya zauna yana sha yana tunanin Abinda yafaru d'azun a kitchen"dan yanda yakejinsa wani iri ko Abincin bazai iya ciba"bayan yagama shan coffee d'in ya kwashe Abincin yaje yabayar yadawo ya nufi side d'insa"gefen bed ya zauna yana tunani"can yasaki tak'aitaccen murmushi yana fad'in my khairee kenan ! yaka mata ki Ajiye tsoro ki barni naji dad'i Ajikinki kamar kowane namiji magidanci yafad'a yana tashi tsaye yanufi bath room"yafi mintina 20 Aciki kafin yafito ya shirya cikin farar vest da boxer"ya d'akko key d'in dayake dashi na d'akin ta sbd ransa yabashi zata rufe k'ofar da key"Aikuwa yana sakkowa down stairs d'in ya gwada murd'a handle d'in k'ofar yajita Arufe...shafa kansa yyi yasaka key yabud'e k'ofar"can k'asan mak'oshi yayi sallama yashigo yamayar da k'ofar yarufe"ya jingina jikinsa abayan k'ofar yana bin ummu da wani irin mayen kallo"motsin rufe k'ofar sa yasaka ta farka har bacci yafara d'aukarta"tana sanye da doguwar rigar bacci, rabin cinyoyinta Awaje"gashin kanta yazubo agadon bayanta"da sauri ta tashi zaune tana murtsuke fuska.... Atake k'irjin ta yayi mugun bugawa sakamakon ganin big man tsaye"dukda d'akin akwai hasken dum night Amma tana iya ganinsa shima yana iya hangota"Abinda yamata d'azun a kitchen ta tuna"wanda dalilin dayasa kenan yau tak'i yarda ta zauna parlourn harya dawo.... khairee! na'am bakayi bacci bah?ta fad'a Ahankali"bacci kuma yanzun ?kofa 10 pm batayiba"shiru tayi tak'i mgn"very slowly yanufo gefen bed d'in ya zauna yana fad'in meyasa yau baki jira nadawo ba kika gudo nan??"nidai dan Allah bacci zanyi yaya Abdallah kaje saida safe mana"hmm! bbu Inda zanje fira nazo kimun"tunda kin gudo nan kin rufe k'ofar"Azatonki banida key d'in d'akin ko?"shiru tayi tak'i mgn"saima matsawa nesa dashi da tayi ta kwanta"Abdallah yayi murmushi shima yamatso ya kama hannunta guda yana fad'in yauwa! wana kama?"nace waye kika watsama ruwa d'azun a kitchen?"yak'are maganar yana k'ok'arin kwantar da kansa samqn cikinta....pls nidai kaje d'akin ka ka kwanta mana dare fa yayi"ta k'are maganar cikin shagwab'a tana k'ok'arin mirginawa gefe"wannan Abin da kikamun yaja bbu Inda zanje nan zan kwana"yafad'a yana rik'e hannunta gam"dan Allah yaya Abdallah ka cikani bbu kyaufa kuma bacci nakeji"fisgo hannun nata yayi ta fad'o samqn jikinsa"yarik'eta da kyau yana fad'in malama khairee"fad'amun tab'akin da nayine bbu kyau ko rungumekin danayi?? yafad'a murya can k'asa"yana k'ara shigar da ita jikinsa"dukiyar fulaninta nashafar faffad'an k'irjinsa"kasa mgn tayi zuciyarta na wani irin bugawa da sauri"bataso Abdallah ya kwanta da ita ayanzun ,tafiso saiya furta mata kalmar datake ZARGI ya b'oye Azuciyar sa....khairee baza kiyi mgn ba?"hannunta ta Aza samqn bakinsa ta rufe masa"ya rik'e hannun da kyau yazura yatsunta guda 2 cikin bakinsa yana tsotsa... zille zille tafarayi Ajikinsa sbd yanayin data tsintsi kanta me girgiza bawa"zare hannun yayi yana sinsinar k'amshin jikinta"yana lalubar k'irjinta"dan Allah kadena yaya Abdallah bana so"tafad'a tana sakq masa kuka"shi kuwa nishi kawai yakeyi idanuwansa sunyi jajir"Ahankali yadinga shafa bayanta yadena romancing d'inta"ta turo baki can k'asa k'asa tana fad'in kodai wani abu kaje kasha ne?"hmm! Khairee kenan tun ranar dakika mu nasiha na dena shaye shaye"kuma danaje malesia doctor na yafad'a mun nadena sbd lafiya ta"ka kyauta daka dena dan Allah"jikina yabani su tj komenene sunansa sune suka koyar dakai"shiyasa bana son Abotarka dasu"dan Allah kadena biye musu"yaya kamal shine kawai mutum na k'warai dana san yana tare dakai dan Allah....duk maganganun datakeyi big man najinta Amma yakasa cewa komai sbd bejin dad'in jikinsa" sakamakon ciwon mara"ummu dataga yayi shiru ta d'auka bacci yafara"saita gyara kwanciyarta Ajikinsa tafara baccinta hankalinta kwance..... Abdallah kuwa sai wajen 11 pm bacci ya d'aukesa"misalin k'arfe 2:35 pm wayar Abdallah dake Ajiye samqn bed side drower tayi ringing"kasancewar beda nauyin bacci"ya bud'e idanuwansa yana salati"saidai yaji fad'uwar gaba"ya kalli ummu dake jikinsa tanata bacci"wayar ya mik'a hannunsa yajawo"da mamaki ya d'auka sbd ganin sa'ada ce"tun kafin yayi mgn arikice tace"yaya kana ina?"ina gida mana lafiya?"wlh yaya yanzun naji wasu na waya bayan window d'ina Ana musu kwatancen d'akina dasun shigo main parlour" wai zasuyi garkuwa dani"what?? yafad'a cikin sark'ewar murya"wanda yabama ummu damar tashi"tayaya kika san haka baby bana son k'arya?"gida da security dakomai tayaya zasu iya shigowa koma suwaye??"nidai bansani ba yaya"fitsari na tashi nayi nadawo zan kwanta na fara jin mgn k'asa k'asa shine na kasa kunne naji"ta k'are maganar tana kuka"kin kira daddy?"ah ah"to karki kirashi"ki sauka dg samqn bed d'inki ki shiga bath room ki rufe da key gani nan zuwa naga shegen daya isa ya d'aukeki"dg haka ya yanke wayar"sai sannan ya lura da ummu data bar jikinsa tana zaune gefe"bece komaiba yakama hannunta suka sauka dg samqn bed d'in"meke faruwa ne yaya Abdallah??"bbu lokacin yin bayani khairee"kizo muje bazan barki nan ba sbd kar kema Azo Acutarmun dake"yafad'a yana nufar gudan side drower ya d'auki hijab nata daya gani ajiye ninke"tayi hanzarin Amsa ta sakq suka fita"da gudunsa ya haye samqn yasaka jallabiya ya d'akko bindigarsa daya siyo a k'asar England"zuciyarsa Adake yasakko down stairs d'in yaja hannun ummu dake tsaye jikinta keta kirma suka fita"bbu kowa dg bakin shiga cikin parlourn"kuma k'ofar Abud'e take"yaya Abdallah karfa acutar damu?"cewar ummu Ahankali tana rirrik'esa"beyi mgn yajata suka nufi k'ofar parlourn yana rik'e da bindigarsa"saima a sannan ummu ta lura da ita"bbu haske sosai ko ina da duhu duhu dukda Akwai nefa"Abdallah ne yafara lek'a kansa cikin parlourn ya hango mutum biyu maza tsaye da makamai A hannunsu zasu tura k'ofar d'akin sa'ada"fitilar jikin wayarsa ya kunna ya dallesu da ita"A razane suka juyo fuskokinsu"k'irjin Abdallah ya buga sbd kallon cikin idanuwansu da yayi sai yaga kamar yasansu"ummu kuwa jikinta na rawa ta rik'esa sbd ganin sun nufosu da makamai"Abdallah yaja tsaki cikin kakkausar muryanshi yace"su waye ku?"me kuke nema?"yak'are maganar yana saita guda da bindiga ya harbesa ga gwiwar hannu"Atake yafad'i yana ihu"gudan ya yarda makamin hannunsa yana yin siranda"Abdallah da ummu suka ida shigowa cikin parlourn"yana sai tashi da bindigar ya matsa ya kunnah haske"Atake parlourn ya d'auki haske"ummu ta nufi d'akin sa'ada Aguje"Abdallah kuwa yana dg tsaye yakira daddy"bugu 3 ya d'auka cikin wata iriyar murya yace"daddy ganinan a main parlour"pls kazo kaida matarka bbu lafiya"dg haka ya yanke wayar yasaka bindigar cikin Aljihun jallabiyar jikinsa"ya finciko hannun mutumin yakai masa wani wawan punch Atsakkiyar fuska"yasaki ihun Azaba"Abdallah ya fisge safar fuskar mutumin...... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! yafurta with a very shock sbd Arba da yayi da fuskar tj da har bakinsa da hancinsa sun fashe suna jini"girgiza kansa Abdallah yayi Azuciye yafara dukan tj kota ina yana fad'in waye yaturoku kuyi garkuwa da k'anwata??"cin Amanar da zaku sakamun dashi kenan??"hargowar Abdallah yasaka sa'ada da ummu suka fito parlourn"saidai suma sunyi mamakin ganin TJ ne"ummu kuwa batayi zaton Abdallah nada irin wannan jarumtar ba"duk yadda tj yaso yarama Abin yaci tura"sai k'ok'arin k'watar kansa yakeyi cikin galabaitar dashi da big man yayi"can ya hank'adasa yafad'i yamatsa wajen wanda ke kwance sume gwiwarsa na jini ya fisge safar"Atake fuskar junuid ta bayyanah"Adaidai kuma lokacin daddy da umma balki suka bayyanah Acikin parlourn"wanda hantar cikin umma balki saida ta kad'a"k'irjinta na dukan tara tara suka zauna kan kujera"ummu da sa'ada sukazo Aguje suka fad'a jikin Abdallah suna kuka"ya rungumesu cikin wani irin yanayi....ya isa haka Abdallah meke faruwa?"miye dalilin zuwan ku da kukansu??",kuma suwaye wa'annan?"yafad'a yana nuna su tj dake kwance dan bai shaida fuskarsuba"inaga Alh Abari saida safe mana Ayi maganar......yanzun za'a yita bama buk'atar shawaranki"cewar big man yana bin umma balki da mugun kallo"Amamakinta daddy bai tsawatar masa ba.... Atak'aice big man yayiwa daddy bayanin komai da sanar masa dasu tj ne Amma basu fad'i wanda yaturo suba"umma balki tasaki Ajiyar zuciya Ab'oye"wanda Abdallah na lura da ita ta raina gaskiyar ta"daddy kuwa salati kawai yakeyi yana kiran sa'ada"tazo ta fad'a jikinsa tana kuka"Abdallah kuwa tashi yayi ya zaunar da ummu yazo gaban TJ ya damk'i wuyansa yana fad'in fad'amun uban waye yaturoku kona kasheka na kashe banza"da hannu tj yanuna umma balki"tasaki salati tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login