Showing 24001 words to 27000 words out of 93107 words

Chapter 9 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete

masa sallama"ya Amsa yana fad'in ran Amaryar mu yadad'e"tayi d'an murmushi had'e da cewa tare da naka"ina wuni?"lafiya qlau"dama Anjima kad'an wajen 5 pm zamuzo nida sweetie d'inki mu kawo kaya dg nan zamuyi mgn"sbd bamusan wata Al'ada da kansa zaizo yakawo"dato ta Amsa tana masa kwatancen layin gidansu lawisa Inda Anan zasuje su sameta"bayan sun gama wayar ta sanar ma mama"kasancewar ba sallah takeyi bah sai kawai ta shige wanka"bayan ta fito ta shirya cikin lafaya purple colour me tsadar gske irinta y'an meduguri"tasaka bak'ar t shirt me dogon hannu daga ciki"bataso yin make up ba"Amma Anty Aysha da lawisa data shigo yanzun suka tursasata saida tayi"ita kuwa Aranta fata takeyi Allah yasa kar Azo da big man"sosai tayi wani irin mugun kyau kamar Aljannah"lawisa na kallonta tace"masha Allah mrs Abdallah! harara ta gallah mata tana fad'in tun kafin Ad'aura?"insha Allah Ai za'a d'aura d'in"irin wannan kyau haka"karma mu fita wani ya tsaidaki....ummu na k'ok'arin mgn kiran mubashshir ya shigo cikin wayarta"haka nan taji k'irjinta yabuga"ta daure tayi sallama bayan ta d'aga" daga d'ayan b'angaren mubashshir yace"my sweet heart ina nan waje ki fito zamuyi mgn five minutes pls"ka manta me yace maka A last time?"kidai zo pls"batace komaiba ta kashe wayar"lawisa ta kalleta tana fad'in waye?"mubashshir ne"tab'e baki tayi tace"kinga biyar saura minti 25 gashi idan munje zan gyara parlourn bak'i mu tarbesu Acan"to Akan me zai wani zo yab'ata mana lokaci?"muje naji meye mintina 5 yace na bashi"wanene?"cewar Anty Aysha"Amm telana ne"cewar ummu...suna barin d'akin"lokacin da suka fito tsakar gidan Asiyace zaune kawai"suna fitowa soro lawisa tace"zan tsaya dg gefe kuyi mgn Amma karki jima"saidai kuma in har da wata mgn yazo miki game da fasa Auren nan karma ki saurareshi"bema isaba k'awata yamaida iyayena k'ananun mutane"cewar ummu suna fitowa layin"mubashshir na zaune kan mashin nasa roba roba"tunda ya hango ummu yatsareta da ido"shi yau sai yaga tafi koda yaushe kyau da tsari da komai"tun kafin ta iso k'amshin turaren jikinta yafara isowa hancinsa"sallama tamasa "ya Amsa suka gaisa"ummu ta dubesa tana fad'in ina sauraronka sauri nakeyi"saurin naki yafini mahinmanci?"hmm! kai rannan saurin naka yafini mahinmanci da har ka kasa jiranah da mukaje gold stone ka tafi?"saidai na fito nasamu wayam baka nan"yanzun ba wannan ba"na shawo kan mahaifina ya Amince muyi Aure d....bakin Alk'alami ya bushe mubashshir! saidai kayi hak'uri mu jira lokacin dazai sakeni sai muyi Aure"sbd biki yau saura kwana8 kaga bbu zancen fasawa" bazan maida iyayena k'ananun mutane ba....ummu pls ki fahimci ceni mana"jikinah yana bani kar in yadda inyi sake ki Auri wan....kaga sai Anjima"ta fad'a tayi gaba"yayi tagumi yana binsu da kallo itada lawisa har suka b'acewa ganinsa...bayan ta gama yiwa lawisa bayani taja tsaki tana fad'in daga shi har shid'in duk bana sonsu na tsanesu"ni kuma wannan lusarin mubashshir d'in nafi tsana"da zaizo yadawo da hannun Agogo baya"idanma yakoma kiranki karki sake ki koma d'auka"ta k'are maganar tana jan tsaki"har suka iso gidansu lawisa mita takeyi"tare da ummu suka gyara parlourn bak'i cikin hanzari suka turare sa"suka jera snacks da dambun kaji samqn center table da drinks masu sanyi"lokacin k'arfe 5:4 pm"rufe k'ofar parlourn sukayi suka wuce cikin gida"sai wajen k'arfe 5:15 big man da kamal da sa'ada suka iso k'ofar gidan su lawisa"wanda big man Azatonsa nanne gidansu ummu"kuma kamal be sanar masa ba nan bane gidansu"daga wajen get d'in gidan sukayi parking"kamal ya fito dg cikin motar yaje ya sanarwa me gadi zasu shigo da kayan lefen"ya Amsa da to"kasancewar dama Ansan da zuwansu"body guards d'in Abdallah sune suka dinga d'akko Akwatunan har dozing 2 suka shigo dasu sunata Ajiyewa"key d'in sabuwar motar da Aka had'o da ita yana hannun kamal"sai bayan Angama shiga da kayan sannan kamal yakira ummu yasanar mata gasu nan"tunda suka gama wayar da kamal jikinta ke rawa tana jin fad'uwar gaba"lawisa ta fito haraban gidan sbd ta shigo dasu....big man kuwa yana zaune back sit shida sa'ada yana mata warning da babbar murya"saida kamal yamasa knocking sannan suka fito yanata shan k'amshi dan beso zuwa ba"saida yaga ran Ammi zai b'aci sannan ya yadda yabiyosu"yaci wankan k'ananun kaya sabbi dal"yayi wani irin mugun kyau"musammun sbd gyaran fuskan da Aka masa yak'ara fitowa da kyawun fuskar tasa"kamal nata y'ar dariya yana rik'e da ledoji biyu da Alama cards d'in ne Aciki"Ajere suka shigo cikin gidan"sai Akayi sa'a lawisa kuma na k'arasowa"da sauri sa'ada tace"Anty ummul khairy! ba ita bace" yanzun zaki ganta"cewar lawisa tana musu sannu da zuwa"wanda kamal ne kawai ya Amsa"Abdallah kuwa d'auke kansa yayima"ina ita gimbiyar ne babbar k'awarmu?"tana ciki yanzun idan nagama yi muku iso zan shigo muku da ita"dakin kyauta kuwa"batace komaiba ta rik'e hannun sa'ada suna gaisawa suna nufar parlourn bak'i" wanda da k'yar Abdallah ya Amsa gaisuwarta"suna isowa bakin k'ofar ta bud'e tace"ku shiga ciki pls ina zuwa"zan biki dan... baby! Abdallah yakira sa'ada bbu Alamar wasa samqn fuskarsa"lawisa batayi mgn ba ta juya Aranta tana tunanin dole ummu ta had'a da kissa wajen zama da wannan gadararren mutumin"bakin get ta nufa tayiwa me gadi mgn yasaka masu bama flowers ruwa su shiga ciki da kayan"bayan ta sanar masa ta wuce cikin gidan"ummu na zaune a bed room d'in umma tana tunani"tana ganin lawisa tace"harda wannan mr arrogant d'in Akazo?"bakida kirki wlh"hardashi mana"ga kayan nan za'a shigo dasu"masha Allah! kaya kam Abinda ke kaya"Akwati 24 ne"dukda banduba kayan ba"Amma su kansu Akwatunan Abin kallone"24 fa kikace lausy?"wai kin manta wa zaki Aura ne kike mamaki"?shiru ummu tayi"yanzun ki tashi muje kar suyita jira"in bacin sbd cards d'in da bazan ma komaba"da munje na Amsa zan dawo"saidai k'anwarsa nada kirki dason mutane"da zata biyoni naji yamata tsawa"ki nuna mata kulawa sbd tanata tambayarki"damafa shine mugu Agidan su" Amma wlh Amminsa nada kirki daya kaini na gaisheta kwanaki"wai big man d'in ne mugu?"Eh mana" kinsan irin muguntar dayake mun ne?"ko rannan wlh saida yasani kuka"shiyasa idan Akayi Auren rufe k'ofar d'akina zanyi tunda bbu ruwan kowa da kowa"ta fad'a tana tashi tsaye ta k'ara gyara lifayar dake jikinta suka fito"lawisa nata murmushi tana fatan Allah yasa soyayya me zafi ta shiga tsakanin Abdallah da ummu"..... Ab'angaren su big man kuwa"sa'ada k'in shiga parlourn tayi ta tsaya jiran isowar ummu sbd su shiga atare"bbu laifi mutumin naku ya yaba da tsabtar tasu Azuciyarsa"suka zauna gefen kujera"Ahh kace dai Ana murnan zuwanka Abokina tunda gama Abin kusa da baki nan Anshirya mana"cewar kamal cikin tsokana"yamutsa fuska big man yayi yana wani hura hanci yace"matsalata dakai Acici ne" da lafiya ake cin komai"kuma wlh kafini ci kake mun wani sharri"to nidai bazanci komai ba Anan kaima bazaka ciba"wannan kuma kayi babban sab'o wlh"kaima nasan kanaso kana kaiwa kasuwa sbd nasan kaji k'amshin girkin nasu"Amma wlh kaji na rantse sai naci har nayi guzuri"dg k'arshe na lura yau da y'an shan k'amshi ka tashi "to kagadai da sa'ada muka zo"idan kasaki wata b'araka zata sanarwa Ammi"look kamal! wai yazaka maidani kamar wani k'aramin yaro"tajima bata sanar da wani Abuba"itama hukuncin laifinta na nan idan mun koma gida"yafad'a yana jan tsaki" yaci gaba da cewa karfa yarinya taga nazo nan kanta yafashe tayi zaton takai wata har ta wani jamun Aji"dan wulak'anci zamuzo muyi zaune Amma shiru bbu kowaccensu"haba big man! dan Allah ka koyi hak'uri da juriya mana"kajira zasu zo mana"tunda mune ke nema dole muyi biyayya.... what?"cewar big man da k'arfi"kamal yadinga dariya sbd dama yasan saiya k'ular dashi"doguwar tsuka yaja yana duba wrist watch d'in dake d'aure A hannunsa adak'ile yace"tashi muje banga macen data isa na mata irin wannan jiran ba wlh"kamal na k'ok'arin mgn ummu ta shigo rik'e da hannun sa'ada"murmushi shimfid'e Asaman kyakykyawar fuskar ta"lawisa na biye dasu"cikin sanyin muryarta tayi sallama"k'amshin turarenta ya had'u dana big man da kuma wanda Aka turare parlourn dashi yabada wani sabon nau'in k'amshi daban"kamal ya Amsa sallamarta yana fad'in masha Allah A ransa yana tunanin k'aryar Abdallah ya rayu da kamar wannan macen Ace ko sha'awarta beji ba"in har bemajin zai sota tofa dole ko yaya yaji sha'awar ta Akwana Atashi....haba Amaryar mu irin wannan shanyawa haka"durling d'inki duk yayi fushi sbd Ak'agare yake yayi Arba dake"yafad'a yana murmushin mugunta sbd yasan ya kai big man mak'ura" yasaci kallon sa yaga yayi mugun had'e rai"ummu kuwa kasa mgn tayi ta zauna gefen lawisa ta zaunar da sa'ada tana fad'in sannunka da zuwa"yauwa ya kuke ya shirye shiryen biki?? Alhamdllh"ga card d'in da Abinda zaku iya buk'ata"cewar kamal"to shikenan muna godiya"cewar lawisa ta taso ta Amsa da hannu biyu ta fita dg cikin parlourn"ummu kuwa hankalinta na wajen sa'ada suna mgn k'asa k'asa suna y'ar dariya"sosai Abdallah ya tsargu da dariyarsu"yaji haushin ko in kulan da ummu ta nuna Akansa" gashi gaban wannan parrot d'in sa'ada d'in"saidai ya Ayyanah Aransa muddin bata kulashiba wlh tayi kad'an ya kulata....be gama wannan tunanin ba yaji sa'ada na fad'in dama laifin da yayan ya miki kenan?"Eh mana"cewar ummu tana sakkowa k'asa ta fara k'ok'arin zuba Abinda suka jera kan center table"Abdallah kuwa kallon zamu had'u dake yajefawa sa'ada yana cigaba da danne danne Awaya"Amma Azahiri duk yana Ankare da komai"kamal dai murmushi yayi beyi mgn ba"lemo exotic na kwali ta zuba cups 3 ta mik'a ma kamal da sa'ada"kafin ta bud'e sauran warmers d'in"k'amshin dambun naman yadaki hancinsu ta zuba musu cikin plates ta zuba spoon" kowa ta mik'a masa nasa"ta d'auki na Abdallah tana k'ak'aro fara'ar dole yayinda bugun zuciyarta ke tsananta bugawa"ta kuma k'udurta Aranta sai yaci wannan dambun naman duk zafin kan nasa"dan tasan zai iya cewa bazai ciba....dukda ummu najin kunyar kamal Amma haka ta d'aure ta zauna gefen Abdallah dake lura da ita ta wutsiyar ido"ta wani marairaice murya ta kallesa tana fad'in haba my hand some irin wannan fushi haka"kasan yanayin hidima"ina rok'on Amun Afuwa kaji??..... d'an sassauta murya yayi yad'ago kansa suka had'a ido da ita"Atare gabansu yafad'i"dan Allah fa nace?"shikenan na hak'ura"kamal tamkar yayi dariya k'asan zuciyarsa yana jin dad'in zuwan da akayi da sa'ada" sbd yasan dan ganin ta yasaka suke wannan pretending d'in....indai da gaske ka hak'ura to kasha mana"ta fad'a tana nufar bakinsa tafara k'ok'arin bashi lemon"saidai bata yadda ta kalli cikin idon saba"sa'ada ta dinga murmushi tace"kunyi kyau yaya"dama haka Anty nah keji dakai??"harara ya Aiko mata da ita"ta d'auke kanta tana b'ata fuska"Abdallah kuwa bisa tilas ya shanye lemon"suna had'a ido ummu ta ballah masa harara ta masa gwalo"be kulataba yabarta sbd ganin basu kad'ai bane "Ajiye cup d'in tayi sbd yasha fin rabi"k'ok'arin motsa dambun naman ta farayi yayi saurin cewa"no sai Anjima ba yanzun ba"nidai yanzun nakeso ko spoon biyu kayi"ki barshi zuwa Anjiman mana"yafad'a yana take mata k'afarta me uban laushi.....wani iri taji "sbd shima tashi k'afar nada taushi da gumi kasancewar bada takalmi yashigo cikin parlourn ba"sunkuyowa tayi kamar zata d'auki wani abu" ta mintsinesa daga tsakkiyar k'afarsa me cike da gargasan gashi"bata janye hannunta ba saida ya janye k'afar tasa"ta d'ebo spoon guda ta nufi bakinsa dashi tana dariyar yadda kamal ke santi"Ahankali tace" ga snacks nan sai sa'ada takai muku mota ko?da sauran dambun"gaskiya kin kyauta sosai muna godiya Amaryar mu"dama da my leemart nazo Amma ranar dinner zaki ganta" to shikenan Allah yakaimu lafiya...dinner? Abdallah ya maimaita kalmar Azuciyarsa yana tauna dambun naman"saidai d'and'a nonsa ba k'aramin dad'i yamasa ba"Amma A bad'ini saiya yamutsa fuska" kamal yatashi tsaye yana fad'in tashi muje mu jirashi Amota ko baby?"yafad'a yana k'ok'arin d'aukar warmer guda"sa'ada da dama ta gama ta tashi ta d'auki warmer guda ta kalli ummul khairy tace"Anty ai zaki rako yaya idan zai tafi ko?"Eh"to shikenan sai muyi sallama dg nan idan kin fito"dato ummu ta Amsa tana jin tsoron subarta dg ita sai Abdallah a parlourn"bata gama wannan tunanin ba suka fita....✍️

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤‍🔥❤‍🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤‍🔥❤‍🔥

*21&22*



....... Da sauri ummu ta matsa nesa dashi tana wasa da yatsun hannunta"Abdallah kuwa tab'e baki yayi yana danna waya"Ahankali tace"ina wuni?...."bana son ita gaisuwar taki"yafad'a kamar daman jiran ta gaidashin yakeyi"shikenan insha Allah bazan koma gaisheka ba"kikace mene?"yafad'a yana tsareta da ido"tak'i kallonsa kuma tak'i mgn"yaja tsaki yana fad'in saura 8days Ai?"mekake nufi?"bansaniba"last warning d'ina dake na k'arshe"duk lokacin dakika koma sawa naci Abinda yafito dg k'azamin hannunki saina baki mamaki"ban mance motar da kika saka na bud'e miki ba"ga yanzun kin koma sawa naci Abinda banyi niyaba"to sonake ki cika na ukkun dan Allah kiga yadda zamu kwashe dake"ni sai yanzun nake tausayawa wanda kikeso sbd ba k'aramin k'ok'ari yayiba"yafad'a yana jan tsaki ya mik'e tsaye yanufi bakin k'ofa"har zai fita sai kuma ya tsaya saida yagama shan k'amshin sa kafin yace"naji zancen dinner"bansan da itaba kuma bbu Abinda zanyi Akai"keda wanda kukayi gulmar buga invitation d'in sai kusan yadda zakuyi Amma ni baranjeba"ke wai nan Amarya ce ko?"yafad'a yana juyowa yana murmushi yana kallonta"zaki san ke Amarya ce kuwa very soon....duk irin bak'ak'en maganganun dayake gaya mata tanaji Amma ta lashi takobin bazata kulashiba"yaso ta tankasa Amma saita share"ya bud'e k'ofar yafita ya bugata da k'arfi"ta mik'e tsaye ta biyo bayansa sbd suyi sallama da sa'ada"saida ta had'a da sauri sannan harta taddosa suka jero suna tafiya bbu me mgn Acikinsu"sosai maganganun sa sukayiwa ummu zafi Azuciya"hakan yasa suna fitowa kallo d'aya kamal yamata yasan tanada damuwa"sosai yaji tausayinta"ya diro dg samqn motar yana fad'in ranki yadad'e sai yanzun aka barsa yafito?"murmushin yak'e tayi batace komaiba"sa'ada ta fito dg cikin motar tana kallonta tace"Anty sai ranar dinner d'in ko?"kanta ummu kawai ta gyad'a mata kafin tace"ki gaishemun da Ammi Allah ya tsare"dg haka ta juya ta koma ciki da sauri sbd kukan dake k'ok'arin k'wace mata"kamal ya harari big man yabud'e mota ya shiga"suka saka sa'ada A tsakkiya"kamal nason yamasa mgn Amma bbu dama"sa'ada kuwa sai surutu takema kamal yana janta da fira"wacce duk firan kan ummu ne"big man dayaji surutunsu yayi yawa ya bigema sa'ada baki"yana fad'in yaushe na zama Abokin wasanki??"kai kuma meye Abin kabiye mata kuna fira irin haka??"yafad'a yana kallon kamal"shikuwa tab'e baki yayi yace"bazan fasa fira da ita ba"kai kuma sai kayita yin shirun da bakinka"okay toko saukeni zakuyi ne? duk yadda ka zab'a haka za'ayi"cewar kamal ak'ule sbd yafara bashi haushi"banza big man yamasa k'asan zuciyarsa yana jin dad'in yadda yaga damuwa Atare da ummu yanzun"da wannan tunanin suka iso gida"kamal ya kalli sa'ada yace"ki kwashe kayan ki kai ciki"gobe zanzo na maida mata warmers d'in"tamkar big man yayi mgn sai kuma yafasa sbd ya lura haushinsa kamal keji"fitowa dg cikin motar yayi hakan yayi daidai da kiran Ammi ya shigo wayarsa"Amsar key d'in motar wajen driver yayi batare da yabi takan kamal ko sa'ada ba ya wuce yana bin kiran Ammin......
Ummu na komawa ciki ta samu waje ta lab'e tasha kukanta"saida taji zuciyarta tayi sanyi sannan ta koma parlourn ta d'akko ruwa swan ta wanke fuskarta"saidai ta fauwalawa Allah lamarinta"sbd tasan jinkirin Aurenta da wanda kuma zata Aura d'in da irin Auren da zasuyi! duk k'addarartace tazo mata A hakan"kawai zata dage da Addu'ar Allah ya azata samqn wannan me girman kan"da wannan tunanin ta wuce babban parlourn gidan"umma da goggo murja da Anty Aysha da lawisa suna zaune tsakkiyar parlourn suna kallon kayan lefen"kowanansu bakinsa washe da fara'a"ummu na shigowa lawisa tayi Ihu ta taso ta rungumeta tana fad'in masha Allah k'awata! kinyi goshi wlh"harda gwalagwalai da key d'in mota"super kala 50"laces kala....dan Allah ya isa lausy nidai basai kin fad'amun ba kizo muje ki rakani gida"ah ah bbu inda zakije kizo ki duba kayan a fidda kala 12 Akai wajen d'inki"tunda kinga wuri ya k'ure"cewar goggo murja"ummu batayi mgn ba ta zauna k'asa kan carpet tana kallon kayan bata tab'a ba"komai classic ne Aciki"bbu lace d'in 40k daga na 50k sai Abinda yayi sama"kaya kala 100 ne sai English wears da dubai Abayas da kayan k'asar turkish kala 50"takalmi da jaka dozin biyune gyalema haka"saidai bbu hijab sai inner wears da kayan bacci dana shafa dana kwalliya"sai sark'oki da y'an hannu da zobba da Agoguna"gwala gwalan kuwa fiddasu akayi daban"itadai ummu tana kallo lawisa nata d'agawa"bayan sun gama gani lawisa ta fidda mata kala 12 da zata kai d'inki"wanda ummu bata soba"sbd Aganinta ta Amshi lefensa bayan ba Auren dindin bane"kuma bbu Abinda zai shiga tsakaninsu idan Anyi Auren"idan yace ta biyashi fa?"ta tambayi kanta lokacin da goggo murja ke cewa nan za'a barshi kowa gobe yazo yagani"dangi da Abokan Arzik'i kowa sai yazo yagani"bazamu kai kayan can ba Aje Asace sbd nasan wacece kakarta da kishiyar mamanta"umma tace"to shikenan sai Ayi hakan"ummu batace komaiba ta tashi suka koma d'akin lawisa"ita ta kwanta gefen bed tana tunani sbd ba sallah take ba"ita kuwa sallar magrib tayi"bayan ta ida ta kalleta tace"ki kira telan naki yazo da dare ya Amsa ko?"wai lawisa manta kalar Auren da zamuyi kikayi?"taya zqn tab'a masa lefe bayan kinsan AUREN YARJEJENIYA ne?"idan naje gidansa yace na biyashifa?"kinsan dai banida halin biyansa Abinda na tab'a ko?"d'an murmushi lawisa tayi ta mik'e tsaye ta dawo gefen bed d'in ta zauna tana fad'in"dama na lura kinada damuwa"to bari kiji wata mgn"muddin kikayi saken da wannan Auren yarabu kin tabbata wawiya ummu"ko bakiso big man sbd dukiyar saba zakiso sbd kyawunsa da kasancewar na daban Acikin maza"musammun daya kasance be kula mata"wanda da wuya kisamu namiji da irin wannan halin awannan zamanin....kin sanfa halinsa lausy wace irin mgn ce kikeyi haka?"bazan iya rayuwa da wanda baya sona ba yana kuma wulak'antani"hmm! ki kasance me d'aukar shawara k'awata"Ahankali Ahankali wlh zaki janye hankalin Abdallah bbu boka bbu mlm"kiyi hak'uri ki shanye komai saiya kamu sannan kijashi k'asa ki nuna masa cewa mata suna suka tara"kuma kowace da irin baiwarta da darajarta"ina fatan kin fahimta?"ba wai ina nuna miki k'i shige masa ba"ah ah shi yak'i d'an siyasane sannu a hankali zaku saba"inaso Ace idan kunyi Auren harma girki kece zaki masa"banaso idan kin shiga gidan ki masa rashin kunya ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login