Showing 27001 words to 30000 words out of 93107 words

Chapter 10 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete

masa musu"no bishi da yadda yakeso ki kuma yi k'ok'arin kyautata masa shida mahaifiyarsa da k'anwar sa"dan yanzun haka umma sunyi bincike mamansa ta fita dg gidansu"matar babansa itace sila kuma big man baya shiri da ita"Abinda yaka mata kiyi kijawo sa'ada Ajiki ki kuma nisanci matar babansa"musammun tunda Ance gidansu zaku fara zama"kiyi hak'uri kiyi Addu'a insha Allah sai kinyi farin ciki da wannan Auren wata rana k'awata"ina jin hakan sosai Ajikina"saidai karki sake ki nuna fara'a garesa ko shishshige masa ko cusa kai"ah ah kema ki nuna da ajinki"ina zaune zanji labarin yasoke AUREN YARJEJENIYA insha Allah"su mabashshir sai kuma Akama wani sarkin"ta k'are maganar tana dariya"ummu tasaki Ajiyar zuciya domin ta gamsu da shawarwarin Aminiyar tata"bbu b'ata lokaci takira telanta Anan ma gidansu lawisan yazo yasameta ya Amshi kayan...."saidai Abin mamaki hjy yaya da goggo luba da Asiya kasa hak'urin gari yawaye suzo ganin kayan sukayi"Acikin daren sukazo suka gani"hjy yaya ta nuna kayama gidanta za'a kaisu sai bayan bikin Akaima ummu"saidai baba yatake mata burki"goggo luba kuwa A daren ranar batayi bacci ba sbd bak'in ciki da hassadar ganin dukiyar da'aka mallakawa ummu....

Ayau friday take dinner"tun wajen k'arfe 4 Aka gama wankema Amarya lalle ja da bak'i da yayi wani irin fitinan nan kyau"kowa yaba tsaruwar lallen yakeyi"tana gama wanka suka tafi wajen make up"sai 6 pm suka dawo gida"wanda dama da kayanta ta tafi ta shirya Acan"duk wanda bema ummu farin sani ba da wuya yaganeta"sbd yanda tayi wani irin mugun kyau"make up yayi kuma an nad'a mata d'aurin d'an kwalin yadda ya kamata"material ne me k'yalk'yali white me zanen silver tasaka"d'inkin fited gownt"takalmi da post da net d'in data yafa dg baya duk silver ne"haka y'an kunne da sark'a da Agogo ful silver ne"ga wani irin fitinan nan k'amshi me dad'i dake tashi Ajikinta"itama lawisa ta shirya cikin sabon material maroon colour tasha make up"itada nura ne da zata Aura a front sit sbd shine yakaisu wajen make up d'in kuma yakoma ya d'akko su"da k'yar sukayi parking dg farko farkon shigowa layin" sbd duk wajen yacika da maka makan motoci na Alfarma"lawisa ta juyo ta kalli ummu dake danna waya tace"k'awata ba 7 pm kamal d'in yace za'a tafiba?"Amma naga tun 6 waje yacika da motoci"Eh nima nayi mamaki" okay Amma muje ciki muga friends d'in mu sun fara taruwa ne"dato ummu ta Amsa ta bud'e k'ofar Ahankali ta fito"duk ga maza nan Abokan big man da y'an ganin k'wam"tj da junuid suka kafe ummu da ido suna ganin Abdallah yadace da samun kyakykyawar mace"ita kuwa batama lura dasuba"lawisa na rik'e da hannunta suka tura get d'in gidan su lawisa d'in suka shiga"wanda hakan yayi daidai da motar sadeeq tayi parking Awajen"ya d'akko k'anwarsa leemart da sa'ada"sbd leemart tace"sun had'u da kamal Acan"dan tasan shida Ango zasu tafi"tasan kuma big man bbu wasa... sa'ada tasha gayunta cikin farin leshi iri d'aya itada leemart"ga make up An musu suka fito rik'e da hannun juna itada leemart"sadeeq na rik'e da hand bag d'in sa'ada yasaka mata kud'in lik'i a ciki sannan ya mik'a mata"ta Amsa batare datasan meya saka ciki ba"itada leemart suka shige gidansu lawisa"sadeeq kuwa ya zauna samqn motar sa yana danna waya"tj dake kallon komai yatab'o junuid yana tab'e baki yace"ina gafa wancan yaron kamar kamun sa'ada yakeyi"ta yaya ka gane?"irin yadda yake shige mata da irin kallon dayake mata"kuma wlh ni sonta nakeyi"nan gaba kad'an idan ta k'ara girma nakeso na nuna"kasan na Auri k'anwar big man Aina warke"kallon bakada hankali junuid yajefasa dashi yana fad'in ka manta waye Abdallah wlh?"ko nayi rantsuwa bazanyi kaffaraba bazai tab'a bari ka Auretaba"kasan ikon Allah?"shiru junuid yayi yana kallon wasu y'an mata da zasu wuce yace"Ango dai shiru be isoba har yanzun"k'ilan yana hanya ko?may be.....
Ango kuwa suna can suna rigima da kamal Akan yakafe bazai zoba"ko Inda za'a yi dinner d'in da Abinda za'a ci duk kamal ne ya d'auki nauyi"kamal kuwa ransa yab'aci matuk'a yasanar masa kuma muddin bejeba bbu shi bbu shi har Abada tunda be isa dashi ba"yayi tafiyarsa yabarsa part nasa"badan yasoba yafara shiri"bayan yagama yaturama kamal text yazo ya d'aukesa ya shirya"shima text ya turo masa yasamesa dg wajen get d'in gidansu"dan dama bayan yabar part d'in Abdallah be tafiba ya zauna cikin mota"dan yatabbatar da cewa da gaske Abdallah d'in bazai jeba"cikin izzah had'e da shan k'amshi yafito wajen"bayan ya disga body guards nasa Akan karsu biyosa"sanye yake da suit farare k'al sabbi"kuma manyan ne da ak'allah kud'insu zasuyi 500k "Agogo da takalmi na fata duk farare yasaka sai zabban Azurfa guda 2 dake sanye Agudan yatsun hannunsa"sumar kansa tsabar gyaran datake sha har walk'iya takeyi"ya had'e rai bbu Alamar Annuri samqn choko face nasa"saidai yyi kyau har yagaji"kamal dai yatab'e baki ya zuro hannunsa yabud'e masa back sit tunda Anan ummu itama zata zauna idan sunje d'aukarta yanzun"kasancewar Abdallah cikin haushi yake bema tsaya tambayar ma'anar shigarsa back sit ba kawai sai ya shiga ya zauna"bbu me mgn Acikinsu suna dai tafiya"kamar Ammasa tilas yace"ina zamuje?"gidansu Amarya"kana nufin sai munje d'akko wannan kucakar?"girgiza kansa kamal yayi yace"kana bani mamaki Abdallah"be halattaba cin fuskar musulmi da wulak'antashi da bashi tsoro batare da hakk'in shariah ba"karka manta itama bata sonka da wanda takeso Allah ne yawanzo wannan kaddarar tsakaninku"meyasa ka kasa ka manta sab'anin daya faru tsakaninku da ummu ?"wanda kai hukuncin daka d'auka yafi nata"ita marinka tayi"kai kuwa jini ka fidda mata"kasaka tayi jinya bayan ta zubar da hawaye"idan har kasan zaka wulak'antata meyasa zaka nunawa duniya kana sonta kana son Auren??"to bari kaji Akwai friends namu da kuma Abokan kasuwancinka da sukazo har dg kasashen waje sbd suje gun dinner Akuma d'aura aure dasu"yanzun haka duk na kaisu masauki"idan kasaki wata b'araka kaine zakaji kunya"ka kuma san jajayen fata suna matuk'ar bama soyayya daraja da mahinmanci Arayuwarsu"suna kuma girmama matansu"idan kaji shawarata fine idan bakajina ma fine"nidai Abinda nasani ina tare dakai tsakanina da Allah tun muna yara"sau tari idan yakama nayi badaidai har hjy (mahaifiyarsa) tana kiranka ta sanar maka"ka kuma bani shawara koka tursasani nayi Abinda banaso sbd ka isa"Amma ni ka nunamun ban isaba"kafison kabi shawaran su junuid da badan Allah suke tare dakai ba"dg k'arshe kaji tsoron Allah karka cutar da yarinyar mutane ku zauna lafiya har kurabu lafiya....shikenan! iya Abinda Abdallah yafad'a kenan sbd yaga Abinda yayiwa kamal be kyautaba"kamal kuwa parking yayi dg bayan wasu motoci Alayin gidansu lawisa"y'an mata nata fitowa anata jidarsu cikin motoci"wayarsa yazaro yakira leemart"bugu 3 ta d'auka"sweet heart kuna kusa da Amarya?"dg d'ayan b'angaren leemart ta Amsa da Eh"okay kice nace ta fito mu wuce lokaci na tafiya"kema ku fito Atare"dato ta Amsa ya yanke wayar"yajuyo suka had'a ido da Abdallah"harara Abdallah yasakar masa"yayi murmushi yana fad'in baka tab'a yin kyau kamar na yau ba"lallai Aure rahama ne"be kulasaba ya bud'e k'ofar motar yafito"duk wasu sauran matan da mazan kallon big man dake tsaye gefen motar yana Amsa waya sukeyi"Anata cewa ga Angon can"Adaidai lokacin kuma security mota guda suka iso sbd suyiwa couples d'in rakkiya.....lawisa ce Agaba tana rik'e da hannun ummu"sai sa'ada data rik'e gefen rigar ummu dake jan k'asa"sai leemart ne gefensu"da sauran friends nasu na biye dasu"masha Allah!! masha Allah!!! Abinda kamal yafad'a kenan yana satar kallon Abdallah yaga yaya zaiyi idan yaga wannan kyakykyawar Amarya tasa?"danshi inba daya gansu sun fito da itaba bazai gane taba Inda ita kad'ai yaganta"mutumin gata nan fa Anfito da ita"yafad'a yana kallon big man"tab'e baki yayi yad'ago kansa"cikin second 10 yak'arema ummu kallo"Aransa yace"she is beautiful!"d'an sakin fuska yayi tun kafin su k'araso yanufesu cikin tafiyarsa ta kasaita"su tj da wasu samari suka saki Ihu"wasu y'an matan na bud'a"ummu kuwa gabanta ne keta fad'uwa"tunda ta hango big man"gashi yamata wani irin shegen kyau Ayau...wani irin harbawa zuciyarta tayi dataji mayataccen k'amshin turarensa"da sauri ta d'ago kanta"befi tak'i biyu ba ya iso gefen ta"sa'ada tayi murmushi tana fad'in sweet heart baka jiran mu rakota?"Amamakin ummu sai taji Abdallah yace"No baby gara dai nazo na Amshi kayata nagaji da jira"yak'are maganar yana tsayawa gaban ummu"duk y'an matan nata kallonsa kamar tv" suna matuk'ar mamakin wanda ummu zata Aura"lawisa na murmushi ta cika hannunta ta matsa gefe"Aikuwa yakama hannun nata guda ya d'an duk'o saitin kunnanta na gefen dama murya can k'asa yace"bakiyi kyau ba....rintse ido ummu tayi tana saka hannunta guda da nufin ta ture masa fuska yarik'e hannun yana sakin murmushin mugunta" da hanzari Aka fara d'aukarsu pics"wanda kowa d'aukar masoya masu matuk'ar son junansu ake musu"shidai kamal nata smiling yana musu photo da wayarsa iphone"Abdallah kuwa cikin mugunta yayi k'asa da hannun nata yana murd'e mata shi"gashi yayi tsaye gabanta jikinsu na gugar juna...yaya muje kushiga mota mana"cewar sa'ada"big man beyi mgn ba ya rik'e hannun ummu suka fara tafiya"ana biye dasu bbu me mgn Acikinsu"kamal yayi hanzarin bud'e musu back sit yana fad'in ranki yadad'e barka da isowa"batayi mgn ba ta daiyi murmushi"itace tafara shiga sannan Abdallah yashiga"leemart ta zauna gefen kamal sannan yatashi motar"yayinda sa'ada na cikin motar sadeeq....tunda suka shiga motar ummu ta takure jikinta Awaje guda ta matsa can nesa"shima bebi takantaba sbd ganin basu kad'ai bane Acikin motar"bbu me mgn sai kamal dakema leemart surutu"tsoron ganin Abdallah yasaka ta kasa Amsawa"yayinda Abdallah keta Amsa wayoyin jama'a dake jiran isowarsu wajen dinner d'in"ba k'aramin mamakin ganin wajen cike da mutane Abdallah yayi ba"motoci gasu nan basu k"irguwa....ku zama on ready danayi muku knocking saiku fito"cewar kamal yana fita dg cikin motar shida leemart"sai sannan Abdallah yasaci kallonta yace"sannu Amarya kinji?"ya mutsa fuska tayi tace"niba Amarya bace sbd kafi kowa sanin irin Auren da zanyi"nan gaba kad'an dai zan zama Amaryar"dan Allah?"shiru tayi tak'i mgn"yaja tsaki yana fad'in duk ki Adana wannan tsiwar taki gaba kad'an zata miki Amfani"Akwai friends nawa da sukazo har daga k'asashen waje dole idan Angama dinner ku gaisa ki musu godiyar Attending d'in bikin ki da sukayi"saidai da harshen turanci zakiyi musu mgn"idan kinsan baki iyaba garama ki sanar mun karki bani kunya gaban mutane.....ummu na k'ok'arin mgn kamal yamusu knocking"hakan yasa batace komaiba ta bud'e k'ofar dake side d'in datake zaune ta fito"jerawa sukayi"Abdallah yasak'alo hannunsa gefen k'ugunta ya rungumota"subahanallahi! gaskiya bazan iyaba"mlm ka cikani kasan dai bbu k.....K! wlh ki kama kanki"An fad'a miki nima Ason raina na miki hakane?"da zakice mun bbu kyau"wato ga wanda be san Addini bako??"matsalata dake kanan gidadanci da k'auyanci"yafad'a cikin b'acin rai"saidai Ahankali yake maganar"nidai bafa haka nake nufi ba"tsaki yaja bece komaiba"hakan yayi daidai da isowar friends nasa dasu sa'ada da dangin Ammi dasu Anty wasilah"Adole big man yak'ak'aro fara'ar dole"itama ummu tana d'an smile"saidai gaba d'aya wani iri takeji Ajikinta sbd irin yadda suka shigema juna"dan ita bata tab'a barin ko hannunta wani namiji ya rik'e ba"flowers ne da turaruka aka dinga watso musu"wasu kuma na musu lik'i na y'an 1k har suka shiga cikin hall d'in"sai k'arar kid'an music ke tashi"ga cake Ajiye gefe dazasu yanka"bayan sun zauna sannan mutane suka cigaba da shigowa suna zama"sai pics da vedio ake musu"preety na zaune gefe tana kallon komai kamar ta kurma Ihu haka ta dingaji"lokacin da MC yafara magana tayi sauri ta tashi ta fita"kamal yafito yabada tarihin Ango da k'arshen turanci"hakama lawisa"bayan Angama Aka buk'aci couples su fito su yanka cake"cikin nutsuwa suka taso"yana rik'e da hannun ta guda"kamar Ance ummu ta kalli gefen damarta"saiga goggo luba da Asiya da mariya zaune kan kujeru sunata kallonsu"Aranta tace"da Azo Abasu labari gara suzo su gani kenan"da gangan ta zame k'afarta kamar zata fad'i"tasaki k'aramar k'ara"da hanzari Abdallah ya fisgo hannun ta dake cikin nasa ta fad'o Ajikinsa ya rungumeta"Aka saki tafi"Adaidai saitin kunnansa ummu ta sakar masa zazzafan mintsini"yaja kwafa murya can k'asa yace"gobe idan Ance kimun haka wlh da lada baza kiyiba"danma kin samu na taimaka miki"Aida na bari kinsha k'asa"yak'are maganar yana janyeta dg jikinsa"wanda duk Abinda yafaru kan idon mutane"Aminu da umar kuwa sunji dad'in ganin hakan domin suna ganin Abdallah na matuk'ar son yayarsu....
cikin nutsuwa suka iso gaban Inda cake d'in yake" Abdallah ya d'auki y'ar wuk'ar ya'aza hannunsa"itama ummu ta Aza nata suka yanka"Aka hau musu tafi"shine yafara bata cikin mugunta"sannan dazata bashi ya ciji yatsanta manununiya"kamar tayi Ihu tadai d'aure"bayan sun gama yankawa"suka nufi filin rawa"Abdallah beyiba itama haka sunadai tsaye ya rik'e hannun ta mutane sun rufu Anata musu lik'i harda doulers"sun jima Aciki filin rawar sannan suka koma suka zauna"akya fara service d'in Abinci"wanda layi Ake bi komai mutum keso ya d'auki plate yakai Azuba masa"ummu data hango yanda goggo luba da zuri'arta ke cin Abincin saida taji kamar tayi kuka sbd kunya"fans d'in AUREN YARJEJENIYA kuwa suna dg zaune Aka kamusu komai.....bayan Angama ciye ciye aka fara pics wanda Abdallah besoba"da haka taro yatashi lafiya"kowa na kallon Abdallah da ummu Amatsayin masoya"sai bayan ta gaisa da turawan da sukazo sannan suka shige mota"duk yadda Abdallah yaso yatak'aleta da suyi fad'a kin biye masa tayi"kamal nagama parking ko sallama bata masa ba tayi wuf ta bud'e k'ofar ta fice"Abdallah yatab'e baki bece komaiba"sbd leemart na zaune gefen kamal"shima kamal beyi mgn ba yaja motar sukayi gaba"ummu kuwa cikin gidansu lawisa ta wuce sbd Acan zata kwana.....

Washe gari✍️

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯ *AUREN YARJEJENIYA* ❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯

*23&24*


........washe gari misalin k'arfe 12:00 pm dubban jama'a suka shaida gagarumin d'aurin Auren *Abdallah mohd jibo & ummulkhairy rufa'i* Akan sadaki naira dubu d'ari biyar"d'aurin Auren da Aka d'aura Ababban masallacin Anguwar tudun wada"wanda bbu masaka tsinke sbd taruwar jama'a"Ango na gefen Amininsa yaci wankan shadda sky blue da Akayima Aiki da blue d'in zare! Hmm big man saima yafi kyau Akayanmu na hausawa"y'an jarida nata k'ok'arin yimasa tambayoyi yabasar"marok'a nata wasashi da masa kirari"saidai kawai yaji kamal yace"yabaka kyautar mashin ,yabaka kyautar dubu kaza"kusan Akan mutum 5 yana yin haka"can Abdallah ya ballah masa harara yana fad'in malam duk wanda kakoma yima kyauta da sunan injini kaine zaka biyasa wlh"dariya kamal yadin gayi"yayinda daddy bakinsa yak'i rufuwa sbd farin cikin d'aura Auren Abdallah"manyan mutane nata yimasa Allah yasa Alkhairi"Anyi pics shida Abokansa dasu daddy sannan suka nufi wajen reception"Acikin gidan daddy kuma umma balki ta shirya taron yini"wanda Aranta bak'in cikin Auren takeyi"Amma sbd tayi suna wajen daddy da danginsa saita nuna son Auren takeyi tanata hidima"daddy kuwa yabata manyan kud'ad'e sbd Aci Asha kowa yaji dad'i"saida ta wafci Abinda ta gadama sannan tayi Amfani da sauran kud'in...part d'in Amarya Aljannar duniya"dg bayan gidan Aka gina musu b'angaren su kuma harda get"fad'in tsaruwarsa b'ata bakine"dan yafi cikin gidan kyau da tsari da komai"daka shigo main parlour"gefen upstairs dining area ne"daga gefe kuma kitchen ne"sai gefen dama d'akunan bacci biyu ne kowane da toilet Aciki"parlourn ma Akwai toilet"sai up stairs Anan parlourn Abdallah da bed room d'insa yake"komai na cikin gidan coffee brown ne"gaba d'aya komai dg waje aka kawosa"d'aki guda ne kawai Aka shiryawa ummu dg gidansu"sai kayan kitchen"dama kuma Abdallah be kaiga zuba kayan kitchen d'in ba"saida Akayi jere shekaran jiya yagani"hakan yasa yafasa"gudan d'akin kuma kayan dubai ne had'add'u masu masifar tsada"Abin saidai wanda yagani"Ana gama reception Abdallah ya sallami friends nasa"turawan kuwa sai gobe zasu tafi"silalewa yayi kamal be koma sanin Inda yakeba.... sa'ada kuwa tana gidan Ammi itada leemart sbd Ammin itama taro takeyi"
Ab'angaren Amarya ummu kuwa tun wajen 11 am me make up datazo har nan gida ta tsantsara mata kwalliya ta musammun"bayan ta gama mata"ta shirya cikin shadda giznah light pink"An mata Aiki da blue d'in zare"sosai ta fito Amaryarta"uwar Amarya ma ta shirya cikin sabon leshi"gidan cike yake da bak'i y'an me duguri da kuma dangin mahaifin ummu"sai k'awayen ummu"tun wajen k'arfe 12 k'irjinta ke bugawa har su babah suka shigo da me photo"Aka kama bud'a hakan ya tabbatar ma da ummu cewa ta zama matar Abdallah"sosai gabanta ke fad'uwa tana jin kamar tayi kuka"haka dai ta daure Akayi musu photo da mutane"goggo luba ta dai tursasa kanta tayi wanka ta shirya Amma bata shiga photo ba"kuma bata shiga cikin sabgar komi"mama kuwa bata damu ba"dan tamafi buk'atar hakan"saidai komai da aka dafa na biki An d'iba An bata"dan mama bata jiran baba"kusan dubu d'ari biyar danginta suka had'a mata"babah kuwa da k'yar yabada dubu d'ari biyu sbd bedashi"sune Aka had'a da kud'in sadaki dana neman Aure Aketa hidimar komai"sai wajen k'arfe 3 ummu ta canza kaya zuwa leshi"kuma Alokacin kowa yasaka Anko"Amma banda goggo luba da zuri'arta"burunta Afara zancen kai Amarya sbd tabi taga gidan dan Akwai y'an binne binne da boka yabata tayi Agidan Amarya"wai Auren bazai jimaba za'a sakota kamar yadda Aka sako Asiya"hidima tayi domin komai Anyishi waja waja"sbd naira dubu d'ari biyar kamal yabama lawisa su sayi komai na buk'ata da zasu bama mutanansu"wanda Asali million guda yabada ummu tace"sunyi yawa dubu d'ari biyar yayi"wanda hakan ya tabbatar ma kamal batada son Abin duniya"Inda watace Amsa zatayi ko tace Ak'ara tunda tasan Abdallah nada kud'i.....
Bayan sallar magrib motocin d'aukar Amarya suka iso k'ofar gidan su lawisa sbd Acan da marece Akaje da ummu Aka shiryata cikin lifaya green"sai k'amshi takeyi"taci uban kuka kamar ranta zai fita"goggo murja da umman lawisa da yayar babanta sune rik'e da ita suka sakata cikin motar da Aka nuna itace Amarya zata shiga"bayan ta shiga suma suka shiga suka sakata tsakkiya"yayinda lawisa ta zauna gefen me zaman banza"kamal ya shigo driver sit ya gaida manyan yaja motar yana jin yanda ummu ke shashshekar kuka.... Aransa kuma yana tunanin ina big man yashige wayoyinsa duk Akashe? kuma ba'asan ina yajeba"da wannan tunanin suka iso katafaren gidan Alh mohd jibo"gaban ummu ya tsananta fad'uwa"duk Addu'ar data zo mata Abaki yi takeyi"sai bayan mutane sun fara shiga ciki sannan Aka fito da ita"saida Aka tabbatar tayi Addu'o in daya kamata sannan ta shiga da k'afar dama cikin gidan"kai tsaye babban parlourn gidan suka nufa"Anan ne masu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login