Showing 15001 words to 18000 words out of 93107 words

Chapter 6 - Auren Yarjejeniya Book 1 Hausa Novel Complete

bin umarnin mahaifina"idan An kwana biyu lokacin mommy tasami lafiya kin Ida karatunki zan saketa muyi Aure"Amma baby....Amma what? na riga na gama mgn"itama tanada wanda takeso"and last one kinsan bansan surutu da k'ananun mgn ko?"hakane"is good"banaso ki sanarwa kowa komai kina jina?"muddin naji labarin nan wani waje zan iya fasa Auren ki"be jira Amsar taba yashiga mota batare daya koma kallontaba"ta tab'e baki ta nufi motarta itama ta shiga tabar wajen.....
shiru Abdallah yayi yana tunani yasan dai dole ta Amince dan wannan shine mafita"zuwa sadda zata nemesa sannan sati gudan ya Ida cika saiya sanarwa daddy ya fidda"can kuma yasaki murmushi sbd tunawa da yayi da irin uk'ubar daya tanada dazai mata sbd rashin kunyar datake masa"zai sakata ta masa ladabi kotaso ko kar taso....da wannan tunanin suka iso gida"bayan ya fito dg cikin motar "Aharaban gidan ya hango sadeeq da sa'ada suna karatu"d'auke kansa yayi yacigaba da tafiya cikin nutsuwa"fuskarsa Ad'aure kamar koda yaushe yashigo cikin parlourn"Amamakin sa ya sami hafsat da wani saurayi zaune suna fira"yashige mata sosai...yatsina fuska big man yayi"yaya Abdallah sannu da zuwa"ta fad'a cikin fad'uwar gaba"be Amsaba yatsaya cak! yana binsu da wani irin shegen kallo yace"waye wannan??"Amm....dama d'an uwanmu ne"tsaki yaja ya kalli saurayin yana fad'in get out"duk ranar daka koma shigowa zaka san ka shigo da hujjja"ya fad'a yana jan tsaki"saurayin jikinsa har kirma yakeyi dan sosai yaji shakkar Abdallah" ya mik'e tsaye zai fita"yayinda kan hafsat ke Ak'asa"umma balki ta fito dg cikin kitchen da warmers Ahannunta"da sauri ta dubi sayyeed ta kuma dubi Abdallah dake tsaye yana danna waya yayi bala'in had'e rai"wai tafiya zakayine sayyeed?"Eh hjy zan wuce sai Anjima"be jira cewar taba yafita dukda tana kiransa....bazai koma dawowa ba sbd na hanashi zuwa"nan gidan matan Aure ne"be kamata baligi kamarsa yana shigowa yana shigewa wannan Abarba"ya fad'a yana nuna hafsat"yana kai Aya Azancen yatafi cikin izzah "umma balki tabishi da mugun kallon tsana domin tasan mgn cikin mgn yagaya mata sbd Abinda tayima sadeeq jiya"kuma tunda taji daddy beyi mata zancen Abdallah be fidda wacce yakeso ba"tasan tabbas ya fitar"saidai tasha Alwashin kota halin k'ak'a sai taga bayansa ta mallake komai na gidan"taja wata iriyar kwafa ta nufi dining Area"ita kanta hafsat bataso korarsa da yayiba"sbd tanaso tasamu ta Auri sayyeed d'in d'an k'awar umma balki ne.....
kwance Abdallah yake samqn katafaren royel bed nasa"ya lumshe sexy eyes nasa"yana shafa gashin dake kwance samqn faffad'an k'irjinsa"yana d'aure da towel"tunanin Abinda zaiyiwa wannan cakuri cicin cikon benci yakeyi idan ta shigo gidansa"dukda yana tunanin bazaima kaita gidansa daya gama ginawa last 6month ba"saidai yakaita wani gidan Acikin gidajensa"bud'e lumsassun idanuwansa yayi sbd jin wayarsa na ringing"yatab'e baki sbd ganin kamal ne"d'auka yayi yak'i mgn"hmm! dama su hjy ne zasuyi order d'in kayan Auren wata"inaso na shigo da dare muyi mgn"okay Allah yakaimu"dg haka Abdallah ya yanke wayar"yatashi tsaye yanufi bath room....
da misalin k'arfe 8: 45 pm"big man ne da kamal tsaye A haraban gidan bayan sun gama mgn game da kayan da sukayi waya kansu d'azun"kamal ya kalli big man cikin marairaice murya yace"pls ka rakani gidansu my leemart" inaso na ganta sbd nayi bacci cikin nutsuwa....kallon bakada hankali big man yajefasa dashi kafin yace"mudena y'ar haka dakai"karma kaja yarinya ta rainani wlh"wannan zubda girman badaniba"kaida kaji zaka iya sai kayi tayi"kamal yatab'e baki yace"kaji dashi wlh"yanzun dai ka hak'ura da takalar ummulkhairy ko?"yatsina fuska yayi yace"wace haka?"kafini sani"tamace Agaidaka Ai"wani kallo Abdallah yamasa yana tab'e baki yace"banfi 6 hours da rabuwa da itaba"kadena k'arya"dan nasan wannan matsiwaciyar baza tace Agaidani ba"hmm ! kaidai kasani wato har yanzun kana shiga harkanta kenan?"meza'a fasa?"Ai ba yanzun zatayi kukan sanina ba Arayuwa sai nan gaba idan na Aureta"ta hakane kawai zan takata na jata k'asa yadda naga dama"yak'are maganar yana d'age kafad'a irin ko'a jikinsa d'in nan"kamal ya dubesa cikin mamaki yace"mekake nufi Abdallah?"kodai soyayyar k'arya ka k'ullah da itane?"banza yamasa yana danna waya"saida yagama shan k'amshin sa kafin yace"AURE zamuyi da ita Amma na YARJEJENIYA"what?"kasan mekake fad'a kuwa?"kaga dan Allah karka kamun matsala mana"kanata wani zaro ido da razana sai kace wani Abun furgici ne yafaru"jiya daka tsaya ka saurareni dana sanar maka Abinda daddy yafadamun"kaji tsoron Allah Abdallah! dan Allah kasanar mun gaskiyar meke faruwa?"bazan fad'a ba saida safe... rik'e gefen jallabiyarsa kamal yayi yana fad'in wlh saika fad'amun kaji na rantse"shikenan bazan fad'a ba kaje kayi kaffarah"haba Abokina pls ka sanarmun sbd soyayyar da kakema preety"had'e rai Abdallah yayi yaja tsaki yana fad'in na rasa wane irin mahinmanci kabama soyayya Arayuwarka kamal??"cikani na fad'a maka"dan Allah karka tafi"idan tafiya zanyi bana jin komai nace maka tafiyar zanyi"yak'are maganar yana fara yiwa kamal bayanin komai....dg k'arshe yace"taimakonta nayi Akan Amata Auren dole kuma bbu zancen rabuwa da wanda zata Aura"Amma ni idan nagama saitata zan saketa"haba big man! da iliminka da komai zaka Aikata haka?"babufa kyau irin wannan Auren"sannan karka tursasa y'ar mutane idan bataso kabarta mana.....babu wannan zancen dole ta Amince!kuma na tsara wannan Auren ne da ita sbd na takata yadda na gadama"idan na sai tata na koya mata yadda Ake iya mgn da manya saina saketa"saidai inaso kasani muddin kasanarwa Ammi wlh sainayi sanadin daka rasa leemart har Abada kuwa"wani murmushi me ma'anoni da yawa kamal yasaki yana fad'in bazan sanar mata ba huta rantsuwa"saidai inaso kasani ba'asan Inda rana ke fad'uwa ba"kuma bbu wanda yasan me gobe zata haifar?" Amma idan harta Amince bazaka kwanta da itaba idan Anyi Auren ko?"yatsina fuska big man yayi yana fad'in gaskiya ka cuceni" Allah ya isa dakayi wannan banzan tunanin"ni banga Abinda zan kwanta Ajikin taba?"Allah ko?"to shikenan Allah yakaimu bakwai"Aikai dutsene ko?"banza Abdallah yamasa yana tunani"dan shifa yama manta da Ana yin wani sex idan Anyi Aure sai yanzun yatuna"shifa be tab'a zama yaji yana jin sha'awar mace ba"saidai kawai duk sadda yayi mafarki yayi wanka"shi kansa har yana zargin kodai bashida lafiya ne??harka fara tunaninta tun kafin tazo?"wani wawan punch big man yakai masa"ya goce yana dariya yayi gaba"shi kuma yatab'e baki ya wuce ciki.....

*bayan kwana2*✍️


wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤‍🔥❤‍🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤‍🔥❤‍🔥

*13&14*


*Bayan kwana biyu*

kwana 2 kenan da zartar da mafitar da Abdallah ya yanke musu"wanda yayi daidai da saura kwana 1 wa'adin kwanakin da baba yabama ummu su cika"to Alhmdllh ummu tun jiya ta sanarwa mama ta fidda miji"ta nuna mata dama sun jima da Abdallah suna son juna sai yanzun data masa zancen zata fidda wanda takeso yace"shine zai turo"da farko mama tace"ah ah"Amma da Aminu da ummu da suka mata bayanin babu matsala ta Amince"saidai mama dataji wai Abdallah mohd jibo ne tayi mamaki dg ita har Aminun"sannan kuma Ajiyan taje har wajen ummar lawisa sukayi mgn game da Abdallah da kuma Abban lawisa yabinciki halayensa kafin su sanar da baba wata fidda"to Alhmdllh yau da safe umma da mama sukayi waya bbu wata matsala Abinciken da Abba yayi "cikin gidan kuwa goggo luba tama gama yadda ummu babu wanda zata fitar"tasha kuma Alwashin bazata tab'a bari tayi Auren hutu ba....ummu kuwa har ranta hankalinta yak'i kwanciya da wannan Auren"badan tasoba tadai Amince"tun safe takeso ta kira Abdallah tasanar masa ta Amince Amma tana jin shakku....misalin k'arfe 5:35 pm"ummu na zaune kan kujera A parlourn su tana chats"mariya ta shigo parlourn bbu ko sallama tace"Anty ummu baba yace"kizo"saida gabanta yafad'i ta kalleta tace"jeki gani nan"mama dake d'aki ta fito ta kalleta tana fad'in kije kisanar masa kin fidda"nasan dai be wuce zancen ne zai miki"in sha Allah ubangiji bazai tab'a bari mu tozartaba"ummu batayi mgn ba ta d'auki mayafin doguwar rigar dake jikinta ta yafa ta fito ta shiga d'akin baba"goggo luba dake zaune tsakar gidan ta bita da kallo harta b'acewa ganinta...da sallama ta shigo cikin d'akin ta duk'a k'asa ta gaishesa"be Amsaba sai tambayar daya jefo mata gun cewa" kin fitar ko baki fitar ba? na fitar baba Amma sai zuwa nanda kwana 3 zai turo"bbu matsala har zuwa sati ma"dan bana gaggawa sbd Aikin shed'an ne"saidai muddin sati yacika zuwa kwana 10 be turoba zakiji hukuncin dana yanke"batace komaiba tayi shiru"ki tashi ki bani waje"sosai ranta yasosu"ta rasa meta kashewa mahaifinsu Aduniya dayake nuna mata tsana da tsangwama?? ta tashi ta fito dg cikin d'akin"yanayin yadda goggo luba ta lura da fuskarta bbu walwala sai tayi zaton bata fidda mijin ba"sosai ranta yayi fari k'al"ummu kuwa can k'uryarsu ta shige k'irjinta na tsananta bugawa ta zaro card d'in Abdallah dg cikin jakarta"ta zauna gefen bed ta kwafi number d'insa"cikin fad'uwar gaba da tsoro tayi dealing d'in number d'in"busy tajita hakan yasa ta kife kanta samqn pillow tayi shiru"sai bayan mintina 5 sannan ta koma kira aikuwa ta shiga tafara ringing"sai gab da zata tsinke Aka d'auka Amma ba'a yi mgn ba"Ta girgiza kanta tana mamakin zafin kai irin na Abdallah"ko sallama Ai yayi tunda ya d'auka"sanin halinsa zai iya kashe wayar yasaka tayi saurin yin sallama cikin siririyar muryarta"dg d'ayan b'angaren big man dake zaune Akatafaren office nasa kamar Ak'asar turai"kujera na lulawa dashi iskan fanka da sanyin AC na dukan jikinsa"yatab'e baki domin sarai yagane ummul khairy ce"be Amsa sallamarba cikin cool voice d'insa yace" wacece?"kiyi gaggawar sanar mun dan bana tsayawa jin shirme"idan kuwa bakida mgn me mahinmanci maza kashe wayar ki"dg haka yayi shiru yana jiran jin me ummu zatace??"batayi mamakin jin kalamansa ba"saita basar tace"ummulkhairy ce"dama kan maganar da muk...ke dallah banganekiba"kimun bayani ta yadda zan gane"zaki kama yi mana surutu haka bbu kamun kai"koda yake dama ba k'auyen mutum ina yaga wani kamun kai.... uhmm! nasan kagane ka nuna baka ganeba"zancen kamun kai dakake mgn ban d'aukeka cikakken namiji ba balle har na tsaya nayi wani kamun kai Agaban ka"Abinda nasani kawai kowa tushensa A k'auye ne....K! yafad'a Atsawace"yanzun da kika nuna mugun hali naganeki ko baki fad'a ba"fad'i Abinda yasaka kika kirani"maida mun mgn kuma ki cigaba dayi karki fasa"laifin waye idan banakaba"kaine kaja na maida maka mgn"dama na kiraka ne sbd nasanar maka na Amince"doguwar tsuka yaja yayi shiru"saida ya mula yasha Iska kafin yace"wannan tsohon zance ne da kin Amince tunda dama nasanar miki dole ki Amince"na riga na gama mgn bana buk'atar Amincewar ko"kin sanarwa yaron da kuke soyayya dashi?"yafad'a yana yatsina fuska kamar yana ganinta"na sanar masa ya Amince"zamu had'u a gold stone dani dakai dashi muyi mgn"yaushe?"duk sadda katashi"gobe da yamma mu had'u can"saidai wlh muddin kika mun rashin kunya gabansa ko gayan maganar banza wlh tattakaki zanyi Agaban nasa....batace komaiba ta kashe wayar tana fad'in kaji dashi fitinanne.....
washe gari misalin k'arfe 5:11 pm"ummulkhairy ce zaune kan kujera"gefenta mubashshir ne"wanda yau da safe yadira Agarin sbd yana Abuja"ya shirya cikin milk d'in shadda"zuciyarsa fal kishi"yanaso yaga waye wanda zasuyi wannan Auren da ummu??"yayinda ummu ta shirya cikin k'uru Adakarta"sabon leshi ne na sallarta red colour me zanen golden tasaka"ta yafa mayafi golden Amma batayi make up ba"tun wajen 4:30 sadda suka iso ta turama Abdallah text sun iso"Amma gashi zaman mintina 41 sukayi wajen shiru be iso ba"tasan dama tunda yanaji da girman kai Ai bazaizo kan lokaciba"idan kuma shine Am ba daidai ba yayi wulak'anci son ransa....kinga gaskiya inada Abin yi idan bazai zoba kawai natafi"cewar mubashshir yana jan tsaki"ummu batayi mgn sbd tasan besan waye Abdallah ba"wayarta ta d'auka tafara k'ok'arin kiransa"yana ganin kiran yamata banza"dama kuma suna dg waje kusan mintina 10 kenan da isowqrsu Amma yasha Alwashin bazai shigoba sai ta gaji da jira ta kirashi"sosai ranta yab'aci da k'in d'aukar wayar da yayi.....cikin nutsuwa had'e da Aji big man yashigo wajen"cikin takunsa na zaratan mazan da suka Amsa sunansu maza"yasha wankan manyan suit dark blue"takalmi da Agogo duk dark blue ne yasaka"yayi kyau Abin saidai ace masha Allah!yayi bala'in tsare gida"wanda hakan ba k'aramin kyau yamasa ba"body guards nasa su shidda suna biye dashi dg baya"tunda ya shigo hankalin maza da mata yakoma wajensa"duk Inda ya gifta saiya bar musu ni'imtaccen k'amshin turarensa"directly Inda ya hango ummu yanufa"tunda taji zuciyarta na tsananta harbawa ranta yabata big man ya shigo wajen"da sauri ta juyo ta hangosa yana nufo Inda suke cikin nutsuwa"cikin second 5 ta k'are masa kallo tana fad'in masha Allah! beda Aiki sai saka k'ananun kaya"ta fad'a Aranta"saidai yau taji yamata wani irin mugun kwarjini....ummu bakice komai ba ,kodai mutafi kawai?"cewar mubashshir"gaya nan fa"bece komaiba yajuya bayansa sukayi 4 eyes da big man"k'irjinsa yabuga ya juyo ya kalleta yana fad'in banga kowaba sai Abdallah mohd jibo gasu nan zasu wuce"shine ai! kafin yayi mgn k'amshin turaren big man ya dira Awajen"da hannu yayiwa body guards nasa Alamar karsu k'araso su jirashi"befi taku ukku ba yayi ya iso gaban table d'in dasuke zaune gabanshi "cikin taushin muryanshi ya musu sallama"wanda ummu tayi bala'in mamaki"itace tayi k'ok'arin Amsa sallamar tasa"mubashshir kuwa tsabar mamaki yakasa mgn"sannan yakuma yi bala'in raina kansa dayaga Abdallah yong bolonia"Abdallah be tankawa kowa ba yaja kujera ya zauna yana danna waya"kyakykyawar fuskar nan tasa a murtuke"y'allabai sannu da isowa"cewar mubashshir cikin rawar murya"yama kasa had'a ido da shi"ummu kuwa mamakin rikicewar mubashshir dayaga Abdallah takeyi"da yauwa Abdallah ya Amsa yana shan Alwashin bazaima ummu mgn ba muddin ba itace ta fara masa ba"kusan second 30 bbu wanda yayi mgn Acikin su"kanta ayk'asa tace"ina wuni?"lafiya"dama gashi nan mun gama mgn dashi"d'ago kansa yayi yakoma kallon mubashshir"shi kansa sai yaga kamar ummu tafi k'arfin wannan saurayi"Amma saiya tab'e baki cike da izzah yace"it's okay"dama nace tazo dakai ne"dukda banida tsarin maimaita mgn"kuma nasan ta maka bayani"so bbu damuwa zan Aureta duk lokacin dakaga katashi Aurenta kamun mgn zan sakar maka ita ka Aura"sai Abu na k'arshe shine zaka dena zuwa wajenta da kiranta yanzun sbd za'a saka mata rana"kulaka zai sakq mutane su zargi wani Abu"idan Anyi Auren zaka iya cigaba da mgn da ita banida matsala ko damuwa da hakan"sbd Aure ne bana dindin ba"kowa kuma harkan gabansa zaiyi bbu ruwan wani da wani"sai warning d'ina dakai da babbar murya banaso koda wasa kasanarwa wani ko wata Ainahin irin Auren da zamuyi da ita"idan kuwa naji maganar hmm! yafad'a yana d'allah yatsunsa biyu sukayi k'ara"daga haka be koma mgn ba"itadai ummu shiru tayi domin duk kalamansa sun mata sai abu d'aya dayace bayan Auren su cigaba da waya da mubashshir"dukda tasan Auren da sukayi Amma Ai duk Aure Aure ne"Allah bbu ruwansa da wasa tsab za'a rubuta mata zunubi idan takula wani...to y'allabai duk naji zan kuma kiyaye"na barka lafiya"sweet heart ina dg waje "dg haka ya mik'e tsaye "ummu kanta kawai ta gyad'a masa"yana barin wajen ta tab'e baki tana fad'in zaman me kakeyi da bazaka tafi ba?"tamkar da bango take mgn"yamata banza"ta tab'e baki tana k'ok'arin tashi taji Amon tattausan muryanshi yana fad'in gaskiya na tausaya miki"ta kallesa taga yana murmushi me wuyar fassara"Akan mefa kenan?"sbd wannan Abin da kika d'auka Amatsayin masoyi"dama shine kikeso?"kaga dan Allah kabarni da wasu k'ananun mgn"narasa meyasa idan baka k'untatamun ba bakajin dad'i?"shiru yamata yana d'aukar wayarsa da sa'ada ke kiransa"idan bbu wata mgn nizan tafi"cewar ummu batare data kallesaba"be kulataba sai mgn yaci gaba da yiwa sa'ada ba'a majin meyake fad'a"bayan yagama wayar ya mik'e tsaye beko kalletaba yyi tafiyarsa...ta tab'e baki itama tatashi ta fito ta samu mubashshir yagaji da jiranta yatafi"wanda tayi mamaki sosai.....
kwana biyu da faruwar hakan"ummu na zaune a parlourn su da yamma tana markin d'in CA text ta ɗalibanta"yayinda mama ke zaune tsakar gidan tana shan Iska"goggo luba ma na zaune tayi kwad'on tuwun ruwa da daudawa tanaci tana jan yaji....wayar ummu tayi ringing"dubawa tayi taga bak'uwar number ce"d'auka tayi tana yin sallama Ahankali"dg d'ayan b'angaren kamal ya Amsa yana fad'in ranki yadad'e Anyini lafiya?"ta Amsa da Alhamdllh"masha Allah! sunana kamal! big man yabani contact naki"pls idan kina gida ki turomun Address d'in gidanku zanzo yanzun zamuyi mgn idan babu damuwa"shiru ummu tayi tana tunanin wato shiyafi k'arfin zuwa gidansu shine zai turo wani"to Inda ta godema Allah itama bata buk'atar zuwan nasa"koyace zaizo bazata bari yazoba balle idan yaga gidansu yamata gorin cemata talaka bak'auya...kina jina ummulkhairy?"Eh inaji bara naturo maka Address d'in yanzun"dato ya Amsa"ita kuma ta yanke wayar"bayan ta gama tura masa tayi tagumi tana tunanin dame kamal zaizo?"Anya batayi kuskuren Amincewa da wannan Auren ba?"tabbas big man ba k'aramin mutum bane"karma Ayi zaton kwad'ayi dason Abin duniya yasaka zata Auresa"shin idan Anyi Auren wane irin zama zasuyi ma?"zai barta taci gaba da Aikinta?"wanda Aikin nan shine komai nata dana mahaifiyarta....tana wannan dogon tunanin taji sallamar yaro yana fad'in wai Ance ummul khairy tazo inji Abdallah! k'uri da ido goggo luba tayiwa d'an Aiken gabanta na fad'uwa"mama dake lura da ita tayi murmushi me ciwo kafin tace"jeka gata nan zuwa"dg haka mama ta mik'e tsaye ta nufi cikin d'aki"goggo luba kuwa y'arta ta kira d'aki mariya"tasanar mata idan ummu ta fita ta bita taga da waye suke mgn??....mama ta dubi ummu tana fad'in kiranki Akeyi fa nasan kuma kinji ko?"Eh yanzun zanje Ai"ki tashi ki k'ara saka turare mana"dato ta Amsa ta wuce ciki tana mamakin meyasa kamal zaice Abdallah ne?"da wannan tunanin ta d'an fesa turare ta yafo mayafi samqn red d'in Atamfar jikinta ta fito dg cikin d'akin"bbu kowa tsakar gidan"goggo luba na hangenta ta taga harta fice dg cikin gidan....
kamal na zaune samqn motarsa yana danna waya"yasha gayunsa cikin k'ananun kaya yanata k'amshi"kasancewar shima wajen gayu badaga baya ba"cikin nutsuwa ummu ta k'araso da fara'a samqn fuskarta tamasa sallama"yad'ago kansa ya Amsa yana fad'in kin zata da mutumin mukazo shine aka shanyani?"ah ah nasan kai d'aya ne"shi kuma Ai bankai matsayin dazaizo k'ofar gidan muba"ba haka bane ummulkhairy"tayi d'an murmushi ta gaishesa"Ahaka mariya ta fito dg cikin gidan tana tsaresu da ido kamar tv"sai kuma ta koma ciki Aguje"ummu tayi murmushi Aranta"dan tasan uwarta ce ta turota "taga kuma mamaki da rud'ewa A samqn fuskar mariya"sbd ganin kamal datayi"yanzun Inda Abdallah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login