Showing 1 words to 3000 words out of 122108 words
Chapter 1 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
1⃣
Na : *SAJIDA*
sadaukarwa wa *ummu lalla Fatumah sisna Hawwer*
Haba Aïsha, haba Aisha har yaushe zaki daina irin wannan mugun halin? Shin mai mahaifinmu ya rage mu da shi, daidai karfinsa yanai mana, du abinda muke bukata daidai gwargwadon iyawarsa yanai mana aman a kulun idan kika budi bakinki ba zaki yabi tarin alkhairan da yake yi mana na yau da kulun ba sai dai ki fadi wani wajen da ya gaza, a kulun ina fada maki ki daina kokarin hada rayuwarki da ta sabuwar kawar da kika yi.. kin ga iyayenta masu hali ne sannan samarinta sun tsaya mata...............ki........m
Wace aka kiraya da Aisha wace ta yi tsai tamkar tana daukan nasihar yar uwarta ta dago fuska a hade ta watsawa yar uwar tata harara ta ja wani uban tsaki ta ce" kinga malama ki saurara min haka, shin tambayar ki nai ki yi min kari a kan tarbiyar da kike ganni bani da ita ko mai? Ni ina mamakin idan kika sakoni gaba kinai min fada tamkar ke ce yayar tawa ni kuwa kanwarki,,, idan ke ita rayuwar nan ta yi maki sai ki je ki karata da talauci aman ni na fada maki idan baba ya nacewa FASKARE ni ba zan iya ba, ga ayuka nan barkatai a duniya aman shi ya nace sai dai faskare da shi ne zai ciyar da mu? To zan fada maki ko ta tsiya sai na shiga banban gida na hau babar mota domin Allah ya bamu halin auren nairar tunda ya kayatar da halitar mu.......
Ta gama tana mai juya dara daran idannuwanta ta zarce wajen dan karamin madubinsu ta zauna ta shiga fence fuskarta
Ta jima zaune tamkar ruwa ya cinyeta tana mai takaicin halayar yayarta, a hankali ta mike ta karaso kusa da ita ta dora hannunta na dama saman kafadar yayar tata ta marairaice murya ta sada kanta alamar zata bada hakuri ta ce" ki yi hakuri Autyna, ban fadi haka dan na bata maki rai ba idan na ga irin haka na faruwa ne sai hankalina ya tashi domin bana so ki fada *tarkon samarin zamani ne* inai maki son da ba zan juri ganinki a wani hali ba plz auntyna ki yi hakuri kar ki yi fushi da ni
A hankali Aisha ta juyo ta kamo hannun kanwarta wato *RAUDA* wace take yiwa kiranye da LALLA ta ce" *LALLANA* ki gane ni du abinda ya shafi talauci batan raina yake, ki duba fa ki ganni kulun Abanmu jalabiyarsa kwaya daya ya fice da ita da gatari ya tafi yawon anguwa anguwa kofa kofa yana neman itacen da za.a bashi ya faskara, bayan ya gama a hada shi da naira ashirin naira talatin baban samunsa naira dari watarana sai ya wuni bai samo komai ba ya dawo haka zasu yi ta samun matsala da mama sannan da wannan samun ne yake ciyar da mu ya siya mana atampa roba ya yi mana dinkin naira dari bibiyu, sai fa sallah ta zo bamu da kayan sallah dududu har muka yi yarinta muka gama hijabanmu hudu a duniya muna arawa juna muna canzawa...... makaranta litafinmu kwaya daya da shi kike rubutu nima da shi nake yi.... haba ko yaya na ga haske ai zan nufe shi shi ya sa nake fada maki yanzu mun taso mun kai mizanin yin samari muna jami.a dole mu so daukan wanka ko dan gudin raini , sannan samarin nan harin mu suke ina mai baki shawarar ki kula su tun suna kula ki ba sai su yarda ke ba ki dawo kina zubar da kwalah kina haukan neman su
Ajiyar zuciya Rauda ta sauke, kwata kwata magangannun yayarta banda caza mata kai ba abinda suke... a kulun adu.arta shine Allah ya katsewa yar uwarta irin wannan dogon buri na mahaifiyarsu tun kafin ya zame mata matsala, ita bata ga abin damuwa a rayuwarsu ba mahaifinsu yana nema tun karfinsa da shi yayi ta fafutuka wajen gannin sun yi karatu sun samu ilimin adini da na boko, da yake mutun ne mai tsayuwar dare mai fawalawa Allah lamuransa sai ya kasance duda makarantar gomnati suke yi sannan a jarabawa basu da mai kama masu sai Allah Ya tsaya masu suke tafe cikin nasara har Aisha ta samu shiga University sannan Rauda...... manema aurensu kuwa ta ko.ina fitowa suke sai dai idan har sunanka bai zarce ba Aisha Bata sauraronka ita kuwa Rauda tana saurare sai dai mahaifiyarta ta shiga ta fita ta kori mutun sannan ta....
Tunanin mai kike ne Lallana?
Muryar Aisha ya kashewa Raudat tunanin da ta fada ta zabura ta kakaro murmushi ta ce" ba komai Auntyna , Allah ya shige mana gaba
Aisha ta amsa da amin sannan ta juya ta ci gaba da gyara fuskarta dan zuwa makaranta
Haka suka fito Aisha ta gyara fuskarta tamkar zata je wajen biki Raudat kuwa banda kwali da ta dan furta a idannuwanta ko hoda bata shafa ba
Mahaifinsu ne zaune yana wanke hannunsa da gatarinsa gefe ya saka jalabiyarsa wace dan tsufa har yamutsewa take sai hularsa irin zigegen alhazan nan wace a kadan ta shekara hudu da aka yi masa kyautarta
Amsa gaisuwar yayan nasa yake cikin sakin fuska da basu mahinmanci sannan ya shiga laluben aljihunsa ya jawo naira dari da ashirin ya mikowa Aisha wace ita ce baba ya ce" Aisha ga wannan ba yawa sai ku sha ruwa a hanya
Aisha ta bi hannun mahaifin nasu da kalo naira darin ta yakune du a cicire hakama ashirin din ta sama ta kakaro murmushin yake ta ce" baba ai ka barshi kawai
Tana gama fada ta mike ta fice inda suka rakata da kalo jikinsu ya mutu murus
A hankali ya juyo da dubansa wajen Raudat ,
Saurin basar da abinda Aisha ta yi ta yi ta kakaro murmushinta mai kyau da tsari ta mika hannu biyu ta ce" Lah Abanmu ni dai ina so, bani naira ashirin din sai na kara da sauran canjin da ka bamu jiya bamu kashe su duka ba shi ya sa aunty ta ce bama so, tana son cewa ai da saura ne
Ta karasa maganar tana karbar ashirin din da iya kokarinta dan gannin ta mantar da shi dabi.ar yayar tata
Murmushi yayi ya sakar mata ta mike ta kama hanyar fita
Har ta daga kasarin da ya kare kofar mahaifinta ya ce" *Raudat*...
A hankali ta juyo tare da amsa kiransa
Cikin murya mai cike da nutsuwa ya ce" Allah ya datar da ku da dukan alkhairin rayuwa, ya daukaka ku, ya sanya farin ciki a cikin rayuwar ku, ya baku mazaje na kirki masu tsoron Allah da bin umarninsa ,
A hankali take amsawa da amin a dukan adu.ar mahaifinta har inda yake cewa" Allah ya shiryar da yar uwarki tun kafin dama ta kubuce mata, ya sa ta daina hangen na wasu ya kasance ta daina *raina inda take kar taje ta yi biyu babu domin mafi yawancin irin haka inda zasu ya raina su*
Saurin dago da kanta ta yi bata ce komai ba sai lumshe idannuwanta da ta yi ta mike ta kara gyara hijabinta ta juya tana sauri kar Aisha ta yi tafiyarta
Wani irin haushi da bacin rai ne ya turneke mata zuciya hango yar uwarta da ta yi tana kokarin shiga motar sabuwar kawar da ta yi mai suna Aminah
Dan tsayawa Aisha ta yi tana kalon Yannayin Raudat, dan haka ta hade fuska danma kar ta kawo mata wargi gaban Amina
Tana karasowa ta ce" mu je ko? Kin ga Allah ya kawo freind ba sai mun sha wahalar tafiya kafin mu hau bos ta sauke mu a bakin titi mu kuma yin wata tafiyar kafin mu karasa jami.a
Ta karashe tana dage gira dudan ta shawo kan Rauda duda ta san abu ne mai wuya ta yarda ta shiga dan ba shiga take yi ba
Rauda ta dan kakaro murmushi ta ce" ai kin san ina son tafiyar kafar nan ko dan na dan ringa mike kafana aunty ku je kawai sai na karaso
Tun kafin ta gama maganar Aisha ta daga kafadu irin ke kika jiyo ta bude gaban motar ta shige Amina ta ja da mugun gudu suka bar wajen
Ajiyar zuciya Rauda ta sauke ta daga kafa ta nufi bakin titi dan shiga bos ta kaita makaranta
Lecture din awa hudu ne da ita a yau, haka ta yi karatun nan ba tare da ta saka komai a cikinta ba dan tana son kudin su isheta komawa gida
Karfe 2 na rana suka fito ta nufi bangaren su Aisha dan gannin ko basu sauka ba ta yi jiranta sai dai mai tana karasowa ta tardo Amina kawar Aisha ta kwashi wasu yan mata a motar nata tana baiwa Aisha hakuri cewar zata sauke su ita ta yi hakuri gobe sai ta dauke ta, cikin raini da isa take fada mata hakan
Aisha ta yi sororo jikinta ya mutu ta kasa koda daga kafa ta bi motar da kalo har suka kai bakin gate din agriculture suka fice har ta daina hango su aman ta kasa daga kafarta
A hankaki Rauda ta ce" aunty, mu tafi plz ai har sun bacewa ganinki kina tsaye,
Da sauri ta juyo tana kalon rauda , maganar rauda ya fado mata inda take cewa" Aunty a duniya idan kina son ganin wulakanci ki kwalafa rai da *abin mutun* komai kusancinki da shi ya kasance kina nesa da abinda yake malakinsa ne hakan zai saka tarayarku ta jima sannan mutuncinki ya dauwama a rike a wajensa
Idannuwanta ta lumshe wa.inda suka yi jajajir ta ce" WALAHI WALAHI WALAHI SAI NA HAU MOTAR DA TA FI TA AMINA SAI MURZA NAIRAR DA KO UBANTA BAI MURZA BA..........
Baki bude Rauda ta bi yayarta da kalo, inda gabanta ya tsananta faduwa har ta furta tambayar " *AUNTY ta ina? Ta yaya? Ta wace hanya kike irin wannan tunanin?*
Aisha ta ja tsaki ta ce.............
Shan koko bukatar rai😍❣😍
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
2⃣
NA: *SAJIDA*
Allahuma ajurni minna nar......👏🏻
Aisha cikin kakausar murya ta ce" ki sani Raudat, ko ta hanyar Allah ko ta tsiya sai na yi kudi sai na kamo kawayena sai na shiga motoci , sai na rike babar waya sai na kwatarwa kaina inci na arziki
Ran Rauda ya baci iya baci hakan ya saka ta shiga hawaye wanda mafi akasarin lokuta hakan zaka ga yana faruwa idan ranta ya baci wajen mutumin da ba yanda zata yi da shi sai kawai hawaye su balewa idannuwanta
Juyawa ta yi kawai ta bar yayarta a nan dan ta lura Aisha fa ta yi nisa bata jin kira, burinta na ta zama mai kudi ko ta auri mai kudi ya girmami tsoron Allahnta (wa.iyazubillah)
A wannan rana kowace ta dawo gida ne ranta a bace ba mai yiwa yar uwarta magana
Suna zama mahaifuyarsu ta shigo, tun fitar karfe shiga da ta yi da sunnan ta tafi gidan biki sai wannan lokacin ta dawo da leda a hannunta
Fuskokin yayan nata ta bi da kalo ta dasa ayar tambayar abinda ya dauke annurin fuskokin su
Ansa gaisuwar Rauda take hankalinta na kan Aisha ta katse amsa gaisuwar ta ce" *Jarina* wani abin ya faru ne? Nake gannin fuskokin naku du a hade ko abin da ta saban ne ta yi maki???? Ta karashe tana zabgawa Raudat harara
Aisha ta kara hade rai ta shiga kwararowa mamansu abinda ya faru
Ran mamansu Raudat ya mugun baci da wannan cin mutunci da kawar yarta ta yi mata, cike da bacin rai ta ce" mai ta fi ki? Kyau fari gashi sura ko mai? Abinda ta fiki uba mai "Takaici" ita mahaifinta ya gane cewar faskere banda kashe zuciya ba abinda zai hadasa masa, ya fahimci cewar mutunci kankaro shi ake sannan kudi su ne jin dadin gidan duniya idan babu su sunanka wulakantace kaskantace marar galihu
Tunda ra fara fadan nan kan Rauda yake sade a kasa tana sharar hawaye a kasan zuciyarta tana fadin ikon Allah wannan shine wani da aikata laifin wani da shan duka
Dan haka nake fada maku ku mu tashi mu nemawa kanmu yanci...
Wannan rayuwar talaucin haka na sha ta tun da jan sahunna wai ni soyaya... a soyayar nan banda tsufa da karewa ba abinda ta kara min , ku fa sani ba soyayar nan ake ci ba idan tafiya ta yi tafiya baka da abinda zaka zama sai abin "tausayi"
Aisha ta bude idannuwanta ta ce" mama, ki daina bata yawun bakin ki domin ni nan da kike ganni talauci shakar kanshinsa sai dai idan na shigo gidan nan kafin mu kenkyara namu mu koma....... abinda Amina ta yi min ban ga laifinta ba domin wa.inda ta dauka yayan masu fa shi ne
A gaskiya mama ke kika cuci rayuwar mu da kika auri baba..... ni nakan rasa amsar tambayar mai kika gani baba dai ba wani kyau ba gaba daya ke muka biyo bafilatanar usil aman kika auri mutun irin baba
Ta karashe maganarta fuskarta na nuna tsantsar bacin ranta a lamarin
Mahaifiyarsu mai suna nana Mariama ta ce" uhum ke dai a bar naganar kawai , kun ga fa fogayen riguna na gani na sayo maku sai dai kwaya uku ne maimakun hudu dan haka ke Rauda ki yi hakuri da dayar Gaba sai na kara maki
Rauda kam bata cewa komai tana bin su da kalo nan Aisha ta shiga dadaga kayan tana ta murna domin kaya ne masu kyau duda ba masu kudi da yawa bane
Cikin mutuwar jiki Raudat ta mike ta shige dakinsu ita da Aisha
Zama ta yi gefen katifar su ta kurawa madubi ido tana kallon fuskarta a ciki
A hankali ta lalubo hoton mahaifiyarsu inda take ganiyar kuruciya ta zubawa hoton ido
A jikin hoton bata fi shekara ashirin ba komai na cikakiyar mace akoyshi a jikin ta
Ajiyar zuciya ta sauke a fili ta ce" shin ikirari takama da su mama suke yi da kyau da yarinta da kalar fata bata lura aya ta kasance a kan kanta ba? Ita da ta yi gadon kyan gaba da baya wajen mahaifiyarta da mahaifinta bata ga yanda yanzu fatarta ta dawo ba? Duda tana fadin cewar wahala ta dawo da fatarta haka aman ai daman kuruciya kyau ba madawama bane, ita fa a ganinta ai gwara ka yi anfani da kyan naka wajen aikata alkhairi da shi ka kilace shi ka rufe shi ya anfaneka sai mijin da ka aura ba? Da ka biyewa rudin dun....... ..........
Tunaninta ya katse daidai lokacin da Aisha ta jefo mata jar riga cikin rigunan wato ra zabi kala biyu ta bata guda sannan ta ce" ki tashi mu je mu dora tukunya mai nemowar ta kawo mana yau nama zamu ci,.... kai da ba dan Mama ba da mun yi anagon nama da sai muna tafe muna kalo a wajen masu siyarwa
Mikewa Rauda ta yi ta cire hijabinta ta shanya shi saman yar igiyar da suka kula suke shanya kananun kayansu a dakin nasu ta daura dan kwali ta fito
Itatuwan da mahaifinsu ya sara ya kilace masu fan dora tukunya ta fauko kwara hudu ta ajiye gefe ta share cikin murhun da bakin murhun ra hada tokar ta kai cikin shara bakin kofar gidansu ta dawo ta tsintsinto ledoji busasu ta karaso bakin murhun ta saka itatuwan ta hasa wutar
Juyawa ta yi tana kara wanke tukunyar sanan ta dora saman murhun ta dawo ta zauna tana wanke naman nan tana zubawa cikin tukunyar bayan ta gama ta kawo kayan yaji atarugu da gujiyar miya dakakiya ta zuzuba ta rufe ta juya ta shiga yanka albasa kananuwa domin so take ta yi ta gama fan du infa mahaifinta yake ya kusa karasowa gida
Nana mariama ce ta fito da tarin tafarnuwa a hannunta tana fada ta ce" daman na san ba zaki zuba ba dan ubanki yace baya ci sai kika manta cewar ni na nemo na kawo shi abinda ya iya kawowa masara da gero ne, malama karbi ki zuba min a ciki tun kafin ranki ya baci
Raudat ta dago da kanta tana fan share irin hawayen nan na zafin albasa ta ce" haba mamanmu, naga ai mu idan da akoy ko babu ma muna iya ci ko? Mai zai hana idan na gama na fitarwa da baba nasa sai a zuba a namu mamanmu? Kinga ba kyau ka ci tafarnuwa ka je masalaci domin ita warinta yana fa naci ne, yakan zaunawa a jikin mutun na tsawon lokaci koda kuwa ya wanke bakinsa , ki yi hakuri idan na fitar masa da nasa sai mu saka
Nana Mariama cikin bacin rai ta dauke Rauda da mari, daman ita akoy saukin hannu ga zafin zuciya ta ce" ki shiga a taitayinki Raudat, ke banda shirme irin naki mutumin da datin jikinsa ma ya ishe shi shine zai fito mana da karyar wai shi baya cin tafarnuwa? Yaushe ma ? Sannan ki bari idan ya shigo gidan nan da leda dauke da nama sai ku yi mana iya yi
Tana gama fada ta bude tukunyar ta afka tafarnuwar sannan ta juya ta yi tafiyarta aka bar Raudat da takaici
Zaune yake yana irga kudin da yayi a yau, cike da farin ciki domin wata mata ya samu irib masu kasa itacen nan ce sannan bata da bakin ciki ta bashi faskaren mai yawa wanda sai da ya kasa shi uku ta biya shi wajen dubu guda da dari uku
Bayan ya gama irgawa ya shiga tunanin mai zai yiwa yayansa da matarsa dan ya faranta ransu???wani mai siyar da takalma ne irin na robar nan na mata bakake da chocolate ya zo ficewa hakan ya saka Malan Ahmad mikewa fa dan hanzarinsa ya tsayar da mutumin ya dauki taki uku bakake biyu da chokolate guda suka yi cikini
Da kyar ya bara masa su a dari takwas ya biya cike da farin ciki ya dauki hanya da naira dari biyar