Showing 108001 words to 111000 words out of 122108 words
Chapter 37 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
sai da karfe goma sha daya ta yi, tafiyar kafa ne ta sha har can, idan ka ganta dole ka ajiyeta a dayan biyu ta haukace ne ko tana kan hanya
Sannan a wannan lokacin du wata majalisa ta anguwar, du wasu masu zaman kawai du wasu yan mata masu zaman kofar gida, du wasu yara masu bin mahaukata suna tsokana sun yi cccccaaaaa sun cika anguwar kowa yana abinda ya fi kwarewa ana ta labarai ana iya shege
So take ta shige ba tare da an ganeta ba sai dai ina, tunda rabe mai man ja ya ganeta ya fito ya daga murya ya ce" jama
a me nake ganni ne nan tamkar matar gwomna? Kai dadina da bariki har ta jefo ki ?
Yara maza da yan mata kai harda matan auren mararsa aikin yi suka aniya bin bayan Aisha suna tofa mata mugayen kalaman da idan da ne sai ta tsire su sannan ta take su ta fice, aman a yau kanta a kasa, kunya take ji ta rayuwa, mamaki take na abinda duniya ta yi mata tun ba.a je ko.ina ba, mamaki take na yanda mutanen duniya suka fasarata, su tunanin su ta je yawon bariki kennan? So take ta juya ta roke su , su ji kanta su barta ta yi tafiyarta sai dai jinsu take tamkar sirikanta ta kasa hada ido da su tamkar ta yi masu karya, nauyinsu take ji fiye da girman kanta
Bata gama mamaki ba sai da ta ga raliya ta yi wani irin dirowa gabanta, ai kuwa du ake kallon su ,
Raliya ta juya kananuwan idannuwanta ta ce" ke mai kyau , gashi, fari ko? To yau ni mumuna na kwace maki saurayin naki wanda yake kashe maki kudi auren har sauran kwana hudu! Toh idan ma labarin auren kika ji kika zo ki wargaza min farin ciki karya kike, idan takamarki sauko wani a can ya kwana fahad ba zai zauna da yar bariki sauran karti ba
Tana fada tana kada jikinta , jira take kadan Aisha ta furta wani abu ta nuna mata itama fa ta fantsamo barikin ta iya tas sai ta dameta ta shanye, a da ne take binta tanai mata fadanci ko dan a anguwa a ringa kallonta a babar yarinya tana kawance da Aisha wace du yawancin samarin anguwar ke sonta, a haka ne ta yi sayrayi fahad, yana kashewa Aisha kudi sai dai a kulun tana nuna masa itafa ba zata iya abinda yake so ba wato a more a titi, du mugun halayen Aisha abinda bata saka kanta a ciki ba kennan, mugun halinta ita kawai lashe mony ce, hakan ya sa Fahad ya janye domin shi daman abinda ya kawo shi kennan,
Raliya na gannin hakan ta fara bin fahad du inda ta san zata same shi, bayan barin aisha gida ne Fahad ya amaince mata aman da sharatsin sai ya santa a ya mace daga baya zai aureta
Da yake idannuwanta sun rufe ta amince masa suke kebancewa ba tare da ta kiya masa ba , a haukanta da gaske auren nata zai yi bayan ya gama wanketa da karyar cewa zai je ya zo da iyayensa da kudin aure da komai dan haka su shiga shirye shirye sai ya dawo daga Kd
Aisha ta sada kanta bata iya cewa Raliya komai ba tana son zagayeta ta fice Raliya ta janyo hannunta da dan karfi
Wani saurayi mai suna Musa ya ce" ke ralos baki da hankali ne? Bakya tsoron cutar S? Kinga fa jini take zubarwa ki je ki kwasa?
Ai da sauri ta bata gu, jin hakan ya saka sauran ma suka sakar mata hanya ta ci gaba da tafiya kirjinta na wani irin dokawa ta nufi gidansu da dumbin tashin hankalin me zata cewa iyayenta? Me zata ce masu? A irin yanda ta fice ta bar su idan ta koma yanzu ta kale su a yaya? Daman gidansu shi ne aljanarta? Gaban iyayenta koda a cikin akurki ne nan ne konciyar hankalinta?
Tana tunkarar gidan ta fara hango wani tashin hankalin, ba gidansu ba labarin gidansu sai wani shago da take gani a madadin gidansu,
Ido ta murza da dan karfi ta zabura ta waigo bayanta manyan dun sun gudu gudun kar ta goga masu cuta sai yan tsiraku yaran da basa jin maganar iyayensu sunna biye da ita sunai mata wakar mahaukaciya yar macukule
Da sauri ta ji wani karfi ya zo mata ta karasa wajen kanta ta rike ragar ta ce" kai kai malan, ina suke? Ina iyayena suke? Ina mamana? Ina abanna? Wayo na shiga uku, wayo ni Aisha kaicon rayuwana, ina iyayena suke , ina suka shiga? Ina zan gansu? Ya Allah kar ka sa na yi mugun ji, ya Allah ka sa iyayena na nan a raye, ya Allah ka farkar da ni a wannan dogon mafarkin na gannin da kanwata mun fito a makaranta , ta Allah
Ta fashe da kuka ta duke a jikin ragar da aka mugun kayatata an zuba kayan abinci na zamani na talakawa da masu hannu da shuni, da ma.aikata yan yara suna ta kulawa da wasu datijai biyu maza wa.inda tunda Aisha ta karaso suke kallonta, dayan ya juya da sauri ya kalli datijo daya wanda ke sanye da kayan mu na hausa ya yi kyau abinsa da gemunsa da carbinsa a hannu da alama shi ne mai wajen
Da sauri mutumin ya kara juyowa ya kali mutumin ya kuma kalli aisha dake ta magangannu hannayenta bibiyu a saman kanta fadi take mamana Abanna
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
5⃣9⃣
A razane ya ce" malan wannan ba nana Aisha bace?
Malan dake kallon Aisha a tsugune, ya maido dubansa wajen amininsa malan tanko, ya kuma duban Aisha, bai iya cewa komai ba sai mikewa da ya samu ya yi gwuiwa a sace ya zo inda take ya dan duka ya kamo hannunta ya ce" tashi ki suturta jikinki ki daina janyowa kanki maganar duniya mana ya Aisha
Da wani irin razana ta dago tana dubansa, tsoro da mamaki suka saka ta wangale baki, mikewa ta yi tana kokarin rukunme shi sai dai ya dan baya kadan ya mika mata abinda ke hannunsa wani abin rufa ne dake daya cikin kayan da ake rufe kayan sana.ar idan xata rufe shagon
Jiki a sanyaye ta karba ta luluba a jikinta tana mai binsa da kallo aman ta kasa furta ko wace kalma
Ta ciki shagon ya shiga ratsawa ana kallonsa ana gaishe shi ana bin wwace ke biye da shi jiki a sanyaye da kallo har suka shige ta wata yar kofa suka bilo ta cikin wani gida
Kallon gidan kawai take, gaba daya farar kasa ce a kasa luflufluf
Haka suka shige suka tafi har suka karaso wani mamakeken falo
Ita dai bata juya ba dan kawai ta sani ne ko me zai zama ba zai bace mata ba a rayuwa, aman tana cike da fargaba
Suna shiga ta zaro ido, wanda idannuwanta suka sauka kanta ta danyace ta dawo wata sabuwar yarinya, tana zaune tana faman linki tana fadin" haba malan kai nake jira, ni fa wannan lamarin sai ya saka zuciyata ta mutu da yawa, ka ga yaron nan fir ya hana na mktsa jikina har ciwo yake, wai yanzuma na dauko kayanka na ware masu dati wai yarinyar nan saude ta zaburo na kawo ta wanke, Allah na tuba sai kace ina hauka ne? Ni na baiwa wata aikin mijina? Da kyar malan ta amince ta bar min aikin ladana bayan na yi mata jan ido na nuna mata fa sai na..........
Shiru ta yi gannin yanda malan ya tsaya ya kafeta da ido har idannuwanta suka sauka kan abinda yake son ta ganni
Ido ta zaro, gabanta ya bada wani irin dukan da ta ji zata sume dan razana, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,
Shine abinda ta furta a lokacin da Aisha ta cire rufar dake kanta ta bayanna a gabn Mama,
Gaba daya kafafuwanta ne suka dauki rawa, so take ta karasa wajenta aman ji take tamkar ba ita ba, mamana ce wannan? Abana daman kai ne?
Aisha ta furta tana mai rarabe kalmomin tamkar mai koyon magana
Mama ce ta ji wani abu ya tsaya mata a zuciya, tsoro ya dirar mata, Aishanta ne haka? Aishanta yarinya yar gayu? Ina ta je haka ya sameta? Wai a haka suna masu binta da adu.a ne? Ya salam
Kwalar dake tare a idannuwan Aisha suka samu suka zubo, a hankali ta fara takawa dan karasawa kusan mama sai dai wani abin da ya fadar mata da gaba, abinda maman bata taba yi mata ba du irin fitsarewar da tayi zaman yi mata
Wani mugun harara ne mama ta zabgawa Aisha kafin take juyawa wajen Aba da alamun bacin rai ta ce" Malan , me wannan marar godewa Allahn ta dawo yi min? Ko dan ta ga yanzu muna cikin daulan ne ta dawo a ci da ita? Haba malan ya zaka yiwa butulu hanyar dawowa wajen mu? Wannan yarinyar bata san alkhairi ba, sannan ta kasance mai son konta fiye da yan uwanta , kana gani du irin yanda nake tafe da ita nake yiwa dukan muradinta biyaya tamkar itace uwar ni kuwa yar aman irin sakayar da ta yi mana yanzu me ta dawo nema?
Malan da ya tsare mama da kallo, irin kallon nan me sakawa ka yi gum da bakinka ne, tun tana zubar da dan karfinta har ta yi shiru ta sada kai tana sheshekar kuka tamkar a lokacin abin ke faruwa da ita take ganni
A hankali makan ya taka ya karasa kusa da ita, murya a nitse ya ce" ya Mariama, ya ummu nana Aisha da Rauda, uwar gidan Malan Ahmad, ya dan rage murya ya ce" kai harda amaryama du ke daya
Kamar yarinya mama ta dan turo baki ta juya bayanta irin ta ki rarashin
Dubansa ya kai wajen Aisha ya ce" ki shiga cikin wancen dakin ki yi salar da baki yi ba Aisha
A hankali ta juya bata daina kukan ba ta nufi inda Aba ya nuna mata wani tsoron mama wanda a da bata ji ne ta ji yanzu ya sauko mata
Malan ya juya inda ta juya yana dan murmushi ya ce" tunda bakya so ace maki amaryar shikenan zan kawo maki kanwa sai ta taya ki zama
Murmushi mama ta yi tana kallonsa bata ce komai ba
Malan ya ce " su dai mata lamarinsu sai su, haba maman yara na yi tunanin zaki yi farin ciki ne ki godewa Allah da ya dawo maki da ita da ranta ki yi mata fatan kara shiryuwa? Har kin manta hawayenki na kowani dare kina rokon Allah da ya kare maki yarki? Ko na tuna maki irin yanda zaki dadaba ni cikin talatainin dare ki haske min ido da kwon fitila ki ce" malan ka tashi kawai, ya zaka iya rintsawa bayan bamu san halin da Aisharmu ke ciki ba?
Da sauri mama ta sada kanta dan ta ji kunya ainun na abinda yake fada domin da yanayin zolaya ne yake fadar abin
Mirmushi ya yi ya kuma dago da kanta ya ce" ki duba ki ga sakayar ubangiji da hakuri inda ya kai mu, mu ne a cikin wannan gida a matsayin malakinmu ga shago wanda kaf anguwarnan nan suke sari a matsayin malakina, harda masu gadin gidan da muke da mota da mai tuka mu,
Ina gannin godiya ga Allah shine abinda yafi dacewa da mu sai Allah ya kara yi mana haske a zamantakewarmu
Kanta kawai take gyada masa alamar ta gamsu da abinda ya fada.......
Tunda ta fara tashin hankalin nan ya tayar da sallar asubahi wanda tunda ta ga fitowarsa daga dakin Rauda take biye da shi tana rusa kuka tana fadan magangannun da ba wani anfani ko ya dawo da agogo baya ba
Yana salamewa ya kai dubansa wajen agogo, ya makara a sallah yau shi yasa ya yi abinsa a gida, a hankali ya bude alkur.ani ya kawo bakara ya bude ya shiga karantawa cikin nutsuwa
Bata dubi girman karatun nan ba, bata dubi irin lokacin da mijinta ya ware dan kusanta kansa da ubangijinsa ba , ta dage, ta murje idannuwanta tana tayar masa da hankali dan kawai ya kwana a dakin yar uwarta har tana yi masa ikirarin ya ji kunya
A hankali ya rufe alkur.anin domin a gaskiya karantawa yake aman du ta tayar masa da hankali baya jinsa yanda yake so
Dubansa ya kai kanta, wai tashin hankaline ya sameta du ta tsige acucin dake kanta ta yi firifiri da ita tana ta haikar baki har fadi take ita walahi yarinyar can ta yi kadan ta raba miji da ita, ita ba da ita ba zata yi sai dai ta yi da shi shi Sudais, shi Elhaj sudais, idan an ce ta hadu da shi a titi ne ta gaya masa irin maganar nan yayi imanin ko hada ido da shi ba zata iya ba, aman aure mai daraja ya sa har take iya kallon kwayar idannuwansa ta kafta masa rashin mutunci, kai da ba dan yana so wannan ranar ya wuni cikin farin ba da ya baiwa rashin hankalinta dama ya samu shima ya koya mata hankali ko ta daina tunanin girmansu daya ne
Mikewa ya yi ya canza jalabiyar dake jikinsa ya fito da niyar shiga dakin Rauda sai dai me ganninta ya yi a fallo zaune, duda cikin dabara ta dan karkace a zaman kamar ta bada salon zama ne ita kuwa tana kauce azabar da jikinta ke yi mata na radadi,
Wani irin fayau ta yi masa a ido, baiwar Allah sai ta dan kanance masa a ido,
A hankali ya nufe yana mai oyoyo da kanshinta dake yi masa maraba bai ma lura da Hafsat ba shi dai burinsa ya jingina da ita ya ji batu daga gareta
Humaira ce ta biyo bayansa tana girgizar jin masifa ta karaso har fallon ta iso tana taunar cingom ta ce" aikin banza wai ba sabon ba, ke nan har dadin miji kika sani? Yaushema ya aure ki? Ke har kin samu waje kin fito fallo kin hakimce ke ga matar gida ko
Da mamaki Sudais ya juyo wajen Humaira zai yi magana sai dai ya ji......
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
6⃣0⃣
A gagauce
........
Hafsat ce ta muke ta ce" sis tashi ki ga mu tafi
Da haushi Humaira ta ce" eh man sai ta tashi ku tafi, ku ai dangin miji haka ne , ku raka wannan ku raka wannan, to ni nafi karfinki yarinya banza kawai
Sudais ya kama habarsa a ransa ya ayanna ikon Allah, kaucewa nake kara takaloni take yarinyar nan
Hafsat ta girgiza kai, da ba fan tana tsoron yayanta ba yau da Humaira ta ga tashen iskanci, yau da ta bambance iskanci koyo da wanda aka iya, sakara da bata iya kishi ba, ita du iliminta du dadewarta a cikin gayu ashe a 0 ne?
Kokarin jan hannun Rauda take wace tunda Sudais ya fito ta sada kanta tamkar ba ita ce ta yi iya yinta ta tsala wanka dan su yi tozali da juna ba, bata so kwatakwata ya dauketa a wata raguwa, sai dai wata gungurmemiyar kunyarsa ta hana ta yi ido hudu da shi sai sisine kai take tamkar tana gaban sirikinta, du kuwa irin rashin mutuncin da matarsa ke girbawa sai ta kasa koda kallonta bare ta mayar mata da martani, kai ita bata ma tunanin zata iya tsayuwa ta biyewa wannan matar domin ta lura yar hayaniya ce, idan ta sako abu da tashin hankali ganninta a haka zata cin masa ko menene.......
Ido ta rintse ta samu ta mike sai dai ta kasa cirawa ta yi gaba
Hafsat da har ta yi gaba ta juyo, cike da jin haushin wai yaya yana jinta aman dan ya daure mata ya kasa tsawatar mata sai shuka iskancinta take son ranta,
Humaira ta ce" ba zaki taba fada a wajen mijina ba, domin kuwa koda ya radeki da abubuwa dan wani nufinsa ne, ko ya taba furta maki kalmar so ne?
Gaban Rauda ya fadi, idan ba a lokacin da yake sex da ita ba bata ji inda ya furta mata kalmar so ba, ya dai fadi magangannu masu sanyayar da zuciya irin inda ya ce da ita" *sai da ita rayuwarsa*, aman ai hakan kana iya gayawa mutun ko dan ya kontar da hankalinsa a kanka,
So take ta kawar da tunanika irin haka sai dai abinda da zuga, shedan ne ko meye ita dai wani abu na ingizata, fadi mata yake" hakane man, wannan ita kadai yake iya so, ba gashi ba tana fadar abubuwan nan ya kasa magana, ba gashi ba tana zage zage tana yayabawa kowa magana aman ya kasa tsawatar mata? Gata dai tsaye tana fadin komai ya kasa cewa ba haka bane
Shikenan ta saki jiki har ya kaita irin wannan wajen ?
Da wani kallo ta dago ta sauke idannuwanta saman kansa,
Ita yake kallo da tsumamun idannuwansa, a hankali ya tako inda ta ja ta