Showing 9001 words to 12000 words out of 122108 words

Chapter 4 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

408

mahaluki ya zage shi ko ya so fada masa maganar banza, ba gori ba ki dubi girman gidannan ke kin san koda bayar da motarki yayi idan ya tashi baki wata sai ta ninka taki a komai, hukunta ni ne zai yi ta wannan hanyar dan haka ki kiyaye
Ta karashe tana kara hade rai

Amina kali Aisha wacr har wani gumi ke tsatsafo mata a fuskarta ta ce" kawas kin ga yanda birthday din ya koma, zaku iya jira har a bamu motar ko kuwa tafiya zaku yi?

Da sauri Raudat ta ce" aa zamu tafi Baba yace kar mu yi yama , kin ga bamu san lokacin da zai hakura ba kar a yi mana fada

Amina ta tabe baki bata ce komai ba

Hafsat ta ce" ohk aman ku da kuka zo tare yanzu ai ba zaku shiga motar haya ba ko? Kun ga yanda yayana yaki jikin ya ga mace a cikin motar haya cakule da maza sai haka kawai yayi ta fada tamkar ya santa

Amina ta ce" basu da ita Ne motar!

Cike da mamaki Hafsat ta kalo wajen su Rauda, suturar jikinsu ta karyata abinda Amina ta fada a zuciyarta aman duda haka sai ta ce" kai freind hali dai yana nan, ki kali yannayin shigarsu ai suturar jikinsu zata sayi hudun taki domin wannan a wani shago a abuja na ga irinsu

Cike da jin haushin maganar hafsa amina ta ce" eh haka nima na yi mamaki , aman kuma basu da ita , ko keke basu da shi bale mota ke fa komai basu da shi.... kin san anguwarsu ne ? Yan anguwar......

*YA ISA* ! Rauda ta fada cike da bacin rai domin sun kaita bango, tun farko ranta ke jagule da irin kallon wulakacin da wannan wulakantacen yayan nata ya yi masu ya gama bata mata rai sannan a zo nan ana cicirasu daga cewa zasu tafi sai a kama fede su haka? Cike da bacin rai ta yi masu kalon sama da kasa , a gaskiya itama ta san hafsa ta hadu dan haka ta juyo wajen Aminar ta ce" eh gaskiya kika fada bamu da komai, mu ba kowa bane , bamu da ko keke ke naira dubu ta fi karfin kaf yan gidanmu bale mu! Sai dai da ace ke mai ilimi da kafin ki yi wannan maganar sai kin karewa *Halitar dukan mutanen dake wajen nan*, kin ga ai wata ta fi wata ta wani fannin wata ta fi wata ta wani, sai ki shaida *Allahn* kennan, wanda ya baki kudi ni kuwa nima ya bani arziki mai tarin yawa wanda na fi ki da shi , ta karashe tare Da kuro idonta farin ya haske su ta juyo wajen yayarta wace ta zama wata iriya ta ce" ai kin ga irinta, da ace kin barni a gida cikin mutuncina da ban yi doguwar tafiya marar anfani na tare a wajen da ba.a san darajar Dan adam ba,

Fuuu ta kama hannun Aisha tana janta ita kuwa tana biye da ita tamkar kwai ya fashe mata a ciki

Da sauri Hafsa ta bi bayansu tana fadin" i.m so sorry plz, ni tambaya kawai na yi

Rauda ta juyo ta ce" ni kuma amsa na baki Hafsa

Hafsa ta yi murmushi ta mikowa Rauda hannu ta ce" ki yi hakuri

Rauda ta sauke ajiyar zuciya ta mika mata itama sukai musabaha sannan ta rako su har wajen gate sukai salama har ta nemi lambar Rauda ta shaida mata bata da waya

Cike da mamaki ta juya , rana mamakin a irin kyan rauda aman bata da waya , lale ba irin yan matan zamani bace domin kuwa da irin wasu yan matan ce da ta mayar da baiwar kyan da allah yayi mata wa *JARINTA*

Haka suka fito suna tafiya a kafa, gashi wajen da mugun nisa kafin a iso bakin titi, baban tashin hankalin ma basu wani fito da kudi ba dan ba wace ta yi tunanin hakan zai kasance

Rauda tana dan gaba da Aisha domin tamkar an zare mata laka take tafiyar,
Can kamar an tsikareta ta kai kasa ta duke ta dora hannayenta bibiyu a saman kanta ta fasa wani uban ihu da kuka mai firgitarwa wanda ya saka rauda mugun faduwar gaba ta juyo da gudugudu ta karaso wajenta ta duka daidai da ita ta kama hannayenta tana tambayarta abinda ke damunta

Aunty Aishana, dan girman Allah ki yi hakuri in dai dan wulakancin da suka yi mana ne ai kin ga na rama mana ko? Ki yi hakuri da kukan nan haka kar zuciyata ta buga Aunty dan Allah ki tashi mu yi tafiyarmu ki yi hakuri haka;;;; Rauda ta karashe tana mai matsar kwalah


Aisha kuka harda majina ta sauko hannunta daya ta dora saitin zuciyarta, ta rintse ìdo muryarta na crac..........k.........in..........g ta ce" Walahi *INA SON SHI*!!!!!!!!!!



*READER SHIN KUNA FAHIMTAN RUBUTUNAN KUWA? KUN GANE INDA NA DOSA?*

Shin Wanene Aisha ke so???



*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*



6⃣



Na : *SAJIDA*





Tamkar zarara take acting, ta damko hanayen Rauda ta dora saman kirjinta cikin muryar kuka ta ce" kina jin yanda zuciyata ke bugawa? Kina jin yanda nake ji kuwa? Zuciyana fitowa zai yi daga gangar jikina, ki taimake ni, koda baya sona ni ina son sa koda zai yanka namana ne ya aureni

Bata san dalili ba, itama sai ji ta yi hawaye na bin kuncinta, sannan daidai da bugun zuciyarta ya canza irin ta tsorata da kalaman yayarta bayan hakan bai dace ya wani firgitata ba domin kuwa hakan ba abin mamaki bane idan ya fito daga Aisha

Cike da tsoro ta share hawayen da ya zubo mata, ta tataro nutsuwar dole ta dorawa kanta ta kama kafadun Aisha da dukan hannayenta ta tausasa murya ta ce" ki yawaita karanta innalilahi wa ina ilaihi raj.une , a bayane ko a boye a cikin zuciyarki, hakan zai saka ki ji sanyi

Tamkar wata yarinya karama ta dora kanta a saman kafadar Rauda tana sauke ajiyar zuciyar kukan fa ta sha

Shatttt mota guda uku bakake suka zo suka fice da gudun tsiya wanda ya saka Rauda saukin dago da kanta cike da jin haushi ta cire takalmin kafarta ta jefi motocin ranta bace domin dai da gabanta ya fadi daman tana cikin zulumin halin da yayarta ke ciki!

Tana ta lalamin Aisha ta mike su tafi motocin nan suka dawo a layansu irin na dazu

A tare suka dago da kansu dan gannin ko su waye haka

Lafe yake a bayan motar, ya zabga masu harara daidai fadiwar gabansu a tare

Raudat ta dago da yatsarta guda ta nuno wajen motar domin sai da yayi hararar kamaninsa suka fado mata, tabas shine mutumen da ya harareta wajen danja! Kwarai kuwa shi ne shi ne!

Takalmin da ta jefa masa ya bude glas din motar, hannunsa saye yake cikin gan ruwan kasa, kansa da hirami sai daukar ido yake ya mayar da wutsuyoyin bayan kansa

Fuskarsa cike da alamun kyankyami ya wurgo mata da takalmin suka juya bayan sun tada masu kura suka tafi

Wannan karron ba Raudat ce ke jan hannun aisha ba, Aishar ce ke jan hannunta cikin wani irin yannayi ta tsayar da mai adaidaita kafar Raudat guda ko takalmi babu domin sam bata saurareta ta saka takalmi ba

Suna karasowa ta sauka ta fada gida, Rauda ta nemi alfarmar yayi hakuri ta kawo masa kudinsa


Tamkar an yiwa Aisha mutuwa ta tarar da ita tana fadawa mamansu tana rusa kuka

Kudin mai napep ta dauka ta kai masa ta juyo ta shige dakinsu ta konta ta lumshe idannuwanta inda take jin muryar Aisha na fadin" wa gare mu umah? Mai gare mu,? Ko keke bamu da shi, bamu da fada a ji koda a kauye ne bale a cikin gari, Umah ta yaya zai so ni? Ta ina zan bi ya so ni?


Shafa kanta magaifiyarta ke yi, cikin sanyin murya ta ce' ba kin ce ELHAJ SUDAIS MALALE BA?

Aisha ta daga kanta

Mahaifiyarsu ta ce" in dai shi ne, banban dan kasuwa, yaron da yayi rantsuwar ba zai taba kasancewa kalkashin wani ba yaron da ya san kan nema, tabas shine dan gidan Omar faruk Malale tsohon ma.aikacin gwomnati wanda dalilin wani wulakanci da aka taba yiwa mahaifinsa lokacin ya taso sosai yayi rantsuwar ba zai kasance karkashin wani ba


Aisha ta dago cike da mamaki ta ce" umah a ina kika san labarinsa, ? Kin kuwa gane da wa nake magana? To ya aka yi kika fahimci cewar da shi nake bayan ni ba hotonsa na gwada maki ba, sunansa kawai na fada maki sai kwatancen gidansu da kadan daga cikin dabi.unsa aman har kika gane? Umah wannan fa da ganni mahaifinsa wani gagarumin mai kudi ne domin jikinsa bai san wahala ba, bai taba saninta ba ,


Daidai wannan lokacin Hafsa dake kallon Kawarta Amina wace ta wuni a gidansu har dare na kokarin yi, take shaidawa Hafsa cewar itafa zaman jiran nan da take harda soyayar yayanta a zuciyarta, da a ce zai so ta da ta more rayuwarta

Murmushi hafsa ta yi ta ce" ni ba zan hana ki ba, domin ban san ko ke zaki zamo ta farkon zabinsa, aman abu daya zan iya fada maki shi ne yayana yana da *aure* iyalinsa na saudiya domin yafi jin dadin zaman kasar fiye da ko.ina a duniya


Amina gabanta ya fadi" ta furta yana da aure fa kika ce? Aman shine yake tare da lafiya haka ?

Cike da mamaki hafsa take kallonta ta ce" ban fahimci yake cike da lafiya ba?

Amina ta sauke ajiyar zuciya ta ce" to ai abin ne, na ga mafi yawancin masu auren nan zakina ganninsu tamkar a firgice suke, ko me yasa haka oho??

Hafsa ta yi murmushin shirmen Amina, ta ce" ni kam ban taba irin wannan luran ba, abinda ma na lura da shine idan ka yi aure ai ka zama cikaken mutun , nutsuwa da konciyar hankali na tabatuwa a gare ga, bale idan ka yi dace da abokin rayuwa nagartace

Amina ta ce" kin ga kawata mu bar maganar nan, dan kuwa a yanzu na tabata ya fi karfina

Bayan Hafsa ta raka Amina ta dawo ta je wajen kakarta ta zauna suna hirarsu cikin nishadi

Can ta nisa ta ce" granny, kin ga wannan kawar tawa da na raka ta karshe cewa ta yi tana son yaya,

Karkar hafsa ta yi tsam can ta yi murmushi ta ce" Hafsa, wai kina nufin uban gida? Aa ai ba zai taba son yarinyar da ta kale shi ta fara sonsa ba, ba zai so yarinyar da take irin shigar wannan ba, ba zai kaunaci yarinyar da zata iya take kunyarta har haka ta bayana abinda ke ranta ba domin kuwa shi din wani mutun ne mai wasu irin halaya, komai nasa yana son ya kasance special.....baya son abinda kowa ya sani .......



*Wanene Sudais?*

*SUDAIS* ya kasance jikan Ramatu da Saidu, dan Muhammad da Fadima, kanin Bilkissu sai marigaya Shafa, Rafi.a, yayan *Hafsa*

Muhamad ya kasance tsohon malamin makarantar boko secondary shi da matarsa Fadima
Da wannan aiki suke rufawa kansu asiri harma su dan taimaki dangi
Tabas arziki basu gade shi ba, basu da shi basu da dalilinsa domin wannan aiki nasu gaba daya albashin nasu bai taka kara ya karya ba

Bayan aurensu shekara na zagayowa Fadima ta haihu ta samu yarta mace mai shegen kyau aka saka mata bilkissu, tun daga nan sai haihuwar ta kasance mata tamkar riritsa, shegara na zagayo ta sake haihuwar Shafa, sai Bilkissu Sai *SUDAIS*

Yayansu sun taso cikin rufin asiri da konciyar hankali, kafin mai faruwa ya faru

Sudais ya taso da wani irin hali wanda dalilin haka mahaifiyarsa ta yi ta shiga asibiti domin kuwa sai da ya kai shekara biyu kafin ya fara dan cicira magana, da farko sun yi tunanin ko kurma ne?
A shekara hudu ta kan zaunar da shi ne gaban dan karamin akwatin tvn su ta kamo masa tashar larabawa domin a abinda ta lura yana kaunar irin tashohin dan ya fi zama ya barta ta yi ayukan gabanta idan ta kuna masan
Shekarunsa na karuwa ne maganar bakinsa ta fito ra

Idan ka kali halitar Sudais ya dauko kamanin kakan mahaifiyarsa domin buzun mutun ne kakarfa irin tsofafin rebel din nan na can cikin garin Timiya dake wajen Agadez, mutun ne dogo sambal, duda ya kai tsufa fata du ta yakune abinka da farin mutun mai nuna tsufa, aman da ka kale shi zaka ga cewar wannan ba karamin basamuden mutun bane, sannan har ya mutu ba zaka ce ga inda ka ganshi zaune ba rawani ba ko yayansa na cikinsa ba zasu shaida irin ranar nan ba sai matarsa wace ta kasance sirinsa ta biyu
Sanadiyar auren mahaifiyar Fadima ya zubar da makaman yakinsa dalilin mahaifinta da ya kasance tsohon malami shi ya nusar da shi ya bashi auren yarsa bisa salatin annabi Muhammad sallalahu alaihi wa salam a matsayin sadaki
Kakan Sudais mai sunna *KULLEY* har ya mutu damatsunan hannunsa basu sauka ba domin halitarsa ce haka ba wai da karfi ya mayar da jikinsa haka ba,
Mutun ne dirare, tsayaye, gashin kansa kuwa har kitse masa mahaifiyar Fadima ke yi (paix a ton ame grand pere Kulley🤧)

Wani lokaci Sudais ya zarce shekara goma suna zaune da mahaifansa ya kali mahaifinsa ya ce" Aba, ina son shigar larabawa, Aba zaka kai ni kasar latabawa na rayu a can?

Wannan magana ta daki zuciyar Muhammad mahaifin Sudai, domin sudais bai taba nuna bukatarsa a komai ba, bai taba nuna so ko kin abu ba asalima bai taba nuna yanada sha.awar rayuwar kanta ba sai dai yakan kure balaraben da ya gani da shigar larabawa harma ka ga alamar yana sakin murmushi

Abansa bai iya furta masa kalma daya ba sai mamansa ta kamo hannunsa ta ce" Sudais, ka yi ta adu.a Allah ya yasare mana ta hanyar da bama zato bama tsanmani ka ga sai Aba ya kaika Kasar larabawa , wai shin ya akayi kake son kasar larabawa?

Ya dago da kansa ya ce" momy dan fiyayen halita balarabe ne, sannan a shigar larabawa daga ta matan har ta mazan ta kasance kamilaliyar shiga, kin ga a tv ko idan mun tafi masalaci da Aba zaki gansu ne sun saka doguwar jalabiya sun dora hirami, Insha Allah zan kasance mai yin irin shigarsu idan Aba ya saya min

Murmushi ta saki, ta dago tana kallon mijinta dan ta basar da yannayin da yake ciki ta ce" ka san wani abu kuwa ABU SUDAIS?

A hankali ya girgiza mata kai, ta ce" idan na kali yannayin Sudais bayan kama da yake da baban cikin gida ( wato mahaifinta) harta yannayinsa ya dauko, duba da shirunsa, da murmushinsa, da kawar da kansa a kan dukan abu koda yana tsananin so, ka ga fa hannayensa yanda suke mulmulewa

Murmushi Muhammad yayi ya ce" *SADAUKINA* Allah ya raya Uban gida

Daga nan suka ware suka ci gaba da hirarsu, aman tun daga lokacin du wata idan ya dauki albashi yakan siyowa Sudais jalabiyoyi farare karkar masu karamin kudi da samon hirami tun daga lokacin yannayin shigarsa kennan

Rayuwa na juyawa, tafiya na kara nisa, a cikin shelaru biyar da suka karu an samu ci gaba an samu jin dadi an samu mace mace ciki harda mahaifin Fadima, sannan an saka auren yan mata ukun nan cikin ikon Allah Allah ya fitar masu da miji a tatare wanda da mai shekara goma sha biyar rafi.at, da mai shekara goma sha shida Shafa, sai mai shekara goma sha takwas Bilkissu kowace ta samu mijinta mai mutunci har an saka rana

Bakar rana wace ta zo masu da canje canjen rayuwa ta sanadiyar zamowar Sudais zakara
Aure na sauran kwana biyu , sai shirye shirye ake... daidai karfinsu sun ciru sun kulu sun yiwa yayansu kayan daki daidai gwargwadon iyawarsu
A ranar juma.ar nan suna farkawa Gaba dayansu sun tashi da wani irin yannayi, gidansu kuwa har ya fara cika da dangi da aminan arziki

Rafi.at ce tsugene kusan mahaifiyarsu, ta ce" umana yau baki saka mana albarkar ba fa

Fadimatu ta dago ta yi murmushi ta dan jawo kuncinta ta ce" ai yau du sai na tashi da mutuwar jiki Rafi.at, a kulun nakan saka maku albarka safe da yama, Allah yayi maku Albarka ya yafe maku kurakuranku na jiya da yau da safe da wanda zaku yi nan gaba,

Murmushi ta yi ta ce" umanmu yau zamu tafi

Haka kawai ta ji gabanta ya fadi da maganar rafi.at ta ce" ina??

Rafi.at ta ce" ummah fa, wajen aunty? Da ta ce yau ya kamata mu je mu karbo sakon gaba dayanmu har mun shirya aunty bilki ce take ta jan jiki har yanzu

Mahaifiyarsu ta yi murmushi ta ce" ai fa sarkin nawa, ita kam akoy sanyin jiki ai

Suna tsaka da maganar Shafa ta fito, haka take daukan ido domin itama ta dauko fatar kakanta sosai ga tsayin gashi har baya,
Abaya ce ta saka mai ruwan ash coler sai ta kara haska fatar nata
Itama tsugunnawa ta yi suka saka mahaifiyarsu a tsakiya suka ce umah bara mu yi selfi

Ai kuwa suka dauki hoto,
Suna tsaka da yi sudais ya shigo, da yake gaba dayansu ya fisu tsayi da kakarfan jiki sai ya kasance shine karami aman suna shayinsa, gashi ba sake masu yake ba

Rafi.at ce ta yi kalar tausayi ta ce" broh ka zo mu yi hoto plz

Haka kawai ya ji yana son yayi hoton dan haka ya shiga suka yi su hudun

Wayar Shafa ce ta dauki kara ta daga , bayan ta kashe ta ce" umah mu tafiya zamu yi, kinga sai gagawa ake aman mu muna nan kar su tafi ba.a bamu sakon ba zamu karbo mata nata kawai

Mikewa ta yi tana wani irin sauki ta kama hannun Rafi.at ta ja da wani irin karfi na mamaki tana fadin mu tafi....

Fadimatu tana fadin" baku karbi kudin napep din ba fa aman ina har sun fita kofa
Da sauri ta mike tana fadin" ka ga sudais zo ka karba ka kai masu

Shima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login