Showing 63001 words to 66000 words out of 122108 words

Chapter 22 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

415

yi tana ayanna dole na guji fushin ubangiji kafin mu fahimci juna ka sake ni!

Kamar barauniya take sando kar matar gidan ta ganta ta wajen training din wanda daga sama aka rubuta shi din ma kofar dai iri daya ne

Dana open ta yi ta tura Da hannunta na hagu ta shiga
Tana shiga ta dan dakata tana raraba idon inda zata ganshi

Saman wani tapi ta ganshi yana ta abdomino yana dagawa yana komawa muscle dinsa sun firfito, hannayensa tamkar na dan dambe yana yi

A fili ta furta" tap! Tana zaro ido wanda bata san ta fito ba sai da ya dakata ya juyo da sauri gefen da take tsaye

Tun daga yan yatsutsanta dake fili ya bita da kallo har fuskarta, ta sada kanta ita bata karaso ba ita bata juya ba ita bata ajiye kayan ba

A ransa ya ayanna aa, yarinyar nan waima me take boyewa da take fama da hijabi tamkar wata mai takaba, daga ni sai ke a waje ki wani zumbulan hijabi to ko tubewa kikai kin isa ki girgizani ne?

A dan harzuke yayi tima ya mike tsaye ya karaso inda take
Ba tare da ya yi magana ba ya mika hannu ya karbi tiren ya ajiye nan gefe

A hankali ya saka hannayensa biyu ya kama hijabin nata tun daga kasa ya shiga kokarin cire mata

Idannuwanta ta kwalalo cike da tsoro ta yi saurin dafe hijabin ta shiga jujuya ido tamkar zata sume tana kokarin yi masa magiya tana jujuya kanta irin kar ya cire

Nuna mata ya yi bai san yarenta ba, gannin tana ta kicikicin ya matso sosai daf da ita ya dage hijabin har wajen wuyanta ya furta" *ke, ki daina tunanin shirme mana, duniya sai ta nuna nake shanta!*

Yana maganar ne yana idasa cire mata hijabin wanda dan karfin da ya saka ya sa ya biyo da ribom din da ta daure gashinta da shi, ta yo luuu zata fado masa ya ta yi saurin rike kanta ta ja da baya ta juya masa baya jikinta na rawa ta saki kuka mai karamin sauti ta tsugune jikinta na wani irin rawa

OGA ELHAJ SUDAIS dai bai gane komai cikin mutuwa ya yi ko sumewa ya yo a tsaye a wajen ba,
Wani irin zaro ido yayi ya sauke daradaran idannuwansa a kan halitar Rauda,
Rauda ta kasance irin matan na masu diri, tamkar yar gwari haka duwaiwanta suke manya da su , tsatsonta kuwa dan firit sannan mamarta su ba manyan nan ba su ba kannanuwa ba a tsakatsaki suke ,
Gaba daya halitar jikinta sun yi daidai da tsayinta sun yi mata das sai idan tana tafiya ne jikinta rawa rawa yake tamkar iska na kada saka

Yana nan tsaye tamkar bashi da jini ta rarumi hijabinta ta saka ta juya da gudu ta fice a wajen training din wanda fitarta kawai ya gani ya zabura ya.......





🤣🤣🤣🤣🤣🤣


*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




3⃣5⃣




*Na fans na lv❤❤, ku yi min hakuri kunai min uzuri, abubuwan ne da yawa aman a koda yaushe burina na samu isahen lokacin da za.ina typing kulun, ku yi hakuri da wannan a yanzu in sha Allah za.a kara . Fatan za.ai min uzuri*

*IDAN KA RAINA INDA KA KE GRUP, KUN SAN ME? JI NAKE DA KU, KUNYARKU NAKE SOSAI, KU YI HAKURI DA RASHIN JINA KULUN, ZAN GYARA DA YARDAR ALLAH, MUNA MUGUN TARE ... COMMENT DIN KU NA SAKA NI NISHADI*


SADAUKARWAR WANNAN PAGE ga *SALMA, SHALELE, MRS SHUBADO, AISHA*





Yana nan tsaye tamkar bashi da jini ta rarumi hijab dinta ta juya da gudu tana sakawa tana kuka ta fice a wajen trainin din wanda fitarta kawai ya gani ya zabura jin zai dima a kas ya raruri keken gudu😁 na sports ya damki karfen da hannunsa daya inda gaba daya jikinsa ya dauki rawa

Sudais dai bai san adadin lokacin da ya dauka wajen training dinsa ba sai gannin Humaira ya yi ta shigo ta sha doguwar atampa mai kalar ja ja ta sha mak.up dinta sai kwarkwasarta take

Karasowa wajensa ta yi tana fadin" husband, me kake haka a tsaye har lokacin office ya yi direba (tana nufin Samir domin biyayarsa da dadin sha.anninsa ya saka Sudais ya dauke shi suke yawo tare ba dan haka ne aikinsa ba sai dan aminci da yarda domin Samir ya karanci bincike ne shi ba lauya ba aman idan ya sako abu a gaba da yaradar Allah sai ya san me ya kumsa) ta ci gaba ya zo daukanka har yana falo a zaune, ni ina mamaki du yanda kake yiwa mutane iyaka da gidanka shi wannan har damar shigo mana falo yake ka kasa tsawatar masa

Idannuwansa ya lumshe ya bude ya sauke su kan fuskarta, kallonta ya yi tun daga sama har kasa, gaba dayanta firit da ita wai kuma a nan ta cicika abubuwan da ta cicika

A hankali ya cika karfen ya juya cikin takunsa na kakarfen namiji aman jiki du a sake ya dauko tawul din ya dora shi a kafadarsa kawai ya zo ya ratsa ta gefenta ya fice,
Domin ta bashi haushi sam ita ba zata gyara halayenta ba? Ya zata shigo masa waje ba salama, ta zo bata gaishe shi ba bata ji ya ya tashi ba , ba wani magana cikin sanyi aa sai kace tana magana da kanninta ta zo ta yi masa tsaye a ka tana zazaga masa magangannu mararsa tsari kuma ita a nan fada take da gaskiyarta, to ke mace ke ya dace idan kin san da wani a gidanki da ba muharaminki ba ki lulube jikinki , ta fito ta gabanshi haka bata ji kunya ba sai shi ne zata zo ba tare da ta lura da yannayinsa ba ta rufe shi da surutu , shi kam ba za yana zama kulun yana fama da fada mata magangannu ba, shi ba sakaran namiji bane ta ci gaba da yi

Bayansa ta biyo tana dan daga kafa, sarai ta san yau ba aikinta bane aman burinta ta je ta tsare shi kar banzar nan ta kusanto inda yake domin sarai ta san tunda aka kawo Rauda gidan bai taba hada shinfida da ita ba dan kuwa kulun tana biye da su

Har dakinsa suka shiga, ta zauna saman kujera gannin yana shirin shiga wanka

Da ido kawai take binsa ya dauki tawul ya cire baban wandonsa daga shi sai.......da ya sasaka ya tatatare.....abin nan ya nufi bayi dan yin wanka

Sudais ya kai minti arba.in yana fama da ruwan sanyi , ya zuba ya kuma zubawa aman shiru ba alamar za.a sada masa, ba alamar za.a bar shi ya samu nutsuwa

Cike da tsaki ya nado baban tawul dinsa ya karewa kansa kallo ya fito yana kara tamke fuskarsa

Gannin halin da yake ciki a kasan zuciyarta ta ayana jarababe, shi dai kulun a cikin jaraba yake

Aman da yake abin nata na neman fitina ne sai ta mike ta nufe shi, ba tare da ya ankara ba ya jita a jikinsa sannan ta nemi wajen da ya fi tsayar masa da tunani a wannan lokaci ta aniya hargiza masa tunani

Sosai ya so hawa cajinta domin ya jima yana cikin bege, kwata kwata ya manta cewa ma ba ranarta bane yau, a inda yake tsaye ya lumshe idannuwansa yana sauraron lamarin da matarsa ta kai shi

Kira ke shiga yana fita a wayar Samir ana tambayarsa oga, domin babar harka ce ta taso kuma gashi har karfe tara da kwata ba oga kuma ana ta kiran numbersa tana ringin aman baya dagawa dan haka aka shiga kiran number Samir domin suna kyautata zaton ko baya tare da shi ya san inda yake

Dan murmushi samir ya saki ya ce " Hafsat, ko dai Oga ya fita?

Hafsat ta waigo gefen Da samir ke zaune , ta kuma kallon kofar dakin Sudais, a ranta ta ayana aa bai fita ba, ban ga fitarsa ba fan haka ta mike ta ce da Samir tana zuwa ta nufi dakin Rauda dan ta zo ta dubo masa domin ta san yau zuwan RAUDAR ne

Da kyar da sidin goshi Rauda ta mike a koncen da take Hafsat ta fada mata bukatarta inda Rauda ta zazaro ido tamkar ta ga dodo ta ce" ni ni kuma? Ni zan shiga dakinsa? Na yi masa me? Aa, dan Allah ki yi hakuri kar a je na jawa kaina matsala bayan wace nake ciki,

Matsala Rauda? Mijinki ne fa? Kin kuwa san irin girman darajar da Allah ya bashi wace ya umarce ki.ke matarsa da ki yi masa biyaya?

Rauda cikin tsoro da barar da baki ta ce" ke kin san me kike fada kuwa? Ta sha ikirarin sai ta kashe du wanda ya rabar mata abin kaunarta, sai ta ga bayansa, ta sha harowa mama cewar wly ta ba wasa take ba du wace ta yi gigin rabar shi sai ta halakata, ni ban taba sonsa ba, bai taba birgeni ba, ni ba tsarana bane ya fi karfina, ban taba sakawa zuciyata cewar ko na second daya zamu kasance mata da miji ba, nata ne , nima nawa a wani wajen ki yiwa girman Allah ki daina irin wannan maganar na tabata da ta sani da tuni na ganta na tabata haduwar mu ba zatai kyau ba, ina nan ne ina jiran Abana ya neme ni ya raba wannan hadin domin shi kansa bukatarsa kennan

Hafsat mamaki da firgici ne ya darsun mata a zuciyarta, me hakan ke nufi? Matar da yaya ke matukar so da ita bama ta sonsa ko me? Sannan tsananin tsoron Humaira ne ya sakata irin wannan rikicewar? Sai kuma da ta furta daman shima baya so! Maganar ta yita a cakule ba tare da ta banbance wa ba? Abanta ko yaya Sudais?

A hankali Hafsat ta karasa kusa da Rauda, ta kamo hannayenta ta jawota bakin bed suka zauna, kan rauda a kas tana ta shesheka da ganninta cike take da damuwa, sannan Hafsat ta girmi Rauda domin tsarar su Aisha ce, sai kuma yannayin tsoro da ta karanta a tatare da Raudat
Ajiyar zuciya ta yi tana kalon yannayin Rauda, a kasan zuciyarya ta ayanna tabas girman rauda shekara 22 ya rigayi wayonta, koma wacece ke firgita Rauda harda wautarta, sannan da kuma ta karanci du irin tarin dukiyar nan ta gidannan da irin dukiyar da Sudais ya zuba masu sam baya dadata da kasa, da wata ce da ko dan wannan daula ta zauna, sai babar rigimar ta lura kwatakwata a yanzu Rauda bata son yayanta kuma bata san shi irin son da yake yi mata ba, da ta san irin yanda yake kokarin dane soyayarta karta fito fili ya zama tamkar zautace da ta ingiza zuciyarsa ya haukace mata ta ja linzaminsa,
Abu daya zata iya yi dan ceton rayuwar Yayanta domin ta fahimci soyayar wannan baiwar Allahn tana tafe ne da bugun zuciyar Elhaj Sudais Uban masu gida,
Tabas Rauda itace uwar gidan uban masu gida

Murmushi ta sakarwa Rauda bayan ta mika mata ruwa mai sanyi ta sha tana sauke ajiyar zuciya

Hafsat ta mikowa Rauda hannu ta ce" freind????

Rauda ta tsare hannun nata da kallo, freind fa, da wannan? Kawance?

Hafsat ta ce" ki gane, ita rayuwa ba zaka ce kai zaka kare kai kadai ka ishi kanka komai ba, ina gayatarki kawance dan na kama maki da adu.a da shawarwari idan kin yarda da ni dan Allah ya magance maki damuwarki

Rauda kam ta yi tsai ta fada tunani, shin ta aminta da kawancen wannan baiwar Allah wace take kanwa ga mijin da aka aura mata ko aa?


Sudais na karban sakon Humaira, idannuwansa a lumshe ta rungumo shi ta gaba wajen kirjinsa ta cusa wuyanta cikin wuyansa ,
Wani doyi doyi na ruwan wanka wanda ke bayar da mugun doyi domin atach ne dadage a kan nata ga wanka da ya wajaba a kanta yau da gobe hakan yake saka mata kan na doyi

Kansa ne ya ji ya sara masa, a hankali yake bude jajayen idannuwansa ya sauke a kanta, dan kwalin atampar nata ne ya fadi dan haka warin ya dake shi sosai

Hannunda ya sa ya cireta daga jikinsa ya daga kafarsa da kyar dan ya koma bayi ya kuma yin wanka ya tafi , sai dai ta kara rike shi tana kokarin kuma like masa a jiki

Cikin karaji ya ce" get out of my room! ( sorry fa za ina saka freinch, turancin nawa ba cancan bane🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀)

Da sauri ta ja baya kirjinta na dukan tara tara dan tsoro domin ya rikide mata wani kala

Da gudu gudu ta ja dan kwalin nata ta nufi kofa ta bude da mugun sauri ta yi dakinta wanda Samir dake zaune ya rakata da kallo, ba Hafsat din, ba Sudais din. Ba .sannan ga hajia matar oga ta fito tamakr an biyota da gudu......
Girgiza kai ya yi ya kuma buga number Oga

Sudais bayan ya yiwa humaira tsawarnan ya ji juya na dibansa, kamar da wasa ya tafi luuuuuuuuii ya fadi nan wajen bed dinsa domin kwatakwata jikinsa ba karfi sannan tamkar ana zare masa laka,

Idannuwansa yake sonbudewa tun karfinsa yake kokawa dan bude idannuwan nasa dan da ya lumshe su ita yake gani daidai inda ya cire mata hijab, da tsugunnin da ta yi da kuma mikewar da ta yi ta fice da gudu aman ya kasa , da karfi ya dago hannunsa na dama ya shiga dukan gefen zuciyarsa a fili yake ayanna inalilahi wa.ina ilaihi raj.une, ya Allah na tuba walahi kaina ba zai iya dauka ba, Ya Allah ka sanyaya min wannan damuwa tawa, Allah kana gannin halin da nake ciki,
Ban aureta dan wani abin na jikinta , na aureta ne dan inai mata tsatataciyar soyaya... ya Allah yanda ka saka min kaunarta ta hana ni zama ka saka mata ya kasance ko ruwa zata sha sai ta tuno ni , Allah ta damu da ni, ta raine ni
Dan nishi yake fitarwa dan kokari yake ya mike daga faduwar aman ya kasa bashi da karfin hakan, gaba daya karfin jikinsa ya fice
A hankali jikinsa ya fara daukan zafi domin zafi da yawa ne ya hadun masa,
Hakura ya yi da yinkurin tashin yana sauraron yanda wayarsa ke kuka ,
A fili ya kuma furta" *sonki kawai nake Rauda, ban aureki ba dan wannan.... koda kin kasance dumniya mai girma da kokarin saurin nuna ba zan shata ba sai ta nuna, (ko????🤔🤔)


Daya daga cikin vigil din dake gadi a gidan mahaifan Sudais ne su Aisha suka tsatsare ,
Shima gannin yan mata masu kyai sai kwarkwasa suke ya saka ya biye masu domin suna irin haka yan mata na zuwa takanas dan su samu shiga su ga oga Sudais, wasu su ga gidansa , wasu neman nember wayarsA da sauransu a haka suke danfarar yan mata da yawa suna anfani da su ba biyan bukata domin su kansu basu da numbersa wace yake dagawa sai fixe

Fuska ya yatsine yana nuna shima wani ne jin sai tambayoyi suke yi masa sai kace sun ajiye shi

Aisha ta matso kusa da shi sosai ta ce" bawon Allah ko dai ya koma Saudiya ne? Na zo na zo ya fi a kirga wasu sun ce min yayi tafiya, wasu sun ce ya kaura, wasu aun ce yana wajen aiki , ka yi hakuri ka sanar mana inda yake dan girman Allah

Haka kawai yake gannin wautar Aisha, shi yana mamakin zamani koda yake ba abin mamaki bane suniyar ce ta dawo haka,
Cike da kufula ya ce" malama kun ga ku kara gaba, oga fa ya tashi daga nan iyayensa ke zaune a nan ya koma sabon gidansa a can GRA, sannan jita jita ana fadin ya auro wata yar sarki sun tare da tsoruwar matarsa

Daga Sarah har Aisha mutuwar tsaye suka yi , Aisha ta dago da sauri ta ce""""



*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




3⃣6⃣

*i.m sowi readers, babyna ke asibiti, yanzu ma na rubuta ne dan na isar da sakon, insha da an sake mu zakuna jina a kai a kai, muah ummu lallace💓*




Daga Sarah har Aisha mutuwar tsaye suka yi, Aisha ta dago da sauri ta matsa kusa da Mutumin ta mika hannunta ta damko nasa a kidime domin ita ba ta wani ta taba namiji take ba ta ce" bawan Allah ka san kuwa wa nake nufi? Ina nufin Elhaj SUdais Uban Masu Gida wanda matarsa ta mutu yau kwana talatin da hudu, wanda matarsa daya kwal,

Hannunsa ya janye da karfi domin har wani matse masa hannu take a kidime ya ce" kin ga, ki kama gabanki malama kin wani zo kon tsaya min a ka kina min zuba ke ba wani abin kika ban ba sai yawan magana kike sakani sannan idan aka yi katari Oga ya biyo gaishe da iyayensa ki jaza min fitina, ki kara gaba kawai

Yana gama fadar haka ya juya da haushi haushin bai samu hadin kansu ba

Sarah da ta fi Aisha jin bakin cikin wai Sudais yayi aure!

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login