Showing 6001 words to 9000 words out of 122108 words

Chapter 3 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

409

muryar mahaifinsu ke fadin" du abinda kike shuka min a gaban idannuwan yayana ina kawar da kai ne dan a yanzu sun girma sun kawo mizanin rike du abinda muke aikatawa, idan har na biye maki zamu dawo ne muna raba masu abin kunya , ki sani du talaucina , munina kamar yanda kike fadi ina da galihu, nima mutun ne, ba tsananin soyayarki bane ya saka na kasa daukan mataki a kanki sai dan idannuwan yayana kawai, domin ina jin kunyar daya cikinsu ta bude ido ta ga na aikata abinda zai bata kunya shi ya sa nake fama da karfina nake neman abincin bakina da na iyalina dan gobe kar a zage su, ko yau na mutu bani da bashin kowa a kaina sannan ba wanda zai jefe ni da kalmar na taba cutar sa, na iya talaucina, yanzu tun muna mu biyu ki sanar min inda kika samo makudan kudin da kika yiwa yaran nan wannan siyayar domin dai ni a sanina danginki har yanzu basu gama sake maki ba bale su baki , ke kuwa sana.ar mai kike? Banda kawaye da kika tara wa.inda suka fi kargin mu.amalarku?
Ki sanar min , idan kuwa ba haka ba kin ji na rantse ba zasu yi anfani fa suturun nan ba koda kuwa sune zasu daura auren ( domin ta cewa baba wajen aure zasu tafi)

Du irin taurin kan mahifiyar su rauda idan mijinta ya juye mata tana shakarsa domin kuwa mutun ne mai hakuri bai iya fushi ba

Cikin sanyin murya ta ce" aunty salma ce ta kawo masu tun tafiyarta dubai da mijinta, da ta bani sai na ce ta ajiye min domin idan na kawo masu tun a lokacin zasu iya sakawa ne su je makaranta , ga kayan kuwa masu kyau ne , shine yanzu da suka fada min maganar tafiya wajen auren nan na je na karbo

A yanda ta yi maganar sosai ya shagaltar da baba, har ya tino masa zamanin da idan magana ne ba zaka ji muryarta a dage ba, shi ya sani yau da gobe da zugar mutane ne ya sa tun bata damu ba, tun bata kulawa har ta dawo ta fara kulawa

cike da mutuwar jiki ya daina fadan, ya jima yana kalonta sannan cikin sanyin murya ya ce" *shin mai ya sauya maki dabi.unki kyawawa wa.inda suka saka nayi maki lakabi da mar.atun saliha? Mugayen kawaye ne suka yi tasiri a kanki ko ke kanki ce kika raina inda kike? Ummu Rauda Allah ya ganar da ke*
Yana gama fada ya fito ya bar mata dakin da wannan tsohon daren

Jinginar da bayanta ta yi a jikin bangon dakin, a hankali ta sulale kasa tana sharar hawaye, murya kasa kasa ta ce" laifinka ne, komai na zama laifinka ne, ai ba mai son wahala, sai da aka yi maka tayin sana.a ka zo dan girman kai ka nuna aa kai ba zaka yi ba, ba ruwanka da irin damuwar da muke ciki kai dai kanka kawai ka sani , kai a tunaninka a haka zaka aurar da yaya yan mata har biyu? *Ai dole na kara baiwa dangina hakiri kan irin kuskuren da na tafka a baya domin a yanzu da na kuma samun gardin jar miya ba zan dawo na rungumeka mu kare da karnin rana ba* !


A hankali Rauda ta shafa adu.a ta koma ta konta, ita kam dan bata da yanda zata yi ne domin sam tafiyar nan bata yi mata ba ! Cike da adu.ar daidaituwar tsakanin iyayenta ta yi baci

Tun karfe tara wayar Aisha take ringin da sauri ta fito ta daga amina ce take shaida mata tafa yi sauri ta shirya

Cikin gagawa take kara kyalkyale fuskarta tana duban Rauda wace ke shiri cikin nutsuwa , a dan hasale ta ce" yanzu lalana dan zaki rakani ne kike komai cikin sanyin nan? Ki daga kafa kinga dai birthday din nan na surprise ne, kuma an ce karfe goma yake farkawa daga baci ya motsa jikin minti ashirin kafin ya fito kin ga ki daga kafa kar a yi banda mu

Bata bata amsa ba sai tsaki da ta ja cikin ranta ta saka rigarta doguwa mai ruwan peak color , riga ce da ta sha adon duwatsu farare karkarkar kananuwa tun daga wuyanta har kasa an bi an yayarfa masa duwatsun wanda hakan ya karawa rigar kala , sai banban mayafi domin irin rigar larabawan nan ce masu mayafi da kyan fasali da tsada yayar Mahaifiyar su Rauda ta yi masu tsaraba da yayanta
Rigunan kala bibiyu ne bakake biyu sai blue da peak Aisha ta dauki baka guda da blue ita kuwa ta dauki peak din da bakar

Bata yi kwaliyar komai ba sai yar hoda da ta murza kadan sai jan baki pink sai ta dan furta kwali a idannuwanta

Gashin kanta ta kama ta tufke a bayan kanta ta saka ribom dinta fari ta daure sannan ta dauko mayafin ta gyara shi ta ninka shi yanda zai yi mata dadin dauri sannan ta daidaita ta dora shi a kanta ta yane kanta da shi ya kasance ya rufe mata gashin kanta sai yayi irin yanda larabawa suke

Sosai wannan riguna suka karbi jikin su Rauda, domin daga sama sun dan matse daga bakin kugu suka bude sai hakan ya hau da yannayin tsarin halitar jikinsu wato coca cola

Kiran amina na ba adadi ya saka Aisha wartan pos ta fice tana fadin idan kika dora wasu mintunan zan yi tafiyata

A haka itama ta fito, bakin takalmi ne a kafarta mai dan tudu kadan


Sun yi tafiyar a kallah minti talatin kafin suke shigowa anguwar gra

Kofar wani gida suka ja suka tsaya

Dane horn Amina ta yi wanda hakan ya baiwa masu gadin kofar damar jin da mai son shigowa

Daya daga cikinsu ne ya fito ya karaso wajen motar ya ja ya tsaya
A hankali Amina ta sauke gilashin motar tana kallonsa

Fuskarsa a hade ya ce" takardar shedar ke yar familly din ce

Baki sake suke kallonsa, Amina ta ce" ko dai mun yi batan kai ne, shin ba nan ne gidan su *Hafsa* ba?

Bai saki fuskarsa ba yace " eh, aman dokar mai gidan ce idan dai kai ba na gidan bane baka da carte din shedar kai dan gidan ne sai ka yi kiran number oga yayi kiran mu ya bamu izinin ka shigo da mota idan ba haka ba kiwa sai dai ka shiga a kafa koda kai wanene idan kin kula ga motoci nan na kawayen madame domin abinda take shiryawa bata so oga ya sani

Cike da mamaki Rauda ke binsa da kalo garjejen kato wanda ko jayaya ba zaka so yi da shi ba, kofa maganar ne zaka yi gudun yi da shi

Ajiyar zuciya ta sauke da ta ji Amina na koda wannan tsarin tana fadin" lale dole ne manya manya ne bara mu fito, ta juyo wajen Aisha da ta fara yin la.asar tace" kawata mu tafi ko

Haka suka bar motar suka fito, Amina ma doguwar rigar ce ta saka red color sai dai tata ta dameta sosai sai ta yafa mayafinta a saman kanta

Haka suka shiga wannan gidan wanda kallo sai ka shigo idannuwanka zasu baka kalaci domin gida ne mai girman gaske , faduwar tsaruwarsa ba zai yiyu sai dai nace ya hadu iya haduwa ko a kasar waje sai haka


Suna shiga suka tarar da wata mata da uniform na ma.aikata cikin sakin fuska ta tambaye su wajen birthday suka zo

Suka bata amsa da eh, nan ta nuna masu wata hanya da kofa a jikinta ta ce" ga bangaren Ogan nan

Kallon juna suka yi suka nufi hanyar inda Rauda ke biye da su a baya kamar kwai ya fashe mata a ciki domin gaba daya ji take tamkar bata da laka

A tare suka furta waouh!!! Domin tsarin wannan waje ya zarce wanda suka baro, tsari ne irin na turawa domin kasan shinfide yake da gazon wato wannan tsanwar ciyawar irin ta filin ball mai laushi a kafa da santsin takawa

Sai wasu dogayen shukar dabino a jejefe a filin
A nan filin wajen motsa jiki yake an kawata shi fa dukan abubuwan bukata na motsa jiki, da wani dan karamin frij mai cike da dukan abin sanyi wanda bayan ka gama motsa jikin zaka dauka ka fitar da kishirwa

Gefen dama kuwa wasu fararen kujerun karfe ne irin wa.ina ake sakawa daga cikin kasa, sai dan nesa da su abin lilo ne shima an yi masa fenti da fari sosai ya hasku a kan wannan ciyayin

Sai wani dan table da runfa a samansa gefensa kuwa wani dan sip ne cike da litatafai na adini da na turawa

Wata sansanyar iska ce ke kadowa tana badawa dalilin ruwa da ake baiwa wannan ciyayi da kuma shukokin nan sai ya kasance wajen ya zama gurin samun nutsuwar du wani bawa mai cikakiyar lafiya

Wajen mutanen da suka hanga a tsatsaye suna daukan hotuna du yan mata sai yan gidan da basu fi su biyar ba gaba daya dai har su Rauda ba zasu kai su 15 ba

Gaisawa suke da hafsa wanda Rauda ta raja.a a shakar kanshin wajen somin kanshin shuka yake bayarwa da sanyi mai dadi

Hello????????
Hafsa ta maimaita a karo na biyu domun tana yiwa Rauda sanu da zuwa aman bata ji ba

Da sauri ta juyo da fuskarta, kunyar hakan ya saka ta sakin murmushi wanda ya baiwa fuskarta damar lotsawa sosai

Zaro ido Hafsa ta yi ta ce" waouh, masha Allah freind wannan ma kawarki ce? Ta fada tana tambayar Amina

Amina ta ce" kanwar kawata ce baki ga suna gama ba?

Hafsa ta ce" eh gaskiya akoy kama, da farin fatar sai dai wannan ta fi yayar nata manyan idannu da kuma dimple masha Allah, ina son abin nan

Murmushi suka yi gaba dayansu wanda a daidai wannan lokacin murmushin kan fuskar su Aisha, Rauda, Amina, da sauran jama.ar da suka zo a matsayin gaya sanadiyar razannan kyan bayan Allahn da ya bayana a gabansu da shigar yan ballllllllllll




🙆🏽 to fa kar Hafsa maimakun ta birge a samu matsala domin dai Yayanta koda yana mugun sonta a matsayinta na auta sai dai ustaz ne irin mai mugun ustazacin nan......

*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*



5⃣



Na : *SAJIDA*


Murmushi suka yi gaba dayansu wanda a daidai wannan lokacin murmushin kan fuskar su Aisha, Rauda , Amina da sauran mutanen dake wajen a matsayin wa.inda aka gayata ya dauke sakamakon razanannan kyan bawan Allahn da ya bayana a gabansu da shigar yan ball

Bakar riga ce a jikinsa mai gajeran hannaye iya damtse, rigar a lafe take a jikinsa ta kama fafadan kirjinsa , ta rike damatsunan hannunsa kam sannan ta bada damar gannin yannayin girman kafadunsa

Sai wando baki wanda ya dan zarce gwuiwa , ta dan rike kafar daga kasa,
Da yake ya fito ne dan ya motsa jiki bai fito da hirami ba domin shi mutun ne ma.abocin saka hirami, a kashi dari na suturun da yake sakawa kashi casa.in na kayan larabawa ne hakan ya saka ba kowa ya san cewa kansa lulube yake da ni.imtacen gashi konce baki sidik mai laushi da kyan gani ba, sannan shi mutun ne mai matukar kunyar a ga jikinsa, ya kasance yana da wani kazamin kishi wanda shi kansa yana kishi kansa domin sam baya bari a ga yannayin halitarsa shi ya sa du inda gidansa yake toh fa da wajen motsa jiki wanda ya kawata shi da komai domin a nan yake zuwa ya saki jikinsa ya motsa jikinsa ya buga ball yanda ya kamata

Jin alamar mutane a gudansa ya saka shi juyowa da sauri wanda yayi daidai da bugawar zuciyar du wanda yake ba muharaminsa a wajen ba

Mutsuke idannuwansa yake cike da mamakin gannin jama.ar wajen, nan fa yannayin shigarsa ya fado masa a ransa yayi gagawar kallon jikinsa ya kuma dagowa dan kuma shaida cewar wai su waye ma sannan mai suke masa a wajen nan????

Da sauri Hafsa ta tarbo masu katon cake din da ta saka aka yi mata masu aiki biyu suka gunguro si a kan table mai tayoyi

An mugun kawata wannan cake sannan daga gefe gefe an yi rubutu

Da sauri ta karasa kusa ta shi ta saka hannunta a tafin hannunsa ta jawo shi wanda ya zame mata tamkar mutun mutuni wanda hakan ya hana shi nuna dadin rai yake ciki ko akasin haka, shi fa kwatakwata bai fahimci inda Hafsa ta dosa ba, mutanen nan su waye? Mata, sannan du yan mata cikaku, mai suke nema a nan? Kallon mai suka tsareshi da shi??



*SURPRISE*
Cewar Hafsa tana mai nuna masa cake wanda a tare suka kalo wajen cake din da aka rubuta da farin cream *HAPPY BIRTHDAY YAYA SUDAÏSS*

Sai a wannan lokacin ya tuna cewar yau zagayowar ranar haihuwarsa ce,

Hannunsa na dama ya dago ya dafe kansa da shi, daidai wannan lokacin Rauda ta sada kanta kasa domin da ta kallo fuskarsa gabanta faduwa yake, daman akoy bahaushe da irin wannan halita?

Ya salam ya furta da muryarsa wace ta fito a muryar kato sak, domin bata da laushi ko kadan irin muryar sadaukan maza kenan muryar dake fadar da gaban mutane, muryar dake tsoratar da maza sannan ta hautsina tunanin yan mata....

Hannunta da ta riko shi dan ya je ya yanka cake din ya bi da kallo, sannan ya dago fuskarsa wanda ta fasara labarin zuciyarsa domin kuwa ya mugun hade fuskar ya bayanar da bacin ransa

Fizge hannun nasa ya yi ya wurga mata jajayen idannuwansa , a hankali ya taka har zuwa gabansu, ya fice cake din ya tsaya kikam a gabansu

Kudirin da ya saka shi yin hakan , ya so ya tafka masu rashin mutunci domin a ganinsa gaba dayansu ba yayan mutuncin bane tunda har suka iya fitowa a fidajen su cikin kwaliya da niyar zuwa birthday din namiji, namijin ma wanda basu sani ba, zuciyarsa ta yanke masa hukuncin ai suma yara kananu da su sun san su talata kansu wa shi

Tun daga yan matan hudu ya fara fuskarsa a hade wanda hakan ya saka su kyarmar tsoro dan basu san laifin da suka aikata ba abin alkhairi na neman zame masu matsala

Kallon kyama yake binsu da shi har ya zo wajen su Amina wace sai dan murmushi take saki

Kallo daya yayi mata ya ja tsaki domin kara turo kirji take tamkar wata yar bariki,

Tsakin da ya ja ne ya saka Rauda saurin dago da kanta suka
Cikin rashin sa.a idannuwansu suka sarke da juna wanda a tare zuciyoyinsu suka buga

Saurin rintse idannuwansa yayi ita kuwa ta mayar da kanta kasa yayi saurin kawar da fuskarsa a fuskarta ya kalo Aisha
Aisha da ta yi mutuwar tsaye tun lokacin da idannuwanta suka yi arba da shi, wata irin zazafar kaunarsa ta darsun mata a zuciya, hankalinta in yayi dubu to ya tashi a wannan lokaci sai abinda ya kuma tayar mata da hankali shine irin kallon kyamar da ya bisu da shi

Ba tare da ya furta uffan ba ya juya yana takunsa na kakarfan namiji ya shige tare da turo kofar da karfi

Da sauri Hafsa ta dora hannayenta a kai ta ce" na shiga ukuna, daman granny ta fada min na fada masa ya shirya kar na yi surprises dinsa na yi mata gardamar cewa dadi zai ji🙆🏽, ya salam, yanzu ya zan yi yayana yayi fushi sosai domin yana yi min uzuri a kan sauran mutanen gidanmu da tuni ya hukunta ni

Husna ta sauke ajiyar zuciya ta ce" baki ga tunda ya fito jinina yake hawa ba? To kinga tafiyata dan ba zan taba manta marin da yayi ba sai da dan kunena ya cire sannan na saki fitsari da girman nan nawa dan kawai na dauko masa ruwa ban duka ba na bashi a tsaye dalilin mantawa da nayi da dokarsa ta a duka idan za.a bashi abu, ai ni yama yi sanyi nake gani yanzun domin kina gani baifa daki kowa ba dan haka tun muna shaida juna ku fice mu tafi

Jin haka ya saka gaban amina ya fadi, ta juya tana kallon husna, Husna cousint dinsu ce, a komai ta fi amina kyau din , kudin kai komai ma aman tana tsoronsa haka? Ita fa tana son mutun mai irin kirar sa da kyansa da kudinsa aman bata son namiji masifafe, tana matukar tsoron masifarsa aman zata gwada idan har zai daina sai ta aure shi 🤔🤔🤔🤔


Suna sauri suka fito gaba dayansu, kowace ta kara tsorata da rashin maganarsa kowace tana tafe ne tana waigen bayanta domin shirunsa yafi fadansa tayar masu da hankali

Wayar hafsa ce ta yi kara ta daga ta yi tsam tana sauraro sai can ta sauke ajiyar zuciya ta juyo wajensu murya a raunane ta ce" kawayena, ran yayana yayi matukar baci hakan ya sa ya saka a hana kowace daukan motar ta har sai ya waiwaye ku

Gaba daya hankulansu ya kara tashi du suka kali juna,

Amina ta ce" ki rufa min asiri Hafsat, idan na koma gida ba motar momyna zata yi min duka ne domin sai da ta gargade ni kar na lalata mata mota, to na je nace mata me ma wai?

Gaba dayansu ba wace ta yarda zata tafi ba motarta banda su Rauda da suka yi shiru kawai suna bin mutanen wajen da kallo kowace da damuwarta daskare a zuciyarta

Ajiyar zuciya Hafsa ta sauke ta ce" to abinda nake so da ku, ku mu je wajen Granny

Daya daga cikinsu ta ce" hafsy, daman kin san yayanki bashi da mutunci kika gayace mu ? Me yasa kikai mana wannan wulakancin?

Hafsa ta juyo ta dan hade rai ta ce" aman Ramlat baki iya magana ba ko? Kin san ko wanene kike hada shi da rashin mutunci? Wannan da kika gani tamkar mahaifinmu yake, haihuwarmu ne kawai yaya Sudais bai ba! Dan haka ko mai yayi ba zan taba yarda wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login