Showing 69001 words to 72000 words out of 122108 words
Chapter 24 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
ya biyo shi siyen gold din, ya kawar da kansa ya yi nuni da yana zuwa
Wani gold ne da aka kirarsa aka saudiya, A lokacin sai suka nunawa Sudais da Shuraim shima gagarumin dan kasuwa ne
Sai ya dandajar da abin ya yi tayin da basu so ba dan haka suka salamawa Sudais
Sai dai matarsa ta tayar da kafar baya, kin san larabawa da matan su, ta tayar da bali domin ta gansa a shagon Sudais na Nigeria cikin tala zee aflam, sarka ne da yan kunaye ba masu wani girma ba kawai kirar ne aka yi ta yan gayu aka zuba zunzurutun kudi
Tana gani ta ji ai kawai tana so shine ta tayar masa da hankali sai da yayi tafiya gari ya gari ya zo domin Sudais kin daga wayarsa ya yi dan Shuraim akoy kyamar du mutumin da ba balarabe ba, wannan ya sa basa hayewa juna da Sudais domin shi kuwa yace ba zai je yanai masa fadanci ba kowa yana neman na kansa dan haka kowa yayi iko da nasa... idan sun hadu ma sai dai su gaisa daga haka ba wani abin dake shiga tsakanin su
Sudais na zama a office dinsa Basma ta nemi izinin shiga ya bata
Tana zuwa ta gaishe shi kafin take gabatar masa da bakin da sukai na kasashe uku a safiyar yau kuma du sun zo ne a kan wannan gold din
Sudais ya yi tsai yana sauraronta,
Sai da ta gama ya lumshe idannuwansa bai bata amsa ba kuma bai salameta ba,
Wayarsa ya dauka yar karamar wace ke dauke da numbobin manyan mutanensa
Sakawa ya yi ya buga kira Har kasar Saudiya
Tana ringin na uku aka daga daga dayan bangaren akai masa salama irin ta adinin musulunci bayan ya amsa mutumin cikin yaren inglish ya ce" ogan mu
Sudais ya dan saki murmushi yace" wane ni, ai kaine oga
Mutumin ya ce" na baka, a gaskiya kaine oga, wai da gaske zaka fara harkar gawayi?
Sudais ya yi murmushi ya ce" har na yi nisa a ciki
Mutumin ya ce" masha Allah , mutumina ka fa fi da fasowa, Allah ya taimaka ya kuma kare ka
Sudais ya amsa da " amin mai gidan mu
A tare sukai murmushi,
Sudais ya dan ja numfashi ya ce" Brahim, wannan sarkar zan samu wata ne irinta?
Brahim ya ce" Sudais, sarkar nan ta fito ne a matsayin irin kayan da idan muka yi kwaya daya bama sake irinsu, ku kuka fitar da tsarinku cewar orin kirarku unique kuke so, ai Shiraim kansa ya dawo da matarsa wai irinta yake so, har sai da ya dora min kudin sosai na nuna masa da ina irin haka da ban yi nisa har haka ba, amana daya ce, ni na yi alkawarin du wanda na dauki alkawari da shi ba zan ci amanarsa ta hanyar baiwa wani kirarsa, komin girman kudin da zai ninka min
Sudais ya dan juya saman kujerarsa yana sauraron bayanan Brahim, can sukai salama
Kurawa takardun gabansa ido yayi, kowane da irin kudin da ya baiwa sarkar, kowane kuwa ya bada jibgegen kudi na mamaki,
Murmushi ya yi ya mike ya cire rigar nasa ta sama ya ajiye a nan ya yi gaba Basma ta dauko takardun ta bi bayansa
Bangaren gold gold din ya nufa,
Yana shiga ya shiga can wajen coffre din ya dora babar yatsarsa ta dama wace dole sai da ita zai budu
Yana buduwa ma wani glas ne da wajen code shima,
Gani na yi ya daidaita idonsa na dama abin ya yi wani zuzuzut ya bude,
Zo ka ga sakin baki wajen yar mutan Niger, ya wannan sarka a rataye a jikin wani wuya na mace haka, sai daukan ido take ba wani dabkekiya bace kawai tsaruwa da kyau
Bayansa ya waiwaiya ya ga suna tsaye, da Shuraim, da Frank dan america wanda shi zai kai fada ne, sai mace NADIYA uar kasuwa ce ta zo ne siyanwa yar gidan shugaban kasa wace za.ai aurenta sannan kowane sai da ya fadi ga abinda zai yi da ita dan kowa a wajensa an nuna ana sonta sosai
Mirmushi ya sakar masu sannan ya karaso inda mataimakinsa, da sairan ma.aikatan da suke kula da bangaren du sun halara a wajen sai Basma dake rike da takardun tana kara karanto masa cikin kwararen turancinta
Sai da ya gama sauraro ya mika hannunsa ta miko masa da sauri
A hankali ya kara takawa gabansu, kowane sai ya duba da kyau ya jinjina kai sai ya mika masa takardarsa
Har ya zo kan Shuraim, wanda shima ya amsa suna kalon sa
Dan murmushin ya sakar masu ya ce" i.m sorry ba na siyarwa bane
A tare suka zaro ido, Nadiya ta fara magana ta ce" Uban masu gida, ka kayide mana kudinsa yanda kake so mu saya cikin mu wanda yake iyawa sai ya siya
Sudais ya maida kalonsa kanta ya yi mata kallo daya ya kawar da kansa,
Shuraim ya ce" SUDAIS ka taimaka ka siyar min da sarkar nan, ka dai san a tare akai mana talarsa ban san zata birge matata ba sai yanzu, ko abinci bata ci ka taimaka min na je mata da ita
Shima kallonsa sUdais ya yi bai bashi amsa ba,
Frank ya ce" SUDAIS , kar ka yi zabunta ka siyarwa wa.inda suke adininka, na rigaye dukansu zuwa wajennan sannan ban yi tayin wulakanci ba, idan har kudin ne basu yi ba na linka maka su sau uku
Kamar da wasa fama suke su tayar da yar hayaniya kowane yana kara kudi kan na dan uwansa
Sudais ne ya yi masu salama cikin dan daga murya ko zai katse hayaniyar
Dakatawa suka yi gaba dayansu suna kalonsa,
Gilas din idonsa ya cire wanda hakan ya basu damar gannin kwayar idonsa, muryarsa a dake kamar yanda ya saba ya ce" i said ba na siyarwa bane, ban taba linka riba ba! Ba zan fara a kanku ba
Yana gama fada ya juya da niyar tafiya domin yana da wani meeting din,
Da sauri Shuraim ya riko hannunsa ya ce" aman idan ba saidawa bane me zaka yi da shi Sudais?
Sudais ya bi hannunsa da ya rike nasa da kallo dan haka Shuraim ya yi gagawar cikawa yana kalonsa ,
Sudais ya dan gyara wajen ba tare da ya bashi amsa ba ya yi ficewarsa a wajen
Kowane dai da bacin rai ya bar wajen suna ayana daman shi haka yake sai ya ga dama yake sakewa idan ya ki sai ya daure tamkar wani kurma
Da yama kamar kulun Samir ya tuko Sudais a mahaukaciyar motarsa wace ba a ita suka je office ba canzota ne suka yi , hakan suke ko yana cikin bada kama ko me shi dai ya san dalilinsa na yin hakan
Samir na biye a bayansa har falo da wata jaka wannan karon wace ba da ita ya fita ba bayan ta laptop dinsa
Faman zama suke sai hayaniyar su Rauda da hafsat ta saka Sudais ya yi gagawar kallon wajen kicin din,
Jin kakaniyar ta gaske ce ya saka shi dagawa Samir hannu alamar bye, shi kuwa ya nufi Kicin din gabansa na dukan dari dari
Ja yayi ya tsaya ya harde hannayensa ya zuba mata iso,
Sun bada baya ne wajen Fur suna kara decoration din cake din da suke yi dan murnar zagayowar ranar haihuwar Rauda wace tunda suka tashi suke dan kakayniyarsu fuskokinsu kuwa du sun dan shashafawa juna suna ta dariya abinsu da alama dai Rauda ta mugun sakin jikinta da Hafsat
Wando ne dogo baki slim wanda yake dan kyalkyali ya kameta sosai sannan yana bin yanda cinyoyinta ke rawa da bayanta ko ya ta motsa sai riga mai dan tsayi har daidai gwuiya daga baya daga gaba kuwa ta dan dara cibinta kadan wace itama bata da nauyi ko kadan sai likewa take a Jikin Rauda ko ya ta juya
Kanta kuwa ta daure gashin sai ta dora wata bakar hula mai tiloli ta rufe gashin gaba daya sai na gaban goshinta da yayi lufluf da na bayan wuyanta
Hafsat kuwa doguwar riga ce a jikinta sai hula itama sannan sun jona wayar Hafsat a gefe sun saka waka a karamin sauti tana dan tashi ana ta waka "it's my birthday ........ har dan juyi suke ana dariya ana hada cacadeden cake
Ajiyar zuciyar da bai san ko na meye ba ya shiga jerawa, sai kuma ya fara ji iska ta yiwa hancinsa kadan yana kokarin shidewa domin kuwa Rauda tana dan rawar nan ne tana dan jujuya abinnan wanda ita ba da gangan take yi ba, idan dai ta juya suma sai sun juya
Hafsat ce ta juyo dan daukan abin matsa cream din ta zuba su matsawa cake din ta ga Sudais tsaye ya cika kofar yana kalon su
Bakinta ta bude da niyar yi masa sannu da zuwa ya yi gagawar dora yatsarsa saman lebensa sannan da idannuwansa ya yi mata gargadi kan kar ta yarda
A hankali ya juya ya fice a kicin din ya dauki kayansa ya nufi dakinsa,
Yana shiga ya fada saman doguwar kujerarsa, lumshe idannuwansa yayi yana hangenta, a hankali ya bude idannuwansa ya kai dubansa wajen bayi, shi kadai ya saki murmushi sannan ya mike ya nufi bayi dan shirin zuwa mosque
Haka su Rauda suka sha shirmen su a dakin Raudar suka ci cake din su sukai kallo , a takaice dai a gajiye Hafsat ta yi mata salama itama ta kuskure bakinta ta gabatar da sallar shafa.i da wutiri
Tana cire hijabin tana nikewa tare da salayar ya shigo
Wani irin mikewa Rauda ta yi, jikinta a lokacin ya dauki bari tama rasa yanda zata yi ta mayar da hijabin kan kayan dake jikinta
Tsareta ya yi da kallon nan nasa mai tayar da tsikar jiki yana kara kusantota wanda daga shi har ita du taki daya idan ya yi sai gabansu ya fadi
Saurin sada kanta ta yi kasa, tana damke rigar jikinta tana janta kasa kasa kadan kadan
Kusancin da ba zai yiwu hannu ya ratsa tsakaninsu ba ya bari, wanda shima a hankali ya matso ya kasance kanta yana jikin fafadan kirjinsa
Lumfashinta dake fita da sauri da sauri ne yake dukan kirjinsa wanda hakan ya hadasa masa kasala banda wanda yake ciki,
Dan dukowa yayi ya kai hancinsa daidai wuyanta ya shaki kamshin wajen wanda har sai da ya yi dan hummmmmm dan kamshinta ya tafi da imaninsa, ba karni, ba warin ruwa na kai kamshi ne kawai take
Da sauri ta yi kokarin dan ja da baya wanda ya yi saurin saka hannunsa na hagu ya rikota ya jawota ta hadu da jikinsa sosai
A hankali ya dago hannunsa na dama ya fiyar da sarkar dake hannunsa ya daidaitata a wuyanta ya saka mata ya saketa ya bala mata sannan ya matsar da gashinta ya saka mata yan kunayen kafin yake maido mata gashin nata
A hankali ya rabo fuskarsa da tata ya taho a nitse ya goga karan hancinsa da nata yana dan kara murzawa idannuwansa a lumshe Hakama nata wanda ita kanta bata san me ya sakata lumshe su ba sannan me ya hanata guduwa duda ya cikata
Zuciyar ke fadin" sudais, cafko su, ka cafko su sudais, naka ne , halalinka ne sudais, ka cafki leben Rauda ka yi masu shan alewa mai shinke, ka tande su har sai sun yi jajajir,
Wata kuwa ta hane shi cewar " haba sudais, Raudar nawa take? Ka barta ta gane karatunka tukunnan, ka barta ta fada a tarkon da ka jima cikinsa kana iyo ya kasance itama ta kaunace shi har ta yi gudun fita a cikinsa, ka barta ta girma ta kara shekaru kan nata kafin ka nuna mata wannan hanyar Sudais, Kar ka tsorata Angel dinka
Da alama dai shawarar nan ita ya dauka domin a hankali ya raba fuskarsa da na Rauda, ya dan ja baya yana kare mata kallo wanda har yanzu idonta a rufe yake ruf hawaye yana dan fita ta cikinsu
Hannayenta cikin nasa ya kai daidai lebensa ya sumbace su a tatare lokaci guda sannan ya ce" *HAPPY BIRTHDAY KHALB*
Da sauri ta buda idannuwanta wanda bata yi shirin bude su ba
*KHALB* TA maimaita a kasan zuciyarta , daidai lokacin da maganarsa ta katseta ya ce" da ke ta dace, ta yi maki kyau......., Rauda, *ke ce mai kyau* ,
Yana gama fada ya matso ya bata peck a kunci ya cika hannayen nata ya juya ya fice
Mutuwar tsaye ne Rauda ta yi, ta kusan minti talatin a haka ta kasa gane karatun Sudais,
A hankali ta matsa kusa da madubi ta kali kanta a ciki,
Idannuwa ta zaro gannin sarkar da ya bata, ni kaina idannuwan na zaro domin sarkar nan ce ta kampani ya bata .....
Humaira ce konce tana ta juyi ita da kawarta suna magana a whatsup, kawarya ta ce" lale ne hajiyata , na yarda oga yana mugun sonki, irin wannan kyauta haka? Sarkar gold haka? Aman odan kin siyar ba zai gane ba?
Humaira ta yi murmushi ta ce" hum, ba wani ganewa da zai yi, wai ita amarya an kawota an jibge kawata ki tura ki ji nawa zasu saya na sayar na kashe wutar gabana na samu hanyar da zan kori wannan banzar cikon bencin!
Kawarta ta ce"
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
3⃣8⃣
Kawarta ta ce" ai ni nama yi mamaki hajiata, har ta tare du kina kallon ina sai kace baki faso ba? Bayan kina tare da yan bariki ya dace a ce aikatawan ne kawai da kika hana kanki bakya yi aman du sauran halayen mu bai dace ace kina yi ba, yanzu a irin yanda kike bamu labarin girman bulalar oga kika yarda wata banza ta shigo tana shan dukanta harma tana lashe amanta ! A gaskiya kin yi sakaci da yawa....
Humaira ta ce" ke bai fa taba hada shinfida da ita ba
Kawarta ta ce" kin tabata zaki iya rantsewa da hakan?
Humaira ta yi murmushi ta ce" zan iya bada rayuwana a matsayin wannan maganar, Elhajina bai je shinfidar banzar nan ba, na sani duda ina nuna gajiyawata aman yana ji da ni, ni din nan dai ni ake kira zuma mai harbi, dole sai da ni elhaj zai gyagije ya kwashi ruwa
Kawarta ta ce" bana son wasa, ki kara hima...., bara na shigar da sarkar mu gani idan ta an yi mana tayin kirki sai na saka ki a hanyar da dan uwarta ba zata kara jima maki a gida ba
Humaira ta yi murmushi ta ce" sai na ji ki
Tana kashe wayar da Kawarta ta tabo mutumin da yake saida mata mai, wani inyamuri ne dake yi mata zazafan hadi, shi din da kansa ma shafa man yake domin idan ka ganshi tamkar zabaya du fatar ta cinye ,
Tana tabo shi ta fada masa ya hado mata zafafa zata je ta karbo
Bayan nan ma oder ta yi na kayan kwaliya bayan du irin wa.inda take da su a dakin, ta kuma yi na atach (meche)
Tana gamawa ta kuma dauko sarkar, itama gold ce tsantsareriyarta , itama ya sayota da tsadar gaske sai dai ita ba unique bace akoy irinta a can saudiyar , da ya ga zuciyarsa ta rikice kan sai Rauda ta saka wancen dan yayi adalci itama ya dauko mata wannan aman shine ko ado bata yi masa ya gani ba zata saida.......halayenta kennan mota kanta dan ba wanda zai yi gigin siyan motar da ta fito daga wajen Oga Sudais ne da ta siyar da motocinta ta tabata ba zai barta ba motar hawa ba ,...., kuma du wannan hadamar da take bata yi ginin gidan da za.a kala a ce lale wannan tana auren mai shi aa kudaden sun kare a siyen banza siyen wofi... atash du tsadarta bata gani zata cire ne ta saya ga rashin adano idan ta cire daga kanta sai dai ta zubar
Da mugun tsoro Rauda ta zaro ido, da sauri ta cire sarkar daga wuyanta ta zauna bakin gado tana kallo
Tambayar kanta take mene haka? Me ya sa ya yi mata irin wannan kyautar? Sudais ne Rauda..
Da sauri ta mike ta saka hijabinta ta fito ta nufi dakin Hafsat
Hafsat dake zaune tana yanke akaifunta tana kallon wayarta kira ne ta shigowa sai dai ta yi murmushi ta ki dagawa
Whatsupp ya koma ya rubuto" aa fa, Hafsana a rangontawa zuciyana idan ba haka ba na yi sabko gidan nan sai dai oga ya harbe ni, na zo na gan ki Hafsa, ki yi hakuri ko dan dago hannu ne ki yi min kar zafin ya yi min yawa ga na oga ga naki
Murmushi ta saki bayan ta karanta ta ki yi masa replay, a fili ta furta" lalema yayan nawa ne mai hada maka zafi SAMIR?
Dago kanta ta yi tana amsa salamar Rauda wace ta nufota da dan sauri ta zauna tana miko mata sarkar hannunta ta karkata kai tana ciro yan kunayen ta mikawa Hafsat
Idannuwa Hafsat ta zaro, tabas ta san sarkar nan ,
Dago da kanta ta yi ta kali Rauda ta ce" Sis??
Rauda ta samu waje gefen bed din ta zauna itama, murya a dan raunane ta ce" ana kyauta ne wa masoyi, wannan kyauta ne irin na masoya, sis wace ni ? Na tabata dan ya fita a hakina ya bani sarkar nan dan ya baiwa matarsa, ki yi hakuri yayanki ne aman kuma gaskiya ce... da bakinsa ya furtan kalmar kiyaya,! Ke bama wannan ba dalilina na kin komai nasa mai karfin gaske ne
Hafsat da ta saki baki tana kallon Rauda, a ranta take ayanna anya kuwa rauda zata yi wayo? Tana fadin haka wa ni kanwar mijinta🤔,
Kawar da hakan ta yi ta ce" sister kin san da sarkar nan Gold ne?
Zaro ido Rauda ta yi harda mikewa da sauri