Showing 78001 words to 81000 words out of 122108 words

Chapter 27 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

423

a inana zara ajiyeta? Ita kadai sai yarta suka san sirin gidan nan..... aman bara Sarah ta zo su yi shawara ita baban abinda ma zai sa ta rike Aishar dan su kwace Uban masu gida itama ta samu fada a wajen mijinta domin Sudais din uban gidansa ne

Aunty ta sauke ajiyar zuciya ta ce" aman ya aka yi shima ya fi son Raudar a kanki ne? Gaskiya bai yi mana adalci ba

Aisha tana kara sheshekar kuka ta ce" haka muka taso, shi kulun ni yake sakawa a gaba yanai min fada ita kuwa sai dai ki ji yana fadin Allah ya yi mata albarka, yanzu mai gaba daya ya bata mutumin da nake so

Auntu ta yatsina fuska a ranta ta ayanna kike aon kudinsa dai, a fili ta ce" ina ai kema ba zaki yarda ba, ba kince ta ce ba abinda ya shiga tsakaninsu ba? Ai dabara zaki mata ya kasance ta takura shi ya saketa ya aure ki ko?

Aisha da idannuwanta suka rufe sai kawai ta ga hakanma za.a yi, aunty ta kawo kyakyawar shawara

Aunty gannin kamar ta yarda da shawar nata ya sa ta ce" tashi ladi ta kaiki dakin Sarah

Mikewa Aisha ta yi ladin dake rabe ta mike da sauri har kamar ta fadi ta raka Aisha cikin wani dan koridor ta nuna mata dakin

Aisha cikin dan gadara itama yar gida ta ce" ki kai min kayan ciki mana

Da sauri ladi ta kali Aisha kafin take sada kanta ta ce" ki yi hakuri hajia, Uwar gidanmu ta hane mu rabar dakinta sai in gyara za.ai mata shima idan tana nan ki yi hakuri
Tana gama fadar haka ta juya da sauri ta bar wajen

Tura dakin ta yi ta ja ta tsaya,
Gaskiya Sarah babar yarinya ce, domin ko mamanta bata saya mata ba zata nemo kudinta ne ta sayi abinda zai gyarata, bed daya ne a daki sai irin sif din nan na roba mai hotunan barbi cikinsu ne wani kayanta wani takalmanta, sai wajen madubinta dake cike da kayan shafe shafe da su turare dai da sauransu

Kayanta ta raba nan kafin take zuwa ta dare saman gadon Sarah , abinka da ba sabon ba sannan ana kwadayin hakan nan da nan baci ya kwasheta............











Yar mutan niger ce πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“

*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




4⃣2⃣

*ALLAH KA KASHE MU DA IMANINMU,*




Sarah na zuwa ta shige dakin mamanta dan shafa mata wannan labarin mamanta ta dakatar da ita ta shaida mata ta ji komai sannan ta fada mata Aishar ma na nan ta baro gidansu tana dakinta

Bata fuska Sarah ta yi ta ce" haba mom haba mom, wani irin dakina kuma? Ke ki kawota naki mana? Haka kawai dan ta takura min?

Aunty ta ce" ke baki da hankali? Baki san sai da na gwalgwali du wani shege mai bakin tsiya kan kar ya yarda elhaj ya ji tana gidannan ya hada daga ni har ita ya wulakanta mu a gaban idon kishiyoyi ba? Idan na barta a dakina kin san sarai du safiya sai ya bi dakunanmu ya ga me muke muna bama dai kwanan masa da ac da sauransu kema san ban san ya akayi kuke dasawa ba har dakinki ya fi karfin shigarsa ba aman da ai sai dai nima na koreta , dan haka hakuri zaki yi na dan kankanin lokaci idan muka gama abinda muke so da ita sai mu koreta!

Sarah dai ranta bai so ba ta mike buguzun buguzun ta fice ta nufi dakinta

Tana zuwa da gadara ta bude dakin ta shiga, sai dai hango Aisha ta yi dadaya saman gadonta ya sakata yi mata kallon tsaf
Wani sakaran murmushi ta saki, a kasan zuciyarta ta ayanna nama har gida..... πŸ€¦β€β™€


Tun karfe shida da wani abu take jin magana sama sama , firgigit ta farka ta fara raba ido ta yi zaune saman bed din ta kai dubanta wajen da Sarah take sai ta ganta konce ba riga a jikinta sannan hannunta na wani sasa na jikinta
Da sauri Aisha ta kawar da kanta tana mamakin meye kuma wannan? Sai dai bata gama ba kanta amsa ba ta jiyo muryar aunty tana fadin" ELHAJ walahi walahi rabin kofi ne na kara awon jiya sakamakon rashin koshi da ake, kuma naman nan na kan table ban taba shi ba, kamar yanda ka hana kace a ringa dorawa saboda banda kama dan mutane kulun ana dorawar kuma bama ci, kudinka kuwa ai na biyaka na fada maka manufar kyautar nan da na yi da su, ka yi hakuri dan Allah kar ka sake ni

Muryar wani baban mutun ta ji ya ce" ki rufe min baki, ke kam an yi asara a kayanki, ke ke nemo min shinkafar ne? Baki da godiya, sannan kin ga yarana suna yi min korafin mota na baki mota ban baiwa sauran ba, ni nakan manta lokacin da kike shigata haka , haka kika tarda budurwata kika ci mata uwa, to ki kiyayi ranar da zan saka ki a hannuna! Kar ki kara min awo gidana ne ni ke nemana dan haka a daina yi min shishigi

Yana gama fada ya fice ta zauna ita kuwa ta yi zaman dirshan

A hankali Aisha ta shiga kikifta ido, idan dai ta fahimta mahaifin su Saeah ne ya gama wannan wulakancin? Me hakan ke nufi? Du wannan uban dukiyar? Aman ai ba za.a kirashi talaka ba domin ko a balbalin gidansa zaka gane ya nema ya samu !mahaifin Sarah irin mutanen nan ne masu da shi, mai kudi ne sosai sai dai kudinsa bai andani iyalansa ba, komai na gidansa a ka.ide yake, ya kasance mutun mai mugun son kansa, yakan dauki mace ya fita da ita kasar waje tunbama Maman su Sarah ba domin ga fari ga kyau sai dai inda kuka saka kafa da shi kun raba hanya, sai bukatar a ganku ya taso zaki ganshi, mahaifiyar Sarah tana kasuwanci sosai hakan ya sa ta fi karfin wasu abubuwan harma take kona ran kishiyoyi wajen nuna masu cewar shi yake bata , tana saka abinda take so ne ta ci dadinta da yarta sai dai idan ya tardota daki ita da jaka du daya, gashi da shegen bin mata yana raba masu kudi yana kara su iyalansa kuwa ya ka.ide masu komai, dan mugunta ya tsara masu abubuwa wanda idan wani ne ya shigo daga waje zai yi tsamanin wannan gida gidan daula ne daman ya samu shigewa ya wanke goma ya tsoma biyar ya side biyar, sai dai da ka shiga zaka jika tamkar a kaso kake, matan basu da damar kawo yan uwansu su zauna kirikiri zai fito ne ya nuna bai yarda ba kar a dora masa nauyi

Bata gana mamakin abinda ta saurara ba ta shiga kokarin sauka a gadon dan zuwa ta dauro alwalah sai dai me sutura ne idannuwanta suka ci karo da su, wato irin maganin nan na tsarin iyali wanda gogagun yan bariki da kuma matan aure masu bukatar yin tsarin iyali ke andani da shi ne nan yashe wanda Sarah ta bala ta sha kafin ta konta dan a kulun take sha dan gudun bacewar rana, itama Aisha ta sanshi ne sanadiyar wata kawa da ta yi matar aure wani lokaci zata sha take tambayarta bata jin dadi ne ? Nan ta bude baki shaaaaaaa ta shatata mata komai domin itama matar ba dai kamun kai ba

Da tsoro tsoro ta dadawa Sarah duka tana fadin ke Sarah ke sarah tashi

Da sauri Sarah ta mike tana sosa inda Aisha ta daketa tana kallon Aisha ta ce" ke meye haka zaki yi min wannan dukan??

Aisha dake tsorace ta nuna mata abin hannunta ta ce" me me kike da wannan ke kuwa? Ko wani ya baki ajiya ne?

Sarah ta hade girar sama da ta kasa ta ce" nawa ne, wani abin ne?

Aisha ta ce" pil Sutura ne fa? Me ya hada ki da shan maganin tsarin iyali?

Sarah ta zabga mata harara ta ce" ke malama, zan yi maki kashedi biyu, ba.a tashina a baci ko uban waye baya gigin tashina idan lokacin tashina bai yi ba, sannan ko me kika ga ina yi ba abinda ya dameki rayuwana ne ke in banda rainin hankali ke ya aka yi kika san ko na menene? To ki fita harkata idan kuwa ba haka ba zan ci maki uwa!

Gaba daya idannuwanta Aisha ta zaro, ta saki maganin nan kasa tana kallon Sarah, daman sarah yar iska ce har haka? Me yayi zafi daga na tambayeki harda zagi? Ba komai zan yi hakurin har na samu abinda nake so na bara maku tsohon gidanku ke nan har gida nema gareku? Zaki ga daula gidan mijina sai na ci uwarki idan kika yi gigin rabarsa
Tana gama wannan tunanin ta shige bayin

Kusan a nan suka wuni har dare, Hafsat na dan lekowa sai can bayan magarib kawayenta suka tafi bayan sun dorata sosai ta hau kuwa ta yi alkawarin sai ta fida Rauda daga hayacinta kafin ta koreta daga gidanta
Murmushin mugunta ta yi kafin ta daga kafarta ta nufi dakinta

Rauda ta kali Hafsat ta ce" dan Allah sister ki barni na je dakina mana

Hafsat da itafa a dan tsorace take an yi casun nan a gabanta ta ce" kin ga Rauda aa, kar a je ki fita su yi maki taraya kin ga su uku ne mu biyu kuma sun fimu girma kinga shekaru da kuma girman jikin kansa kinga kar aje su ilata mu

Yar dariya Rauda ta yi tana nuna Hafsat ta ce" lah kike cewa na cika tsoro,

Hafsat ma dariyar ta yi tace" na janye wancen maganar , gaskiya kin ban tsoro da mamaki yau, ke nifa bana bugawa aman na iya kuri wayo idan na buda bakina sai ki ji tsorona aman da naga za.a taban lafiyar jikina sai na buya

Sosai itama Rauda take dariyar ta ce" kin san Allah ban san na kai haka kekashewa ba, ni daman na fiya hakuri ko a makaranta sai an kaini makura kuma fa idan na yi bugu wly sai na jiwa mutun ciwo tamkar wata kato, aman ai yanzu kuma an ajiye fannin taba lafiyar jiki, zamu goga ne ta inda ya dace an daina kishin hauka

Ido Hafsat ta zaro cike da murna ta ce" kina nufin zaki zauna da yayana har zaki yi zaman kishi da matarsa? Kina nufin kina sonsa yanzu

Rauda ta tsare Hafsat da ido, sai yanzu take gannin wautarta, a gabanta fa take furta bata son dan uwanta jigon rayuwarsu, ya salam aman na jima ina tafka shirme haka? Ina tunanina ya je ne?, irin murmushin sangarta ta yi ta dan daki gefen kafadar Hafsat bata bata amsar tambayar nan nata ba ta mike tana fadin " oya freind zo ki rakani na je na canza kayan nan da safema da su ya ganni kar kuma na fita matarsa ta jijiga ni ....



Tambayoyi= shin Rauda ta kudiri aniyar zama da sudais dan ta fara sonsa ko dan takaicin irin wulakancin da take ganni wajen mutane daban daban da suka sako rayuwarta a gaba? Tofa tana so ta nunawa kishiya ta karbi miji shin hakan zai haifa mata da da ido kuwa? Zata bile a basajar soyaya ko zata jita a kame tamkar an kama bera? Wa zai ci wasan nan ne tsakanin Rauda, Humaira, Aisha da kuma Sarah?????????????
*tsakanin Rauda da Sudais wa zai ci wassanπŸ€”*

Aisha.....ta fito duniya ta fada wajen da take ganin gida ne...........................

Ya kuke jin labaran yar mutan niger? ? ? Me ke hasalaku a cikin labarunta? Me kuke son gannin ta daukaka ko ta zurfafa a cikin labarunta????????????






*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




4⃣3⃣

Tare suka fito suka nufi dakin Rauda da dan saurinsu domin Humaira an sha wani uban lesh baki mai adon ja an hakimce saman babar kujera sai dai fuskarta ba fara.a sannan bata daura dan kwalin kayan ba tana zaune tana jiran uban masu gida dan fara aiwatar da shawarar da kawayenta suka bata

Dakin Raudat suka shige wanda suna shiga Rauda ta shige bayi dan yin wanka ita kuwa Hafsat ta bude bangaren tufafin Raudar

Wata doguwar riga mai kalar blu wanda ya ciza har yana satar baki ne ta ciro ta ajiye gefen bed daidai ana kiran sallar isha.i dan haka ta dauki hijab ta saka ta tayar da sallah

Har hafsat ta gama sallah Rauda bata fito ba dan haka sai ta yi zaune tana adu.a tana duba hanyar fitowar Rauda

Bayan nan ma ta kusan wani minti goma kafin take fitowa ta daura tawul sannan ta sako hijab
Zanninta ta daura ta saka riga ta cikin hijab dinta kafin take tayar da sallah,
Sai da ta gama ta yi adu.arta ta shafa sannan ta mike ta cire hijab din ta mikowa Hafsat abin busar da gashi ta zauna kasa Hafsat kuwa ta zauna bakin gadon ta jona ta shiga busar mata da gashin kanta tana caje mata shi
Mamakin irin baiwar cikar gashin da kuma tsayi ga baki gashin Rauda ko ita da ta shafi buzaye gashinta bai kai na Rauda tsayi ba, koda yake itace batai gashin mai tsayi ba yayanta har ya fita izgar gashi hakama idan tana kallon hoton yayunta da suka rasu suma har gaban goshinsu lumbuk, kasa hakuri ta yi ta ce" sis ku kuwa wani yare ne?

Rauda ta dan sosa kanta domin zafin cazar take ji, ita kam ba dai son jiki ba bata son kwata kwata a taba mata kanta kuma itama bata taba shi dan bata son kitso ko cazar gashi, Rauda ta ce" Abana bahaushe ne, mamana ce buzuwa

Hafsat ta gyada kai ta gama caje mata ta dan shafa mata mai kadan kafin ta tambayeta ra.ayinta yanda zatai masa

Rauda ta turo baki ta ce" ki daurw shi kawai sister

Hafsat ta ce" aa, ke da ga abinda kika dauki niya, to ina gannin kawai a bada kai da fata

Kai kawai Rauda ta gyada tana hasashen abubuwa a kasan zuciyarta

Hafsar ta gyara mata gashinta sosai ta daure shi a tsakiya ta sake shi ya bazu a gadon bayanta

Mikewa ta yi ta je gaban miroir ta dauko hoda da jagira da jan baki mai ruwan kasa,
Cikin nutsuwa ta dan shafa hodar, ta samu ta saka jagirar a idonta sosai ya shiga ta ajiye ta dauki abin jagirar mai dan macaji karami a jiki ta caje girarta,
Bayan ta gama ta shafa wannan jan bakin kadan ta kara gyara shi da kyau

Juyowa ta yi da niyar dauko kaya Hafsat ta miko mata rigar nan tana fadin please sis
Ta yi kalar tausayi

Murmushi Rauda ta yi ta karba Hafsat kuwa ta shige bayi tamkar zata yi wani abin ita kuwa dama ne ta bata ta shirya cikin nutsuwa

Rauda ta gane yaren Hafsat dan Haka ta cire rigarta ta dauki turarukan dake kan sif ta fara daukan farin humura ta bude ta shiga shafawa a wajaje kamar haka: kasan wuyanta, tsakanin yan biyu🌚 da kasansu, bayan kunanta bayan ta saka auduga ta hoge dan ruwan wanka ciki da bayan, guiwar hannunta daga gaban, sai kasa du inda keda lungu a jikinta sai da ta shafa
Tana gamawa sa humurar ta dauko deodorant ta daga hamatarta ta fesa sosai kafin take bari ta dauko pant mai ruwan rigar ta saka da bras mai siririn hannu wace ta yi mata dam a jikinta
Rigar ta warware, rigar ta bugu laushinta har sosa hanu yake πŸ₯³ domin auduga ce kada,
Namaki take ba wani mugun kwaliya a jikinta, sai dai kawai zagayen wuyanta da wasu irin perle kananuwa sosai masu kalar zumuwa aman kyalkyalinsu na jifan ido aka zagayasu a iya nan kawai
Bismilah ta yi sannan ta yi adu.ar saka sabon kaya ta saka rigar
Juyawa ta yi wajen miroir tana so ta daidaita ta, sai dai me ja ta yi ta tsaya cike da mamakin irin yanda rigar ta karbeta
Wato wuyan rigar irin mai bateau din nan ne wanda kafadu suke waje wuyan rigar kuwa ya rike damatsunnan hannu hakan ya baiwa yan perles din nan damar layuwa suna dan kyali mai daukan hankalin mutun
Rigar gaba dayanta a matse take domin ta bi jikinta ne har kasa ta mugun fitar da halitar jikinta da yannayin halitar nata, hannayen rigar mamar ta boye cikin rigar tana kalon gaban rigar ta dan bayanar mata da saman mamarta sannan ta kara matse su ta kumburo su tamkar zasu fashe, hannun rigar ne kawai budade sosai sannan akai masa tsaga wato fant.. sai gashinta da ya hau rigar ya konta lumbuk

Hafsat ce ta fito daga bayi sai dai ta ja ta tsaya ta shiga shoki tana dariya ta ce" matar yaya masha Allah,

Rauda ta yi dariyar itama ta ce" gaskiya ba zan iya fita a haka ba, haba da kunya...bamu yi sabon da zan iya yawo haka a wajen nan ba ni ke kanki kunyarki nake da wannan kayan

Da sauri Hafsat ta karaso dan kusan Rauda ta ce" haba ke kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login