Showing 81001 words to 84000 words out of 122108 words
Chapter 28 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
kawas so kike ki dizga ni ko me? To meye a ciki? Mijinki ne fa da abokiyar zamanki, ni kuwa kanwar mijinki ce uwa daya uba daya fa, ba yara kanana ke da akoy a cikin gidan ba bale ki ce idan sun ganki da irin shiga haka yau da gobe abin na iya shafar tarbiyar su, kinga Allah ne fa yayi umarnin ki gyara dan ki birge mijinki idan ya ji dadi kina da lada mai yawan gaske a wajensa, ki kasance mai kokarin samun yardar mijinta mai kara kusancinta da mijinta kin ji?
Rauda ta gyada kanta a kasan zuciyarta kuwa ayannawa take" ya Allah, daman aunty Aishanama haka halayenta yake, da na tabata ba wanda zai ji kan mu du duniya kai ko iyayen mu, zamuna kashewa ne mu bine abinmu, Hafsat na da kyakyawan hali domin tana sowa dan uwanta abinda take sowa kanta, tana iya kokarinta dan kare kalmar imanin dayanku ba zai cika ba har sai ya sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa
Mikewa Rauda ta yi cike da kwarin gwuiwa ta kara fesa wani dan.karamin turare mai sunna bonbon ta shiga wani sanyin kanshin mai damkewa a zuciya
A hankali ta bude kofarta bayan ta saka takalmi matar tudu sosai irin taka biredin nan kalar perle din rigar
Suna kara kusanto palon suke jin muryar Humaira a dan dage tana ta kuka tana magana kamar haka" gayar kawaye ta yi husband suka hadu sukai min dukan nan, ka duba ka ga fuskana .... to haka shatin har bayana , ina zan saka raina? A ina ka auro matarnan? Ya kake so na yi da raina muna zamanmu ka kawo macen dake dukana har tana gayato mutane?
Sudais dake zaune Humaira kuwa a saman kirjinsa sai murzarsa take tana bashi labarin Wai Mata ta gayato mutane an zo an yi mata duka kuma har ga shaidar abin a fuskarta wanda ya tabata a yada take da son jiki ba zata taba yiwa kanta hakan dan ta bata wani ba, a gaskiya yana cike da matsanancin mamaki, *MATA*? dama ta iya fada? Sannan a ina ta yi kawayen da zasu iya aikata irin wannan aika aikar? Shi dai a cikin binciken da Samir ya yi masa bai ma sako cewar tana da kawaye ba, to ko bai sansu bane bai tsananta binkciken ba, sam ba zai lamunci irin haka ba shi saima ya rabata da kawayen idan dai na banza ne domin fa ko halayen banza gareta ba zai iya rabuwa da ita ba dan haka dole ta daina, ya shaka fa sosai sannan Humaira ta bashi tausayi , ya tausayawa fuskarta abin shafe shafen nan ya sa abin du ya wani daukaka ya haye suntum
Hafsat ce ta ja ta tsaya, tsoro karara ya bayanna a fuskarta
Rauda da ta yi gaba kadan itama zuciyarta na bugawa tana mamakin wai ta gayato kawaye, ita? A ina aka yi? Wannan shine sharin da ake fada na kishiya ko me? ( ni kuwa nace hum Rauda sharin kishiya muguwa ai girma ne da shi ),
Gannin hafsat ta tsaya ya saka ta dawo wajenta ta ce" lafiya?
Hafsat ta yi mata kallon baki san yaya ba, ta ce" kina jin abinda take fada? Yaya baya son fada kar mu je ya dake mu gaba dayanmu
Rauda ta zaro ido itama ta dan tsoratan aman ta dake ta ce" daga ta fada masa ba zai bincika ba sai kawai ya dauki hukunci?
Hafsat itama kasa kasa ta ce" ai baya son fitina kwata kwata, idan ka jawo masa fitina yakan iya tataka ka ne, baya zama gari sosai aman du ranar da aka fada masa na yi izgili da wani baya bin sahun abin zai dake ni ne a wuce wajen
Rauda da ta ji gabanta na tsannanta faduwa ta daure ta ce" zan dauki kasada, ki shige kicin ki dauko ragowar cake din nan sister ki taho da shi .......
Kafin Hafsat ta gama fahimtar me Rauda ke nufi kawai t ga Rauda ta dan daga kafarta da dan saurinta wanda nake iya kiransa da sauri mai hade da salo, bayan girgizar da halitar jikin Rauda ke yi nature ta kara da salo tana tafiyar sangartatun yara ta nufo falon gadan gadan aman a kasan zuciyarta tana ayana" shikenan Rauda shikenan kin gama yawo, lokacinki ne yayi kawai Rauda, mutumin da baya sonki? Shine zaki aikata wannan kasadar har ki je ya karya maki kafa? Ki koma abinki ki labe kinga kanwarsa da yake matukar so kanta tsoronsa take bale ke da kika diro basa daga sama
Wata zuciyar kuma tace" ke haka zaki kare? Idan kin dauki iskancin yayarki ta zame maki dole ne, aman wannan kam ki nuna mata kema fa kin iya, yau ko zuwa makarantar islamiya da ta boko ya ci ace ka koyi yanda zaka zauna da mijinka , sannan ko baka da kawaye ko baka shiga gidajen mutane ko a gidanku mamanka ita daya ce a wawuya zaka tsintsinci abubuwa bale yayan zamani da suke binkitawa cikin hikima mai wayo na shanyewa dan gobe, ki jure ki je kawai du abinda ya faru ki dauka kan shinfida kike, sannan za.a ga ke da shi waye zai yiwa daya satar da bai shirya ba?
Lumshe idannuwanta ta yi daidai lokacin da fitinanen kanshin turarensa yayi mata dirar mikiya cikin hancinta ya sakata sauke ajiyar zuciyar da bata shirya ba
A hankali ta furta " tawakaltu alaLah
Rauda ta shirya ta shagwabe fuskarta sosai, ta dan mumurza idonta kadan ta bude bakinta da wani irin salo na rigima ta fado falon ba tare da ta yi salama ba,
Dan kukan shagwaba ne take yi da gangan tamkar bata gansu ba ta shiga dan kai kawo ta gabansu tana mugun jijiga jikinta tana hadawa da dan tsale tana kukan shagwaba
Tunda ta afko falon nan Sudais ya dauke wuta ,, binta kawai suke da kallo wanda ita Humaira mamaki ne take wata sabuwa an cewa kare dan daudu, shi kuwa kiris zaka taba jikinsa ya biyoka , a zaunen dai yake aman ya afka wata duniyar, yama manta cewar ransa ne a bace yana shirin yin hukunci, haka kawai saukar hukunci ya sauko daga sama ya fado masa haka
Daidai lokacin da ta dan didira ta dan bura tana kukan shagwabar nan shi kuwa ya kankame Humaira dake jikinsa wanda ya ji kamar zai suma kuma a fili ya furta " Wayo Allahna
Humaira ce ta juyo da sauri ta sauke kwayar idonta a kan fuskarsa wada ta fara jan jaraba idannuwansa du sun kara girma sun yi jajajir da su , du uban ac din dakin zufa ta gani saman goshinsa
Da bacin rai ta janye jikinta wanda hakan ya farkar da shi ya shiga murza yatsunsa yana jin yanda zuciyarsa ke yi masa fat fat fat fat ita sai ta rungumo Rauda ta rufe bakin nan nata ko ta samu nutsuwa
Kasa jurewa yayi ya mike tsaye ya dan nuno yatsarsa ta kusan babar da yannayin ya jigata ya ce" *MATA, FA, ke ko? Ke ko? Menene ? Wa ya saka ki kuka?*
Rauda ta turo lebenta na kasa, a kasan zuciyarta kuwa wani irin faduwar gaba da shaukin wannan yannayin take ji, haka kawai ta ji bata jin tsoronsa, kalonsa take irin na cikin idonnan , ji take tamkar tana yawo a gajimare a wannan lokacin , sannan ta jita gaba dayanta tamkar wata yar karamar baby yar wata bakwai a gaban mamanta
Sosai ta kusanto shi, hakan ya bashi damar jin kanshin turaren da ta bulbulawa jikinta, ta kara shagwabe fuska ta nuno wajen da Hafsat ta yi mutuwar tsaye daria cike da cikinta, so take ta bushe da dariyar da sai ta fasa falon nan, yayanta ne? Wai dan Allah yayanta ne? Yanzu take na.am da matar da yayanta ta aura, ya ilahi ya manta abinda aka sako shi gaba ana fada masa ,
Kin fadin menene ta yi sai nuna hafsat da take cike da shagwaba da sangarta,
Hafsat ta kwalalo ido, da idonta take girgizawa Rauda tanai mata maganar kurame ba ita ba Ta nuna Humaira, ama Sai Rauda ta yi mata murmushi kuma taki fadin nunawar na mene
Sudais gaba daya ya rikice, yafa rikice, tamkar ba shine yayi alkawarin sai fa ta furta masa so kafin ya zube, sai dai kash ya zube din ne ba tare da an furta masa kalmar so din ba
Nufo wajen Hafsat ya yi gadan gadan dan ya tambayeta me ke damun Rauda domin irin yanda take haskawar nan so yake ta haye kafafuwansa ta yi masa bacin nan, tana murmushi ta yi masa sangartar nan
Muryar Humaira cike da bacin rai da hayagaga ce ta ce" Husband meye haka? Menene wannan kake yi?
Sudais ya ja ya tsaya, zuciyarsa ce ta ce" Kai? Inalilahi, Sudais farka farka farka kafin ta karanto sirin zuciyarka ta yi anfani da shi ta halaka ka, Sudais Farkaaaaaaaaaaaaaa!
Mutumin da ya tatara gaba daya hankalinsa wajenta sai ya juyo girar sama hade da ta kasa, sai da yayi da gaske yayi kundunbala da zuciyarsa kafin yake dawowa falon
Rai a hade ya ce" ke! Ki natsu ki daina tayarwa mutane hankali!
Cikin kakausar murya yayi maganar wanda ya saka rauda ta yi tsit, ya rikide mata ya dawo mata wancen mutumin da take tsoro take shayi, kikifta idannuwanta ta yi tana mai binsa da kallo
Ki daina kawo min shirme a cikin gidan nan, sannan gobe da safe inna nemanku ke da auntynki, na gane dan ban zaunar da ku bane har batanci ya fara yaduwa a cikin gidana, ke ana tausaya maki aman har kece da kawo kawaye gida ku rufun mata ko? To ba dani ba! Ba zaku lahanta min *Matata* ba kin ji na fada maki *MATA*
a gaskiya zan iya cewa tunda take da shi baganarsa bata taba yi mata ciwon na yau ba, ya haka ya fara yaudararta sai da ta fara kokarin karanto lamarinta na birge shi ya wulakantata haka? Ya kama maganar matarsa, ya nuna mata matar soyayarsa ta fita matar sadaka, *ke matar sadaka, na ji datijon ya ban tausayi na karbi tayinsa ya aura min ke kyauta* wa.innan kalaman suka daki zuciyarta tamkar yanzu take karantawa, hashi yanzunma ya tabatar mata ya kuma bita mata karatun wato daban take da dayar
A hankali ta juya ta bi ta dayan bangaren kujerar ta zagaye ta fice da sauri ta nufi dakinta ba tare da ta nuna fushi take ciki kuka take yi ko hankalinta konce yake
Da ido suka bita har ta shige, da murna humaira ta juya idauuwanta ta juya ta nufi dakinta itama dan sanarwa Kawarta ta ci galaba sannan ta fada mata irin barikin da Raudar ta yi ya gwaleta🤔
Bayan tafiyarsu, Sudais ya dago ya sauke jajayen idannuwansa kan Hafsat, so yake ya fada mata ta je ta rarasar masa MaTa , so yake ya fada mata ta cewa MATA ta yi hakuri aman ya kasa, shi fa kamanta adalci ne yayi, dole ya kawar da kansa tun kafin ya fara da ya sani
A hankali ya zauna saman babar kujerar ya afka duniyar tunani yana jin wani irin ciwo a zuciyarsa yana jin yannayin da take ciki sosai a jikinta da zuciyarsa yana jin tamkar ya dawo da lamarin baya ya kasance yana shigowa bai tsaya ko.ina ba ya shige dakinta ya ga wannan rigar a jikinta, dan murmushi yayi kafin ya ce" Kampanin kulley ashe haka kayansu ke keruwa? Sai na karo mata dayawa da yawa..............
Tunda ta shiga ta rufe dakin yanda ba wanda zai shigo a hankali ta je ta zube nan kasa ta rufe idonta
Sauraron irin dokawar da zuciyarta ke yi wanda ta fasara hakan da dan an yi mata wulakanci ne,
Ta jima tana sakawa tana koncewa, daga baya a fili ta ce" Ke Rauda, sai me? Dan yayi maki haka sai me? Da ace ma wanda kike so ne da sai ya dame ki aman mutumin da kun tsani juna ke da shi??
Mikewa ta yi tana yarfe hannu irin sai me, kafin ta murguda bakinta ta shiga kokarin zame rigarnan ko ta walala da ranta
Tana zage zio din rigar ta kallo waje daya ta bata rai a fili ta furta" wai *MATATA, MATATA MATATA!* ta karasa tana mai daga muryarta da irin abin na dukanta.......
🤣🤣🤣🤣 Raudancy love🤣🤣🤣🤣
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
4⃣4⃣
*na fans grup IDAN KA RAINA INDA KA KE, sabon tsari gabannan shine sai kun karanta kun more sannan a yada pagessss.......*
Yau kwanan Aisha hudu a gidan su Sarah, sai dai tamkar ta shekara a cikin ukubar rayuwa ne, abin al.ajabi, abin mamaki, halin kananta wanda bata gani a gidansu ba, kai du safiya ta Allah sai ta ji muryar mahaifin su Sarah ya zo ya wanke mahaifiyarsu tas da mugayen kalamai har yayi mata burgar yana iya sakinta ya auro yar shila ita kuwa ka ji muryarta tana ta yi magiya tana dukawa tana rokon ya yi mata rai kar ya saketa, sai ya kama sunnayen iyayenta ya luluka masu ashar ya ce sun hada shi da masifa kafin wani lokaci ya dan cajeta kudi tukun ka ji ya tafi abinsa...... da safiya ta yi ta cakare ta fito falo da yan fadarta da sangartaciyar yarta a zauna a yi yinin yada habaici wa kishiyoyinta
Yau kam tun wajajen karfe hudu na asuba kake jin yar hayaniyarsu,
Firgigit Aisha ta farka daga saman salayar ta tashi da sauri zaune
Tantar dakin da fitila domin Sarah tsoron kashe fitila take wai idan ta kashe mutun take gani yanai mata gwalo🤔 (rashin adu.a)
Abubuwan da ta hango kusan Sarah ya saka ta yi gagawar kawar da kanta gabanta na tsananta faduwa
Idan baki barni na yi ba sai na kaurace maki na shekara sannan sai na fadawa kishiyoyinki cewar bana zuwa shinfidarki
Muryar baban su Sarah ce ta karade falon domin shi a rayuwa kwata kwata bai iya magana ta sirri ba,
Saurin rintse idonta ta yi, jin muryar aunty tana fadin" ka ga ka rufa mini asiri, al.ada fa nake elhaj? Gashi kai ba ruwanka a haka zaka ce zakai idan fa da rabo sai na sami ciki cikin jini
Wata shegiyar dariya yayi ya ce" ciki fa, ke yaushe rabonki da ki ji kukan jariri a gidan nan? Haka kawai kartin banza na zuba ku a gida na ciyar da ku, daga na rabe ku da sunnan hutu ko nutsuwa sai a fara amaye amaye na rainin hankali, zaku gane ne
Da sauri ta saka hannayenta ta cushe kunnayenta, a hankali ta shiga maimaita na shiga uku, na shiga uku, menene wannan? Ina ne na fado haka? Tunda nake, tunda muka taso bamu taba jin ko gannin alamun irin haka a wajen iyayenmu ba, duda dakinsu daya basu taba nuna mana alamun hakan ba, wannan murya a bude basa tsoron Sarah ta ji su???????????????
Du yanda ta kai ga rufe kunnenta sai da ta ji komai a kunnenta, a karshe dai du najasarta sai da ta amince dan kar ransa ya bace ya aiwatar da abinda ya fada ya saka ta damuwa cikin kishiyoyi (wato ta take fadar Allah ta faranta ran mijinta dan kar tata rayuwar ta shiga wani hali😌.... to muje zuwa mu ga .....)
Tun daga lokacin bacin ya kaurace a idannuwan Aisha,
Gari na wayewa bayan ta gama sallah ta koma gefen bed ta dan shiga tayar da Sarah
Sarah ta juyo ta saki mika ba salati ba adu.ar farkawa daga baci ta kalo wajen Aisha ta kashe mata ido daya kafin take saka hannunta ta cire abinda ta yi masha.arta da shi a jiya a jikinta ma take kwana da shi kuma a gavan Aishar ta cire ta kara gyara konciyarta dan komawa bacinta
Aisha bata dadara ta hau gadon da kyau ta tausasa murya ta ce" haba yar uwata, ki tashi mu yi magana mana
Sarah ta kebe baki a ranta ta ayanna zaki ci ubanki ne aman a fili ta ce" ina jinki ai
Aisha ta ce" sarah ki ji tsoron Allah, abinnan da kike ya huce misali, kina dabi.a irin wace ba ta musulmai ba ko a yahudawan ba kowa ke irin haka ba, masturbat@ da kike yana da baba matsala ga rayuwar dan adam , zaki gurbata rayuwarki ne kuma ki je ga Allah ki hadu da azabarsa , Sarah rayuwarnan duka ma nawa take? Idan kika yi hakuri kika yi aurenki komai sai ki cikin nutsuwa tare da mijinki ga lada ga konciyar hankali kinga kuwa jin dadi dole zai tabata a gare ki, aman kina wannan abin tamkar karuwa Sarah ko kunyana bakya ji a gabana ????
Sarah ta mike ta yaye bargonma gaba daya ya kasance halitar jikinta ta bayanna idan ka ga mamarta tamkar macen da ta shayar da yaya uku kuma irin mai nonon nan mai lalacewa , sun nuna cewa wahala suke sha harda ta mamaki,
Murya sama sama sarah ta ce" ka ji mini jaraba ina zamana a gidan ubana an zo ana fama a caza man kwakwaluwa!
Aisha cike da tsoron kar mamanta ta ji muryarta sama sama haka ta zo kuma ta ga abinda take yi murya kasa kasa ta ce" ba haka bane Sarah, ki sasauta muryanki kar mamanki ta ji mana....
Ai kamar daga sama, kamar da wasa Aisha ta ji saukar mari a fuskarta daidai nan mahaifiyar Sarah ta shigo wato Aunty tana tambayar lafiya? Domin maganar sarah sama sama sosai ta yi, ita kuwa auntyn tana tsoron aban sarah ya dawo ya ji haka ya tambayi da wa take fada kuma kilu ta jawo masu bam
Sarah cikin bacin rai bata rufe suturarta ba ko dan kunyar mamanta ta ce" ke