Showing 57001 words to 60000 words out of 122108 words
Chapter 20 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
ma sai dai tausayin Rauda ya sa ta yi mata magana
Kin ga, Hafsat ki fita a maganar nan, ba abinda ya shafeki da abinda nake yi a gidan mijina ehe, ni ai har na shiga fargabar kar a je ya auro min wata big girl ne ashe tsami girl ne, no bani da wajen zamanta a gidana
Murmushi Samir ya yi jin abinda SUDAIS ya fada cewar ya gwadawa Rauda dakinta gayanan zuwa gidan,
Ya tabata a yanda ya yi maganar a kausashe sai ya ci uban wannan mai karyar rashin kunyar
Wajen rauda ya kallo ya ce " hajia mu je ga dakinki can inji Oga
Da sauri Rauda ta bi bayansa domin daman jira take tamkar ta tashi sama dan sauri haka tsoron Humaira da haukanta ya darsu a ranta
Da sauri ta shige bayan ya danna wasu number ya bude mata dakin tana shiga ta turo kofar da karfinta irin dai ta shigowar ce ana gannin na falon ba.a gannin na ciki
Tsaye ta yi dan nesa ba tare da ta lura da irin aljanar duniyar dake dakin da aka kira malakinta ba ta tsurawa Humaira ido yanda take ta masifa har dira take tana kumfar bakin yau ko ita ko Rauda sai ta bara mata gidan mijinta
Hannayenta biyu ta dora a saman kanta ta silale saman kafafuwanta, a fili ta furta" *wayo Allahna ni Rauda tawa ta same ni, Abanna kana ina Abanna ? Aba wannan bawan Allahn shi ne Aunth Aisha ke matukar so, shi ne na daga hannu na mara, shi ne ya tsane ni tun kafin mu hadu da juna, shi ne mai arzikin da ko a kafarsa aka kula masa ni zai cire ni ne ya yar, matarsa mahaukaciya ce tsoronta nake Aba, Abana bana son sa, bana sonsa Abana bana son fitinar dake tatare da shi, SHIN YAYA ZAN YI?*
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
3⃣2⃣
*ALHAMDULILAH YA ALLAH,*
Haikewa Aisha ta yi tana fadin" in ba jaraba ba irin na maza mai ya gani a jikin wannan? Idan farin ne gashi a gidansa, kyan na tara mai ya rude shi?
Ta juyo wajen su Samir ta kananage ta hana Samir fita ta hana Hafsat magana sai masifa take wai taya ma za.a baiwa wannan yar talakawa mai datin wannan dakin? Ita ta tabata ya fi nata dan haka ba zata yarda ba ita ce baba ita zata zaba kafin ya zuba wanda yake so
Kan samir a kasa yake yana sauraron yanda Sudais ke gudu da mota, a ransa kuwa yana fadin da ba.a san asalin balbale ba da ta ce daga turai ta fito
Bata ji karan shigowarsa ba tana ta masifa sai ganinshi ta yi
Dif ta yi da magangannun da take tana kalon sa sannan ta dan matsa da sauri kusan Hafsat
Kofar Rauda ya kala ya ga daga ciki tana gannin na waje domin yana iya canza abin ya dawo na waje ke gannin na ciki, dan haka ya sakarwa Humaira murmushi ya kali samir ya salame shi
Hannun Humaira ya rike tamkar suna maganar soyaya yana dan murmushi ya jata har zuwa dakinsa
Suna shiga ya tabatar ya rufe ya hankadata wanda ya saka ta yi tagatagal ta fadi kusa da bed, kansa ya dafe yana tir da irin halayan Humaira, sai ta saki baki ta ringa fadin magangannu mararsa tsari sai daga baya ta yi zuru zuru, tabas zai ringa biye mata har ya ga wacece ainahin wada ta haukata zuciyarsa haka kafin ya mugun daukan mataki a kanta
Taku ya yi zuwa da zauwa ya kai sau uku ya tsaya daidai inda take, murya a matukar kaisashe ya ce" ki iya takun ki Humaira, ki iya harshen ki, ki kiyaye ranar da idannuwana zasu rufe kan izgilancin ki, ki kiyaye shiga sabgar *SIRINA*
Yana gama fadar haka ya juya ya fada bayi
Shatata ta yi da baki ta bi bayansa da kallo, ya aka yi ya ji abubuwan da ta fada, me yake nufi da *SIRIN SA? WAYE SIRRIN SA?*
tunda ya shigo ta tsayar da kukanta ta zuba masa ido wanda ita kanta bata san ta yi ba, tana gannin tun budewarsa da shigowarsa , du irin tijarar da matarsa ke yi sai ta ga ya sakar mata murmushi ya ja hannunta ya yi daki da ita harma da alamar ko fada ya yiwa Samir?
Wani irin gum ta yi ta rasa tunanin mai zata yi, ita kanta ta san Sudais ba tsararta bane ya fi karfinta nesa ba kusa ba, sunanta da nasa basa kama da juna , matsalolin dake tsakanin tarayarsu ta girmameta, Aisha Aisha, Humaira
A hankali ta juya dan ta samu ta nutsu sai dai kara waro ido ta yi,
Wannan fa? Ko dai Samir bai gane inda aka ce ya kaita ba? Daki ne ciki daya, sai dai girmansa ya isa a yi ciki uku da shi, ba komai sai makeken bed da wani abu tamkar runfa a samansa, an yi masa shinfidar alfarma iri daya da jikin bangon dakin wato fari, labulaye ne a jikin runfar wa.inda take kyautata zaton Ana sakin su ne
Sai gefe daya wajen gabas da tapi na sallah da dan table na silba mai kyalkyalo samansa kur.ani me da litatafai
Kara kallon bed din take da dakin, mamaki take wannan tankamemen dakin na wane? Dakin kadai ya kai girman gidansu harda dakuna
Kanta ta kai gefen bed din daga sama sai ta ga wasu manyan buton da rubutu a jikinsu
A hankali ta matsa tana adu.a abinka da mai ilimi ta karanta,
Hannunta ta mika ta danna wanda ke nufin bayi, ai kuwa sai ga kofar bayin ta bude wanda hakan ya sa har ta tsorata, ta yi saurin rufe shi ta kuma danna na kusa da shi sai ga armoire ya bude, sutura dai mai sunnan sutura shake a ciki, kwalalo idannuwanta ta yi ta girgiza kanta kawai ta rufe ba tare da ta matsa ko kusan kayan ba,
Haka dai ta yi ta zuba kauyancinta tana kara bin dakin da kalo , ba wani katsamniya sai sanyin ni.ima dake tashi
A dan hanzarce ta kuka bude bayin ta shiga, nan ta ga idan da mutun dole sai shi zai bude ya fito aman wani ba zai dana ya kara bude masa ba
Rufewa ta yi tana bin bayin kansa da kallo, a fili ta furta" tamkar ba za.a mutu ba, tamkar wannan watarana ba zai dawo kasa ba, tamkar kasa ba zata linke shi ba
A hankali ta cire hijabinta, ta tube ta shiga kasan shower wanda kana shiga kasan sa zai bada ruwa kana fita ya tsaya, da ba dan ta ji yan ajin su da Aisha na fadar wasu abubuwan ba da ta kurma ihun tsoro
A hankali ta sabe jikinta da sabulun ruwa da sabon soso fari kar har gashin kanta,
Tana gamawa ta dauro alwallah ta yi tsaye wajen kayan da ta cire , dauka ta yi kawai ta mayar da abinta ta fito a hankali ta zauna kan darduma ta dauki alkur.ani mai girma ta shiga karantawa da kudirin yana zuwa zata roke shi da ya sawake mata, ta bashi hakurin abinda ta yi masa (uhum.....)
*Me ya gani a jikinta in ba jaraba ba irin ta maza !* maganar ta kuma dakar dodon kunnen Sudais wanda ya yi tsaye kasan shower tana ta zubun masa saman lalausan gashin kansa
Idannuwansa ya bude tarrr ya tsurawa waje daya ido,
A kasan zuciyarsa yayi murmushi, ya shiga bin miscle din jikinsa da kallo, dukan wata gaba ta jikinsa ruwa na sauka kanta yana binta da kallo, wani murmushin ya kuma saki a fili ya furta" she is yng
Sudais ba wani abokai ne da shi ba bale ya ji zantutukan yau da kulun na rayuwa,
A film kuwa du abinda zai kala ya dauke shi a matsayin karya domin yana kallon film din turai, wai zaka ga wani wajen sunna koda wannan harkar shi dai sai ya yi murmushi ya fice wajen, KHAIRATH marigayiya ta kasance mace mai jiki sosai, yar lukuta ce ta gaske wanda tana son kai shi wajen da ba.a dawowa ma aman sai abin ya yi mata wuya yannayin girman jikin
Ita kuwa hajia Humaira abubuwan sun taru sun yi mata yawa, shegen son jiki ita sai dai ta sankame masa, ga warin man bleating din nan wanda ta dorawa kanta!, ga dan uban ciko ita ce acuci na gidan nono ita ce na baya , gashin kanta a kulun cikin saka kari take, idan ta tube yanda ka san tabarwa bata da tsari ko wani abinda zai fizgeka gareta , SUDAIS ya kasance yana shan ruwa ne dan korar da ishirwa kar ta kar shi bai san banbance dadin ruwa ba bai iya banbance ruwan tafki na rijiya da na pampo ba shi dai kawai gugarsa yake sakawa ya ibi ruwa ya sha, abinda ya sani daya ne, karamar randa tai masa kadan,
Idannuwansa ya lumshe ya fita daga kasan pampon ya dauki fari kar din towel sabo fil ya nado iya kugunsa ya fito ya zauna gefen bed,
Shiru yayi ya hasko Rauda a idannuwansa, shi dai bai taba ganninta da garamar shiga ba, ainahi ma idan ba zumbuleliyar doguwar riga wace watan takan dan matse mata daidai mama watan kuwa yanda ka san buhu a jikinta sai zumbula zumbulan hijabai wanda ba zai iya tantance ya take ba domin iya tsintsiyar hannunta kawai ya iya gani a zamansu tun lokacin da ya fara ganninta har zuwa yau ba, ba zai iya sifanta ta ba,
Lumshe idannuwansa yayi, a fili ya furta" yarinya ce, abu na farko da zai hana na sota dan wani abin na jikinta kennan domin na fi karfin taraya da yarinya karama, ya kuma sakin murmushi a kasan ransa ya ayana ko harbawa ba zatai ba idan na taketa, wly ko motsi ba zatai ba zata je inda ba.a dawowa,
Wani murmushi ya kuma saki ya ce" baby , na baby girl, no Humaira ba dan jikinta na aureta ba ba dan kyau ko wani fari dake daukan hankalinki ba ni kaina na rasa takamaimai abinda ya sa nake kaunarta, just na wayi gari ne cikin bakon yannayi, na farka ne na tsinci kaina a halin soyayarta, abinda na yi ta kaucewa ko nace na yi ta tunanin ba zai faru da ni bane ya faru da ni, ina tsananin son *MATA*
Ko ya Raudat take? Mama ke zaune tana zancen zuci har ya fito fili
Aisha dake mike saman tabarmar leda tana dadana yar karamar wayarta ta tabe baki , ita fa mama ta fara isarta, shi kennan ita daga an zauna sai tunane tunane da tambayar infa Rauda take? To siyar da ita za.ai ne ko me? Ba aure akai mata ba? An hada ta sabuwar rayuwar talauci ba dole ta labe ba
Mama ta kai dubanta wajen Rauda, a ranta take aiyana" Allah sarki Rauda, da tana nan ba zata bari na shiga kicin ba, ba abinda take bari na yi, ta wuni tana aikace aikace hakan ma cikin rigingimun gidan nan, ya Allah ka sa ta samu farin ciki a gidan da aka kaita a matsayin gidan mijinta
A hankali ta kuma kallon Aisha, yau tunda ta farka ta karya ta mike kafa saman tabarmar nan ko tsinke bata dauke a gidan ba, aiki kamar ya kashe mama sai dauke nan ajiye can take , yanzu kwatakwata basa wani dasawa da Aisha, ko dama dan tana gannin Rauda ne take like mata ita kuwa tana ture Rauda? Ita kam takan rasa kan Aisha,
Bata gama tunaninta ba Sarah ta yi salama
Aisha ta mike da saurinta ta tarota tana murnar ganinta
Sarah ta yatsina fuska ba tare da ta gaishe da mama ba ta ce" ke yanzu baki ma shirya ba me kike ne haka?
Aisha tamkar zata shige jikinta take fadin" ai kayana kawai zan saka ki shigo na saka mu tafi
Sarah ta yatsina fuska ta ce" aa aa, na zauna a ina? Ke dai je sako kayan mu je
Tana gama fada ta jiya ba tare da ta gaishe da kanwar mahaifiyarta ba ta nufi motar mamanta da ta dauko
A gurguje Aisha ta fito ta ce" mun tafi sai mun dawo mom
Mama da baki wangale ta bita da kallo, a ranta take ayana ina kuma zata je? Me suke aikatawa ne yaran nan?
Rauda ta wuni karatun alkur.ani wanda tana gamawa ta bingire a nan baci yayi awon gaba da ita
Hafsat ce ta shigo dakin bayan ta jima a falo har magarib ta shigo bata ga fitowarta ba
Tausayinta ne ta ji ya kamata, gannin hijabin nan dai shine a jikinta, gaskiya ya dace ace ta canza domin kuwa da ganni ya jima a jikinta sannan Samir ya kawo mata akwatin tufafinta domin sudais ya bada umarnin a kawo mata ko dan ya kara gannin halayenta sai samir ya canza kano ta yi zahin ya zuba kayan a akwati
A hankali ta karaso kusa da ita ta duka ta shiga tashinta ta hanyar dan jan hijabinta tana fadin" aunty amarya aunty amarya
Firgigit Rauda ta farka a bacin da take mai dadi ta kali Hafsat, dan ja da baya ta yi tana kokarin tashi du a dan firgice take domin bata ji shigowarta ba ko dan bata samu isashen baci jiya ba sai ta yi shi tamkar ta mutu a yanzu har aka shigo bata ji ba
Hafsat ta dan dago hannunta ta ce" Aunty lafiya kuwa?
Rauda ta yi dan raurau da ido, ta sada kanta kasa tana kokarin saita bugun zuciyarta domin ta tsorata ainun ta yi tsoron ko matarsa ce? Ko shi din kansa aman da alama kanwar nan tasa tana da mutunci
Dan girgiza kanta ta yi alamar aa, ba komai
Hafsat ta sakar mata murmushi ta ce" ki tashi ki canza kayan nan Aunty sai ki fito ki ci abinci, baki ci na 12 ba har dare ya kawo
Rauda ta sauke ajiyar zuciya murya na rawa ta ce" kakayana ban dauko ba
Hafsat ta yi murmushi a kasan zuciyarta take ayana innocent
Kayan ta miko mata ta fice ta bata waje
Ba tare da ta sake wani wankan ba ta canza kayan jikinta ta saka daya cikin atampopin da Abanta ya dinka mata,
Wa.inda ta cire ta koma bayi ta wanke ta sarkafe jikin karfen da ake shanya towel
Fitowa ta yi daga bayin tana fan tsane hannunta tana gyara daurin zanin dake jikinta bata lura da mutun ba sai da ta dago da kanta ta ganshi tsaye ba fuskarnan tamkar zaki ya hadeta ba alamun wasa a tatare da shi
Gabanta ne ta ji ya mugun buga mata wanda har ta saki.....m
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
3⃣3⃣
Kabewa a dafata ta dafe a murjeta sosai ta yi kitib a hadata da madara peak da karankafi a saka a firij ya yi sanyi a sha da safe kafin lokacin zuwa turaka , kana iya sha ko ba sanyi zabinka ne🚪🚪🚪🚪🚪🥰🥰🥰🥰
Gabanta ne ta ji ya mugun faduwa, wanda har ta saki dayan hannun zanin da sauri ta raruma ta daura haka kuma jikinta ya dauki rawa domin ba hijab a jikinta danma Allah ya taimaketa dinkin Aba da ya kai gaba daya manyan dinkuna ne akai mata du idan ta saka zubul take yawo a ciki aman wuyanta da yake a bude sai tana jin tamkar ana gannin sauran sashin jikinta
Kalo irin na kurulah ne ya kafeta da shi wanda shi kansa bai san ya shagalta da kalonta haka ba, so yake sai ya karanto abinda ke saka shi afkawa a soyayarta har haka , yanzu ma wannan kayan na jikinta tamkar ta aro sun mugun yi mata yawa baka iya tantance ainahin tsarin jikinta
Ya kai sau uku tana dan dago idannuwanta tana satar kallon sa sai ta ga ya tsura mata ido tamkar yana hararanta
Kanta ta sada a karo na ba hudu tana dan murza yatsunta
Ajiyar zuciya ya sauke, a kasan zuciyarsa yake ayana" inama wannan sabanin bai shiga tsakanin mu ba, inama kin fahimci irin macewar da na yi a kanki kin fito kin furtan kalmar so kin amshi tarairayana, Rauda sonki kawai nake
Takawa yayi har zuwa daidai inda take ya ja ya tsaya, ya hade girrar sama da ta kasa ya ce" fatan kin shigo gidan aure dan bautar aurenki ba dan hutu ba
Bata iya cewa komai ba sai zuciyarta dake ingizata kan ta nemi sakinta tun kafin tafiya ta yi tafiya,
Sudais ya ci gaba" ina so idan ina magana a ringa bani amsa
Kanta ta dan dago sai ta ga kusancin nasu yayi yawa dan haka ta dan ja da baya sannan bata bashi amsar da yake jira ba
Kankance idannuwansa ya yi ya ce" ko baki ji abinda na fada ba?
Kanta ta daga irin ta amsa shi, itafa a kasan zuciyarta bata ma yarda cewar shi din ne mijinta ba, me hakan ke nufi? Abanna ko bai san wanda ya aura min ba
Hum ya ce , ya taka ya karasa wajen armoire
Bouton ya mika hanu ya dana gaba daya suka bude, tsai ya yi yana bi da kallo kamar